← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 160

Sashe 154

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar dai jiya haka yauma gidan aka wuni mutane na shigowa ciki kuwa harda Abba dasu uncle h, inda little ya gabatar dasu ga mahaifinsa amatsayin iyayen matarsa kuma ya gabatar dashi a matsayin mahaifinsa, Abba kam yaji matuqar nauyi akansa sosai bisa abubuwan da suka faru amma haka ya daure ya bayyanawa Dr Nuraddeen komai abunda yafaru wanda daga baya yayi nadamar hakan batare da sanin cewa ashe yana gab da dawowa ba, Dr yaji Babu dad'i Kuma abun ya Sosa ransa yanda akankusa hanawa d'ansa aure saboda ana zargin cewa shi shegene bayada uba, Amma komai yariga daya wuce tunda gashi ya dawo antabbatar da cewa d'ansa d'an halak ne don haka bazai iya maido da hannun agogo baya ba, cikin mutuntawa yayi masu godiya tare da fatan alkhairi akan d'orewar zumuncinsu sannan suka tafi, ganin rana na somayi Dr Nuraddeen yaba little kudd'i yaje yayi masu bkin d'in jirgi don lallae lallae yau bazai sake kwana garin ba har sai yaje wajen habibty d'insa kamar yanda mahaifiyarsa ta umurcesa, yanzu kam gaba d'aya baya fahimtar komai kuma baya gane komai inba ganinsa yayi wajen habibty d'insa ba gashi tunda little yafita bai dawo ya barshi sai faman duba agogon hannunsa yakeyi, ashe shi saida yabiya wajen batool yaga tashinta da yaransa sannan yatafi wajen booking d'in ticket d'in jirgin, cikin sa'a ya samu akwai har sauran ticket uku na jirgin da zai tashi misalin qarfe biyu narana, nan take yayi duk abunda ya kamata sannan ya kama hanyarsa ta komawa bayan ya tsaya ya saiwa mahaifin nasa waya da layoya har guda biyu mabanbanta network.

Yana isa ya isko dandazon mutanen da suka kawowa mahaifin nasa ziyara ta b'angaren ma'aikatar lafiya, yana ganinsa ya taso batare daya damu da mutanen daya bari wajen ba. nan yayi masa bayanin jirgin da suka samu wanda zai tashi qarfe biyune na rana, cikin jin dad'i ya d'an bubbugi kafad'ar little yace ya maza yaje ya shirya yana zuwa shima da zaran ya sallami mutanen,

Bayan yayi sallama dasu yaje ya sanarwa da Yaya hawwa zai tafi tayita sanya masa albarka da addu'ar ALLAH yakaisa lafiya yasa ya dace su dawo tare da matarsa cikin qoshin lafiya, anan bayen dake shiyar Yaya hawwa yashiga ya watso ruwa agurguje ya shirya, dama ya sanar da su baffa don haka suka d'auki hanyar zuwa airport d'in auna masu yimasu addu'ar zuwa lafiya sudawo lafiya.

Kasancewar koda suka isa airport d'in akwai sauran lokaci yasa little ya zauna yakira battool ya sanar da ita don mantawa yayi da yaje d'azu bai fad'a mata ba, addu'a tayi masa tare da fad'a masa Abba yasa an d'auko motarsu da sukayi accident jiya har an gyara, Saida yace tayiwa Abba godiya kafin yakirasa sannan ya kashe wayar yakira dady da Dr nura ya sanar masu suna tafe shida mahaifinsa kuma jirgi zasu biyo.

Wayar mahaifiyarsa ya gwada kira bai samu ba don tun safe ya kirata lambar akashe, murmushi yayi tare da kad'a wayar a aljihu sannan yaciro ta abban nasa ya dinga saka masa lambobin da yasan zai iya buqatarsu ciki kuwa harda ta mahaifiyarsa da yayi saving da my wife.

Sannan ya miqa masa yana fad'in.

"Baba ga wayarka, nasaka maka lambobin da zaka iya buqata."

Karb'a yayi had'e dayin murmushi yace "agaisheka ALLAH yayi maka albarka."

Sannan yafara dudduba lambobin har yakai gata Rashida da yayi masa saving da my wife, editing ya shiga ya mayar habibty sannan ya jefa wayar a aljihu little na kallonsa ta gefen ido yayi murmushin shima, aransa yace.

"ALLAH dai yasa Kar habibty d'innan ta kwabsawa babansa don yalura ba kad'an yake jinta ba."

Yana wannan tunaninne yaji anfara kiraye kirayen sunaye har aka kai ga sunansu suka tashi suka shiga, bayan sun zauna cikin jirgin da yake waje d'aya suke kafin jirgin ya tashi Dr Nuraddeen ya ciro wayarsa had'e da kaikaita idanuwan little yashiga akwatin tura saqo yafara rubuta saqo kamar haka.
_I am sorry for all the pain, I am sorry for the tears I am sorry for the anguish, But please fulfill my only wish, Please forgive me this time, And I won't do this again, Nothing to pretend, Just forgive me! I am sorry!_

Ya karanta yafi aqirga kafin ya lalubo lambar habibty d'insa ya tura mata, Rashida da bata dad'e da kunna wayar ba tana zaune taji qarar shigowar message ta d'auko wayar ta karanta, ganin lambace yasa batare data damu da tabada amsa ba ta ajiye wayar, can bayan wasu mintuna tasake jin qarar shigowar wani message d'in ta d'auko wayar ta sake dubawa tana karantawa kamar hakan.
_Iknow it's very pain and It's hard to make you understand, But, believe me I don't pretend, Mistake has happened and I won't deny, Blame on the situation to defy, I just want that you forgive me through, So that I don't feel blue, Please forgive me now habibty!, b'coz it's all part of our destiny and I don't have any words or how! Forgive me! Habibtyyy_

Awannan karon wasu zafafan hawaye suka zubo mata domin tafahimci daga Ina saqon ke zuwa, juya wayar ta shigayi tare da rashin sanin mema zata cemasa kawai ta cillata saman gadon takife tana kukan da da'ace hawaye na qarewa to da tsakanin jiya da yau nata sun qare kaf.

Tun daga umma dasu Dr Babu wanda ya sanar da Rashida zancen zuwan Dr Nuraddeen saboda yanayin da suka ganeta aciki, gashi dama tun safe bata fito d'aki ba har zuwa wannan lokacin, abun karinta dana Rana duka saidai mai aiki takai mata a d'aki hakan yabasu Fatima damar yin shire shiren tarbarsu Dr yanda ya kamata kafin su iso,

Kasancewar akwai banbanci tsakanin tafiyar jirgi data mota yasa cikin mintunan da basu wuce arba'in zuwa arba'in da biyarba su little suka iso,

Gaban Dr Nuraddeen ne ya shiga fad'uwa saboda rashin ganin amsar saqonsa ko d'aya daga Rashida Wanda ya tabbatar tagani kuma tasan shine, hakan yasashi fargabar kada taqi amincewa ta amshesa bayan yayi nadamar abunda ya aikata kuma bayin kansa bane.

Little bai tsaya jiran azo d'aukarsuba ya tari taxi, saida suka shiga yakira dady ya sanar dashi sun iso gashi har suna cikin taxi ina zasu sauka yace su sauka gidan Dr suma gasunan kan hanya in Sha ALLAH.

Motarsu little Bata dad'e da ajesu ba tasu dady ta tsaya inda a babban falo Dr yayi masu masauki bayan yayi ma Dr Nuraddeen wato takwaransa babbar tarba.

Rashida kuwa har lokacin tana can a d'aki duk da kuwa qarar tsayawar motar da taji har sau biyu, tsananin bugawar da taji zuciyarta nayi yasata fitowa da sauri tana share qwallar idanuwanta taci Karo dasu umma, ummie, dady da hajiya nafeesa da suka shigo yanzu, da sauri ta qarasa jikin umma tare da fashewa da wani irin kuka dake tsima zuciyar duk wani mai sauraro.....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___105💎

"A'a, a'a! Rashida meyene haka kikeyi sai kace wata qaramar yarinya?, Don ALLAH ni d'agani kada ki karyani, daga shigowa kongaisuwa babu sai kifad'omun ajiki kina kuka, fisabillahi ko gajiya bakyayi abu tun jiya!" Umma ta fad'a tare da cireta daga jikinta,

Riqo hannunta dady yayi suka nufi falo suka zauna itama ya zaunar da ita qasan qafafuwansa had'e da dafa kanta yace.

"Yi haquri Rashida, ita rayuwar mumini haka take, matuqar kayi Imani to dole sai anjarabceka, to Alhamdulillah yau Ina cike da alfaharin cewa 'yata tayi Imani kuma anjarabceta ta canye jarabawar da akayi mata, Abu d'aya yarage shine kimiqa godiyarki wajen ALLAH daya baki ikon canye jarabawar da yayi maki tahanyar rungumar sakamakon da yayi maki da hannu biyu kinji ko."

Cikin kuka ta d'aga masa kai yaci gaba da rarrashinta shi dasu ummi, umma kuwa batace komai ba sai kallon 'yar tata da takeyi har suka gama bata baki,

Dr ne ya shigo shida Fatima fuskokinsu d'auke da fara'a suka gaida iyayen nasu bayan suma sun nemi waje sun zauna,

"Ina shi little d'in dr."

Dady yafad'a yana kallonsa.

"Ai dady little ba'a magana, don yau shima yazame mana baqo yana can liqe da Dr suna cin abincin."

"Ah to Masha ALLAH, ai haka akeso, banga laifinsa ba iyaye ai rahamane, aqallah shima yanzu zaiji irin dad'in da kowane d'a kiji idan yana tare da mahifinsa, fatan dai sun iso lafiya ko?"

"Lafiya klw dady."

Dr yabashi amsa yana kallon fuskar Rashida data bayyanar da mamakinta qarara jin cewa wai little na garin kuma wai harda mahaifinsa, murmushi yayi kafin yace.

"Gwaggon yara kinfito?, Yau sai kika yimana yajin fitowa Saida kikaji takwarana ya iso ko.?"

Batace komaiba kanta na aqasa ta sake nocesa tana maijin zuciyarta na wani irin matsanancin bugawa da sauri da sauri,

'Dan harararsa ummi tayi had'e da cewa.

"Meye haka son? So kakeyi ka tsargamun 'ya agabana ne."

"Afuwan ummi, 'yar takice nakasa gane kanta daga jiya zuwa yau, ita da tayi haqurin shekaru da yawa sai naga tana qoqarin b'atasa tsakanin jiya da yau."

"To ya za'ayi, mubita ahankali, wlh al_amarinne da ciwo, Amma tunda ALLAH yakawo sauqinsa sai a haqura don asamu a cike mizanin lada ko kuwa 'yata."

Taqarashe maganar tare da d'ora hannunta saman kan Rashida, a daidai lokacin little ya shigo yana shafar ciki fuskarnan tamkar hasken farin wata saboda annurin dake kwance akanta na kasantuwarsa tare da mahaifinsa, ganinsu ya dashi sakin wani murmushi had'e da buga wata irin uwar gyatsa yana fad'in.

"Alhamdulillah."

Wajen dady yaje ya zauna tare da gaishesa idanuwansa nakan mahaifiyarsa yana son yaga awane yanayi take ciki amma taqi d'agowa,

"Barka da arziqi Nuraddeen, yau dai kewa ta qare, gaka ga mahaifinka, don haka sai kayi qoqarin kyautata masa tare da nuna masa nagartacciyar tarbiyar da mahaifiyarka ta jajirce wajen baka, kada ka kuskura kayi abunda zaisa ko kad'anne yaji aransa don baya tare dakai shiyasa kazama haka, Ina yimaka fatan gamawa lafiya tare dashe cikin amincin ALLAH da yardarsa."
Chapter 154 · 0% Book details