← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 160

Sashe 72

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Part d'insa ya bud'e har ya fara qura yana bin ko Ina da kallo, memory d'in da sukayi da Rashida tashiga dawo masa akai musamman daya kalli kitchen wanda ya zamomasu tamkar wani waje da suke d'ebewa juna kewa wajen aikawa da juna kalaman soyayya da kuma isar da saqon zuciya, bud'e cikin d'akin yayi ya shiga nan take yaji qafafuwansa na nema su gagaresa tsayi ya durqushe wajen yana kuka kamar ransa zai fita.

Yanajin qarar sautin ihu da bugun qofar da yaya hawwa keyi tana Kiran sunansa Amma rad'ad'in da yakeji azuciyarsa yanzu daya dawo masa fal ba zaisa ya iya sake waiwayarta ba,

Qarar wayarsa data fara ruri yasashi tsaida kukan nasa had'e da miqewa yashiga uwar d'akan ya jawo wata jikkar dake d'auke da pics d'in aurensu na ranar walima yaciro hotunanta inda take ita kad'ai tare da d'aukar wayarta data bari sannan yabar d'akin, Saida ya kulle part d'in yaba baffa makullan yana d'iba agogon hannunsa qarfe bakwai daidai ya d'auki butar dake gefe ya wanke fuskarsa su Inna Bilkisu na tsaitsaye suna kallonsa idanuwansa sunyi jawur saboda kukan da yayi har sun d'an kumburo.

"Inna Bilkisu mu zamu wuce asamu a addu'a." yafad'a yana kallon muneera data rakub'e gefe ya sakar mata murmushi, dashire hauru tayi tana fad'in.

"Ya nura ALLAH ya kiyaye hanya yabada ilimi Mai albarka, ALLAH yasa koda zaka dawo aunty rashidarka itama tadawo, akaro nafarko da yaji muneera tafara burgesa kenan yasake sakar mata wani murmushin had'e da cewa

"Amin muneera, ALLAH yazab'a maki kema miji nagari kafin nadawo In isko kin haifi mani d'a ko d'iya."

Washe haqoranta tayi gaba d'aya tana fad'in "amin ya nura amma d'an bunni irinka." Juyawa yayi yana kallon Inna ruqayya da tun d'azu ke zabga masu wata it muguwar harara had'e dayin tsaki yace. "Nawuce Inna ruqayya."

Ko kallonsa batayi ba balle yasa ran zata tanka masa daga qarshe saima tashi da tayi tabar wajen,

"Nuraddeen zo mutafi mana ga malan bello can a qofar gida da motarsa kai kad'ai muke jira." Baffa Usman yafad'a tare da bin bayan baffa daya fice daga gidan, rufa masu baya shima Nuraddeen yayi inna Bilkisu da sauran mutanen gida nabiye dashi suna yimasa addu'a,

Koda suka isa har motocin wud'anda zasuje sun soma tashi zuwa filin jirgin aminu kano da sauri yafita shima yaje ya gabatar da takardar shed'arsa da i.d card d'in da suka bashi sannan akace yashiga motar dake qoqarin tashi wacce itace ta qarshe.

Bayansu su baffa suka sake bi har suka isa filin jirgin, suna Isa aka fara kiran sunayen matafiyan kafin akai ga sunansa yaje ya duqa ya kwashi albarkar su baffa tare da rungumesu yana mai sake roqon dasu kula da mahaifiyarsa Wanda ananbaffa ya tabbatar masa da cewa kada yadamu suma dasun koma zasu wuce sokoto sufara amsar katin Kai mahaifiyar tasa asibitin ta mahaukata da sauran shire shire.

Yaji dad'i sosai kuma yasamu qwarin guiwar tsayawa ya jajirce akan karatunsa don ya tabbata mahaifin nasa zaikula da mahaifiyarsa duk da kuwa bata a qarqashin inuwar aurensa.

Basubar wajen ba har saida sukaga tashin jirginsu sannan suka juyo suka dawo gida cike da kewarsa....

_'yar uwa mekika fahimta acikin rayuwar littafin SANNU SANNU?, Nidai nafahimci girman uwa komai lalacewarta awajen nuraddin😍don haka bana wasa da mamana kaima karkai wasa da mamankaa,💃🏼💃🏼 domin itacee farincikinka duniya gabaa d'ayaaa (D.one voice)_

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___54💎

Kimanin awanni biyar da rabi suka shafe akan hanya kafin su isa garin kano, iya jigata Rashida tayita don ba kad'an ta tsargu da zaman na mota ba kasancewar bata tab'ayin koda makamancin irin sa bane, bini bini Fatima da Nuraddeen ke juyowa baya su kalleta har zuwa lokacin da suka iso.

Kai tsaye gidansu dake unguwar sharad'a phase2 suka nufa, da sauri mai gadi ya taso ya bud'e masu had'e da russunawa yana gaishesu dr.nura ya d'aga masa hannu yana fad'in "ahh...malan sule sannu da aiki, kana lafiya?."

"Lafiya klw ranka shidad'e barka da hanya an iso lafiya?"

"Lafiya klw malan sule" Dr .nura yafad'a daidai lokacin da yake karya starring motar had'e dayin parking, Fatima ce tafara fitowa tana fad'in.

"Ya ALLAH! Sweety wlh duk nagaji."

Daga can cikin motar taji yace, "To matar ke kenan, inata ga mmn baby ko ba haka ba?" Ya qare maganar had'e da juyawa yana kallon Rashida dake qoqarin sab'a Little Nuraddeen a kafad'a zata fita, dariya Fatima tayi ta zagaya tacan gefe tabud'e mata gambun motar had'e da karb'ar little tana fad'in.

"Sannu maman boy, ai ko da gani babu tambaya kinfini jigata, tafiya kam mai tsawo babu dad'i ko kad'an gaskiya in bata jirgi ba."

Ita dai Rashida Banda murmushi da takeyi tana shaqar yanayin iskan garin tare da bin tsarin gidan da kallo babu abunda takeyi har yafito cikin motar ya kulle tare da wucewa gaba sukabi bayansa,

Suna shiga duk suka zube tsakiyar falo a gajiya, Saida suka d'an huta sannan Dr nura yawuce part d'insa ita kuma Fatima tamiqe d'auke da little had'e da cewa Rashida tabiyo bayanta suka wuce part d'inta, har ga ALLAH Rashida ba hakan taso ba aranta, taso suna isowa sukaita wajen iyayenta duk da lokacin dare ya somayi don takwas na dare tawuce amma babu yanda ta iya dole tayi haquri idan talura da yanayin yanda kowanensu ya dawo agajiye,

"Maman boy kishiga toilet kifara watso ruwa kafin nan nima naje na watso nawa, sai in kawo maki little shima ayi masa." muryar Fatima ce taji tadaki kunnenta tana qoqarin ficewa daga d'akin, sai alokacin tayi yunqurin fita daga tunanin data shiga tare da d'aga mata kai sannan tafice sab'e da little dake faman baccinsa hankali kwance.

Rashida tajima zaune agefen gadon tana qarewa d'akin kallo kafin tamiqe tashiga toilet ta watso ruwan,

A b'angaren Dr.nura kuwa koda Fatima taje har yafito wankansa, "sweety shine baka jira nazo nataya kaba?"

Tafad'a cikin shagwab'e fuska. "Ina tuba matar kawo little maza kije kema kiyo naki musamu muranka sallolin dake kanmu mukai maman boy gida."

Shiru tayi na tsawon daqiqa d'aya dake nuna damuwarta akan maganar, har ga ALLAH tanajin rad'ad'i aranta idan ta tuna halin da Rashida zataje ta riska na rashin iyayenta, ba wani dogon shiri yayi ba face doguwar riga jalabiya daya zura ajikinsa sannan ya karb'i little a hannunta yana fad'in.

"Kidena bana son irin wannan dogon tunanin zai iya sakaki cikin damuwar da zata iya ankarar da ita halin da ake ciki."

"Shikenan Dr, Amma kana ganin bazamu bari sai gobe muje kaita ba? Ni sai nake ganin kamar dare yayi yanzu.

"Noo...hakan zaisa tayi kuka damu idan mukace mubari sai gobe, amma in mukaje yanzu mun kaucewa duk wani zargi daga gareta akan cewa rashin zuwanmu ne akan lokaci ya haifar da hakan kin gane?."

'Daga masa kai tayi sannan tashiga toilet, batafi mintuna biyar ba itama tafito tawuce falo tajawo akwatin kayanta dama tun d'azu Mai gadi ya shigo masu dasu ciki tawuce itama tashirya cikin doguwar rigar wani yadi marar nauyi, karb'arsa tayi takoma d'akin da Rashida ke ciki ta isko ita har tagama shiryawa tana ranka sallolin kanta tunda qasaru ne, tad'an jima zaune kafin taqarasa tamiqa matashi had'e da cewa.

"Ungoshi kiwatsa masa ruwa kifito falo muna jiranki."

Karb'arshi tayi tana fad'in "sannu aunty yaron nan nabaku wahala, shikenan shi baza'a ajiyesa shi kad'ai ba sai an tsaresa?"

"Ikon ALLAH! kin jiki da wata magana mmn boy, ai lalura ce takawo hakan, Amma badon haka ba mezaisa yana baccinsa ayita reto dashi hakan?"

Fatima taqarasa maganar tana murmushi sannan tamiqe tafice daga d'akin, a falo taci karo da Dr nura yadawo daga wajen ba maigadi saqo ya sawo masu abinci a wani restaurant dake kusa dasu a can bakin titi.

Hijab d'inta ta d'auko tadawo falon yana zaune ya miqe had'e da kabbarta sallah har suka gama ranka sallolin atare, suna zaune Rashida tafito d'auke da little ta gyarashi sai qamshi yake saye da hijab d'inta har qasa, duqawa tayi ta gaishesu suka amsa kowanensu fuskarsa d'auka da murmushi kafin Dr nura yamiqe had'e da karb'ar little d'in a hannunta ya zauna d'aya daga cikin kujerun dake falon, ita kuma ta zauna kusa da Fatima da har lokacin bata tashi daga inda sukayi sallar ba tana addu'a, sai da tagama suka shafa tare Rashida nafad'in. "Amin ya Allah masu albarka auntynah."

Zaro idanuwa wje Fatima tayi had'e da cewa.

"Nashiga uku ni batulu, yaushe kika fara shiga zuciyar mutane mmn boy kina gano sirrin addu'o'in da sukeyi."

Dariya Rashida tayi sannan tace. "Ba shiga zuciya bane auntyna, abunda ya tsaya mani araine har yakai yasa bana iya gama duk wata ibada tawa ba tare dana roqi ALLAH daya kawo mana qarshen saba, balle ke da nasan duk yanda nakai ga jin zafinsa kinfini shiyasa natabbatar idan ni ina yin addu'ar samun yayewar wannan abun toke zaki fini yin hakan sosai, ubangiji ALLAH yanda kuke bawa yaron nan kulawa kuma ALLAH yakula daku yabaku zuri'a masu albarka."

Tare duk suka had'a baki ita da Dr.nura suka amsa da Amin.

Maigadi ne yayi sallama Fatima taje ta karb'o saqon ta kawo falo ta ajiye sannan taje ta d'auko plates guda uku da cokulla da wani tray babba da yuqa ta ajiye bayan ta d'aurayosu, zuzzuba abincin tayi dake cikin robobin take away sannan taje ta wanko fruit d'in Rashida takarb'a ta gyara masu, miqewa tayi taje ta d'auko little a saman jikin Dr nura dae kwance saman kujera tana fad'in.

"Bisimillah yallab'ai."

Saida sukaci suka qoshi Dr ya d'auki makullin motarsa tare da d'aukar little dake saman kujera yana 'yan wasanninsa da hannuwa sannan ya fice yana fad'in.

"Ina jiranku a waje."
Chapter 72 · 0% Book details