← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 160

Sashe 119

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu bazaki iya dakatar dashi daga qoqarin illata maki 'ya da yake shirin yiba?, kinfiso kirasata tahanyar biyewa zab'in da mahaifinta yayi mata."

Cikin dauriya don ita kad'ai tasan irin damuwar dake cunkushe acikin azuciyarta hajia mama tace.

"Ai ita tajawa kanta, mezanyi mata bayan addu'a, mahaifintane yanada iko akanta, ni kuma matarsa ce dole inbi duk wani umurni nasa, don haka ALLAH yayi mata magani kuma yarabata da wahala, gadone tariga tayisa, yanda baza'a iya saukar dashi ya sauka ba haka itama baza'a saukar da ita ba ta sauka,"

Tana gama fad'ar haka tawuce ciki daidai lokacin yana fad'in.

"Koda zaki mutu kina dawowa batool ni bazan tab'a d'aukarki naba wanda bayada asali ba, yarage naki kihaqura da zab'inki kibi nawa saiki zauna lafiya, idan Kuma kikace a'a to tabbas hawayenki zasu qare aduniya ba tare da ni nabi naki zab'in ba, shashashar banza da wofi."

Ko kallon gefen da suke hajia mama batayi ba taje ta jere abincin akan dining table tana qoqarin maida qwallanda suka zo mata,

Har zata fita dady yace.

"Zo kifice Mani da ita ad'aki kafin na kakkarya ta."

Dawowa tayi tasa hannu tariqo batool zata miqar da ita batool tariqe qafar Abba d'aya tana fad'in.

"Wayyo Abbana, nice batool d'inka, katuna lokacin da kake sakani dariya idan zaka kaini makaranta Ina kuka kana fad'amun cewa inyi shiru kukan da nakeyi na tab'a maka zuciya!, katuna lokacin da idan aka sakani kuka anan gidan kake cewa da ab'ata mani rai kafison a b'ata maka naka!, Abba ka tuna cewa tun ina qarama kasaba mani da nema mani duk abunda nake so kuma ka riqemun shi yanda bazani tab'a kukan rasa shiba, Abba don ALLAH kada yau da kanka ka nosantani da abundanake so, kada ka bari narasa Nuraddeen domin daidai yake da rasa rayuwata."

Hannunsa yasa yacire hannunta daga riqon da tayi masa ya juya mata baya, haka hajia mama tayita jan hannunta tana kuka tana kiran Abbaaa.

Duk da yanajin damuwa aransa na kukanta amma yafiso yayita saurarensa akan dawwama da zuciyarsa zatayi cikin damuwar aura mata wanda take so da yake yiwa kallon shege da bayada uba.

Ganin abbanta naci gaba da shire shiren auren nata gashi fushin zuciya yasa su uncle h fita batunta yasa batare da sanin kowa ba ta tsere tabar garin tanufi borno, kai tsaye gidan Dr ta sauka wajen Rashida mahaifiyar little don dama tasan gidan, suna zaune ita da Fatima tashiga bakomai ahannunta tana daga ita sai kanta tana kuka, sun matuqar firgita ayanayin da suka ganta don tarame tayi baqi tamkar wacce batada galihu aduniya.

Tana zuwa ta zube agabansu tana fad'in.

"Gwaggo don ALLAH da girmansa kije kiyiwa mahaifina bayani, gwaggo bazan iya rayuwa babada Nuraddeen ba, shi kad'ai nake so kuma zan iya bashi rayuwata, mahaifina, mahaifiyata, baffannina, gaba d'aya sun juya mani baya, sunnkasa karantar zuciyata balle susan irin zafi da qunar da take yimani, kitaimaka kifad'awa abbana kece mahaifiyar little, kafad'a masa mahaifinsa naraye wataqil zai..."

Bata qarasa ba sanadiyar fad'uwar da tayi daga durqushen da take tasuma, kallo d'aya zakayi mata kafahimci irin jigatar da tayi.

Ruwa Fatima ta d'ebo ta yayyafa mata tare da tada ita zaune, d'ago kai tayi tana kallon Rashida da tayi tagumi da dukkanin hannayenta hawaye na zubar mata saboda tsananin tausayin yarinyar, wato haka ita rayuwa ta gada kowane irin mutum da tasa jarabawar rayuwar, ayau taqara jin zafin mahaifin little a ranta domin duk shine silar faruwar wannan abun ga yaronta da kuma wacce yake so.

Ganin batool naqoqarin yin magana yasa tagoge hawayenta had'e da dakatar da ita da hannu, cikin sanyin murya tace da ita.

"Kina son little?" Da sauri batool tashiga kad'a kai kamar qadangaruwa had'e da cewa.

"Eh.."

"Zaki iya zama dashi aduk yanayin da take?"

"Eh?"

"Kingamsu da cewa shid'in d'an halak ne gaba da baya?"

"Eh."

"Wane yaqini kike dashi akansa?"

"Zai kula dani har qarshen rayuwarsa."

"Wace tabbaci zaki bani akan soyayyar da kike yimasa?."

"Ban saniba, amma nasan Ina sonsa domin ALLAH, kuma Ina qaunarsa har zuwa fitar lumfashina naqarshe!."

Wata ajiyar zuciya rashida tayi had'e da cewa.

"Shikenan, share hawayenki, kina sonsa domin ALLAH, shima haka, don haka narantse da wanda lumfashina yake a hannunsa a matsayina na mahaifiyarsa Ina tabbatar maki da cewa matuqar ALLAH nanifin alkhairi acikin aurenku kamar yanda akoda yaushe nake roqa maku to tabbas babu abunda zai hana ku auri junanku, sai dai tabbas bazaku gujewa tsarin qaddarorin da za'a jarabceku dasu aciki ba, girman imaninku da yaqininku ga ALLAH shi zai tseratar daku daga kaidin dukkanin masu kaidi, kisa aranki in Sha ALLAH, ALLAH zai kawowa soyayyarku d'aukin da bazaku tab'a rabuwa ba, ni inajin haka ajikina."

"Yanzu dai ba wannan ba ke gwaggon yara, inashi little d'in? Yakamata akirashi."

Fatima tafad'a tana kallon Rashida.

"Kwana uku kenan shima yana d'akinsa baida lafiya sanadiyar kiran da tayi masa ta sanar dashi halin da ake ciki, na hanasa bayyana hakanne saboda kada yatayarwa da dady hankali, kina ganin yanda shekarunsa keja bai kamata acika kai masa duk wani abu da zai jefasa cikin damuwa ba, mubi komai a sannu ALLAH zai kawo mafita"

Yanda Rashida ke maganar cikin kwarin guiwa shiya dad'a kwantarwa da batool hankali domin itace last hop d'inta akan soyayyarta shiyasa tayo wajenta atunaninta nacewa ita kad'aice zata iya gamsar da mahaifinta, sai gashi tasamu qwarin guiwa da gamsuwa daga wajenta, murmushi Fatima tayi had'e da cewa.

"Anya kina ganin hakan zai yuyu?"

"Sosai kuwa, ai SANNU SANNU bata hana zuwa...."

"Shikennan! Amma dai taci abinci ta watsa ruwa sai a sanar dasu dady da Dr kokuwa?"

"A'a basai anfad'a masu ba, zansa shi da kansa ya d'auketa yamaida ita gidansu."

"Anya Rashida kina ganin hakan yayi?."

"Eh mana, hakan shine daidai."

Bayan tayi wanka taci abinci wanda sharabonta dashi har ta manta Fatima takira little awaya tace yazo tana son ganinsa,ba'afi mintuna biyar ba sai gashi yashigo tamkar a hura sa ya fad'i cikin 'yan kwanaki uku kacal da yayi acikin damuwa, yana d'ago kansaya hango batool d'insa zaune kusa da fatima tana wasa da 'yan yatsun hannunta.

Da sauri yaqarasa wajen gaba d'aya ya manta ko wacece awajen had'e da cewa

"Gimbiya, waya kawoki nan?, ya akayi kika zo nan?, Meya sameki haka gimbiya?."

Kasa maganatayi saboda wani nauyi da takeji, sab'anin d'azu da Bata masan kalaman da take fad'a ba saboda tsananin halin da take ciki,

"Kice dani wani abu mana, dama nasan bazaki barni ba, pls gimbiya kiyi..."

Bai qarasa maganar ba Rashida dake shigowa lokacin tace.

"Rufe mana baki marar kunya, agaban maman taka kake wud'annan suruttan?"

Sai alokacin ma yatuna tana wajen cikin rashin qwarin jiki yaje ya zauna qasan qafafuwanta yana kallon batool qasa qasa.

Murmushi Fatima tayi had'e da cewa.

"Dama na kirakane saboda kazo kaganta ku gaisa, idan kun gama gaisawa sai kaje kawatso ruwa ka d'auki motar Dr ka maida ita gida."

'Dago kai yayi kamar zaiyi kuka Rashida tace.

"What ever the situation is..Dole yau d'innan kaje ka maida ita wajen iyayenta kaji nafad'a maka." Sannan suka miqe sukabar falon yarage daga shi sai ita.....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Gaisuwa tare da fatan alkhairi agareki, haqiqa kulawarku agareni ta musammance da bazan tab'a iya mantawa daku ba, *NANA RUKAYYA GUMMIEY, DOTA HADIZA ZAINU (KUBRA), NAJIDA ALIYU🐒, MUM NUSAIBA, TEEMAH M SANI, HAFSAT HASSAN USMAN, SA'ARBUKAR RABI'U CE, ABLAH SORPEEEY, UMMUL ADNAN, ZAINAB GARBA FARUK, SHAMA HALLIRU, UMMI ABIL BAITY, XEEEE, JAMILA YUSHA'U* Ina godiya bisa qwarin guiwa da kulawar da kuke yimani dama littafina, fatana amincin ALLAH da kuma yardarsa ya lullub'eku kuma yabaku aljannah da rahamarsa👏Fillah Ina matuqar girmama karamcinku agareni, ngd ngd ngd sosai 😍🤝_

Page___87💎

Abba bai zame ko Ina ba sai tsakar falon hajia mama wato mahaifiyar batool, kira yadinga qwala mata tamkar wacce tayi wani laifin, tafito daga kitchen riqe da ludayin miya da alama girkine take qoqarin qarasawa, kallo d'aya zakayi mata ka hango tsantsar damuwar da take qoqarin b'oyewa daga cikin idanuwanta, wanda ko shakka babu kasan hakan yasata zubarda qwalla ba adadi lura da yanda idanuwanta suka kumbura, cikin sanyin murya yace.

"Gani alhaji lafiya?"

"Bana buqatar jin wannan tambayar daga bakinki, Ina so daga rana mai kama tayau karki sake kisake barin yarinyar nan tashigomin part domin nadad'e da cireta daga cikin 'ya'yana, don haka dole tanisanta da duk wani abun daya shafeni kuma yazamo mallakina, wannan umurnine nafad'a maki, qoqarin sab'ashi kuma zai iya jawo b'annar rayukka tsakanin ni dake, ban haifi d'iyar da zatazo tana walaqantani agaban idanuwan duniya ba kuma har in zauna da ita, wlh bazai yuyu ba, ta zab'i wani akaina duk irin gatar dana bata saboda kawai cikar nata burin, tayi fatali akan cewa wane irin hali zan iya shiga a matsayinta na 'ya tilo mafi soyuwa araina don haka taji tayi duk yanda take so nacire hannuna a al_amurranta, nayi qoqarin ganin nabata gata tare da inganta rayuwarta amma takasa fahimtar hakan, amma shikenan taje, in dai duniyace ta isheta riga da wando, in Sha ALLAH da SANNU SANNU..."

Bai qarasa ba tayi saurin d'aga masa hannu idanuwanta na hawaye tace
Chapter 119 · 0% Book details