← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 160

Sashe 128

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Babu inda zaki jefa Inna kawai kihaqura, fisabillahi dubeni yanda nabi duk na tsofe akan titi nakasa samun koda d'an qauyene balle d'an birni ya aureni saboda son zuciya irin taku, izuwa yanzu yakamata ace kun zubar da makaman yaqinku, donni kukeyi kuma tuntuni nace nahaqura meyasa ku bazaku haqura ba, duniyar nan takarantar dani darussa da dama wud'anda a matsayinki na iyayena kun kasa fahimta, ada ana yimani kallon shashasha, sakarai, samna da batasan inda duniya tanufa ba, ana kallon cewa na cika hauka da shirme amma ayanzu inada gwargwadon hankalin da zan iya banvance qarya da gaskiya, Inna baran nan bayada amfani don girman ALLAH kihaqura dashi, bayin ALLAH nan su ake cutarwa amma duk da haka akoda yaushe suna iya qoqarinsu na ganin sun sauke haqqin zumuncin dake tsakaninmu dasu sai muyita shurewa hakan!, Yau ina roqonki don ALLAH da darajarsa kihaqura da zancen bara mukula da baffanmu da 'yar gudun mawar da zamu samu daga wajen 'yan uwansa kafin lokaci ya qule mana, munyi abubuwa da yawa da yakamata mu natsu munemi yafiyar bayin ALLAH n nan..."

Ai kafin taqarasa ta qwace sandar jin zata b'allo masu ruwa sannan tace.

"Ya isa haka, sai kikeki ki zauna, zanga tsiyar da za'a yimaki kuma wlh kika sake kika bud'e baki akan wata maganar da ta shafemu saina tsine maki, jeki ni bazan iya zamaba don ALLAH baiyini da matacciyar zuciyar da zan zauna sai wani yabani ba."

"Assha innarmu, ai inaga duk tafiyar d'aya ce, dama dama wannan shida ba roqa zakije kiyiba, taimaka makine za'ayi acikin gidanki a matsayinki na uwa kuma matar d'an uwansu wanda sune dolenmu."

"Dallah tafi can, nadai fad'a maki ni kinga tafiyata."

Ta ficewarta tanata maseefa da ita, har takusa fita tadawo tanufi d'akin da baffa Ali ke jinya, tana kaiwa bakin qofar kafin ta d'aga labule yajefo wata gora dake gefensa tabugeta ga qwabri yana fad'in.

"Wane d'ebabben albarkane abakin qofar d'akinnan, tsinannin yara, d'iyan abun kware!, Magulmata da basuyi gadan mutunci ga iyayensu ba, wanene anan?"

Muryar Inna ruqayya yajiyo tana fad'in.

"Kai ka kai ka kai!, Ali yau maseefar taka akaina zaka saukar da ita?, Ni kake jifa da gora salon nima ka kaini kabaro gaba d'ayanmu mukoma zaune ana nunamu, to wlh kaga inda nayi nafasa shigowa, wannan muguwar gora dad'a so kakeyi ka karya mun qafa da ita, to nafasa shigowar sai anjima idan na dawo."

"Haba ruqayya, are bansan ke bace, nazata shashashun yarannanne masu kaida komowa da d'an kai suna regena, Yi haquri kiwhigo mana muyi magana."

"ALLAH da sai in tafiyata abuna, wannan ai mugunta ne" tafad'a tare da d'aga labulen ta tura kanta aciki, ai kafin ta ida shiga tayi saurin dawowa baya sanadiyar wani irin wari daya bugi hancinta tana fad'in.

"Nashiga uku ni ruqayyatu, Ali mezanji haka! Kardai kace bayan gidane kayi azaune yake wannan d'oyi haka!,"

"Haba kekuwa! ya za'ayi nayi bayan gida bayan Ina iya motsawa da kaina, ga yaronnan Yusuf kinsan bazai barni cikin qazanta ba."

"To nikam narantse maka da ALLAH bazan iya minti d'aya a d'akinnan ba saboda warin da yakeyi, yanzu ma ALLAH yagani ka cuceni da kasa nashigo ciki bayan kasan akwai irin wannanazababben wari aciki, wai! To nidai zani wajej bid'o maka abunda kaci tunda yanzu ba kada mamora, kakoma mani cima kwance."

"Ikon ALLAH, yanzu da bakinki kike fad'ar haka bayan kinsan irin wahalar da nakeyi daku lokacin da ina lafiya?"

"Yo yanzu kuma aimuke wahala dakai tunda bakada lafiya, ka jika da wani zance, Ina ai gaskiya nafad'a ba qarya ba zaka wani yab'omun gori, yanzu shekararka nawa ahaka zaune? Ai inaga ko ban biyaka ba duka nakusa biyanka wahalar da kayi damu, kajimun zancen banza da wofi, nikam tin wuri wlh ka sawwaqemun indai qafarnan takace ke wari don bazan iya cigaba da rayuwa dakai ba."

Tana gama fad'ar haka tabar wajen batare da tsaya sauraren abunda zai cewa ba duk da tana jiyo sautin kiran sunanta da yakeyi amma ta tafiyarta.

Haka rayuwa taci gaba da gudana tsakaninsu, muneera dai su baffa sun hanata zuwa bara don da sukaga ma tana nema ta tilasta mata baffa Usman yasa takwashe kayanta takoma gidan baffa inda baba nusaiba, kuma tana samun kulawa daidai gwargwado don har makarantarsu nusaiba ta islamiya da daddare take binta, kuma ba laifi tana fahimta, duk da tagirmema baba nusaiba tana bata girmanta daidai gwargwado a matsayinta na matar wan mahaifinta kuma itama tana jin dad'in zama da ita sosai, gaba d'aya muneera ta canza daga muneerar shekarun baya da batasan ciwon kanta ba izuwa kamilar muneera data san ciwon kanta yanzu, duk wani taimakon aikin gida takan riqawa baba nusaiba batare da tajira ance tayiba kuma tana kula da qannenta su Rashida cikin so da qaunar juna.

Hakan yasa su baffa sukayi tunanin samamata mijin aure duk da kuwa shekarunta sunja sosai, inda akwai wani abokin baffa Usman dake gadi acan cikin birnin kano agidan wani alhaji, amma d'an asalin nan qauyensu ne yanada mata biyu da yara goma sha hud'u donnhar ya aurar da wasu ya tab'a ganin muneera tun lokacin da dad'ewa yayiwa baffa Usman maganar yana so yabashi aurenta, Amma saboda matsalar iyayenta da rawar kanta alokacin baffa Usman yabashi haquri saboda kada su samu matsala a abokan takarsu ta sanadiyar aurenta, don haka sai ya iskesa ya sake tuntub'arsa akan maganar idan har yanzu yanada ra'ayinta kuma cikin iyawar ALLAH yanuna masa shi bai damu da tsufanta ba har yanzu yana sonta indai za'a aura masa ita, nan take su baffa sukace suma sun amince yaje yaganta suyi magana, yana zuwa kuwa muneera ta amince masa ba b'ata lokaci don dama abunda ta dad'e tana jirane ALLAH bai kawo mata ba sai yanzu, iya darasin duniya dai izuwa yanzu ta d'aukesa don haka babu abunda take buqata yanzu inba samun abokin zaman da zata ida sauran rayuwarta da shiba.

Duk da yanayin da baffa Ali yake ciki hakan bai hanasu bashi haqqinsa ba na zamansa mahaifi agareta duk da kuwa babu abunda zai iya attakawa alokacin saboda yanzu ciwon qafar har yakai yafara shafuwar lafiyan jikinsa, ya rame sosai tamkar ba shiba, babu yanda ya iya illa yabi abinda sunka zomasa dashi don ko yace yaqi amincewa tofa bayada qarfin da zai iya dakatar dasu, Inna ruqayya kuwa tayi maseefa tayi jidalinta har tagaji lokacin da zancen yazo mata wanda zuba idon da baffa Ali yayi ya matuqar tab'a mata zuciya har ta d'auki fushi dashi tadena kulasa dama can Kuma ba wata kulawar take basa ba tunda tafahimci halin da yake ciki, acewarta bazata iya zaman shaqar wannan warin qafar tasa da yake fama da ita ba.

Yusuf kuwa kullum cikin aikin gini da labaranci yake yana tara kud'ad'e don yasamu yakai mahaifinsa asibiti hakan yasa baya samu ya wuni gida sai da marece zuwa dare, baffa Ali yayita zaginsa yana fad'in wai shima gudunsa yakeyi shiyasa baya zama gida da rana, tsiga kuwa sai wacce yamanta, haka Yusuf zai zauna yayita kuka yana basa haquri amma tamkar yana sake turasa.

Bayan sati biyu aka tsaida zancen auren muneera tare dasu baffa da Yusuf da iyayen baba aminu mai gadi da sukazo nema masa auren nan da wata mai hita in ALLAH yakaimu, inda su baffa suka koma fad'i tashin kayan aurenta batare da sun jira komai daga kowa ba inba Yusuf da ako yaushe yake bibiyar yanda abun zai kasance ba matsayinsa na d'a babba daya rage masu abokin shawara agidan,

Tsananin tausayinsa da baffa keji yasa ya tambayesa in yana son 'yarsa muneera ya aura masa ita ko yasamu natsuwa akan yanayin da yake ciki, Yusuf na matuqar son Rashida amma daya tuna matsalar mahaifiyarsa da mahaifinsa sai ya nunawa baffa cewa bayada halin yin aure yanzu asali ma baida inda zai aje matar, baffa yayi murmushi had'e da cewa.

"Indai wannan itace matsalarka babu damuwa in Sha ALLAH, ALLAH bazai hana yanda za'ayi ba kashirya in Sha ALLAH zan aurama Rashida indai kana sonta, shekarunka naja yakamata ace kaima kamallaki iyalinka izuwa yanzu."

Shiru Yusuf yayi yana jinjina halayyar baffa wacce ahalin yanzu tayi qaramci, a koda yaushe yana qoqarin rama cuta da alkhairi kamar yanda annabi keyi, bayan duk cutawar da iyayensa suka yimasa amma gashi zai d'auki 'yarsa yabashi wannan wace irin kyakkyawar zuciya yake da ita da batada riqo balle qoqarin rama cuta da cutar da aka yimata, kuka yafashe dashi tare da zayyane masa gaskiyar dalilinsa naqin auren baffa yace bakomai, in Sha ALLAH baya hango komai sai alkhairi acikinsa don haka ya kwantar da hankalinsa, baffa Usman kuwa kafe kai yayi akan bai yarda ba Kuma bai amince da had'inba saboda Inna ruqayya, yasan Yusuf baida wata matsala don kusan halayyarsa irin ta ya nura ce Amma abun dubawa shine halin da zasu jefa yarinyar aciki, Kar azo a maimaita abunda yafaru ashekarun baya ga yarinyar mutane abubuwa duk sukabi suka lalace, Inna Bilkisu ce tayita lurar dashi har ya amince amma yace ba yanzuba kamar yanda baffa ke buqata sai idan takammala karatunta na sakandiri, yanzu tana aji hud'u don se daga baya baffa yayi tunanin sasu makarantar saboda yanda bokon gaba d'aya yafice masa arai, badon baffa yaso hakan ba ya yarda tunda har ya samu ya amince.
Chapter 128 · 0% Book details