← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 160

Sashe 143

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Abbana shikenan bazan zoba.."

Tafad'i haka cikin muryar dake nuna hakan baiyi mata dad'i ba, d'an sassauta muryarsa yayi cikin sigar lallashi yace.

"Sorry my dota kinji ko, kinga cikinki ya tsufa bai kamata ace kinyi doguwar tafiya ba, ki zaunawarki gidanki in sha ALLAH ni da kaina zanzo nadubaki."

"To Abbana Amma meyasa?"

"Bakomai, ina shi mijin naki." Yafad'i hakan don yabasar da maganar saboda baya son tayi masu tsawon da dole sai tasa ya amince mata da tazo d'in.

Miqawa little wayar tayi tare da tashi tabar wajen tana kuka, meyasa abbanta zai hanata zuwa alokacin da take son ganinsa, halama ya manta da tsawon shekarun data kwashe tana jiran ganin wannan ranar? Kodai wani abun yafaru agidan da ba'aso tasani shiyasa abbanta saukowa daga fushin da yakeyi da ita?, gaskiya akwai boyayyen al'amarin dake faruwa da bata san dashi ba, badon haka ba yakamata ace shima zaiyi farinciki idan taje tunda yana son ganinta, wud'annan tambayoyin da wasuwasi ta dingayi azuciyarta tana kuka har zuwa lokacin da little yagama waya da Abba ya biyo bayanta,

Sosai little yayi farinciki da zuwan wannan ranar da hawayen gimbiyarsa zasu dena zuba saboda kewar mahaifinta kuma yaji dad'in yanda mahaifinta ya nuna masa ba komai yanzu aransa akan auren 'yar tasa da yayi ya fahimci abunda ada yakasa fahimta kuma ya roqesa yafuwa tare dasa masa albarka sosai....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_i will like to extend my gratitude in dis page to you my dear sister, *FATIMA UMAR ANKA (MOMYN J)* you're truly among the most important people i have ever gotten in my life, you're such a kind and very nice person dt i will never be able to forget, you did so much things to me sister!, the way you care, luv, respect, advice and so on to me is beyond the expected, all I pray, is ALLAH to protect you, guide you, luv you and take very good care of you every where you are, may he hills all your worries and put so many smile on your face, give you what ever you want in dis dunya wal akhira and make his jannatul firdaus to be your finale abode👏, thank you so much sister, FILLAH am rilly luv you more than how words can say😍_

Page___100💎

Yana shiga d'akin batool ta sake fashewa da kuka sosai ta yanda duk yanda yaso rarrashinta bazai iyaba, gaba d'aya tabi ta tayar masa da hankali, tun yana d'aukar abun zata gaji tagama har ya fahimci da hasken gaske takeyi bazata dena ba, hakan yasa ya d'auki wayarsa yakira mahaifiyar tasa ya sanar da ita halin da ake ciki, ita da kanta ta tabbatar da hakan lokacin da suke waya don tanajin sautin qarar kukanta, don haka tace masa yabata mintuna gatanan tafe.

Ajiye wayar yayi gefe had'e da komawa inda take kwance idanuwanta sunyi lutulutu saboda kukan data dad'e tanayi ga fuskarta gaba d'aya tayi jajir abunka ga farin mutum, d'agota yayi tare da rungumota ajikinsa har lokacin tana kuka yace.

"Gimbiya wai meyene haka!, Kina son jefa kankine keda babynmu cikin wani yanayine da bazaki haqura kidena wannan kukan hakan ba?, Ko kina so ne kiyiwa ALLAH butulci bisa baiwar da yayi maki ta juyo da hankalin mahaifinki akanki a lokacin da baki tab'a tsammaaanin hakan ba?, Ko so kikeyi ni kijefani cikin damuwa saboda kawai natsani ganin kukanki?"

"Ni Ina son kawaine inga Abbana, karka manta wannan kukan bashine karo nafarko ba da nakeyi akan mahaifina, idan har zanyi kuka alokacin daya yimani kashedin zuwa inda yake make tunani idan aka hanani zuwa alokacin da da kanshi yabani damar zuwa wajensa?, don Abu sumayya ka kaini wajen Abbana Ina son ko sau d'ayane na sake ganinsa kafin ayimun wannan aikin! Ina matuqar kewar abbana sosai." Ta sake saka mashi wani kukan had'e da tusa kanta cikin qirjinsa.

A wannan karon kasa cewa komai yayi don tabbas yasan tanada gaskiya, musamman daya tuna shekarun data d'iba bata ganesa ba bayan tsananin shaquwar dake tsakaninsu, wani irin tausayinta ya rufesa tare dashi kansa da tunda yazo duniya sau d'aya yatab'a ganin mahaifinsa shima d'in ga tv ne bawai a zahiriba, bubbuga bayanta ya shigayi a hankali alamun rarrashi amma kamar yana qara cewa tayi kukan, bai tab'a sanin haka batool d'insa take da rigima ba sai yau, gaba d'aya tazame masa stubborn tayanda bama zai iya shawo kanta ba,

Sallamar mahaifiyar da yaji tasa sashi saurin cire batool d'in ajikinsa da sai faman reren kukanta takeyi ko gajiya batayi.

Da sauri yaje ya tarbota daga bakin qofar falo da take qoqarin shigowa tana fad'in.

"A'ah, a'ah Fatima har yanzu kukan kikeyi baki daina ba?, Subhanallahi meyayi zafi haka kekuwa?, Nan da lokacin da Zaki haihu ai kamar gobene ga ALLAH, don ALLAH kiyi haquri kidena wannan kukan hakan."

Rashida ta qare maganar tana qoqarin zaunawa kusa gareta.

Gaisheta little yayi ta amsa tare dasa hannuwa ta d'ago batool, yanda take kukan baqaramin tayar mata da hankali yayiba musamman da taga yanda fuskar tata tayi ja had'e da kumbure sundul.

"Ya Salam maman biyu, yau kece ahaka?, Kiyi haquri ni ban sanki da haka ba ko so kikeyi kitayar mana da hankali?"

"To yi shiru kinji ko, ya isa haka, wannan kukan naki bana sonsa yana d'aga mani hankali"

Tafad'i hakan tana share mata hawaye tare da d'ago fuskarta, "kinga yanda idanuwanki suka kumbura kuwa fatima?, Ai mugode ALLAH tunda har abban naki ya haqura ya sauko, kinga inda rabo bayan kin haihu ai zaku gana ko?"

"Gwaggo idan namutu wajen haihuwar fa?, shikenan narabu da Abbana kenan na har abada?, Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun gwaggo don ALLAH kubarni inje inga Abbana tunda haihuwar nan da sauran lokaci.."

Batool tafad'i hakan cikin wata irin disashshiyar muryar da ko fita batayi da kyau saboda kukan da takeyi.

Shiru Rashida tayi tana nazarin maganarta kafin can taji tariqo hannuwan biyu tare da durqushewa gabanta.

"Gwaggo inajin wani abu mai tsananin rad'ad'i yana kokuwa da lumfashina saboda son ganin Abbana da nakeyi, nasan irin yanda kika damu dani da d'awainiyar da kikeyi akaina a matsayinki na uwa kuma nasan bazaki gaza fahimtar irin kewa da shauqin dake tattare dani na son ganin mahaifina ba aduk tsawon shkarun nan da suka shud'e, a yau Ina roqonki daki amince mani kibada damar da zata saka nahad'u da mahaifina ko sau d'ayane kafin lokacin dazan haihe abunda ke cikina, nasan koda ta ALLAH tafaru kaina alokacin kunyimun alfarma mafi girma arayuwata."

Kallon little daya noce kai qasa hawaye na zubar masa Rashida tayi, tabbas tasan yau shima dole yatuna da nasa mahaifin wanda ko shakka babu ta tabbatar shi yasashi zubarda qwalla.

Cikin sanyin muryar dake nuna itama zuciyarta tagama karyewa tace.

"Shikenan batool, tashi ki goge hawayenki kije ki watso ruwa, ni zantafi nabar 'yan biyu su kad'ai ad'aki suna bacci kada su tashi suyimun b'arnar daba daidai ba, zanyi tunani akan haka kafin anjima kinji ko."

Taqarasa maganar had'e da dafa kanta sannan tamiqe, d'ago kan da batool zatayi sai taga itama kukan takeyi da sauri tace.

"Don Allah gwaggo kiyi haquri Idan na b'ata maki rai..."

"Ko d'aya Fatima, kije kiyi abunda nace kuma ki tabbata kinci abinci kuma kinsha maganinki."

Tana gama fad'ar haka tajuya tafita tana sharar qwalla, yau little ya matuqar bata tausayin da tana buqatar taje tayi dogon nazari koda dangin mahaifinsa ne tahad'asa dasu, idan ma zai iya daga dubu d'ari har zuwa ko nawane zata bashi yaje koda qasar da mahaifinsa yazab'i zamane ya dubosa, tabbas tasan shi yarone mai matuqar biyayya da haquri badon haka ba da tuni shi da kansa yafara neman sanin yanda zai binciko mahaifinsa.

Da yake da drivern gidan Dr tazo bata jira fitowar little ba ta shigewarta mota suka nufi gida zuciyarta namai qarfafa mata akan abunda ta quduri yi,

Little kam gaba d'aya baima san fitar taba balle yabiyota baya har saida batool ta tab'asa yayi firgigit tare da fitowa daga dogon tunanin d'aya shiga yana goge hawayen idanuwansa.

"Gwaggo fa ta tafi!"

Da sauri yamiqe yafita amma koda yaje har motar data kawota ta jima da fita ya juyo yadawo cikin gida jikinsa sanyaye.

••• ••• •••
Tuni baffa da baffa Usman suka iso gida da gawar Inna ruqayya, 'yan uwa da abokanan arziqi sai kuka sukeyi musamman idan sukaji ta hanyar data mutu, muneera kam da sauran 'yan uwanta kam sunsha kuka har sun gaji, ba'a maganar Yusuf da alokacin yana makaranta yana zana jarabawarsa ta qarshe, saida su baffa suka yita bashi baki akan ya haqura ya zauna tunda zuwansa bazai iya canza komai ba, kuma zai iyasa ya rasa damarsa awannan shekarar sannan ya haqura amma yayi kuka kamar ransa zai fita da duk wanda yagani sai ya tausaya masa,

Yaya hawwa ma kuka tayitayi tana nema mata gafarar ALLAH tare da tausayin kanta da batasan lokacin da itama tata zata risketa ba, haka gida yacika anata koke koke, Inna Bilkisu da wata maqwabciyarsu su suka yimata wanka, sunga tashin hankali matuqa wajen wankan domin wani wari gawarta ta dingayi gashi duk inda suka taba ajikinta sai fatarta tabiyosu tamkar kazar da akasa ga wuta tanine, gaba d'aya jikinta ya zimame nan take saika rantse gawarta tayi kwanakkine tasoma lalacewa, haka suka samu suka lallab'a sukayi mata wankan suka yimata sutura kowaccensu hawaye kwance da fuskarta.

Haka aka d'auki gawarta akaje akayi mata sallah akaje kaita gidanta na gaskiya, ana saka gawarta akaga wani qaton maciji baqiqirin yafito daga qasanta tare da nad'id'iye gawar gaba d'aya, kan kace me kusan mutanen da sukazo wajen sun fice aguje saboda tsananin tashin hankali, baffa ne kad'ai da baffa Usman da wasu mutane qalilan suka tsaya, haka akayita qoqarin korar macijin har aka gaji amma yaqi fita daga qarshe baffa na hawaye yace.
Chapter 143 · 0% Book details