← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 160

Sashe 39

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lafiya klw ummata ya kuke kuma da wajensu aunty marwiyya da baba balarabe, kowa duk lafiya ko umma.?" Rashida tafad'a cikin sanyin murya tana qaqaro murmushi a fuskarta tamkar tana gabanta. "Kowa lafiya klw ya qarfin jikin naki, kinacin abinci kuwa?"

"Naji sauqi ummata, abincin daine bana iyaci ummata.." saida umma ta kalli baba dake gefenta sannan yace "dama nasan za'ayi haka, ki daure kinacin abinci kada kirame shima yaron cikinki kisa yafito ba lafiyayye ba kinji ko, fad'amun me kike so inba malan Idris idan yashigo yakawo maki." Murmushi Rashida tayi aranta tana cewa, ALLAH sarki uwa, akoda yaushe kulawarta tamusamman take fiye da takowa aduniya, shiru tayi tana nazarin me zatace kafin can taji umma nafad'in "Akawo maki garin d'an wake kina so.?" nan take taji d'an waken yabiyo mata arai, "eh ummata Ina so, ahad'omun da busashshiyar zogale da kike ajiyewa kina yimana dambu shima inaso"

"To kice dai a had'o har da tsakin yin dambun ko,"

"eh umma har dana fate fate.?"

"Duk dai Rashida, wannan yaro ko yarinya anyi makwad'aita."

Umma tafad'a tana dariyar, tamkar tana agabanta haka rashidar tayi saurin rufe fuska itama tana dariya, naseeha tayi mata sosai had'e da bata 'yan shawarwarin yanda zata reni cikin sannan sukayi sallama, wani farinciki Rashida taji ya mamaye ranta cikin jin dad'i ta yane zanen gadon dake jikinta ta sauko daga kan gadon.

Falo tafito taduba bataga habibynta ba tafito tayo kitchen don tasan bai wuce can yana had'a masu breakfast, ai kuwa tana zuwa ta iskosa yana gyaran kayan miya har ya d'ora sanwar shinkafa ta tafaso saboda electric ne kuma wutar tanada qarfi sosai, qamshin shinkafar data tafaso ne yabugi hancinta lokacin data aza qafarta zata shiga kitchen da sauri takoma baya had'e da toshe hancinta amma ina tuni aman yaci qarfinta da gudu takai bakain makwarara tana sheqasa, ji Nuraddeen yayi kamar ya aza hannu akai yafashe da kuka saboda takaicin wannan abun da yaya hawwa tace ayi gashi aman datayi kusan sati da kwanaki batayi ba yau duk ta rankasa, sosai aman ya galabaitar da ita don tun tana durqushe saida takoma zaune hawaye nabimata a kunci, gashi daya matsota saita turesa saboda warin girkin da yakeyi, rufo kitchen d'in yayi da sauri ya d'ebo ruwa ya wanke mata baki zuwa lokacin batada sauran qarfin da zata iya hanasa rab'ar jikinta duk dako qamshin girkin dake jikinta da bata so, riqata yayi ya kaita d'aki ya kwantar da I bisa gado yana jero mata sannu yaje yacire kayan jikinsa ya watso ruwa sannan ya d'auko plaks d'in ruwan zafi dake kan fridge tare da kayan tea ya had'a mata mai kaurin gaske ya tadata zaune yadinga Bata tana sha, saida ta shanyesa cikin kofin tas tace yaqaro mata wani ta shanye sannan takoma ta kwanta tana fad'in "kayi haquri habiby, kagaji da rashin girkin da nake yimaka ko shiyasa kad'ora abunka yau..." Bata qarasa ba ya d'ora yatsans abakinta yana girgiza mata kai.

"Ko kad'an habibtyn habiby bazan tab'a gajiya da halin da kike ciki ba tunda nine sila, don haka kidena fad'ar haka kinji ko.?" Ya qarasa maganar yana jan karan hancinta, hannunta tasa tariqo nasa had'e da cewa.

Kaima kadena fad'ar cewa kaine sila domin yanayin wannan ibadar gidan aurence tazo mana a haka."
'Dan duqowa yayi ya sumbaceta agoshi yana murmushi ta wani lumshe idanuwa sannan ya gyara mata abun rufarta daidai qirjinta yace.

"Kiyi baccinki kada kifito har in qarasa, kwana biyu naga yadace yau akaiwa su baffa abinci shiyasa kika ga nad'ora girkin tunda ke dake dafawar bakyajin dad'i." Yana gama fad'a ya juya zai bar d'akin tariqo hannunsa alokaci d'aya tana lumshe masa idanuwa bayan ya juyo tace. "Ina sonka malamina habiby nah."

Dawowa yayi yad'an shafa cikinta d'aya d'an fara tasowa sai dai ba sosai ba saboda tsawon da take dashi. "Ina sonki so mai yawa kuma marar misaltuwa habibty."
Bai jira mezata ceba yayi saurin wucewa ransa cike da nishad'i, in dai soyayyace tsakaninsa da habibtynsa yasan basa gajiya kuma ba ranar gamata, yanzunan ne zasu qone abincinnan batare da sun ankara ba shiyasa yayi saurin baro d'akin, murmushi tayi tarufe idanuwanta nan da nan bacci yazo yayi gaba da ita, bai jima da d'aukar taba can cikin baccin aka fara nuno mata miyagun halittu kala kala suna neman firgitata amma sai taga wani glass yayi mata shamaki tsakaninta dasu sun kasa yimata komai, da wata irin kalmar shahada tafarko cikin matsananciyar qarar da tasa Nuraddeen shigowa cikin d'akin a rud'e riqe da ludayin miya a hannu, da alama ita yake motsawa yaji qarar sautin kalmar shahadarta. Saman madubi ya ajiye ludayin yanufi inda take zaune tana karanto addu'o'in data sani abaki zuciyarta cike da tsoro sai faman harbawa takeyi da sauri da sauri, tattab'a fuskarta da tayi sharkaf da zufa ya dingayi hankalinsa atashe yana fad'in "habibty lafiya?."

"Lafiya habiby." Tabashi amsa tan dafe d'an cikinta da yaji yana motsi sakamakon firgitar da tayi,

"Tashi mukoma falo." Yariqota ahankali yana kallon yanayin da take ciki, don riqotan da yayi yaji yanda qarar bugun zuciyarta ke tafiya da sauri da sauri sboda tsananin firgicin da tayi, ruwa ya d'auko a fridge yabata tasha bayan ya zaunar da ita, wayarsa ta karb'a ta kunna baqara tare da cewa yamiqo mata qillen tsamiyar dake ajiye saman fridge ta tsotsa saboda zuciyarta data fara tashi don har lokacin bai qarasa girkin da yakeyi ba.
Bayan ya miqo mata tsamiyar yafice ya nufi can cikin gida da niyar kirawo fadeela tazo taqarasa aikin dama miya ce kad'ai bai qarasa ba.
Yana fitowa yaci karo da muneera zaune bakin rumfarsu tana tsifar Kai, fiye da sati d'aya Inna ruqayya na fama da ita ta tsefesa sai yau da taga dama sannan ta zauna zaman tsifar, tana ganinsa ta dashe baki shi kuma ya d'auke kansa gefe cike da takaicinta, "ya nura."

Muneera tafad'a tare da tasowa tabiyosa har lokacin hannunta nacikin kanta tana tsifar da yatsunta, bai tankata ba har yakai bakin qofar d'akin Inna Bilkisu had'e dayin sallama, juyowar da zaiyi ya jira fitowarta sukayi karo da muneera dake biye dashi kansa yabugi nata sosai tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota tafad'a saman hannunsa, abunka da d'an uwa duk yanda take bazaiso abunda zai cutar da itaba har takai ga taji ciwo, muneera na ganin haka ta dashe baki tare da sake sakin jikinta. "Meye haka, dalla miqe sakarai, meye kike faman bina haka." ganin ko qwakkwaran motsi takasayi sai wni kafesa takeyi da idanuwanta irin na mujiya yasa cike da takaici ya saketa, tim kakeji qasa tamkar an yarda kayan wanki.

"Wayyooo..quguna ya nura zaka karya ni."

Tafad'a tana qoqarin tashi, daidai lokacin Inna Bilkisu tafito had'e da cewa."a'a Nuraddeen shine kayi tsaye anan sai kace baqo injin dai lafiya?."
"Lafiya klw Inna Bilkisu dama fadeela nake son tazo tad'an qarasa mana wani aiki, jikin Rashidar ne yad'an motsa yau.."
"Ya nura nizan qarasa maka kowane aiki ne basai fadeela ba."

Muneera tafad'a tana wani turo lab'b'a ala tilas itaga mai kishi, "to Nuraddeen kuje ga muneera nan kaji tace zata qarasa maku." Muskutawa yayi had'e da gyara tsayuwarsa sannn yace. "Don Allah Inna Bilkisu kitaimaka kituromun fadeela." Batare daya damu da zancen muneerar da tayi masa ba,

"Nuraddeen.." Inna Bilkisu tafad'a cikin sigar lallashinsa akan muneerar taje gudun wata matsala tafaru amma yayi saurin dakatar da ita tahanyar cewa

"Don Allah Inna Bilkisu." Yana had'a hannayensa sannan yawuce ita muneera ta sake bin bayansa. Saida Inna Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya sannan ta qwalawa fadeela kira.

"gani inna"

Fadeela tafad'a tana fitowa daga cikin d'aki da alama baccima ta farayi, "maza jeki yayanku nakiranku, kice ma Rashida Ina gaisheta da jiki."

"To Inna." Fadeela tafad'a tare da komawa d'aki ta d'auko hijabi tasaka tanufi sashensu, tana isa baki qofar shiga shiyar muneera ta riqe mata hijabi. "Wallahi babu inda zaki shiga tunda yahanani nima, munafuka kawai sai wani shishshige masa kikeyi bacin kinsan nice zan qara aurensa."

"Ha'a meye haka kuma aunty muneera, cikamun hijabina."

"Bazan cikakiba, wuce muje kikoma inda kika fito." Nan rigima ta kaure tsakaninsu muneera tayi bake bake a bakin qofar shiga sahen nasu Rashida riqe da hijabin fadeela ta kafe akan ba inda zata fadeela sai kiciniyar k'wacewa takeyi ta shiga, hakan yajawo hankalin Nuraddeen dake cikin d'aki yafito had'e da katsawa muneera tsawa yace.

"Waike wace irin marar kunya ce, zaki sake mata hijab ko sai nazo na takeki wajen." Yafad'a had'e da yowa kanta ransa ab'ace.

Da sauri ta saketa tare da komawa gefe tana fad'in "ya nura to nima in shigo?"

"In karya maki k'afa k'azama."

Turo lab'b'a tayi tana fad'in. "Badai shiyar kane baka so nashigo ba, wallahi saina fad'a inna shima akaika wajen maln ba..." Bata qarasa maganar ba sakamakon wata uwar tsawa da Inna ruqayya dake fitowa daga b'angaren yaya hawwa tayo mata jin zata tona masu asiri, "kee muneera maza kibaro wajennan kafin ranki ya b'aci, yayan naki ke fad'a kina fad'a don rashin kunya, zaki jaye ko saina iskoki." Taqarasa maganar tare da nufar wajen, qafafuwa muneera ta shiga bubbugawa tana fad'in. "Inna shifa zan aura kukace Kuma zakice nabaro wajensa, ya nura ni takace kuma ko bakaso sai ka aureni, kashirya a wannan shekarar dole muyi aure." dariya Inna Bilkisu dake kakkamta kaya a cikin rumfarta tana sauraren suruttan muneera tayi aranta tana cewa tabbas iska na wahalda mai kayan kara, Nuraddeen dake tsaye shikuma yana kallon ikon ALLAH tsaki yaja tare da shigewarsa don bai fahimci ma inda zancenta yayi ba, a fusace Inna ruqayya taqaraso wajen taja hannunta tana d'imarta a baya "ke kam anyi samna anan, shin b'angaren nasa aljannah ne da zaki nace sai kin shiga, bana fad'a maki kifita shirginsa ba kafin yasake nad'a maki wani dukan?"

Dai dai bakin shiga rumfar tasu ta tirje tana kuka had'e da fad'in. "Ni bazan fita harkarsa ba Ina sonsa, kuma ai keda baffa kunce zaku kaisa wajen malan bakada imani asa mashi soyayyata ya akayi har yanzu baya sona, ni bazan yarda ba kawai yau akaishi wajensa a d'aura mana aure gobe bana son aurensa qarshen shikarar nan don wallahi waccan munafukar zata iya aura masa fadeela gashinan sai faman tura masa ita akeyi tana shisahige masa.."
Chapter 39 · 0% Book details