← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 160

Sashe 150

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh hakane!, Amma Ina so kiyi amfani da maganganun Fatima, koma meye ki da kacesa har zuwa lokacin da zakiji ta bakinsa, hakan ne kawai zaisa iya yanke masa hukunci daidai da tunaninki, maganar mata da d'iya da kikayi kuma wannan ra'ayine, sai mutum nada cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali zai buqacesu musamman a inda ba lalle bane yuyuwar samunsu agareka, nidai Ina shawartarki da kinatsu ki kwantar da hankalinki kiyi addu'ar ALLAH yasa wannan dawowar tasa tazamo alkhairi duka agaremu kuma kasa qarshen duk wani sarqaqaqqen al amarine d'aya faru wanda bamuda masaniya akansa."

Ita dai banda kukanta babu abunda takeyi wanda daga qarshe dai cikin zolaya tace da ita gwaggon yara nadai gano wannan kukan naki na dad'ine gaskiya, idan kuwa ba haka ba to kina practicing d'in irin kukan amaren da zakiyine ranar da zamu maisheki d'akinki tun yanzu."

Bushewa da dariya Dr yayi had'e da miqewa yabar falon yana fad'in.

"To mudai koma meye ayiwa takwarana haquri har zuwa lokacin da zaizo ya wanke kansa, ni nama tafi inyowa su dady da umma albishir ALLAH maji roqon bayinsa ya dawo masu da surikinsu lafiya."

"Ah to mudai wlh munyi farinciki sosai, fatanmu d'aya ALLAH yasa hakan ya zamo alkhairi, barima na d'auko wayata nafara riganka wannan albishir d'in."

Ganin suna nema su juyar da tunaninta izuwa nasu yasa tamiqe tana kumbura fuska tabar wajen Fatima nata yimata dariya.

Bayan wucewar tane Fatima tayi wata irin ajiyar zuciya had'e da cewa,

"Tabbas duk abunda yayi farko zaiyi qarshe kuma duk nisan abu SANNU SANNU bazata hana akai garesa ba, yau gashi abunda basu tab'a kawowa zaizo kusaba da SANNU SANNU yazo garesu batare da zato ba balle tsammani.

••• ••• •••
Kimanin awanni hud'u su little suka kwashe akan hanya basu iso kano ba saboda yanayin yanda little ke tuqin, tafiya yakeyi ahankali wanda gudun bai gaza a 40 ba, tun 'yan biyu na qiriniyarsu har suka gaji suka natsu waje d'aya, batool kuwa tayi bacci yafi aqirga saboda wahalar zaman motar da takeji wanda yanzu hakama yad'an ja kujerar da take zaune ta d'anyi baya yanda zata iya kwantawa saboda yanayin tsufan cikin nata dole duk d'okinta zataji gajiyar da zata sakata bacci.

A b'angaren su Abba kuwa su duka sun kasa zaune sun kasa tsaya, bini bini Abba dake faman safa da marwa ya d'aga kai ya kalli qatoton agogon dake maqale ajikin bangon makeken falon da kamar ya zamo matattarar dukkanin ahalin gidan.

Ganin an kwashe awanni hud'u babu labarin isowarsu yasa yasa Abba zuwa ya bud'e wani safe d'insa inda yake ajiyar kud'i ya d'ebo adadin da shi kansa baisan ko nawa bane yafita dasu, Saida yabar anguwar gaba d'aya sannan ya dinga raba kud'in ga duk wanda ya had'u dashi dake da buqata da niyar sadaka, saida kud'in suka qare kaf sannan ya koma gida lokacin ya taraddasu uncle h sun tara samari da 'yan matan gidan manya da yara an rarraba masu irin al-qur'anin nan Mai hizib biyu biyu kowa ya d'auki inda ya iya haddasu ana karantawa, wani irin sanyi yaji aransa tare da tabbatar da cewa komai zai faru ga 'yarsa yanzu yanada yaqinin shine yafi zama alkhairi kuma zai amshesa hannu biyu biyu.

Sauran mata uwayen gidan kuwa kowace na kitchen tana ayukkanta ciki d'ure da ruwa, so sukeyi sukirata suji idan sun iso, musamman hajia mama Amma Abba yasa warning akan kada asake akirasu domin hakan na iya d'auke masu hankali, murmushi kawai hajia mama tayi aranta tace, _(ALLAH sarki! alhaji kenan! Wai shi atunaninsa hakan da yayi dubarace da zata iya hana afkuwar abun da ALLAH ya riga ya tsaro?, Baisan ita qaddara kota qaqa bane baza'a iya guje mata ba, ALLAH dai yasa mudace.)_

A b'angaren Dr Nuraddeen kuwa tuni jirginsu ya iso kano wanda tun daga lokacin da suka taso har isowarsu babu abunda yakeye sai kuka, babu abunda yake tunawa irin tambayar da akayi masa cewa _acan baya yace bayada masaniya akan zancen iyayensa, ahalinsa da kuma iyalinsa, mezai iya cewa akan haka adaidai wannan lokacin?_ duk yatuna wannan furucin sai yaji wani zafi da quna acikin ransa, yanzu da wace irin fuska zai kalli iyayensa idan har ya taraddasu?, me zai cewa masoyiyarsa data adalilinsa tashiga halin da har yau baisan a Ina take ba?, Wud'anne kalamai zai yiwa ahalinsa a matsayin ban haquri bisa wud'annna munanan lafuzza dayayi?, Yana cikin wannan tunanin ne jirginsu ya sauka a filin jirgin sama na aminu kano, nan ma dai kamar yanda ya barone acan jahar, 'yan jarida ne birjik da 'yan gidan redio da talevision suna jiran isowarsa, a wani b'angaren kuma mataimakin gomnan jahar da kansane shida muqarrabansa da manya manyan shuwagabannin aiki a fannin lafiya da sukazo tarbarsa wanda gwamnan jahar ne da kansa yabada wannan umurnin don karramawa garesa daga gwamnatinsa da Kuma nuna jin dad'insa bisa nasarar dawowar shahararren likitan aqasarsa lokacin mulkinsa.

Yana fara tattakowa daga matattakalar jirgin manema labaran sukayo ruuuu suna sakar masa hotuna har ya qaraso, nan take jami'an tsaro suka shiga bud'a mutane ana tutturesu gefe saboda mataimakin gwamna dake qoqarin isowa wajensa,

Yanda Dr Nuraddeen yaga ana girmama mutumen yasa ya tabbatar da babban mutumne don haka yad'an saki fuskarsa daga yanayin da take yana isowa kusan atare suka miqawa juna hannu suka gaisa sannan mataimakin gomnan ya gabatar da kansa agaresa, duk qoqarin 'yan jarida nason ganin sun zanta da Dr hakan ya cutara saboda manya manyan mutanen da kai tsaye suka shiga gaisawa dashi suna gabatar da kansu agaresa tare da welcoming d'insa,

Wata zuqeqiyar mota maikyau mataimakin gomnan yayi masa izinin su shiga domin a kaishi masaukin da gwamnati ta tanadar masa wata 'yar qwarya qwaryar walima data shirya masa ta gaggawa don murnar dawowarsa Amma kai tsaye yace da mataimakin gomnan kai tsaye yafi buqatar wucewarsa gida, bayan ya huta zai isa wurin da ake buqatar zuwansa.

Ba musu mataimakin gwamnan ya had'asa da jami'an tsaro mota d'aya bayan yakira gomnan ya sanar dashi yanda Dr N.I d'in yace yana buqata yaci ayi masa hakan.

Saida suka sakeyin musabaha Dr yayi masa godiya cikin girmamawa sannan aka kawo wata motar ya shiga daga shi sai drivern daya jasa zuwa qauyen nasu na bebeji motar jami'ai d'aya na biye dasu abaya.

Dama tuni wasu 'yan jaridar kai tsaye sun nufi qauyen tun d'azu yayin da sauran yana wucewa suma sukabi bayansa.

Su baffa Usman da baffa Ali da kuma baffa na zaune qofar gida suna hira kwatsam sai sukaga motocin 'yan gidan redio da talevision na shigowa cikin qauyen wanda abun ya matuqar d'aure masu kai, tun daga kusan farkon gari suka daza motocinsu har zuwa gaba da qofar gidansu baffa, saidai sun kaga ma'aikatan na tada qarafunan setily da faya fayin motocinsu suna harhad'awa batare da suncewa kowa uffan ba don dama tun a farkon shigowarsu suka tsaya sukayi tambaya aka fad'a masu gidan, su kuwa mutanen qauyen haka suka firfito sukayi cirko cirko suna zullumin wane irin abune yasamu qauyen nasu da motoci suka cikasu haka ana faman tashe tashen abubuwan mota da sauransu, yayinda wasu kuma suka dingi tattaro 'ya'yansu suna turawa cikin gida musamman matansu da basuda yadda akan duk abunda ya shafi mutanen birni.

••• ••• •••
Sai gab dasu little su shiga kano batool ta farka daga baccin da takeyi lokacin su hassana da hussaina sun gaji da qiriniyarsu suma sunyi bacci, bakinta d'auke da salati ta tashi zaune tana buga wata irin uwar hamma had'e da cewa.

"Wayyo Abu sumayya har yanzu bamu isa ba, ni sai nake ganin kamar yau ana jawa garin nisa, don ALLAH kad'an qara taka wuta, namatsu inga Abbana."

Murmushi yayi had'e da d'an juyowa ya kalleta sannan yace.

"Wai! Agaidasu gimbiya, wato kema da kika sharqi baccinki kece kika gaji bani ba ko?, Bawani kin matsu kiga abbanki, kedai kice kin matsu kici abinci wannan uwar hamma da kika buga ai tsaf kan akuya zai shiga ta bakinki."

Hannuwa tasa tad'an duddukesa ga kafad'a yana dariya yace.

"Kai ko, wane kan akuya zai shiga awannan d'an mitsitsin bakin nawa?, ALLAH bana son sheri."

"Bakiga yanda kika bud'esa bane shiyasa, tsaf kan tinkiya ma zai shiga aciki."

Gano salon zolayar tasane ta motsa yasa tayi murmushi had'e da langab'ar da kanta gefe tana cewa.

"Naji d'in, ba dole ba ambar mutum da yunwa fiye da awa hud'u kuma duk ansan dole ajiyarsa zata dami mutum tace itama yunwa, to meye ma idan kan tinkiyar ya shige abakina tunda yunwa nakeji sai nakama abuna na kamtse na cinye."

"Aw abun sharri ne?"

"Eh man, ba yanzu kagama yimun ba nima, kaga narama mun zama 1-1"

"Ai shikenan! Kiyi haquri mun kusa isa saura kilometers biyar in Sha ALLAH"

"To kad'an qara gudu mana sai muyi saurin isa tunda mun kusa kace."

"Ehm.ehm..rufamun asiri, inyi maki ta bakin gwaggo tace uncle, to uncle yace kada muyi gudu, kiyi haquri muqarasa lafiya tunda munkusa isa, SANNU SANNU ai Bata hana zuwa saidai a dad'e ba'a kai ba ko kuwa?"

"Hakane in Sha ALLAH.."

Tana rufe baki sai ga wata babbar mota da alama burkinta ya katse ta nufosu aguje, da sauri little ya koma ta d'ayan hannun ALLAH yasa babu wata mota agabansu tafe ya sauka gefen titi yayi parking gabansa na fad'uwa, yafi mintuna uku aciki yana kallon yanda waccan motar ta fad'i tana qoqarin gangarawa cikin daji ta madubi kafin can ya kashe motar yafito ya nufi wajen yana kallon ikon ALLAH, nan fa sauran motocin dake tahowa wasu suma suka tsaitsaya ana jiran aga yanda sarautar ALLAH zatayi da motar, sai da babbar motar ta dad'e tana juyawa sannan aka samu ta tsaya mutane sukayi ruuu wajen ko za'a iya ceto rayukan wasu, sai gashi koda akaje mutum biyu ne kad'ai a motar daga driver sai na gefensa kuma duka ALLAH yayi masu rasuwa, Saida aka gamo jajantawa sann little yadawo ya shiga motar jikinsa asanyaye yana fad'in.

"Ubangiji ALLAH ya jiqansu da rahama."

Batool da suma kad'aice batayi ba tsabar yanda ta tsorata ta samu daqyar ta amsa masa da Amin, had'e da cewa.

"Duk sun mutu ko?"

"Eh, dayake mutum biyune kad'ai acikin motar sun d'auko kaya da alama legas zasuje."
Chapter 150 · 0% Book details