← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 160

Sashe 93

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tirqashi! Tabbas 'yata kunkoma ga Wanda kad'ai ya isa yabaku kuma yabaku, ubangiji ALLAH ya inganta yabaki rayayyi masu albarka, albarkacin miqa wuyan da kukayi agaresa."

"Amin ammie nagode."

'Dan hararta ammie tayi akn godiyar data yimata, dariya tayi had'e da cewa.

"Natuba ammienmu kiyi haquri."

"Shikenan, ammafa kada kiqara."

"Baran qara ba ammie.."

"Shikenan addu'o'in nakirata taturo akarb'ar mata?"

"Eh ammie, tun yanzu Zaki aika mata?."

"Eh mana, ai qara abugi qarfe da zafinsa."

"To ammie ALLAH yasa adace, Amma ammie kice tayi duka addu'o'in cike da yaqinin cewa ALLAH zai karb'a mata, kinsan yana d'aya daga cikin abubuwan da kesa ubangiji ya gaggauta amsar addu'ar bawa idan yayita da yaqini."

"Ai zama tayi 'yata saboda akullum batada burin da yafi wannan, kinga kuwa dole zata dage, bari naje nadubo maki abinda kikace kina so." Ammie tafad'a tare da linke takardar ta ajiye akan madubi sannan tabar d'akin, miqewa tayi had'e da shafa cikin nata dako motsi bai fara ba tayi murmushi, gaba d'aya ganin ranar takeyi kamar mafarkine takeyi sannan itama tabi bayan ammien.

Rashida kuwa koda ta isa baba na qoqarin shiga mota har lokacin little na ahannunsa, qarasawa tayi wajen baba yamiqo matashi, har tamiqa hannu zata karb'esa cike da zolaya yaja baya dashi yana fad'in. "Bazaki bari naje dashi ba nakaishi wajen kakansa, nasan zaiji dad'in ganinsa fiye da irin dad'in da mukaji."

Murmushi Rashida tayi had'e da cewa.

"Shikenan baba, kaga nida ummata dasu ammie mun huta da fitinarsa, sai yaje can yad'an tab'awasu baffa da inna Bilkisu suji yanda mukaji."

"Wai hakane mai sunan babansa?." Baba yafad'a yana kallon little dake faman tafi da hannuwa yana kallonta, dama Dr nura naganin taqaraso wajen yad'an basu waje yana amsa waya, maida kallonsa baba yayi ga Dr da har lokacin wayar yakeyi ya basu baya sannan yace.

"Rashida don ALLAH ku kula da bayin ALLAHn nan, mutanene masu karamci da halacci, duk abunda suke so kufisu sonshi wanda kuma basa so to kifisu qinsa, inaso kiriqesu tamkar mu da muka haifeki kuma ki kyautata masu iya qarfinki hakan zaisa kirage wata kunyar hidimar da suka yimana kinji ko.?"

"In Sha ALLAH baba, ALLAH yasa kaje lafiya kadawo lafiya."

"Amin ya rabbi, ALLAH yayi maki albarka dake da duka zuriar da zai baki." Yaqare maganar yana shafa kan little had'e da miqa mata shi yana murmushi.

A daidai lokacin Dr yadawo fuskarsa cike da walwala ya shafa kan little had'e da cewa.

"Takwara nazata dakai baba zaije?"

"Yawwa uncle don ALLAH kuje dashi shima yarakashi."

Karb'arsa yayi yayi sannan yashiga cikin motar yarufe gambun yana qoqarin tada motar tace.

"Laaa...uncle congrat, little yakusa samun qane, ALLAH ya inganta uncle yabamu rayayye mai albarka nima narama abunda ake yimani akan d'an wasu."

Batare daya kalleta ba yana key d'in motar yace.

"Amin ya rabbi, Thank you so much maman baby, amma ko kunrama bazaku iya ramawa ba kamar yanda muka yimaku ba ko takwarana?"

Da haka yatada motar had'e dayin ribas ya juya motar suka fara tafiya, binsu tayi tana d'agama baba hannu shima yana d'ago mata har suka fita, haka kurum saita tsinci kanta da fashewa da kukan da batasan dalilin yinsa ba, Saida ta tsaida kukan sannan tajuya tanufi sashen na ammie, umma tahango jikin qofa tsaye itama taqurawa gate d'in idanuwa tana mai addu'ar ALLAH ya saukeshi lafiya,

"Umma ya nagaki a nan tsaye?" Rashida tafad'a jikinta ba qwari.

"Wlh Rashida nidai tafiyannan tashi bata kwantamun ba, daya bari har sai an kwan biyu tukuna tunda muma jiyan nan muka fita alhinin rashinki.?"

"Kai umma, ki kwantar da hankalinki in Sha ALLAH zaije lafiya kuma yadawo lafiya."

Rashida tafad'i hakan saboda takwantarwa da umma hankali don ita kanta tanajin ba dad'i akan tafiyar tasa.

Dr nura bai baro tasha ba har saida yaga motarsu baba nashirin tashi sannan yanufi inda motarsa take, da sauri yajuyo ya tsaida motar had'e da leqawa tagefen tagar da baba yake yace.

"Baba akwai waya a hannunka nasa maka lambata idan ka isa saika sanar damu don hankalinmu ya kwanta."

"Likita kenan! ai inada lambarka tun satin can da alhaji yasaya mani wayar ya saka mani ita, in Sha ALLAH da zaran na isa zankiraku."

"To shiken baba, amma ka kirani sai inga lambar taka nayi saving tunda banida ita."

Nanfa fasinjoji suka fara suruttai suna qorafi akan suna b'ata masu lokaci amma kota kansu Dr baibi ba har saida baba yakirasa yaga lambar sannan yabar wajen, Saida yaga motar tasu tawuce sannan shima yaja tasa ya nufi gida.

Ba'afi mintuna talatin da isar Dr gida ba saiga kira ya shigo ga wayarsa, lokacin duk suna zaune kan dining table suna lunch yana faman jinini wai ammie tabiyewa Fatima anyi masu eba kuma shi baya sonta, ita kuma ammie tace dole yacita don ita kad'ai tadafa kuma bazaibar gidan da yunwa ba, hakan yasashi tusa abincin yana wani b'ab'b'ata rai da kumbura fuska sunata yimasa dariya, ganin wayar tasa naruri yaqi d'agawa yasa dady tsaida dariyar tasa had'e da cewa.

"Sorry son, qyale dota da ammienka, zamu rama kaji ko."

"ALLAH dady babincinnan na garin kwaki bayada dad'i ko kad'an, ci kawai nakeyi badon Ina so ba."

"Ajiye hakanan, kad'aga wayar da akeyi maka tun d'azu." Kallon wayar tasa dake famn ruri akaro na uku yayi had'e da qoqarin d'agawa yana fad'in.

"Kai, Ashe baba ne ke kira tun d'azu, Assalamu alaikum, Eh nine, eh, yanzunnan fa ta tashi"

"What?" Yafad'a da qarfi yana turo idanuwansa had'e da miqewa da qarfi.

Hakan yasa su dady sakin cokullan dake hannunsu suna kallonsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun."

Shine abunda Dr keta nanatawa kafin yakalli dady dake tambayarsa ko lafiya yace

"Dady wai motarsu babace tayi had'ari acan qauyen dake kan hanya idan anfita gari kad'an."

Gaba d'aya sukasa sallami da sauri ammie tariqo hannun Fatima tayi d'aki da ita had'e da kwantar da ita kan gado tace.

"'yata kinkwantar da hankalinki, kinsn yaron ciki kejikinki in sha ALLAH Babu abunda yafaru."

Koda ammie tafito har dady da Dr sun fita.

Sallallami tashigayi tana zagayar falo batare da tasan mezata aikata ba alokacin.

Gaba d'aya su dady basuyi wta doguwar tafiya ba suka cimma inda akayi had'arin ashe suna fita daga cikin garinne sukayi karo da wata qaramar mota garin drivern ya kauce mata motarsu tayi cikin daji takife, kasancewar lambar Dr nura itace ta qarshe da baba yakira yasa lokacin da aka ciccirosu aka sami wayar ajikin baba da ko qwarzane baiyi ba amma rai yayi halinsa, kallo d'aya zaka yiwa gawarsa kasan mutumen kirkine saboda wani irin haske da qyalqyali da fuskarsa kefitarwa.

Suna isa suka isko an jejjere gawarwakinsu agefen titi da sauri suka isa wajen, tsabar yanda hankalin dady ya tashi saida jiri yad'ebesa yayi baya baya zai fad'i Dr ya tarosa, gefe ya zaunar dashi sannan yanufi wajen 'yan sandan dake tsaitsaye suna korar mutane yayi masu bayani tare da nuna masu gawar baba dake kwance an lullub'a masa ganyen bedi akai ya nuna masu i.d card d'insa ta asibiti, suna tsaye motar asibiti ta iso aka kwashi gawawwakin kusan mutun uku wud'anda suka rasu biyar kuma sun samu raunuka, bayan motar su dady sukabi zuwa asibiti akayi 'yan bincike binciken da za'ayi ma gawawwakin da zai tabbatar da cewa mamatan sun rasu sukuma wud'anda suka jimu akayi masu treatment sannan akabasu dady gawar baba sukayo gida da ita,

Baqaramin tashin hankali su baba balarabe suka shiga ba lokacin da saqon rasuwar d'an uwan nasu ya isa garesuba, yayinda Yaya Maryam tadinga sabbatu tana fad'in.

"Ba gaskiya bane, jiya mungansa, munhad'u dashi, munyi magana, mun yi fira da maganganu masu tsayi dashi, wara haka duk muna tare dashi taya za'ace yamutu, inaa banyarda ba, bashar bazi mutu yanzu ba bayan jiya jiya muna tare dashi, ya ALLAH kasa wannan zancen ba gaskiya bane, bashar mutumen kirkine, baikamata ace yamutu yanzu ba.." haka tayita sabbatu tana kuka har saida aka dinga rufe mata baki.

Nan take baba balarabe da mijin yaya Maryam da wasu 'yan uwansa sukayi mota d'aya babba suka d'auki hanya cike da alhini.

Duk da baba baifi shekara d'aya da watanni acikin garin borno ba babu inda mutuwarsa Bata kaiba, kuma duk wanda yab'ud'a baki fad'ar mutuncinsa da alkhairansa yakeyi,

Umma kuwa da Rashida gaba d'aya sun fita hayyacinsu saboda sumar da sukayi, koda suka farfad'o itadai Rashida bata cewa komai si hawaye dake zubar mata tana kallon ammie da Fatima dake faman basu baki.

Umma kuwa miqewa tayi tace akaita inda gawarsa take tana so taganesa, rirriqeta ammie da maqwabtanta da suka shigo sukayi suna fad'in don ALLAH tayi haquri kada take, ganin haka yasa Rashida tasowa tace.

"Ammie don ALLAH kubarta taje."

Matsowa tayi takama hannun umma tace

"Umma zaki iya ganinsa."

Kad'a mata kai tayi tariqe hannunta suka nufi wani d'aki dake gefen sashen ammie da alama d'aya daga cikin d'akunan dasu Dr sukayi zamane, suna kawowa zasu shiga faruq qanen dr yahanasu.

"Don ALLAH kuyi haquri idan bazaku iya ba." yana qara tare bakin qofar idanuwansa cike da qwalla, duk da shi bai fiye shiga shirgin mutane ba saboda haka yake kamar yanajin warin mutane shiyasa baya mu'amala da kowa, amma duk da haka yana mauqar shiri da baba sosai don acewarsa shi mutumne nadaban ko acikin mutane, tasowa Dr yayi yasa hannu yajaye faruq gefe yana fad'in

"Umma kushiga matuqar hakan zai rage maku rad'ad'i arai, saidai Ina so kutuna, ba'ayiwa mamaci kuka irin na jahiliya balle ga irin baba da mukeyiwa kyakkyawan zaton cewa ya dace."

Yana gama fad'ar haka haka yad'an ja da baya yabasu hanya yana goge hawayensa, suna shiga sukaga baba kwance anlullub'esa, da sauri Rashida tarirriqe umma tana kuka tare da toshe bakinta.

Duqawa umma tayi daidai fuskarsa tayaye lulub'in da aka rufa masa, ayanda taga fuskarsa tayi haske yaqara kyau tamkar yana dariya duk da tana cikin rad'ad'in mutuwarsa yasa tayi farinciki sosai.
Chapter 93 · 0% Book details