← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 160

Sashe 45

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___34💎

Habiby wai har ina zamuje ne motsa jikinnan haka naga duk kabi ka kasa ka tsare." Rashida tafad'a tana cuno baki ba, jawo hannunta yayi had'e da cewa,

"Idan mukaje ai kya gani, nalura bakya son kina motsa jikinki kuma kinsan ko awonmu na qarshe da mukaje saida likita ya jamana kunne akan kirinqa yawan motsa jiki zai taimaka maki wajen aihuwa, don haka dole yanxu kiyi hak'uri muje ko don chu luv d'inmu, mud'an zazzagayo"

Zaro idanuwa tayi waje had'e da rufe baki tace, "don ALLAH karufan asiri habiby, wlh bazan iya ba, ka kuwa san halin mutanen garin nan naku kuwa?, Kawai kayi haquri zan motsa anan cikin gida karka jawowa kanka zagi." Zai sake magana ta aza yatsanta akan leb'ensa had'e da cewa.

"Pls.. habibyyyyy." Tare da Jan k'arshen sunan cikin shagwab'a.

Bayanda ya iya da ita dole ya hak'ura don aduk lokacin data yimasa irin wannan kiran ji yake baya iya musa mata akan komai,

"To yanzu fad'amun ya kike so ayi, motsa jikinnan dai kinsan dole kiyisa ko saboda lafiyarki Kuma ina so ki haifomun my chubby luv very strong!" Yafad'a yana kallon cikin idanuwanta.

"Muje ka rik'amun k'afa fuwana zanyi set back (wani salon motsa jikine da mutum zai kwanta ko kuma zaunawa yana yin gaba yayi baya na tsawon wasu sekonni sannan yadawo gaba, haka zai dingayi har na tsawon mintunan da yaji zai iya.)"

"Anya zaki iya habibty." Ya tambayeta cike da tsoro, "o'oh zan iya mana, ai masu ciki nayi kuma babu abunda ke samunsu."

Haka kuwa akayi suka koma falo ya taimaka mata sosai tayi set back d'inta fiye dana mintuna ashirin har tagaji ta dena saboda mararta da taji tad'an amsa mata, sake taimaka mata yayi ta watso ruwa saboda yanda zufa kefita jikinta sannan yariqota suka dawo falo ta zauna tare da miqe qafafuwanta ya shiga yimata tausa har bacci ya d'auketa.

••• ••• •••
Tafiya mai nisa Yaya hawwa tayi kafin takai cikin dajin boka mai abun mamaki (bargaji), tana kaiwa ana kiran sallar la'asar tayi tsaye abakin wani beji tana dube duben ta inda zata hango bukkar bokan da aka fad'a mata cewa daidai wajen yake zama sai gashi ta isko wanen wayam Babu alamar wata bukka awajen, tafi minti biyar kafin tajuya zata bar wajen cikin wani irin sauti marar dad'in ji taji ance.

"Maraba dake hawwaaa.., maraba da zuwa gidan miyagun aljanu, gidan biyan buqatun shed'anu da bau tsoron ALLAH, gidan rashin tausayi da imani, gidan da babu kunya balle mutunci, gidan cin amana da mugunta, gidan da babu jin tsoron ALLAH wajen kashe mai rai ya zamo matacce, Mai lafiya mu maidashi naqasashshe, shikuwa mai hankali mu maidashi mara hankali, marabanki abokiyar ta'bewa da hasara, meke tafe dake." Cikin dakewa da rashin tsoro Yaya hawwa tace.

"ALLAH ya taimaki bargaji..."

"Keee dakata, ba'a kiran sunan ALLAH anan domin wud'anda alqawarin tab'ewa ya tabbata akansu kad'ai ke zuwa wajen, yanda kika manta dashi kika zo nan haka zaki manta da sunan har saikin bar wajennan." Taji ankatseta cikin wata irin murya daban,

"To boka mai abun mamaki Ina roqon ayi mani afuwa zan kiyaye haka."

"An maki abokiyar b'acewa, muna sauraronki fad'i buqatarki."

"So nakeyi a haukata surukata tabi daji Kuma kada takoma dawowa gidan d'ana har abada."

"Bazai yuyu ba, kicanza buqata." Taji anfad'a tawni b'angaren, juyawar da zatayi sai ga bukkar ta hango gabanta da bai wuce taqa goma tsakani da ita ba. "Boka mai abun mamaki saboda me bazai yuyu ba, bana son takoma shiga rayuwar d'ana shiyasa nake son agusar mata da hankali na har bada.." bata rufe baki ba taji an d'auketa kyawawan maruka har guda biyu, tana shirin magana taji ana jawota zuwa inda bukkar take, Saida akazo daidai bakin qofar shiga ciki taji an durqusar da ita wajen ana zuba mata ruwan buloli tako ina ajikinta ana fad'in "kada ki kuskura kiyi kuka domin shizai qaro fushin alhajimalan akan tambayar da kika yimasa."

Yaya hawwa naso tayi kuka amma ta kama bakinta tarufe da hannuwa, duk saukar bulalar da taji ajikinta saita turo idanuwa waje tana had'iye kukan har aka gama"
Gaba d'aya jikinta saida yayi laushi sannan aka k'yaleta ana maimaita mata cewa "ba'a tambaya awajen." Kad'a kai tashigayi tana d'aga hannuwa alamun bada haquri kafin taji an sake janta an maidata ajikin bishiyar da take tsaye d'azu.

"Ki canza buqata muna sauraronki." Aka sake fad'a, cikin rawar murya tace. "Du..du.duk yanda akayi mata boka mai abun mamaki."
Wani irin iska taji ya taso had'e da guguwa taji ance "d'ago kanki." Tana d'agowa cikin guguwar aka nuno mata hoton Nuraddeen zaune alokacin da yake tattausawa Rashida qafafuwa, banda fuskarsa da hannuwansa da tagani bisa qafafuwa yana mammatsawa wud'anda ta tabbatar na Rashida ne bataga komai ba, duk iya leqe laqen da zatayi don taga fuskarta kasa gani tayi bokan ya kece da dariya had'e da cewa.

"Bazaki ganta ba domin ko mu anyimana shamaki da ganinta, tanada matuqar riqon ibada da addininta don haka baza'a iya galaba akanta ba, wannan auren had'in mai sama da qasane don haka bazamu iya rabashi ba, kawai mafita d'aya itace zamu iya fitar da ita cikin gidan idan mukayi sa'a da tana cikin rashin tsalki kowane irine to zamuyi nasarar yimata kurciyar da zata b'ace tayi nesa dashi, iya qarfin addu'arta iya tasirin da kurciyar zatayi akanta."

"To boka haka ma yayi, me zan.." bata qarasa ba tayi saurin rufe baki tunawa da dukan da tagama sha akan tambayar da tayi, dariya bokan ya kece da ita sannan yace.

"Bama karb'ar komai anan, mun b'ace kuma dole mub'atar, juya can kafin kitafi kiyi sallar la'asar."

Kafin tace wani abu taji an sake janta izuwa bakin wancan bukkar ta d'azu, jikinta ne yahau rawa tazata wani dukan zatasha taji cikin wata irin murya daga cikin rumfar ance. "Shigooo, shigoooo"

Jiki narawa tamiqe tashiga cikin rumfar, wani irin mugun hayaqine da wari suka tarbeta nan da nan tafara tari, dishi dishi tafara ganin wani mutum marar ma'ana tamkar mahaukaci yace "kijuyo anan ki sallaci sallarki ta la'asar."

Tsabar b'acewar Yaya hawwa da muguwar zuciya tanaji tana gani ta kabbarta sallah agaban wannan mutumen, ruku'inta da sujada gaba d'aya shi tayiwa su sannan ta sallame. Ji tayi ansake fizgota da qarfi anfito da ita izuwa bakin waccan bishiyar ta d'azu tashiga waiwaye waiwaye tana nemn inda zataga masu jan nata haka saboda tsavar bushewar zuciyarta.

"Kitafi, ki saurari biyan buqatarki akoda yaushe kuma kitafi da baya baya har kifita jajin nan, rashin aikata haka kuma zai ruguza dukkanin murdanki." Taji ana fad'a cikin wani salon murya da tamkar mutum biyu keyinta, da haka Yaya hawwa tafita jejin duk da tsananin nisan da yake dashi kafin akai hanyar cikin gari, fad'uwa kam tashata tafi a qirga kafin tasamu tafito, gashi duk tabi ta guggurje a qafafuwa, amma da yake taji tagani tana fitowa tayi wata irin ajiyar zuciya had'e da cewa "wahala ruwace nasan watarana wucewa zatayi" sannan taja qafafuwanta tawuce gida.

Tana dawowa taci karo da baffa abakin gida suna tattaunawa akan wata magana wacce itace mafitar da baffa yasamawa kansa akan al'amarin Yaya hawwa da zata sama masa kwanciyar hankali dashi har dansa da iyalinsa. Shiru yayi yana kallonta tun daga sama har qasa lokacin da tazo wucewa don lokacin ana kiraye kirayen sallar magrib, cike da takaici ya katsa mata tsawar da saida tasata dawowa da baya har tana shirin fad'uwa saboda rashin kuzarin dake tattare da ita.

"Daga gidan wa kike kuma da izinin wa kika fita?." Baffa yafad'a had'e da yawo kanta a fusace, d'aga hannunsa yayi da niyar marinta ko zai rage rad'ad'inta da yakeji azuciyarsa, baffa Usman ne da tun d'azu ya sinne kansa qasa duqe yayi saurin tasowa yariqe masa hannu, "Haba Yaya kada kayi haka domin kasani annabi ya haramta mana dukan matanmu musamman akan fuskokinsu, koda yaushe kaike tunasar damu akan haka taya za'ayi yau Kai kuma kayi yunqurin aikata hakan kuma awake, inaga hakan bai dace ba, don ALLAH kayi haquri ka had'iye fushinka."

Wani irin kuka mai ban tausayi baffa yafashe dashi yana nunata da hannu. "Wannan wace irin matace Usman kadubeta sama da qasa batada banbanci da jakar da tagama birkid'a aqasa, dubi lokaci qarfe bakwai saura mintota ace mace Bata cikin gidanta, wannan wane irin sakarci da lalacewa ne?, Narasa wane irin girman zunubine dana aikata ubangijiya had'ani da wannan fitinanniyar mace da gaba d'aya bata san ciwon kanta ba, wlh da nasan haka rayuwarta zata kasance agidana da banyi fatar yin aure ba har nakoma ga mahaliccina."

"Kayi hak'uri Yaya jarabawace, itama kayi qoqarin canyeta kamar yanda kacanye na bayan, ALLAH shine masani bisa dalilin jarabtamu ta hanyar abubuwan sonmu da kuma jin dad'inmu, muje muyi sallah kaji har anfara tayar da salloli"
Bugun iska baffa yayi da bayan hannunsa had'e da cewa "tir! hawwa ubangiji ALLAH ya shiryeki ya ganar dake" sannan ya juya suka nufi masallacin.

Cije leb'enta na qasa tayi had'e dayin k'wafa sannan tajuya tawuce cikin gida tana ayyana kalar matakin daya dace ta d'aukarwa baffa idan ta gama da Rashida...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___35💎
Chapter 45 · 0% Book details