← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 160

Sashe 65

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru sukayi suna nazarin kalmanta, tabbas abun duba wane awani b'angaren amma kuma yakamata tayi tunani akan halin da yake ciki, ace matarka da tsohon ciki ta b'ata kuma bakasan inda take ba kimanin watanni uku kenan yanzu cikin na hud'u, wud'anda sune suka kasance watannin haihuwar little Nuraddeen...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___49💎

Daqyar 'yan sandan suka samu sa'ar kamo Yaya hawwa, wacce kallo d'aya zakayi mata kafahimci zallar haukan daya sameta tuburan, Saida sukayi da gaske sukayi nasarar sanyata cikin bayan mota tanayi tanaa buge buge da fisgar kayan dake jikinta, wata uwar cacuma takaiwa boka bargaji dake zube qasan motar batare daya san inda kanshi yake ba tana fad'in.

"Kaine, kaine boka bargaji, kaine?, Mun halaka, Munb'ace, mun halaka, Munb'ace......" Wannan kalmar kad'ai take maimaitawa abakinta tanaci gaba da fizgar kayan jikinta, sudai 'yan sanda Imani da tsoron ALLAH rufesu yayi suka zuba mata idanuwa suna kallo, gaba d'aya takusa yaga kayan jikinta saboda yanda take fizgarsu, gani sunkayi tafashe da wata irin muguwar dariya tana ja da baya cikin motar had'e da dukan qirjinta kan suyi yunqurin riqeta aguje ta dirqo daga cikin motar tafad'o k'asa, kasancewar motarsu ce a tsakiya yasa tana fad'owa ta bayansu ta taka burki da qarfi 'yan sandan suka dirqo daga cikin bayan kantar suka rirriqeta tana sakin wata qara Mai tsananin firgitarwa wacce ko ba'a fad'a maka ba kasan bayin kanta bane, kusan su takwas suka taru saman kanta suna qoqarin maida ita cikin bayan motar, inta d'aki wannan ta daki wancan ta yakushi wancan har aka kwashe kusan mintuna ashirin suna abu guda kafin su samu da qarfin tsiya suturata ciki bayan sunyi mata d'an banzan duka sun jijji mata, Amma duk da haka bata saduda ba abunka ga marar hankali, daqyar da sud'in goshi suka samu suka isa da ita policetation suka jefata cell suka rufe, nan ma buge buge tadingayi tanayin wata qara mai tsananin sauti irin na halittu kala kala wanda hakan yamatuqar razana 'yan sandan da inspector najida, shi kuwa boka asibiti suka nufa dashi saboda acire harsashen dake hannunsa da qafarsa sannan suka dawo policetation d'in bayan anbaro 'yan sanda uku da zasu tsaresa acan asibitin.

Kasancewar koda sunka dawo daga asibitin har ankira sallar azahar yasa musulman cikinsu sukayi harmar zuwa wajen sallah, yayinda da akabar su blessing da sauran Christians d'in dake cikinsu su kula da Yaya hawwa da gaba d'aya hargaginta ya karad'e Police station d'in.

Bayan sun dawo inspector najida ta d'aga wayarta takirawo lambar baffa dake can kwance tun jiya da suka dawo yarimawa zazzab'i yarufesa, Nuraddeen na zaune agefensa sai kuma baffa Usman dake zaune ad'ayan gefen nasa ya rafka wani uban tagumi, da alama yana cikin damuwar ganin halin da d'an uwan nasa ke ciki, har wayar tayi ringing tagama babu wanda ya lura acikinsu shida Nuraddeen don kowanensu yashiga duniyar tunani saida sukaga baffa na qoqarin tashi don wayar nacan gefe ansata charji, da sauri Nuraddeen yariqasa ya tashi zaune daidai yana tambayarsa me yakeso, nuna masa wayarsa dake fidda sauti kad'an tana haske yayi ya ciro masa had'e da d'aga kiran dake qoqarin sake yankewa akaro na ukku, Saida ya kalli sunan inspector najida d'in dake yawo a screen d'in wayar sannan yakara akunne, gaisawa sukayi kafin tashiga yimasa bayanin dalilin kiran data yimasa,

Nan take yace mata tabashi mintuna gashinan zuwa yanzu yanzu, binsa da kallo sukayi lokacin daya gama wayar yana kallon drip d'in da ake qara masa saura kad'an suqare yace,

"Usman taimaka ka qara gudun ruwannan su ida shigewa ko kuma kaciremun haka."

"Amma yaya ina zakaje haka kai da bakada lafiya."

"Ai Alhamdulillah nasamu sauqi, wannan la'anannen ALLAHn ne 'yan sanda sukayi nasarar kamowa, Ina so inje inji inda suka kai yarinyar mutane, Usman aduk lokacin Dana tuna da kalaman iyayen yarinyar nan nakanji wani qunci azuciyata, nakanji damuwa tasa idanuwana gaba d'aya rufewa saboda tsananin kunyarsu, mutanene masu tsananin karamci da halaccin dabai kamata nafita batun wannan al-amarin na 'yarsu ba."

"Hakane Yaya, Amma kabari har kaqara samun sauqi."

"A'a Usman kai dai ciremani mutashi mutafi."

Ko kad'an baffa Usman baya son jayayya da d'an uwan nasa shiyasa ya cire masa qarin ruwan, abincinci Nuraddeen ya fara zuwa ya siyo masa kafin yafito wanka, yana fitowa ya zuba masa yaci sannan gaba d'ayansu su ukun suka nufi Police station d'in,

Tun daga bakin shiga wajen suka jiyo tashin sautin qarar Yaya hawwa, sosai baffa yagano muryar tata Amma yabasar yanufi office d'in inspector najida yanajin wani Abu na tokare masa maqoshi, Nuraddeen kuwa yawo yafarayi cikin wajen yana neman inda sautin ketasowa don yatabbata sautin qarar na mahaifiyar sane, inda suka ajiyeta wajene da ba'a fiye ajiye masu laifi awajen ba,hakan yasa yakasa gano ko inda take, hakan yasa aguje yadawo baya yashiga office d'in da yaga mahaifin nasa yashiga, yana shiga ya tarar da baffa Ali da Inna ruqayya anfiddosu dduk sunyi baqi sun rame sun lalace, baffa Ali kuwa yayi laushi tamkar ganyen daya kasa samun kulawar ban ruwa, Saida Baffa yasa hannu ga wata takardar dake tabbatar da sakinsu baffa Ali d'in sannan inspector najida tafara qoqarin yimasa bayanin halin da Yaya hawwa keciki, da sauri Nuraddeen daya shigo yace.

"Inspector najida ina kuka kaimun mahaifiyata? Me kuka yimata ne take wannan qara marar dad'in ji?" d'aga masa hannu tayi had'e da cewa "pls Nuraddeen calm down, ka zauna kaji abunda zanfad'a inaga anan ne zaka samu amsoshin wud'annan tambayoyin naka."

Riqo hannunsa baffa Usman yayi had'e da zaunar dashi akan kujerar dake kallon wacce baffa ke zaune shi kuma yana gefensa tsaye, gaba d'aya Nuraddeen yagama rud'ewa da fita hayyacinsa qarar mahaifiyarsa dake yimasa amo a kunne, wacce ba ko shakka yatabbatar bata lafiya bace.

Gyaran murya inspector najida tayi bayan ta d'auke idanuwanta daga kallonsa da takeyi had'e da cigaba da cewa.

"Baba kamar yanda muka fad'a maka cewa da bakinta tasanar damu cewa ita takai matar d'anta wajen boka akayi mata asirin data bar gidan d'an nata, Wanda wannan dalilin ne yasa yau da safe muka tasata agaba zuwa jejin da bokan yake, ba qaramar wahala muka sha ba damu har ita wajen kamo shi wannan bokan, a hanyarmu ta isa wajen ne wani iska mai qarfin gaske ya tunkaro wajen had'e da turniqemu, bayan wasu mintuna qalilan kuma sai iskan yakoma ta inda yafito wanda ananne muka nemi ita Inna hawwar muka rasa, bayan mun gamo artabu da bokan had'e da kamasa muka bazama nemanta ajejin Amma bamu sameta ba sai akan hanyarmu tafitowa mukaci karo da ita ayanayin da zamu iya kiransa da kamar tab'in hankali, wanda nan take muka kwasosu mukayo nan dasu, Amma saka makon tirjiyar da boka yayi mana yasa muka kai masa harbi har sau biyu yanzu haka shi yana asibiti mun ajiyesa don ayi treating d'insa, wannan shine abunda yafaru zuwa anjima zamuje muyi masa tambayoyin daya kamata kafin mu hannuntasu ga hukuma".

Mutuwar zaune Nuraddeen yayi, domin idan ya fahimta mahaifiyarsa tana mu'amala da bokaye wanda yanzu haka ake tsammanin tasamu tab'in hankali ta sanadiyar hakan,

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun" ya furta yana dafe kansa.

Ajiyar zuciya baffa yayi had'e da tambayar inspector najida ko zasu iya ganin Yaya hawwa don tabbatar da abunda tasanar dasu yanzu,

"Mezai hana." tafad'a tare da miqewa tawuce gaba had'e da cewa su biyo bayanta, jikinsu ba qwari sukabi bayanta har suka isa cell d'in da take ciki arufe,

Tsaye suka hangota tana surattai ita kad'ai kafin can suga an d'agata sama anbuga qasa kuma ko kad'an basuga wanda ya aikata mata hakanba nan take suka ga anfara lallanqwashe mata qafafuwa had'e da mummurd'e hannuwanta waje d'aya, juyar da kanta sukaga ansake fuskarta na kallon sama, kan kace me anmaidata wata iriyar halitta marar misaltuwa sai gumza takeyi tana wani irin gurnani, nan take hankulansu suka tashi don gaba d'aya basu tab'a ganin hauka irin nataba, kuka Nuraddeen yafashe dashi yana istigfari tare da duqewa qasa yana nemawa mahaifiyar tasa sauqi awajen ALLAH, juyowa inspector najida tayi tana kallon baffa had'e da cewa.

"Ya kamata kajaye case d'innan kuje gida da ita anema mata magani, domin ahalin da take yanzu ba abunda zata iya kuma batada sauran anfani acikin wannan case d'in baba, Amma kafinnan kabari sai nan da kwana biyu mungama tara suran bayanan daga wajen bokan zuwa lokacin kima kagama yanke shawarar abunda ya dace, don kasan ko kotu mukaje baza'a sauraremu ba tunda ba'a shari'a da mahaukaci?"

Jinjina kai kawai baffa yayi yana mamakin yanda Allah ya fara saukarwa da yaya hawwa hukuncinta tun ba'aje ko inaba, shikuwa Nuraddeen banda kukan da yakeyi na ganin halin da mahaifiyarsa ke ciki Babu abunda yakeyi, riqosa baffa Usman yayi ya riqe qarafunan dake jikin qofar shiga cell d'in yanaci gaba da rere kuka, tabbas uwa da d'a sai Allah, duk wanda yaga irin tashin hankalin da Nuraddeen keciki dole ya zubar masa da hawaye, gb d'aya yarud'e ya fita hayyacinsa yanda yaga mahaifiyar tasa takoma, duk munin halinta shi yana son abursa, yana sonta ahaka kuma dolene yashiga tashin hankali ayanayin da yaga halinda mahaifiyarsa keciki.

••• ••• •••
Su umma kuwa kasa kwana sukayi adaren da labari ya riskesu cewa asirine akayiwa 'yarsu, kuka umma keyi sosai tana tausayin awane irin hali 'yarta keciki Wanda shine ke qara haifar mata da zubar hawayen nata, baba kuwa gaba d'aya yasawa ransa dangana, damuwarsa d'aya halinda umma keciki wanda yana tsoron asanadiyarsa wani abu yasameta, ko kad'an bazai iya jure hakan ba kuma adalilin haka shima zai iya sake komawa cikin yanayin da bai dad'e da fitowa daga cikiba.

Kallonta yayi cike da tausayi kafin yace.
Chapter 65 · 0% Book details