← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 160

Sashe 129

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wata d'aya su baffa aka fara shore shiren auren muneera don dama a satin farko na sabon wata yakama, duk abunda yakamata uba yayiwa 'yarsa sunyiwa muneera Kama daga kan kayan d'aki har zuwa na aikin gida da sauransu, muneera kam tayi kuka ba iyaka da nadamar biyewa iyayenta da tayi tun tana cikin qurciyarta ta kasa riqe 'yan uwan mahaifinta da kyau si gashi yanzu sunyi mata gatar da bazata tab'a mantawa ba, baba nusaiba da Inna Bilkisu ma sun tsaya mata sosai wajen gyara kanta duk da tana nocewa, Amma suka nuna mata aishi aure ba ruwansa da tsufan mace matuqar tanada rai da lafiya dole tagyara kanta don samun natsuwar mijinta, Inna ruqayya kuwa ko ajikinta don har ranar da aka d'aura auren muneera Saida ta tashi fita baran Saida Yusuf yayi da gaske sannan tahaqura shima Saida yabata dubu uku tukuna, gaba d'aya haukan tsufa yaqara tarar mata akai da rashin arziqi takoma wata birkitacciyar tsohuwa sai dai ace ALLAH yakyauta.

Alhamdulillah anyi auren muneera lafiya an watse lafiya batare da wata hayaniya ba ko tashin hankali, acan cikin kano inda baba aminu ke gadi cikin wata anguwa ya kama mata hayar d'aki d'aya a wani gidan haya mai d'akuna barjik aka kaita har zuwa lokacin da zai kammala mata nata d'akin acan bebeji inda matansa suke..

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___93💎

Cike da mamaki muneera tabi mahaifiyar tata da kallo tana fad'in, "innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, Inna wai kece?"

"Eh nice nan! lafiya kike rafkamun uban salati haka sai kace wacce ta canza maki?, waima bari na tambayeki, dana ganki anan ke kad'ai ina shi mijin naki da tunda yazo sau d'aya gaishemu shima d'in da daddare har yanzu bai sake komawa ba saboda mugun hali don kar yace mana ungo."

Kallon kallo suka shigayi shi da ita kafin tace.

"Maigida innace fa!"

Da sauri ya duqa qasa yana gaida Inna ruqayya data saki baki tana kallonsa kafin tace.

"Yanzu muneera wai wannan shine mijin naki?"

"Eh Inna." Muneera data rasa yanda zatayi da ita tafad'a tana kallonsa, jitayi mahaifiyar tata nafad'in.

"Tirqashi! Kaico muneera, kice baki rabu da wahala ba, tsiyace ta taradda tsiya don wannan tsohon dagani babu tsiyar da yake tsinana maki, ana mutum haka hannuwa duk aqwaq qwange ba ko wannan ungo ta alkhairi! tun d'azu nake miqa masa hannu kusan mintuna biyar amma bawan ALLAH nan yayi biris dani ya d'auke mani kai don d'ibar albarka, Ina in bazai bani ba sai yafad'amun intafi abina sai yabarni tsaye ina miqo hannu, kaganka wallahi da gani bakada kir.." Bata qarasa ba muneera tayi saurin cewa.

"Haba inna meye haka kuma!, Ai baisan ke bace kuma baya canji Shiyasa bai baki ba."

"Ke rufamun baki, samna wannan ai qwanda kiyita baranki daki zauna dashi, mutum bazaice ungo ba ta alkhairi sai dai yayita karkace karkacen kai yana duqe duqen banza."

Ta qarasa maganar tana zura wuya tana kallonsa daga duqen da yake har ya gaji dajin maganganunta yamiqe yana mummurza hannayensa had'e da cewa.

"ALLAH yabaki haquri Inna."

"Innooo!, nace ba Inna ba innooo..don tsabar mugunta tsofai tsofai dakai ka kalleni kace mani Inna, haka aka Inna ba ungo ta alkhairi.."

Jin kalmar ungo da taketa maybe maitawa yasa mijin na muneer tura hannu a aljihu ya ciro naira d'ari biyar had'e da d'an rissinawa yamiqawa Inna ruqayya, tsabar sauri takarb'a har yakusowa tayi da hannunsa tana fad'in.

"Ikon ALLAH, to ko kaifa! da arziqinka kanemi maida kanka marowaci, to ALLAH qara bud'i kaji, agaisheka maza munneer kishiga ciki dashi kin barshi a tsaye don sakarci da rashin iya kula da miji, kushiga cika mana baffan naku nacan dad'a a guntule qafa abun gwanin tausayi."

Taqarasa maganar had'e da fashewa da kuka tasa mayafi tana sharar qwallan da suka zubo mata.

Muneera da tsabar baqin ciki da takaici sun rufe mata idanuwa tayi fuuu...tawuce abunta batare data qara bi takanta ba, bayanta mijin nata yabi yana kiran sunanta har ya cimmata ya tsaida ita, ganin da yayi idanuwanta sun cika tab da qwallah ya sashi cewa.

"Subhanallahi, muneera meye abun kuka!."

Cikin b'acin rai tabud'e baki zatayi magana yayi saurin dakatar da ita don yasan dole taji ba dad'i aranta, Amma ya zatayi? Mahaifiyar tace dole tayi haquri da ita, d'an murmushi yayi kafin yaci gaba da cewa.

"Baikamata ace kin nuna b'acin rankiba har kiyi fushi kitafiyarki kibarta awajen, ita uwa uwace baza'a tab'a canza taba komai lalacewarta, don haka kijeki idan kinada abun kyautata mata ki kyautata mata tare da magana mai dad'i cikin girmamawa, hakan zaisa nasamu natsuwar cewa koda nan gaba nayi tsufan da zan buqaci taimakonki to bazaki tab'a wofantar dani ba."

Dama damuwar muneera shine kar mijin nata yaji ba dad'i ko yayi qoqarin walakantata akan wannan abun da mahaifiyarta tayi, amma da taji yafad'i hakan sai tasamu wata irin natsuwa da sauri tabi bayan Inna ruqayya dake tafe can gefen titi tana faman qirga 'yan kud'ad'enta da bata gajiya da qirgarsu,

"Inna.." munnera tafad'a lokacin data cimmata tare da riqo hannunta suka koma cikin inuwar wata bishshiya.

"Lafiya muneera, ko saqo mijin naki ya sake turowa ki kawo mani?"

Murmushin da yafi kuka ciwo muneera tasaki had'e da cewa.

"Inna kenan!.." sannan tasa hannu cikin 'yar qaramar jikkarta ta hannu ta d'auko kud'ad'e aciki ta harhad'a, d'ari uku ne da saba'in aciki tamiqa mata had'e da cewa.

"Ga wannan Inna ni nabaki, kiyi haquri banida kud'i wannan ma sana'ar saida 'yan kayan yaji nakeyi d'an cinakin dana samune nahad'o da niyar inba baffanmu ko lemu asiya masa, Amma tunda kina so gashi saiki qara, in Sha ALLAH zan dinga kawo maki masu yawa idan ALLAH ya bud'a mani."

Rawa Inna ruqayya tafara kwasa awajen cike da farinciki kafin ta amshi kud'in tana fad'in.

"Kai a dai gaisheki muneera, ALLAH yayi maki albarka, haka nake son gani kullum don haka kiriqe mijinki hannu biyu yanda zaya yita baki kina bani kinji ko.?"

"To inna, Amma naroqeki don ALLAH kidena wannan baran bayada amfani ko kad'an, yanzu kinga abunda yafaru tsakaninki dashi ai baiyi dad'i ba badon ma yanada tunani ba sai hakan yasa wata rana ya koro makini, amma kiyi haquri Idan hakan dana fad'a ya b'ata maki rai." Taqarasa maganar tana hawaye tare da riqo hannunta.

Fisge hannunta tayi daga riqon da tayi mata had'e da d'aure fuska tace.

"To naji, maza kijeki yana jiranki."

"Kiyi haquri inna..."

"Nikam muneera yaushe kika lalace haka?, nace kijeki naji ba shikenan ba?."

Jiki a sanyaya muneera tabar wajen tanayi tana juyowa tana kallonta tana tafiya harta b'acema ganinta sannan ta ida shigewa ciki tana mai addu'ar ALLAH yaganar da mahaifiyar tata.

Bayan sati uku baffa Ali yaji sauqi sosai saboda yana samun kulawa wajen likitocin da kuma 'yan uwan nasa yanda ya kamata, babu wani rad'ad'i da yakeji kamar da sai abunda baka rasa ba, yanzu babbar damuwarsa d'aya shine yanda zai kalli 'yan uwansa inya tuna da walaqanci da kuma abubuwan daya tayi masu abaya amma duk basu dubi wannan ba sukayi tsaya wajen ganin yasamu lafiya, duk yatuna da wannan yana sashi dana sani da zubar da hawaye sosai, musamman idan yatuna yanda son zuciya da baqin hali yasashi biyewa matarsa ya raba yayan nasa da d'ansa na tsawon shekaru sai yaji gaba d'aya ya tsani kansa.

Yauma zaune suke duk su duka tare dasu baba balarabe sunzo dubasa da mijin Yaya Maryam anata fira ana dariya, shikam banda murmushi babu abunda yake iyayi don rad'ad'in cutar dasu da yayi dake zuciyarsa bazai bashi damar yin walwalar da zai iya dariya ba, wasu zafafan hawaye yaji sun zubo masa a fuska lokacin daya dubi yayan nasa yaga yanda tsufa ya dabai bayesa gaba d'aya don baida baqin gashi ko kad'an a jikinsa inba jefi-jefi gashin gaba d'aya yakoma furfura gwanin ban tausayi, kukane ya kufce masa ya shiga sheshsheka yana share majina, nan take gaba d'aya hankulansu suka dawo kansa, da sauri baffa Usman ya riqesa ganin yanda jikinsa ke rawa daga kan gadon yana qoqarin fad'owa saboda tsananin kukan dake nema yafi qarfinsa.

"Haba Ali!, shin har yanzu bazaka haqura kadena wannan kukan haka ba?, Duk fa mai rai dole ajarabcesa don agwada imaninsa, kai kamata ma yayi ka godewa ALLAH da yasa qafa d'aya aka cire maka, adaidai wannan lokacin akwai wanda gaband'aya dukkanin qafafuwan nasa yarasa, sai yace me?, Ana rayuwa haka ace Babu tawakkali?, Fad'amun naji shin wannan kukan naka zai iya dawo maka da qafarka ne da bazaka haqura kafawwalawa ALLAH ba domin shi kad'ai yasan dalilin dayasa hakan faruwa, kuma duk yanda ALLAH yayiwa bawa to yatabbata hakan shine mafi qololuwar alkhairi agaresa."

Baffane kefad'ar haka tare da riqo hannun baffa Ali cikin sigar lallashi, dik wanda ke wajen ya matuqar tausaya masa saboda baqaramin tashin hankali bane rasa wani sashe daga cikin sassan jikin mutum, su a tsammaninsu adalilin haka yake kuka, gaba d'aya suka taru suna bashi baki da ban magana akan ya yarda da qaddarowar da ALLAH yayi akansa, Saida yayi kukansa mai isarsa sannan yayi shiru cikin jin nauyi ya d'ago kai yana kallon baba balarabe yace.
Chapter 129 · 0% Book details