Sashe 33
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Amin inna dama cewa nayi ko Aysha zata rakata cikin gida tagaishesu?."
"Af kaji nura da wata magana, Aysha ai qanwar kace ko bak fad'amun ba kanada ikon aikinta duk inda kaga dama balle nan cikin gida maza ka hanzarta kaje kasamu sallah kada jam'i ya wuceka in sha ALLAH babu wata matsala."
Kusan tare suka fita da baffa Usman cikin sauri sauri don su samu ayi jam'in dasu,
Duk inda yakamata akai Rashida acikin gidan Aysha ta kaita in banda wajen yaya hawwa da baffa, shima d'in Inna Bilkisu ce tace tabari idan nurah yadawo sai sutafi tare, duk cikin gidan babu inda Rashida tasamu matsala hatta ga 'yan uwansa da suke uba d'aya Wanda b'angarensu nacan gefe sai wajen Inna ruqayya, tasha tambayoyi da maganganu kala kala da kallon banza amma da yake gaba d'aya hankalinta baya wajen saboda ganin yanda magrib ta gabato bai dawo ba zancen zuwansu gida tagano ummata, shiyasa ko ajikinta don bata maji wasu maganganun ba Aysha ce kawai taji itama taja bakinta ta tsuke tamkar bataji ba.
Har akayi sallar isha'i Rashida nazaune tana jiran dawowarsa amma shiru hakan yasa tad'auko wayarta da tunjiya data ajiyeta cikin jikkar hannuta bata sake waiwayarta ba sai yanzu da yake tasan wayar akashe take shiyasa tana d'aukowa tayi saurin kunnawa, tana gama logging tafara qoqarin lalubo lambarsa saiga kiransa ya shigo, cuno baki tayi sannan ta d'aga wayar kamar zatayi kuka tace.
"Shine kayi tafiyarka kabarni ko?"
'Dan murmushi yayi don dama uasan za'ayi hakan sannan yace.
"Yihaquri habibty koda nakammala sallah nasamu suna jirana a mota kinga bazai yuyu in b'ata masu lokaci ba, amma nayarda nayi laifi ayimun afuwa ga munan munkusa qarasowa gida."
"Ai dama nasan haka zakace, shikenan ALLAH yakawoku lafiya, ya umma dasu baba?"
"Lafiya klw suke ga saqonan sun bayar akawo maki,"
"To shikenan sai kadawo."
"Yawwa habibtynah I love you."
"I luv you too" itama tafad'a akunyace sannan takashe wayar,
Bayan yadawo yaci abinci ya watso ruwa ya huta lokacin har qarfe tara na dare yayi suka fito tare da rufo qofar tana saye da hijabinta, d'akin Yaya hawwa suka nufa yayi sallama tana kwance tabashi izinin shigowa tare da qara nishin da takeyi,
"Shigo nura har yanzu dai jikinnan ya qiyamun duk da dai ciwon cikin yafad'a gudawar daice har yanzu."
Tafad'a tana qara mimmiqewa akan gadon batare da tasan tare yake da ita ba sai daya koma gefe yana cewa Rashida dake lab'e bayansa gabanta na dukan uku uku. "shigo mana"
Wata irin zabura Yaya hawwa tayi sai kace ba itace tagama nishi tana fad'in har yanzu jikin nata yakasa koma mata daidai had'e da cewa.
"Fita, fita, fita tsaya can bkin qofa Ina zuwa, Kai ma tashi fita tabarma na nan gefe ka shinfid'a ganinan fitowa" tana nuna masu qofar fita da hannu, jikin Rashida na rawa tajuya zata fita da sauri yariqo hannunta,
"Haba innar mu keda bakida lafiya mezaisa sai kin wani fita, Rashida cefa ba wata ba ni kuma d'anki ne, me zaisa kice muzauna awaje."
"Kaga kayi abunda nace maka, idan Kai d'ana ne ita wannan abarfa, karka manta shifa bare ba'a bashi amana Taya za'ayi inbarta tashigo tagane mani sirrin d'aki asamu damar cutar dani, maza kufita nace." Juyawa yayi yana riqe da hannunta yana d'an mammatsawa ahankali saboda tasamu suka fito d'akin,
Tabarmar dake gefe Rashida tajawo yana kallonta ta qaqaro murmushi ta sakar masa had'e da shimfid'awa ta suka zauna, murmushin shima ya sakarmata kafin Yaya hawwa tafito a dudduqe ta zauna abakin qofar shiga d'akin nata, kallonta yayi yace
"Ina wuni innar mu, ya qarfin jikin?"
"Lafiya klw" tafad'a fuskarta ad'aure tana qarewa Rashida data sinne kanta qasa kallo da yake akwai wuta, d'ago kai Rashida tayi batare da tasan tana kallonta ba tace,
"Ina wuni? ya qarfin jiki."
"Lafiya" ta amsa mata tana dalla mata wata irin muguwar harara, addu'a ta shigayi cikin zuciyarta saboda tasamu sauqin yanayin da take jin kanta aciki, can tajiyo dirar muryar Yaya hawwa akunnuwanta.
"To atashi atafi idan shikenan Ina so inyi magana da d'ana." Jiki ba qwari Rashida tamiqe tabar wajen.
"Kai nura nifa inkan bid'ar lafiya ga yarinyar nan kada ka koma kawo man ita shiyata saboda natsaneta bana son ganinta ko kad'an."
"Haba innar mu, ai yakamata ace ko albarkaci na taci, bai dace ace kinyi mata haka ba ko kad'an, don ALLAH kicire wannan tsanar da kikayi mata tunda batada dalili."
"Iyyeee lallai nura kace wani abu, wato ni zaka gwadama cewa kaima cikakken namiji ne yanzu saboda waccan 'yar abar, koda yake bansan wane kalar surk'ulle akayo maka ba kabi ka lashe dole kafad'a mani magana, to bari kaji nafad'a bana sonta zo ka dokeni, yarinya bare da ita har kace banida dalilin tsanarta bayan ta ruguje mana al'adar gida."
"Haba innar mu, al'adafa ba addini bace.."
"Kai ni tashi tafi kabani waje ban iya sauraren wud'annan suruttan naka."
"To jikin fa?"
"Nawarke tashi kaje."tafad'a cike da takaicins.
"ALLAH yabaki hak'uri innar mu seda safe."
Yafad'a tare da miqewa yafice, yanaji tasaki wani uban qyacci dake nuna akwai wata aqasa amma ransa yaroqi ALLAH ya fahimtar da mahaifiyarsa taso matarsa farincikin sa...
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___25💎
Koda yafito yasamu bata wajen kuma babu alamar takoma part d'insu don arufe yake, shiyar Inna Bilkisu ya leqa ko zai gata acan, cikin sa'a ya hangota gefe zaune ita dasu na'ima da fadila yayun Aysha suna fira ita kuma Inna Bilkisu na d'aura jiqaqqar ayar da take sayarwa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya gaida Inna Bilkisu had'e da cewa Rashida.
"Ashe nan kika shigo?"
"Eh nafita d'auko ayar nan ne naganeta tsaye abakin qofar shiga shiyarku shine nace tazo nan tajira kafito saboda wajen akwai sauro sosai."
Inna Bilkisu tafad'i haka tana kallon Rashidar data noce kanta qasa tayi kamar batasan da shigowarsa ba saboda kunya.
Sosa d'an qeyar kansa yayi had'e da cewa "eh da yake munshiga gaida innarmune shine nace tajirani muje wajen baffa."
Tashi kuje Rashida kinbar mijinki tsaye, miqewa tayi tayi mata seda safe itama su aysha nace mata "aunty seda safe" suka wuce.
Kafin su isa wajensu baffa don da alama duk suna can d'akin da yake ya kalli fuskarta da yake akwai hasken wutar nefa ko Ina agidan yace "habibty kiyi hak'uri da abunda innar mu tayi maki kinji ko?"
"Laa..bakomai mai malamina ai don ta isa ne, karka damu ni banji komai ba tunda mahai fiya take agaremu." Murmushi yayi yan qara jin qaunarta aransa kafin ya jawota ajikinsa "Ina sonki sosai d'alibata." dariya tayi tare da k'wace jikinta daidai lokacin suka iso bakin qofar shiga d'akin baffa sunajin tashin firarsu, sallama yayi suka amsa sannan yashigo ita Kuma tayi tsaye abakin qofar, Sosa kansa ya shigayi had'e da kallon baffa Usman yace,
"Baffa zuwa tayi tagaisheku."
"A'a'ah to to Masha ALLAH, shigo da ita."
Leqowa yayi had'e da cemata tashigo, tashigo bakinta d'auke da sallama kanta na qasa a duqe ta duqa har qasa tana gaishesu, daga baffa sai baffa Usman suka amsa mata shikuwa baffa Ali gefe ya koma abunsa tare da d'aukar redion baffa ya kara akunne don kar yaji abunda suke fad'a, ya jiki tayiwa baffa had'e da yimasa addu'ar ALLAH yabashi lafiya,
Ba baffa kad'ai ba hatta baffa Usman sun yaba da Rashida sosai tare da yimata nasiha akan tabi mijinta akan dukkanin abunda bai sab'awa ALLAH ba, kafin su sake had'asu subiyun suyi masu nasiha sosai akan haqqoqin junansu dake kansu, har suka gama baffa Ali baice komai ba saida baffa yace
"To Ali kai bakace masu komai ba, yakamata a matsayinka na mahaifinsu kasa masu albarka da 'yar nasiha ko kuwa?"
Ganin Babu alamun wasa a fuskar baffa Yasa ya ajiye redion had'e da cewa.
"To duk abunda yakamata ince ai kunce sai dai nayi d'an qari akai, Kai nura kasani zumunci ba wasa bane don haka kanunawa matarka tariqe maka 'yan uwa da daraja kada ta walaqan tasu haka kaima, kada kanunawa matarka fifikonta akan 'yan uwanka don ana rabuwa da mata amma ba'a rabuwa da 'yan uwa, 'yan uwa da kake gani duk inda suke sunfi bare.."
"Haba Ali.." baffa Usman yafad'a ransa ab'ace da zimmar dakatar dashi baffa yariqe hannunsa alamar ya qyaleshi.
Cikin isa yaci gaba da cewa "Kuma kar inji kar ingani kisake inji ance kin ware mana d'aya acikin 'yan uwa duk d'aya muke, bama son had'e had'e balle anyi ance don cikin ahali guda kika shigo bamu yarda kiraba mana d'aya biyu ba, yanada 'yan uwansa mata da kika iskosa dasu don haka kada mugun kishi yasa inji ance kin rabashi dasu ko kin hantaresu kinji nafad'a maki?."
"In sha ALLAH baffa nagode sosai" Rashida tafad'a cikin girmamawa da kuma sakin fuska,
Hakan baqaramin yiwa su baffa Usman dad'i yayi ba don azatonsu nan take yarinyar zata nuna b'acin ranta wanda da wannan baffa Ali zai samu damar cusguna mata akoda yaushe,
"To Rashida munsan gidanku Kuma munsan tarbiyarki don haka kiji kiqi ji ki gani kiqi gani, duk idan akace akwai taron mutane to dole saida hak'uri saboda sai kaga mabanbantun halayye da Kuma d'abi'u don haka kisa haquri kuma kiriqi ALLAHn ki ubangiji ALLAH yayi maku albarka ya zaunar daku lafiya kuma yabaku zuri'a masu albarka."
"Amin baffa ngd" tafad'a tana maijin dad'in addu'arsa.
Miqewa Nuraddeen yayi aransa yana mai godewa ALLAH daba baffa Ali kad'ai yabashi a matsayin qanen mahaifi ba badon haka ba da baisan meye makomar rayuwarsa data iyalinsa acikin gidannan ba, amma yanzu koba komai yasan idan yaji d'aci awani b'angaren to zaiji dadda'an zaqi awani b'angaren guda.