← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 160

Sashe 147

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tabbas shine ne yadawo Yaya, nuran mune bako shakkah." baffa Usman yafad'a yana hawaye, baffa Ali kuwa cikin d'ingishin katakon da yake takawa dashi yanufi wajen Dr Nuraddeen dake nufowa wajensu idanuwansa na tsiyayar da hawaye saboda yanda idanuwansa sukayi masa tozali da iyayensa awani yanayin da ba hakan yaso ba, yanda 'yan jaridun suka yimasa qawanya suna faman d'aukar hotonsa had'e da jefo masa tambayoyi kala kala suna Kara masa makirfon d'insu don neman amsa yasa ya shiga sa hannuwa yana tutturesu gefe don ya qarasa izuwa ga iyayensa dake tun karowa, tsabar saurin da baffa Ali keyi ya isa garesa yasa katakon da yake takawa dashi ya dinga gocewa daga hannunsa yana qoqarin fad'uwa, ganin hakan yasa Dr Nuraddeen d'aga qafa ya qarasa garesa da sauri ya riqesa yana binsa da kallo, zamewa qasan qafafuwansa yayi had'e da rirriqesu sosai yana kukan takaici da nadamar abunda ya aikata, cak Nuraddeen ya tsaya yana kuku cike da tausayin meya sami qaramin baffansa haka har ya rasa qafarsa, cak baffansa ya tsaya lokacin da sukazo dab dashi wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da rufe idanuwansa hawaye suka shiga zarya akan fuskarsa ya durqushe wajen had'e dayin sujada saboda tsananin farinciki, kuka baffa keyi sosai acikin sujadar yana kirari ga ubangijinsa had'e da washi da yabo daya dawo masa da d'ansa kuma gudan jininsa agaresa a lokacin da baiyi zato ba balle tsammani, yajima a hakan kafin baffa Usman da tsantsar farincikin dake kwance a fuskarsa ya kasa b'oyuwa yasa hannu ya d'ago sa, tsananin kukan da yayi yaqara karya zuciyar Dr Nuraddeen hannayensa na rawa yasa duka biyun ya riqo fuskar baffansa da gaba d'aya ya kasa magana sai binsa kawai yakeyi da kallo yana zubar da hawayen da tun d'azu suka kasa tsayawa,

"Baf..ba.baffaa.." Dr Nuraddeen ya fad'a tare da jawosa ajikinsa, riqesa sosai baffa yayi tamkar wanda za'a kwacewa cikin muryar da tamkar yana rad'a yace.

"Nurah..!" Cikin wani irin sauti dake nuna tambayarsa ce yakeyi wai shi d'in da gaske.

Jinjina kai kad'ai Dr Nuraddeen ya shigayi wasu hawayen na zubowa a fuskarsa wasu bayan wasu tare da sake rungume baffa sosai ajikinsa, tun yana kukan marar sauti har yafara wanda kowa ke iyajin sautinsa da qarfi yana fad'in

"Ka yafemun baffa.."

Ciro sa baffa yayi a jikinsa Nuraddeen yayi saurin riqo hannayensa ya shiga marin fuskarsa dasu yana fad'in.

"Ka hukuntani baffa, ka mareni sosai mana, ka dake da qarfi yanda zanji zafi kafin ubangijina ya hukuntani da kansa!, Kaico na kaicon rayuwata, mezan cewa ubangijina bisa butulci da wofantar da iyayena da nayi aduniya?, Ka hukuntani baffa na cancani hakan ko zaka rage rad'ad'in da kakeji azuciyarka, kayimun duk abunda zaisa kaji sanyi aranka baffa ko ubangijina zai yafemun zunubin haqqoqanku dana tauye dake kaina."

Kuka yakeyi yana marin kansa sosai da hannayen baffa har saida yagaji don kansa ya durqushe agabansa, gaba d'aya baisan ta Ina zai fara roqon mahaifin nasa wannan mummunan laifi mafi girma da yayi masa ba aduniya, duk 'yan jaridun da motananen gari dake wajen suma sai hawaye sukeyi yayin da wasu suka dakata da d'auke d'auken hotunan suna kallonsu wasu kuma mutanen garin da suka san da zancen sai qus qus akeyi ana fad'in, ai shine d'ansa daya tati qasar turai yayi zaunensa, shine ai, shine yadawo...haka dai sukayi suruttansu, ji yayi baffa ya d'ora hannayensa akan fuskarsa yana goge masa hawaye had'e da cewa.

"Taya zan iya hukuntaka nura bayan bakada laifin komai?, Taya zuciyata zatayi zafi da quna saboda kai bayan kai aka zalunta?, Kadena kuka baffanka baya fushi dakai balle kaico tazamo cikin tsarin rayuwarka, kai amintaccen d'ane awajena, nasan kowaye d'ana bazaka tab'a wofantar dani ba koda akan juji nake kwana kuwa, nasan ko wace irin tsadaddiyar kyautace kai da ubangijina yayi mani bazan tab'a bari zuciyata taci gaba da zargin kaba bayan gaskiya ta bayyana agareni, ina kukane awannan lokacin kawai saboda farincikina daya dawo Mani bayan wasu tsawon shekaru da shed'anin mutum dana aljanin suka tasirantu acikin rayuwarsa da son zuciyar wud'anda ke tunanin anzaluncesu har suka rabani dashi na tsawon wannan lokacin, na sani kaifin hankalinka da qarfin tunaninka bazasu bari ka iya mantawa damu ba don haka bazan yaudari kaina ba ta hanyar d'ora maka laifin da bai zamo naka ba kuma bazai tab'a zamawa naka ba,"

Cikin kuka Dr Nuraddeen dake kallonsa da sauraran kalaman da gaba d'aya sukasa yaqarajin haushin kansa na nisanta da mahaifinsa na tsawon wannan lokaci batare daya san dalilinsa nayin hakan ba.

"Karka fad'i hakan baffa, ni mai laifine agareka, taya d'an dake da mahaifi kamar ka dake da zuciyar zinare ace ya rabu dashi cikin matsananciyar rayuwa da kuma damuwa na tsawon lokaci kuma har ace baiyi laifi ba?, ace kaico bazata biyo baya arayuwarsa ba, ya ALLAH! Wace irin gagarumar hasarace na tabkawa rayuwata?, Wace cutarwace nayiwa kaina da zata had'ani da shiga ukuna nahar abada?"

Had'a hannayensa yayi waje d'aya cikin wani irin kuka dake qiqqire lumfashinsa yanaci gaba da cewa.

"Natuba baffana kayi haquri ka yafeni, bansa taya hakan tafaru ba!, bansan ko meye ya shiga kaina ba na aikata hakan!, bansan abunda ke faruwa da rayuwata ba, Na gujeka alokacin da kake tsananin buqatata, na butulcewa qasata, na zalinci kaina baffa meye makomata?"

Saida baffa ya share hawayen fuskarsa da goge qasan hancinsa sannan yace.

"Bakada makomar data wuce kyakkyawa aduniya nura, kuma baza kasan dalilin dayasa kayi hakan ba domin bakada niyar aikata hakan aranka, bazaka san meyasa hakan yafaru dakai ba domin ALLAH ya lullub'e mana sanin abunda ke gaibi, kayi imani da cewa wannan qaddarar kace da bazamu iya hana tafaru akanka ba, ka yarda ALLAH shiya tsaro maka hakan kuma karoqesa akan hakan yazamo yafiya da kankarar zunuban da kayi masa, ni nayarda da tsarin qaddara mai kyau da marar kyau akaina da kuma dukkanin zuri'a ta, fatana kawai ALLAH yasa daraja da d'aukaka ta biyo bayan amincin da mukayi ga qaddarar daya tsaro mana. Ka kwantar da hankalinka araina banida wani qaiqayi ko damuwa akanka"

"Amma baffa..."

Zaiqara wata maganar baffa Usman yayi saurin rufe masa baki tare da d'agosa daga durqushen da yake agabansu yana fad'in.

"Ya Isa haka mana nura, kasan ko waye mahaifinka don haka kayarda dashi akan abunda ya fad'a kaji ko?."

"Kuyi haquri baffa Usman wlh bada son raina na ba hakan ta kasance.."

"Nima nasani nura, ubangiji ALLAH ya tsare gaba kuma yaqara kareku aduk inda kuke, mukam Alhamdulillah mungode ALLAH tunda ya dawo mana dakai lafiya babu sauran wani Abu tsakaninmu dakai sai ALLAH yayi albarka." Juyowa Dr Nuraddeen yayi yana kallon baffa dake murmushi hawaye kuma na kwance a fuskarsa lokaci d'aya ya jinjina masa kai alamar gaskiyane abunda baffa Usman ya fad'a.

Baffa Ali kuwa da tuni kunya da nadamar abunda yayi tasa yaji Bari shi da kansa ya tona asirin kansa duniya tasan ko meye silar rashin dawowar little qasarsa masu zaginsa da zarginsa sudena, don inba hakan ba yasan 'yan uwansa bazasu tab'a bayyana masa ko meye gaskiya abunda yafaru akan saba, don haka kai tsaye yanufi wajen 'yan jaridar yace suzo zai basu labari akan abunda yafaru da Dr Nuraddeen har yakasa dawowa qasarsa, su baffa nacan na koke kokensu saidai suka hangosa 'yan jarida sunsa shi agaba yafara basu labarin komai..

_"sunana Aliyu Aliyu amma amfi sanina da baffa Ali kamar yanda ake kirana, ni qanene ga mahaifin Dr Nuraddeen, nakasance mutum mai son kansa Wanda hakan yasa nayi sha'awar aurawa shi Dr 'yatah batare da nayi la'akari da yanada wacce yake so ba ko baya da ita wanda sanadiyar hakan yasa da bai aureta ba muka azawa yarinyar daya aura tsana....." Haka yayita basu labarin komai tun daga farko har zuwa qarshen sakamakon da suka samu daga wajen ALLAH dashi har matarsa, ya qara da cewa.

"Masu zargin sonkai da abun duniya yasa Dr Nuraddeen ya guji qasarsa yaqi dawowa to ku dena ba haka bane, sahrrin shaid'an yasa batare da nayi la akari da cewa shid'in d'and'an d'an uwana bane muka aikata masa abunda yasa ba qasarsa ba hatta iyayensa da ahalinsa saida ya manta, nayi kuka sosai da nadamar hakan lokacin da shiriya tazo mani bayan ubangiji yayi masa sakayya shida mahaifinsa tun duniya akaina, wannan kuwa shine sakayyar da ALLAH keyi ga bayinsa da aka zalunta koma fiye da hakan."

Ya qare maganar had'e da nad'e qafar wandonsa da aka guntulu gundululun wajen yafito, sannan ya bud'e wasu sassansa qurajen da ke jiki suka bayyana dama tuni na fuskarsa sun bayyana.

Ana hakanne su baffa suka ahamo da abunda yakeyi da sauri Dr Nuraddeen da kusan yaji duk wasu abubun yazo ya jayesa yana qare masa kallo tun daga saman fuskarsa dake cike da quraje har zuwa qafarsa da aka yanke ya rungumesa yana fad'in.

"Meyasa baffa Ali?, Me yasa zakazo ka tonawa kanka asiri bayan ALLAH yarufa maka, idanma laifine aini yakamata na sani ba duniya ba, don me zaka zab'i tozarta kanka hakan?"

"Kayi haquri nura, son zuciya ne, gashi yanzu ta kaini ga nadama kala kala, don ALLAH ka yafemun kuma kayafewa ruqayya."

Yafad'a cikin kuka had'e da qoqarin zamewa yaduqa agabansa yayi saurin d'agosa.

"Baffa na yafe maka duniya da lahira, Kai mahaifina ne da har yanzu nake alfahari da shi, kuma zanci gaba da alfahari dakai har iya qarshen rayuwata, kowa na kuskure kuma mafi girman mutum acikin mutane shine wanda zaiyi laifi kuma ya gano cewa yayi laifi ya tuba har yayi qoqarin guarawa, haqiqa kai d'in babban mutumne mai girma baffanmu,"

A yanayin yanda Nuraddeen ya karb'i zancen har yayi saurin yafewa qanen mahaifinsa shine babban abunda yafi burge wasu daga cikin 'yan jaridar har yasa suka dingi tafawa Dr Nuraddeen.

Sosai Dr Nuraddeen yake jin rad'ad'in abun aransa amma ganin irin yanda rayuwar baffa Ali takoma yasa Dole ya haqura da duk abunda yakeji ya yafe masa kamar yanda yake fatar shima ubangiji da sauran al'ummar da take tare dasu suyafe masa laifin da yayi masu tunda mai faruwa tariga da tafaru.
Chapter 147 · 0% Book details