← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 160

Sashe 137

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Duniya ce tafi bagaruwa iya jima ruqayya, yanzu ke ko aya bazata isheki ba ganin yanda nakoma nida Yaya hawwa kisan cewa annabi ya faku? Yakamata wannan qiyayyar da tsana da kuma d'aukar fansa ta tsaya haka, yakamata kimanta da komai kitubarwa ALLAHnki kamar yanda mukayi nida yaya, kiroqi bayin ALLAHn nan da muka zakinta suyafe maki kafin ta ALLAH takasance akanmu, ni daine abokin tarayyarki acikin wannan adawar da mukeyi, Kuma natubarwa ALLAH don haka kema ina roqon ki d'aki tuba mutaru mugyara laifin da muka aikata ko ALLAH ya dubemu da idanuwansa na rahama."

"Ali! Kanka d'aya kuwa, shin kaji me kake cewa?, to narantse maka da ALLAH indai don yaron nan yadawo kake yimun wannan wa'azin to wlh tuba ba yanzuba,"

Arazane baffa Ali yace.

"A'uzubillahi minashshaid'anir rajim, ruqayya idan baki tuba yanzu ba yaushe kike son tuba?, Kin manta da rayukanmu ba ahannunmu suke ba, kafin kituba ALLAH zai iya zare rayuwarki, Haba don ALLAH kiwatsar da wud'annan makaman yaqin naki idanko ba haka ba zamu farraqa tsakanin ni da ke don yanzu ni nagane gaskiya da kuma kuskuren dana tabiye maki muna aikatawa."

"Ahaf, kanka akeji ni bacci nakeji, indai kuskurene ai kai nabiyewa har nayi shi ba kace kabiye mani ba."

"Naji tunda ni kika biyewa to nagane gaskiya kema kigane gaskiyar don ALLAH kifad'a mani wajen da muka binne maganin, in Sha ALLAH Babu abunda zai samemu, idan ma yasamemu ai kinga zamu mutu muna masu baraa'a daga laifukan da muka aikata, ko banza ai dama zamu mutu ba tabbata zamuyi ba aduniyar."

Tsabar batada lokacinsa duk wannan surutan da yakeyi saidai yaji hansarinta, bubbuga kafad'arta yayi yana cigaba da roqonta amma tayi biris dashi tamkar da dutse yakeyi.

Haka dai suka kwana babu wani Abu daya samu daga wajenta, da safe ma yadinga roqonta amma fir taqi tankasa ma balle yasamu amsa daga wajenta hakan yasa ransa b'aci sosai yarufeta da maseefa akan lallai lallai saita fad'a masa ko kuma yau babu inda zata fita da sunan bara yakama bakin qofar ya tare, hakan ko kad'an bai girgiza taba balle yasa tadamar da kanta saima cigaba da shirinta da tayi hankali kwance tana gamawa tanufi bakin qofar had'e da cewa.

"Jaye kabani waje ko in ingijeka kasan qafa d'aya ke gareka."

"Ni zaki ture ruqayya?"

"Kana wasa, to Bari kagani..."

Ai kafin takawo baffa Usman dake fitowa daga cikin d'aki don tun jiya yanajin yanda suka kwashe da ita ya qaraso aguje yana fad'in.

"Kul...wlh karki kuskura ki ingije Mani d'an uwa ko hukuma tashiga tsakaninmu, shashasha sakarya da batasan ciwon kanta ba."

Yaqare maganar tare da jaye baffa Ali gefe dake faman qwalla, zata fice tana suruttai yace.

"Karka batta ta tafi, ita kad'aice mafitarmu kuma tunda arziqi bazaisa tafad'i komai ba akaita ga hukuma dole su zasusa tanuna wajen da kansu, don ALLAH Usman kada kubari tafita ku kira ko 'yan sandane...."

Ai kafin yaqarasa rufe baki Inna ruqayya najin yace 'yan sanda ta arta dana kare duk da bawani gudu bane tunda tayi tsufan da batada qarfin da zatayi gudun sosai.

Tunda tafita bata sake dawowa gidan ba har aka buge kwana hud'u saboda tsoron kada 'yan sanda su kamata, kullum saidai taje can wajen wani shago cikin tasha takwana, baffa kuwa dama koda sukaje masa da zancen d'aukowa Inna ruqayya 'yan sanda cewa yayi a'a su qyaleta bayason 'yan sanda sukoma shiga sha'anin gidan saboda ya fahimci hakan naqara rura wutar tsana acikin zukatan 'yan uwa wanda dama yanadaga cikin matsalar data haifarda sasu d'aukar fansa akan d'ansa Nuraddeen don haka aqyaleta, yana nan yana addu'a kuma yasa ayi masa sosai idan da rabon zaingana da d'ansa to ko yaushene zai dawo garesa, hakama ya sanarda little komai yace yatashi tsaye da addu'a sosai akan mahaifinsa in sha ALLAH zai dawo nan kusa bada jimawa ba, little yayi kuka sosai daga baya yakoma ga ALLAH yana fad'a masa damuwarsa, kullum cikin sadaka yake ga gajiyayyu tare da taimakon mabuqata da nufin ko meye ALLAH ka yayewa mahifinsa.

Shi kuwa Yusuf dama baya nan balle yasan meke faruwa, yana can wajen karatunsa a.b.u zaria a matakin qarshe duk da baiso ma cigaba da karatun ba saboda atunaninsa yayi girman da daqyar in zai iya amma baffa yace dole sai yaje yayi saboda yarage masa ganin matsalolin dake cikin gidan da damuwa kuma yasamu ingantacciyar rayuwar da idan yayi aure bazasu samu matsaloli sosai ba tunda yanada iliminsa.

Baffa Ali kuwa ko ajikinsa rashin dawowarta gida don yanzu ko ganinta baya sonyi balle yanemi sanin inda take, muneera ma batasan wainar da ake toyawa ba har aka buge wud'annan kwanakin hud'u,

Ita kuwa Inna ruqayya abunda bata sani ba ashe wasu 'yan iskan tasha na nan nayi mata kallon mahaukaciya suna dakonta ko yaushe, haka wata qatuwar mota duk marece sai tayi parking inda take zama an miqo mata kud'i kusan dubu uku, wannan dalilin yasa taqara yin zaunenta acan aganinta idan takoma gida bazata samu wud'annan kud'in da masu gidan arziqi kamar yanda take fad'a suke bata ba.....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___97💎

Yau baffa Ali na bacci yadinga ganin kansa a inda suka binne maganin shida Inna ruqayya wai yanata tonon wurairai ita kuma tana masifa dashi tana rufewa, yana kaiwa bayan wani ginin wasu shaguna da akayi kusan qwara ashirin jere da juna yafara tonon wajen tana turesa sai ya tashi yaje yaci gaba da tono wajen ita kuma ta sake turesa haka sukayi tayi yana tonon wajen tana hanasa, can yaga kamar wata bulala daga sama ta sauko a laftawa Inna ruqayya ajiki tafad'i awajen some shi kuma yaji sautin muryar da bazai iya tantance kowaye ba ance yaci gaba da tono wajenne zai cimma maganin da yardar ALLAH.

Firgigit sai ya farka daga baccin da yakeyi yaga ashe mafarkine yakeyi amma aransa yatabbatar da wannan wajen da akace ya tone shine inda suka binne maganin, bako shakka isharace akeyi masa kuma da yardar ALLAH kome zai faru yau sai ya tone wajen, goge zufan da yabi duk ya jiqe masa jiki ya shigayi yana karanto addu'o'i a bakinsa don mafarkin yamatuqar tayar masa da hankali, gashi lokacin qarfe uku nadare balle yaje ya sanar da d'an uwansa, dole ya haqura yakoma ya kwanta yanata istigfari da hailala da kuma tasbihi daga kwancen da yake har aka kira sallar asuba, yana jin baffa Usman ya qwanqwasa masa qofa ya amsa tare da jawo iccensa (crutch) wanda yake dogarawa yamiqe yanufi bakin qofar yabud'e yafitoa.

Bayan angama sallar asuba ya zauna masallaci yayita tasbihinsa har rana tafito sannan yanufi gida, yana kaiwa bakin qofar gida ya tarar da baffa Usman shida baffa suna magana wacce akan d'an uwannasu ne baffa Usman yake roqon yayi haquri ya yafe masa, nan yafad'a masa cewa tun ranar da abun yafaru ya yafe masa amma baya buqatar alaqar komai tahad'asa dashi ko shekara nawa za'ayi har sai sun warware qullin da sukayiwa Nuraddeen.

Baffa Ali na kawowa baffa ya miqama baffa Usman hannu sukayi sallama yabar wajen tun kafin ya ida qarasowa, binsa kawai yayi da kallo sannan ya qaraso wajen ya miqawa baffa Usman hannu suka gaisa fuskarsa cike da damuwa, ganin haka ya shiga kwantar masa da hankali har yake sheda masa cewa ai d'an uwan nasa ya yafe masa dama yafad'a masa b'acin raine yasa yayan nasu fushi dashi har ya d'au matakin daya d'auka akansa, gashi yanzu ya sauko abunda kawai yarage sukoma su rarashi Inna ruqayya tahaqura hakan shine zai ida daidaitawa tsakaninsa dashi.

Baffa Ali yajima yana zubarda qwalla kafin ya d'ago kai ya sanarda baffa Usman labarin mafarkin da yayi jiya had'e da cewa.

"Na tabbata wajenne Usman kuma zanje na tono wajen in Sha ALLAH, roqona d'aya agareka idan nura da Rashida sun dawo kace su yafemun, suyafemun abunda nayi masu, nayi nadama sosai, bansan abunda zai faru ba, zan dawo koko ta ALLAH zata kasance akaina."

Duk inda jikin baffa Usman yake yau saida yayi sanyi sosai, yamatuqar ji tausayin d'an uwan nasa domin gaba d'aya ya sare ma rayuwarnan ta duniya, yayi tuba taubatan nasuha tare da miqa wuyansa gaba d'aya,

Qarfafa masa yayi tayi sannan yace sushiga cikin gida su, bayan sun gama karyawa sukayi arwala tare sannan suka nufi wajen tono inda maganin yake,

Gaba d'aya zuciyar baffa Ali ta dake haka ya dinga shiga cikin juji har suka isa bayan shagunan, runtse idanuwansa yayi don yatuno daidai wajen kamar yanda ya gani a mafarki sannan yabud'e a hankali yanaci gaba da taku har ya isa wajen, kallon baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Kaga wajen nan in Sha ALLAH.."
Chapter 137 · 0% Book details