← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 160

Sashe 125

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye gidan dady aka nufa da amarya lokacin ankawo imana amaryar Shakur itama, haka dady da matansa da Dr suka had'asu tare suka yimasu nasiha, nan ma saida batool ta sakeyin kuka don ta tabbata tarabu da iyayenta kenan sai Kuma idan ALLAH ya sake had'asu in tatafi kosu in sunzo wajenta, bayan an gama masu nasiha hajia nafeesa tayi gyaran murya zatayi magana dady ya dakatar da ita had'e da cewa "kutashi kutafi ALLAH yayi maku albarka kuma ya zaunar daku lafiya da mazajenku yabaku 'ya'ya nagari."

Suna fita dady ya juyo ya kalli hajia nafeesa had'e da cewa.

"Karki kuskura koda wasa naji kin shiga hurumin yaran nan har sai lokacin da kikayi hankali.."

Su umma najin haka suka miqe ita da ammie sukabar d'akin don basuda alaqa da maganar da yake qoqarin yi, batare daya dakatar dasu ba yaci gaba da cewa,

"Ayanzu bakida wani iko akan batool tunda takoma qarqashin inuwar mijinta wato Nuraddeen, dama nafad'a maki cewa duk abunda zakiyi baki isa ki dakatar da qudurar ALLAH akan wud'annan bayin nasa ba domin yana tare dasu, to kinga ya nuna maki d'aya daga cikin ikonsa wanda da kinci gaba da tsaurarawa to da tabbas kin jawowa kanki matsowar ajalinki kusa don shi rabo Kashi yakeyi, sai maganar hafsat wato iman, ban yarda koda wasa wani abu marar dad'i ya shiga tsakaninki da itaba don tana auren d'anki, kitsaya matsayinki in ba haka ba tsattsauran hukunci zai biyo bayanki kinji nafad'a maki."

"Amma meye dalilinka na hanani yin magana amatsayina na uwar miji ga surukata da aka kawomun kuma agabanta bayan kowa ka barshi yayi magana? Wannan ai salon arainani ne da kuma cin fuska."

"To koma dai meye kinji abunda nafad'a maki don haka sai ki kiyaye kafin tab'atar mana ni dake."

Yana gama fad'an haka yafice ya samu su uncle Hussain awaje suka sake gaisawa tare da damqa masa amanar batool ahannunsu don tuni baffa da mijin yaya Maryam suna tare dasu tunda suka iso,

Ita dai iman gidanta aka wuce da ita, ita kuma batool gidan Dr aka nufa da ita inda Rashida, cike da farinciki Fatima ta taso ta tarbosu tana rungumota ajiki,

"Oyoyo takwarata, sannunku da zuwa kunsha hanya."

A mai makon Fatima tabarta ta zauna aqasa saita zaunar da ita akusa da ita tana riqe da hannunta suka shiga gaggaisawa da mutanen da sukazo kawota, matar uncle hassance tace.

"To iyayen batool, don yanzu kam kune iyayenta bamu ba, batada wasu agarinnan da suka fiku, gata nan mun kawo maku bisa amana, intayi ba daidai ba alurar da ita, ayimata afuwa bisa kuskurenta domin qaunar d'anku tasata rabuwa da iyayenta, don ALLAH muna roqonku daku d'auketa a matsayin 'ya ba suruka ba hakan zai taimaka mata wajen jajircewa agidan aurenta, muna roqon ALLAH daya bata ikon kyautata maku tare da yiwa mijinta biyayya har ace qara da ankayi."

"Amin ya ALLAH,"

Rashida dake zaune can gefe sai faman murmushi takeyi tafad'a, gaba d'aya yau wani farinciki takeji a tattare da ita marar misaltuwa, wai yau itace aka kawowa suruka had'e da damqa mata amanarta, tabbas duk abunda yayi farko zaiyi qarshe, tana roqon ALLAH daya sanya tarin albarka mai yawa acikin rayuwar auren d'anta ya karesu daga dukkanin sharrin mutum da kuma aljani, nan dai itama tayi mata nasiha sosai ita da Fatima wadda tamatuqar faranta rayukkan matansu uncle h kuma sun samu natsuwa d'ari bisa d'ari akan cewa batool zata samu ingantacciyar rayuwa acikin wannan ahali data jajirce wajen zab'awa kanta domin nagartasu ta tabbatar masu da cewa batayi zab'en banza ba, daga nan aka d'auki amarya batool aka wuce da ita gidanta da sai tashin qamshi yakeyi kana gani zaka san cewa ya dace da masu shi.

Su uncle h kuwa tuni suka d'auki harmar komawa kano su da su baffa da kuma mijin Yaya Maryam, babu yanda Dr da dady basuyi dasu ba akan subari sai gobe saboda dare yayi amma sukace a'a sudai yimasu addu'a, hakan yasa dady cewa to subar matan su su kwana anan har zuwa gobe, kasancewar sun san da zancen walimar da za'a gudanar yasa suka amince da hakan don bai kamata ace ba'a bar wani nata anan ba.

Saida su Uncle Hassan sukasa dady yayi masu sallama da hajia nafeesa suka sheda mata cewa suna sane da duk abubuwan data aikata don haka ga 'yar uwarta nan sun kawo mata suna son tayi qoqarin aikata abunda yafi wanda ta aikata abaya, sukuma suzo suyi mata aika aikar da bata tab'a tsammani ba, suka dai yimata fad'a sosai tana tafaman nonnoce kai qasa saboda wata irin kunya data rufeta, gaba d'aya batayi tsammanin sunsan da abunda kefaruwa ba don tasan halinsu ba itaba ko mahaifiyarta tayi ba daidai ba a matsayinsu na yayunta zasu iya zuwa su b'ab'b'allata balle ita, Saida suka tabbatar sunja Mata kunne sosai saboda karsu tafi subar baya da qura sannan uncle hassan yakira matarsa awaya ya sanar da ita cewa si zasu wuce, hakan yasa ta tattaro sauran 'yan uwa suka nufo gidan dady a tsammaninta tare zasu wuce, don haka gidan yarage amarya ce kad'ai aciki tana jiran angonta,

Suna isa uncle hussain yayi masu bayanin anan zasu kwana sukuma zasu wuce, addu'a sukayi masu tare da fatan ALLAH ya kaisu lafiya sannan suka wuce sukuma suka shige nan gidan dady wanda mafi yawancinsu a part d'in ammie suka sauka, aunty marwiyya da Yaya Maryam kawaine suka kwana apart d'in umma a zaune suna firar yaushe gamo, wacce rabinta duk akan Nuraddeen sukeyinta wato mahaifin little.

••• ••• •••
Cikin wata shadda milik d'unkin babbar riga little yashiga d'akin da acan ne yake tsammanin batool d'insa na ciki shida abbaty daya rakkosa riqe da leda, bakinsa d'auke da sallama ya shiga tana zaune akan sallaya tagama ranka sallolin da ake biyarta da batayi ba, qasaqasa ta amsa sallamar batare data d'ago kai ba har sai da taji muryar wani abayanta, da sauri ta juya taga abbaty ne yana murmushi ya ajiye ledar dake hannunsa had'e da cewa.

"Kar dai har kin tsorata matar qaramin baba?, To kwantar da hankalinki nasan matuqar kina tare da wannan mai sunan dadyn nawa babu abunda ya isa ya matso kusa dake ya cutar dake, so yayyarki agaresa ta Isa ta wadatar dake wajen samun kariya har iya qarshen rayuwarki, Ina fatar zaki kula mana dashi sosai had'e da gusar masa da duk wata kewa taki data kasance a tattare dashi na tsawon shekaru."

sosai kalaman abbaty suka yimata dad'i tare dayin murmushi tace dashi.

"ALLAH yabani ikon aikata hakan!"

Ya amsa mata da cewa.

"Amin ya rabbhi, Bari naje dare nayi, ALLAH yabaku zaman lafiya tare da zuria masu albarka."

Saida yakalli little da tun d'azu ita yake kallo yana murmushi sannan yace.

"To sarki! Yau fa gaka ga gimbiyarka, ubangiji ALLAH yasa adaren yau ka amsa sunan nan naka na abu sumayya."

Yaqarasa maganar cike da shaqiyanci tare dayin dariyar qeta sannan yafice, girgiza kai kawai little yayi yana dariya tare da bin bayansa yayi masa Saida safe sannan yarufe gidan had'e da tofa addu'a.

Koda yadawo ya tarar batool tamiqe akan sallayar da tayi sallah tana lunkewa yace.

"A'a keko gimbiya, kibar mana ita muyiwa ALLAH godiya bisa wannan burin soyayya tamu daya cika mana mukayi aurenmu na sunnah koba haka ba?"

Murmushi kawai tayi masa ta maida sallayar ta shimfid'a a inda ta tashi shi kuma yashiga toileta yayo arwala suka kabbarta sallah.

Raka'a biyu sau biyu yayi masu yana sallamewa sannan yayi addu'ar neman alkhairan ALLAH acikin aurensu mai tsawo, yayiwa ALLAH washi da kirari, yayi masa godiya tare da yiwa annabi salati, sannan ya roqesa daya dawo masa da mahaifinsa agaresu ya tsawaita masa rayuwar mahaifiyarsa ya kuma sanyawa aurensu albarka albarkacin girman haquri da ktawakkalin da mahaifiyarsa ke dasu, yayi hakanne saboda yanada yaqini akan duk abunda mutum yayi tawassali dashi matuqar anyisa domin ALLAH to ALLAH na amsawa yabiya buqata.

Jawo ledar yayi sukaci naman dake ciki atare tare da lemun hollandia sannan yaje yacire kayan dake jikinsa ya watso ruwa tare da kakkashe fitillun dake gidan,

Gab da zai shiga d'akin batool tayi saurin kashe fitilar yayi murmushi tare da tura gambun qofar sannan ya hau gadon, a tsammaninsa zai jita saman gadon a kwance amma yana lalubowa yaji wayam, hakan yasa ya zabura da sauri yamiqe yana kiranta a hankali,

"Gimbiya,gimbiya, Ina kike ne, Ina kika shigene?"

Tana jinsa tayi shiru had'e da shan jinin jikinta a bayan gambun qofar, tun yana kiranta ahankali yana lallalubowa har yasoma d'aga murya.

"Pls batool, where are you ne?, Kada kisafa jinin abu sumayya ya hau ko zuciyarsa tabuga, zo mana gimbiyata, sanyin idaniyar abu sumayya,.."

Maganar yakeyi yana qoqarin kamo abubuwan dake cikin d'akin ko zaici sa'ar damqota ita kuwa tanayi tana qara maqewa ajikin bango dariya na neman kuccikke mata, duk taku d'aya da zaiyi sai yafad'i kalmomi masu matuqar tsada da isar mata da saqon irin tsantsar qaunar da yake yimata, tun yana saran zai kamota har ya gaji ya nufi inda makunnin fitilar zai kunnawa, tana ganin haka tayi saurin juyawa tare da aza fuskarta ajikin ginin taba d'akin baya har lokacin tana saye da hijab d'inta.

Yana kunna fitilar haske ya mamaye d'akin ya hangota awajen, dariya yayi tare da sakin wata ajiyar zuciya sannan ya sake kashe fitilar ya taka ya iskota har wajen, azo kansa yayi asaman kafad'arta had'e dasa hannuwansa ya rungumota yana shaqar qamshin dake fitowa daga tsakankanin wuyanta, lumshe idanuwa yayi had'e da cewa.

"Gimbiya ni kaka shammata haka?, Wato kina so ki auna girman soyayyarki awajena ne ko kuma kina son irin wannan wasar tajawo narasa raina ne?."

Da sauri tajuyo had'e da aza yatsanta a saman lab'b'ansa tana girgiza kai,

"Kadena fad'ar haka Abu sumayya, mutuwa bazata ziyarcemu awannan lokaci d'aya zame mana mafi tsada acikin lokutanmu, idanma zatayi hakan to na tabbata anan gabane kuma atare zata d'aukemu, tsananin soyayyarka tasa na aikata hakan Amma idan na b'atama kayi haquri kayafeni."

Taqarasa maganar had'e da d'ora kanta asaman qirjinsa, shafa bayanta ya shigayi tare da lumshe idanuwansa sannan yace.
Chapter 125 · 0% Book details