← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 160

Sashe 31

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida suka shirya tsaf sannan ya d'auko abun karin da baffa Usman yasa Aysha takawo masu ya ajiye agabanta, soyayyen kwaine sai ruwan tea da kuma qaton burodi guda sai suga da gwangon madarar ruwa guda biyu tare da bonvita, qananan cups ya d'auko a kitchen tare da plate yajuye soyayyen qwan akan yahad'a mata tea mai kabrin gaske yabata, tana jin yunwa sosai hakan yasa ba musu ta karb'a tafara sha tana had'awa da soyayyen qwan tak'i cin biredin, Babu yanda beyi da itaba akan taci tace taqoshi don dama ita ko agida biredi bai shamata kai ba.

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___23💎

Haka yagaji ya qyaleta yaci gaba da cin biredinsa tare da kora ruwan tea kafin can ya turesu gefe yana kallonta, murmushi tayi ta tura soyayyen k'wan data d'ebo cikin baki had'e da sunkuyar da kanta k'asa.

"Malamina wannan kallo haka fa?."

Tafad'a tana kai ruwan tean abakinta,

"Ke d'ince indai kina agabana bazan iya dena kallonki ba, musamman idan kina motsa wannan d'an mitsitsin bakin naki dake d'auke da tausasan lab'b'a tamkar tuffa sai inji bana gajiya da kallonki."

"Ehhm."

"Baki yarda bane?"

"Haba! Nayarda sosai kuwa."

"Habibty! Hak'ik'a ba k'aramar sa'a nataka ba da ALLAH ya mallaka manike a matsayin matata kuma asusun ajiyar 'ya'yana har nakanj alfahari araina tare da ganin babu abunda yai sauran mani aduniya face naci gaba da yiwa ALLAH godiya bisa wannan kyauta da yayimun, haqiqa kowace mace da irin baiwar da ALLAH yayi mata aduniya amma inada yaqini akan cewa taki baiwar ta musammance, nayarjewa kaina in rayu rayuwa ta har abada a qarqashin inuwarki ke kad'ai batare dana kwad'aita izuwa wata inuwar ba."

Yanda taqura masa ido tana sauraren kalamansa ya sashi jinjina mata kai had'e da rufe idanuwansa yabud'e alamun tabbatar mata da zancensa sannan yaci gaba da cewa.

"Kiyarda dani Rashida Kuma kibani damar d'awainiya da dukkanin murdanki da burukanki aduniya natabbata zanyi qoqarin cika makisu koda kuwa zan rasa raina, ni Nuraddeen nayi maki alqawarin zan kula dake, zan tarairayeki zan bud'e maki dukkanin qofofin zuciyata kiyi duk yanda kike so aciki, zan mallaka maki dukkanin sassan jikinsa da kuma rouhina, zanyi maki uzuri acikin lafuzzanki da kuma ayukkanki agareni, zan killaceki tayanda Babu wani mahaluqin daya isa yacutar mani dake, zan d'aukaka darajarki da martabarki acikin 'yan uwanki mata, burina d'aya shine ki soni so mai girma kuma ki qaunaceni tayanda duk tsanani bazaki tab'a yarda arabaki dani ba domin farincikina yana wan zuwane matuqar kina tare dani to tabbas zan kasance mai alfahari da rayuwata har abada, Rashida Ina sonki so marar misaltuwa, Ina qaunarki qauna mai tsananin da zan iya sadaukar da dukkanin farincikina akan naki farincikin." Murmushi tayi tana maijin wani sanyi na ratsa zuciyarta da kuma sassan jikinta, tabbas tayarda cewa idan ALLAH ya jarabci bayinsa awanI b'angaren to yana kawo masu mafita a ta wani b'angaren daban, daga daren jiya zuwa wayewar safiyar yau cike take da tsoro da kuma tashin hankali ganin yanda mahaifiyar mijinta da wasu 'yan uwansa suka nuna qarara cewa basa farinciki da aurota wanda hakan ba qaramin jefata cikin damuwa da karaya yayi ba amma ayanzu ganin tsantsar soyayyar da mijinta keyi mata acikin idanuwansa da saqon da bakinsa ya isar Kai tsaye daga zuciyarsa yasa tasamu natsuwa da qwarin guiwa d'ari bisa d'ari wajen jajircewa ta nayarda martani akan soyayyar da mijinta keyimata kuma tashirya tsaf wajen yaqar duk wani shamaki da zaizo ya shiga tsakaninta dashi, zata lullunka dukkanin haqurin da akace tayi tare da jurewa dukkanin b'acin ran da zata fuskanta don ganin sunyi rayuwarsu yanda suka tsara cikin so da qaunar juna.

Wata kasalalliyar ajiyar zuciya tayi had'e da riqo hannayensa biyu tana kallon cikin idanuwansa tace.

"Ka kwantar da hankalinka malamina domin kai kad'aine zuciyata keso, Kai kad'ai taquduri alqawarin yiwa hidima har qarshen rayuwarta, bazan gujeka ba komai rintsi komai wuya, zanyi maka biyayya iya qarfina, zan kula da kai iya qoqarina sannan zan baka farinciki daidai iyawata, zan zauna da 'yan uwanka lafiya zan Kuma kyautawa iyayenka tamkar nawa iyayen sannan zanyi fad'a da qarfin ALLAH ga duk abunda zai rusa rayuwar aurenmu, abu d'ayane bazan iya yimaka alqawari ba, shine na baka soyayyata tahar abada."

Taqare zancen tana sinne kanta qasa had'e da qumshe dariyar da tazo mata saboda ganin yanda ya turikke idanuwansa awaje, cikin rud'ewa ya rumk'e hannuwanta sosai kamar zaiyi kuka had'e da cewa.

"Why Rashida!. Meyasa bazaki iya bani soyayyar kiba tahar abada?"

D'ago kanta fuskarta ad'aure tana kallonsa tace.

"Kayi hak'uri saboda gaba d'aya nariga da nabaka ita tunda dad'ewa har agaban Aabadan kaga kuwa bazan iya sake baka itaba tunda tuni tana hannunka."

Taqare maganar tana dariya had'e da kallon yanda ya dafe saiti zuciyarsa da hannayensa biyu yana murmushi, cikin wani irin shauqi yariqo gefen kuncin ya d'aga d'ayan hannunsa kamar zai mareta yana fad'in.

"Ke ko!" tayi saurin runtse idanuwanta tana dariya, ji tayi ya rungumeta had'e da sumbatar goshinta yace.

"Kai habibty Zaki kasheni da soyayyarki, waya koya maki soyayya haka." Yana sake sakar mata kiss agoshi, gyara zaman kanta tayi a qirjinsa had'e da cewa.

"Malamina mana.." duk sukasa dariya, atak'aice dai ranar sun faranta zukatan junansu da dad'ad'an kalamai dake d'auke da nagartacciyar soyayya.

Ganin ruwan basuda ranar d'aukewa yasa qarfe d'aya da rabi nayi na rana ya fito haka don gabatar da sallar azahar, kallo d'aya zakayi masa katabbatar da natsuwar dake cikin zuciyarsa saboda farincikin dake shifid'e a fuskarsa, kasancewar ruwan sun d'an rage yayyafine akeyi amma mai d'an qarfi yasa bai tsaya yin sallarsa b'angaren baffa ya wucewarsa masallaci, bayan yadawo yashiga inda mahaifinsa yake cike da jin kunyar rashin fitowarsa da safe ya gaishesa, sallama yayi baffa ya amsa masa sannan yashiga yana zaune riqe da littafin majma'ul baharaini yana tilawarsa, kallo d'aya yayi masa ya d'auke kansa ya mayar ga littafin yana murmushi ganin yanda yake wani faman sissinne kai qasa.

"Baffa Ina wuni?" Yafad'a kamar zai nutse aqasa saboda kunya, batare da baffa ya d'ago kansa ba yace.

"Lafiya klw Nuraddeen, ya yinin iyalin naka duk lafiya kuke?"

"Lafiya klw baffa ya ruwa?."

"Ruwa kam gasunan Masha ALLAH sun sauka, kaga badon rashin qafafuwannan nawa ba da sai gona."

"To baffa ya za'ayi sai haquri, in sha ALLAH ijaba takusan sauka, inaji ajikina ka kusan miqewa da qafafuwanka da yardar ALLAH"

Murmushi yayi irin nasu na manya tare da rufe littafin sannan yace,

"Hmm! Nuraddeen kenan! Kai yanzu kana tunanin zan miqe awannan halin da nake ciki?, Duk da dai shi ciwo da mutuwa duka a hannun ALLAH yake bana tunanin zan wud'an qafafuwan nawa zasu sake taka qasa"

_Laa taqnad'u min rahmatillah (kada ka yanke tsammani ga rahamar ALLAH)_

sukajiyo baffa Usman dake qoqarin shigowa yafad'a had'e da yin sallama, murmushi baffa yayi had'e da cewa.

"Malan Usman uban ango yau Ina kashige tun safe ban sake ganin kaba sai yanzu?, kodai d'an naka kake tayawa angwanci?" Sosa qeya Nuraddeen yashigayi yana murmushi tare da kallon baffa Usman dake qoqarin zaunawa kusa ga d'an uwan nasa yana dariya yace,

"To Yaya idanma nayi ai ba garemu farauba balle ta qare kanmu, in banda abunka Yaya duka duka shekarun naka nawane da kake zancen mutuwa koda yake ita batada takamammen lokaci amma muna fatar ba jikoki kad'ai ba har 'ya'yansu kariqa a hannu kafin wannan lokacin har su girma suna biye da kai kuje gona, rayuwa dai muke fatan tayi mana fad'a."

"Usman kenan tunda ALLAH kace nayi shiru, Amma karka maanta shekaruna fa yanzu sun haura hamsin da wani abu aduniya, idanma ALLAH bai nufi nagani ba ina roqon kai da d'an uwanka yagwada maka." Yafad'a yana sharar k'wallah ganin haka yasa baffa Usman ya kauda zancen had'e da cewa,

"Ya qarfin jikin naka? Kasha maganinka?"

"Eh yanzu da hawwa tashigo tabani nasha, jiki kam gayanan Alhamdulillah, yawwa kai namanta infad'a maka maman taka ba tada lafiya, shine dalilin shigowarta tace mun tana fama da ciwon ciki da gudawa don haka ka aika ko filagin da limotin ne asiyo mata ko kuma kaje da kanka."

Baffa yaqarasa fad'a yana kallon Nuraddeen

Baffa Ali ne ya d'ago labulen qofar had'e da kallon Nuraddeen sannan ya kalli baffa daga bakin qofar yace,

"Ya jikin?."

"Da sauqi Aliyu bazaka shigo ba?"

"A'a sauri nake zanje gona nad'an duba wasu abubuwan kasan zaman gida bana namiji bane sai mata."

Batare da baffa yadamu da maganar daya soka masa ba yace.

"To ALLAH yayi taimako yadawo da kai lafiya." Shidai baffa Usman na zaune yana kalonsa don tun jiya take d'aure masa fuska had'e da rashin yimasa magana.

"Baffa Ali ina wuni?" Nuraddeen yafad'a daidai lokacin da yake qoqarin barin wajen batare data kalli ko gefen da baffa Usman yake ba, dawowa yayi had'e da sake d'ago labulen sosai yanda zaiga fuskar Nuraddeen d'in snnn yace,

"Af..shin nura ne? Ai ban lura da kaiba, ashe kasamu damar fitowa yanzu, to agaisheka."

Baice masa komai ba saima noce kansa qasa da yayi shi kuma yawuce yana dariyar qeta don acikinsu yasan babu wanda bai b'atawa raiba da kalamansa.

Murmushi baffa yayi sannan ya fara ba baffa Usman magana akan yaci gaba da haquri da halin d'an uwansa, in Sha ALLAH da SANNU SANNU zai gane dukkanin kuskuren da yakeyi.

Miqewa Nuraddeen yayi had'e da cewa. "baffa Bari naje na siyowa innar mu maganin"

"To adawo lafiya."

Yabashi amsa atak'aice tare da maida hankalinsa wajen baffa Usman sukaci gaba da firarsu.

Bayan mintuna biyar da fitarsa sai gashi yadawo da ledar magani a hannunsa yanufi sashen mahaifiyar tasa yana isa tana fitowa da sauri daga d'aki had'e da cewa,
Chapter 31 · 0% Book details