← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 160

Sashe 15

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'ok'arin maida hawayen da suka zubo mata tayi tare da ciro zanenta dake rataye ajikin k'usa ta d'aura sannan ta yafo towel d'in da tashiga dashi yarufe mata daga samn kai zuwa qirji tafito kanta na sunkuye qasa tawuce d'akinsu,

Kallo suka bita dashi kafin baba yace "ALLAH ya kyauta, ni bari inje muyi magana da balarabe yana waje yana jirana.!"

"Shine bakace ya shigoba zaka barshi zaune awaje sekace wani baqo"

"Bari dai natafi kije ki ajiye kud'innan idan nadawo ma k'arasa maganar."

"To ALLAH ya kiyaye kuma yasa adawo lafiya, ka gaidashi"

Yana fita itama Rashida tafito saye da hijabinta na islamiya tace "umma natafi" batare da tabari sun had'a idanuwa da ita ba don kada ta fahimci halin da take ciki,

"To adawo lafiya" itama tabata amsa atak'aice, sannan tamik'e tawuce cikin d'aki.

Rashida kam tana cikin yanayin da ita kanta batasan taya zata fassarashi ba, karatu akeyi amma tayi zaune tahad'a tagumi tana tunani, gashi dai auren da takeso za'a yimata amma damuwarta d'aya shine yanda alokaci guda soyayyar da malaminta ya dasa azuciyarta cikin kwana biyu tayi tasiri aranta har tana tunanin yanda zata iya auren wani idan bashi ba, ji tayi tafashe da kukan da batasan lokacin da yazo mata ba saidai taji malami na fad'in

"Ke Rashida me yake damunki ne?" Firgigit tadawo cikin hayyacinta tana zarar idanuwa had'e dasa hannuwa tana goge hawayen da suka zubo mata,

"Mik'e tsaye." Taji ya sake fad'a tare da nufo inda take riqe da bulala, mik'ewa tayi da sauri tana runtse idanuwanta don duk duniya babu abunda ta tsana kamar a tab'a mata jiki da sunan duka,

"Me kike tunani!"

"Babu malan" tafad'a atsorace har lokacin idanuwanta na arufe, har zai dukanta sai kuma ya qyaleta had'e da cewa tafitar masa daga aji, maimakon tabashi hak'uri kawai sai taja jikkarta tafice daga dama tun d'azu hankalinta baya wajen balle ta fahimci karatun da yakeyi, acan bayan wasu azuzuwa taje ta zauna, ta d'ora daga inda ta tsaya ga tunanin da yakeyi, Bata bar wajen ba har sai da taga antashi sannan tabi sauran d'alibai suka wuce gida,

Tana isa gida ta isko umma na waya da 'yan uwanta dake borno akan zancen aurenta tana fad'a masu ai har ankawo mata sadaki an kuma sa ranar aurenta nan da sati biyu hakan yasake dagula mata lissafi tawuce d'akinta da sauri, kasancewar dama tana fashin sallah yasa batabi takan kiraye kirayen sallar magrib da akeyi ba tayi kwancenta, ita kuma umma kota kanta batabi ba tad'auki butarta tayo arwala sannan tawuce d'aki ta tayar da sallah.

Can misalin qarfe tara nadare bayan baba yadawo sun gama tattaunawa da umma sannan yayi mata bayanin cewa ai bayan sun gama dubiyar da sun kajene aminin nasa ya bijiro da maganar nemawa d'ansa auren Rashida ashe cikin ikon ALLAH ganin da yake yimata a makaranta yaji yana sonta tun kafin inyi masa magana sae gashi yafad'awa mahaifin nasa cewa ya nema masa aurenta." nan dai ya fayyace mata yanda komai yafaru, ajiyar zuciya tayi had'e da cewa "Alhamdulillah, aini sai yanzu nasamu natsuwa, amma tunda kabarni nake wasu wasin wannan al-amarin tare da taraddi jin kace nan da sati biyu za'ayi auren, amma yanzu Alhamdulillah, ALLAH yatabbatar mana da alkhairi, naji dad'i kuma nayi farinciki sosai ai malan idi mutumen kirkine da kowa zaiyi sha'awar had'a zuri'a dashi, ubangiji ALLAH ya bashi lafiya kuma yasa ayi munada rayuwa."

"Amin ya rabbi, ai don ma bakiga yaron ba, ALLAH dai ya tabbatar da alkhairi, tashi kije ki kirawomun ita" cike da farinciki umma tanufi d'akinta ta tsaya abakin k'ofa tana fad'in "Rashida, Rashida.." jin bata amsa ba yasa taqarasa cikin d'akin, kwance ta hangota saman katifarta, kallo d'aya tayi mata tasan da cewa ba bacci takeyi ba kawai idanuwan natane kad'ai a rufe, matsawa jikin katifar tayi had'e da cewa,

"Ke Rashida lafiya kikekuwa?" Firgigit tabud'e idanuwanta had'e da saukar dasu akan nata, "lafiya kike?" Tasake maimaita mata akaro na biyu, qoqarin miqewa zaune tayi had'e da sauko da k'afafuwanta k'asan katifar sannan tace,

"Umma kainane yake yimun ciwo."

"Ashsha shiyasa yau najiki shiru tunda kika dawo makaranta baki fito ba balle kid'auko abincinki kici, daure kitashi mahaifinki nakira inyaso daga can sai kici abinci kisha magani kinji ko" Kai tad'aga mata ita kuma tajuya tabar d'akin tana fad'in

"ALLAH yasawaqe ciwon kai kam ai babu dad'i"

Ko minti biyu umma batayi da zaunawa ba Rashida itama tashigo cikin d'akin tajawo hular hijab d'inta ta lullub'e mata rabin fuskarta tanemi gefen qofar d'akin daga ciki ta zauna, "Baba ina wuni andawo lafiya?" Tafad'a tana gyara hular hijabin zuwa kanta."

"Lafiya klw Rashida, lafiya kike kuwa?" Kafin tace wani abun umma tace

"Au kagafa na manta infad'a maka ba tajin dad'i, na iskota kwance shine dana tambayeta take fad'amun kanta ke ciwo don tunda suka dawo islamiya banga tafito waje ba balle ko abinci tasamu ta d'auka taci."

"Subhanallahi, injin to da sauqi" yafad'a yana kallon Rashida

"Eh da sauqi baba," tafad'a tana goge zufa a goshinta, wani d'an guntun tsaki yaja had'e da cewa

"Matsalar ku kenan mata baku fiye kula ba wani lokacin, shiyasa ake ganin sakacinku yayi yawa ace mutum nada d'a yaga yayi awa kusan biyu a d'aki bai fitoba kuma bazai je yaduba halin da yake ciki ba sai mai faruwa tafaru kaji ana fad'in ai kuwa tun d'azu najishi ko najita shiru ad'aki ashe kaza da kaza yafaru bamu sani ba, to meye amfanin hakan? Kin jita shiru amma kin kasa dubota kiga ko lafiya take sai yanzu da nace ki kirawota, ALLAH ya kyauta"

"Ayi hak'uri malan in sha ALLAH za'a dinga kula"

Hannunsa yamik'a gefensa a qarqashin pillow dake kan gadon ya d'auko kud'in da yakarb'a a hannun umma ya mik'awa Rashida had'e da cewa,

"Ungo wannan ki k'irgamun su nawa ne?"

Mik'o hannunta tayi yana makarkata ta karb'a sannan tafara k'irgawa d'aya bayan d'an shi kuma yana kallonta, saida tagama sannan ahankali ta d'ago kanta tace,

"Dubu ce guda hamsin" murmushi yayi had'e da cewa, "ban fahimta ba"

"Ina nufin naira dubu ce sau hamsin " girgiza kai yayi cike da takaicin dubu hamsin ma 'yarsa bazata iya fad'a daidai ba, wannan wane irin rayuwace, kallonta yayi yanaji kamar ya maketa kafin yace,

"Rashida kenan, ai bahaka ake fad'aba, naira dubu hamsin zakice a hausance kinji ko?."

'Daga masa kai tayi tare da sake mik'a masa kud'in,

"A'a kiriqesu a hannunki, nakine mallakinki duniya da lahira" d'ago kai tayi tana kallonsa cike da alamar tambaya atattare da ita,

"Eh, kud'in kine na sadaki da aka bayar kuma a musulunce bai halatta kowa yayi amfani dasu ba idan ba keba koda kuwa mune saboda hak'k'in k'ine shiyasa na hannunta makisu a hannunki duk abunda kike so kiyi dasu, mudai munfita hak'k'inki koba haka ba?" Yaqare maganar yana kallon umma, jinjina masa kai ita Kuma tayi alamar tabbatar da zancensa.

Muryarta na rawa tace "Babu abunda zanyi dasu baba don ALLAH ku karb'a umma"

"A'a kirik'e hannunki abunda babanki yafad'a shine daidai kinji ko?"

"Umma nifa babu abunda zanyi dasu, baba.." dakatar da ita yayi had'e da cewa, zaki iya ba ummanki ta ajiye maki, tashi kitafi ALLAH yayi maki albarka"

Mik'awa umma kud'in tayi sannan tamik'e zata fita, har ta aza k'afarta abakin k'ofar mahaifin nata yace,

"Rashida bazaki tambayi ko wanene na zab'a maki ba?"

"A'a baba, babu buqatar hakan domin nasan bazaka tab'a yimun zab'in daba daidai ba." Tana gama fad'ar haka tafice idanuwanta na hawaye, tabbas tasan takamu da soyayyar malaminta amma bazata iya yiwa mahaifinta musu ko kuma gardama akan zab'in da yayi mata ba, kawai zatayi k'ok'ari ta yakisheshi aranta kafin lokacin auren.

Shikuwagogan naka matsuwa yayi safiya tawaye yaje makarantar saboda yaga sahibarsa, wacce ke Shirin zamowa matarsa kuma uwar 'ya'yansa, cikin daren yaje yasiyo mata waya k'irar tecno L7 saboda ya dinga jin muryarta duk da dai gaba d'aya wannan satin zai ganta har yagaji.

Tunda sassafe yatashi yayi wanka sannan yaje wajen mahaifiyarsa ya gaisheta tare da cemata zai wuce, ciki ciki ta amsa mata saboda fushin da takeyi dashi akan zaije ya auro masu bare, cikin sanyin murya yace,

"Inna har yanzu fushin kikeyi dani?"

"Ai dole inyi fushi da kai nura zaka jawo mani abun kunya."

"Kiyi hak'uri inna da kin fad'amun tun farko bakyason in auro maki bare agidan nan da bazanyi ba, amma yanzu kinga su baffa sunyi magana bai kamata ace anwatsa masu qasa a idanuwan duniya ba."

"Aiho shiyasa ni kuma aka watsamun qasar, shikenan tashi katafi."

"Taya zantafi inna fuskarki ahaka, kiyi hak'uri don Allah kiyafemun, natabbata idan kikaga yarinyar kema zaki sota kamar yanda nake sonta" Saida ta sheqe da wata dariyar shaqiyanci kafin tace,

"ALLAH natuba kayafemun ni hawwa, ai har abada bazan sota ba, kaidai tashi katafi ALLAH yatsare hanya."

Jikinsa ya matuqar mutuwa dajin kalamanta amma babu yanda ya iya saboda ALLAH shine shedar yanda take jin soyayyar yarinyar bazai iya rabuwa da ita ba, fatanshi dai ALLAH yasawa inna sonta kamar yanda yake sonta,

"Me kake tunani haka!" tafad'a a d'an tsawace da yasashi saurin mik'ewa tsaye yana fad'in

"Natafi."

"Adawo lafiya," tafad'a tare da mik'ewa ta rakosa har bakin qofa.

Adaidai bakin k'ofar fita gidan bayan yaje wajen mahaifinsa shima sun gaisa yafad'a masa zai wuce ya had'u da qannen mahaifin nasa baffa Ali da baffa Usman kamar yanda suke kiransu, duqawa yayi har k'asa ya gaishesu, baffa Usman ne yafara amsa masa kafin baffa Ali dake gugar bakinsa da ashuwaki ya tofar da yawu agefe yace,

"A'a malan nura zaka tafi"

"Eh baffa Ali nama yi latti sosai yau gashi inada daraai qarfe takwas naga har bakwai da rabi tayi"

"Eh gaskiya kama tashi katafi, ALLAH yatsare hanya."

"Amin baffa Ali nagode."

Har yafara tafiya yakira sunansa ya juyo zai dawo inda suke yace

"A'a basai kadawo ba, cewa nayi to adai kula kasan halin mata kar ake kabiyewa shashancinsu suhanaka yin abunda ya kaika kaji ko?" Shiru yayi yana nazarin kalamansa kafin yace, "to baffa Ali in Sha ALLAH." Sannan yawuce cikin sauri.
Chapter 15 · 0% Book details