Sashe 21
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kiyi hak'uri innamu bari nakira yarinyar nafad'a mata cewa amfasa kawo lefen gobe, shikenan haka yayi maki." Da sauri tace "eh yayi, kirata yanzu agabana kafad'a mata" ba musu ya ciro wayarsa yakira Rashida, bugu d'aya ta d'aga had'e da cewa "hello malamina." Cikin jin dad'in sauraren muryarta yace
"Habibty ya kike? Kina lafiya?."
"Lafiya klw, ya naji muryarka bayanda nasanta ba, ko kana kewatane. Taqare zancen cike da zolaya tana dariya, murmushin yayi shima had'e da kallon mahaifiyar tasa data kafesa da idanuwa tana harara suna had'a idanuwa ta d'aure fuska tare da kauda kanta gefe, murmushin ya sakeyi sannan yace.
"Sosai habibty I really missed you." Murmushi tayi don tafajimci meyake nufi saboda duk k'ananan kalmomin nan na soyayya yafara koya matasu kuma tana saurin fahimta da kuma haddacewa, matsalarta d'aya bata iya rubutawa balle takaranta sai dai inda ajami za'a rubuta mata, sanin har izuwa lokacin tana kan layi yasa yaci gaba da cewa, "habibty zancen kawo lefe da za'azo gobe odan baki fad'awa su umma ba to kifad'a masu sai ranar attanin za'a kawo saboda wani dalili kinji ko."
"To shikenan, dama ban fad'aba sai yau nake tunanin fad'a masu don haka babu matsala."
"Yawwa nagode sai anjima idan nakira" da haka yakashe wayar yana kallon umma da farinciki kwance a fuskarta fal tace.
"To ko kaifa, yanzu kaga sai ad'auko lefen akawo zuwa gobe 'yan uwana sun gani an uma tsaida wud'anda zasuje jebi sai akai ko kuwa"
"Hakane innamu ALLAH yatabbatar da alkhairi." Qirikiri tayi mui da baki batare data amsa masa da abin ba don itakam Bata fatan yazauna da yarinyar ballantana tayi fatan wani alkhairi a tsakaninsu.
Mik'ewa yayi zai fita tabiyo bayansa had'e da cewa
"Nace babu d'an wani abu a hannunka nan, kasan kullum mahaifin naka nanan zaune waje guda sai abunda 'yan dubiya suka bashi, d'an tanadin da yayi kuma ya lalatashi wajen wannan ginin wahala, baice komai ba yasa hannu a aljihu yaciro d'ari uku a aljihunsa ya miqa mata had'e da cewa, "kiyi hak'uri da wannan innarmu sukad'ai suka ragemun" karb'a tayi ta saka a hab'ar zane ta d'aure tana biye dashi har waje tace "ba laifi, ALLAH yayi albarka"
"Amin innamu," inna balkisu ce taqaraso wajen riqe da leda irin poly bag d'in nan tana murmushi "A'a malan Nuraddeeni fita za'ayi" tafad'a batare data kalli gefen da yaya hawwar takeba, cikin sakin fuska da girmamawa yace
"Eh inna bilkisu fita zanyi in ALLAH ya yarda, ina wuni?"
"Lafiya klw yaron kirki dama saqone 'yan uwanka saleema da kareema suka aiko dashi sukace akawo maka ka k'ara a lefe." Washe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa tasa da tunda taga inna bilkisu taqaraso wajen ta d'auke kai ko zata juya, karb'ar ledar yayi tare da komawa cikin rumfar d'akin mahaifiyar tasa ya jawo tabarma had'e da zazzage kayan, cike da mamaki yace
"Kai kai kai inna bilkisu kice hidima na d'orawa 'yan uwana, wannan irin abun arziqi har ina, gaskiya nagode sosai wlh ALLAH yabar zumunci km yasaka masu da alkhairi."
"Amin ya rabbhi ai ba komai yiwa kaine, kadaici da haquri abunba yawa kasan d'iya mata ne basu san amshi ba saidai karb'a" murmushi yayi yana kallon mahaifiyar tasa da tabbas yasan maganace inna bilkisu tasakar mata amma hankalinta nawajen kallon kayan dasu kareema suka aiko dasu atamfa biyu sai sarqoqi kala biyar da jikkar ribon dozin biyu da kuma hulunan sawa masu kyau qwaya biyar, murmushi inna bilki tayi ganin yanda Yaya hawwa tasaki baki sannan ta sake fiddo da wasu bugaggin shaddodi irin wud'anda akeyiwa rini har guda biyu ta sake miqa masa tace, "Nima ga tawa gudun mawar aqarawa 'yata dasu, ALLAH ya sanya alkhairi kuma yakauda idon maqiya." Tana gama fad'a tajuya tayi tafiyarta don gurinta ya gama cika, damuwar da takeso tagani a fuskar Yaya hawwa da takaicin da take son tusa mata arai tagansu qarara kuma taji dad'i,
Godiya ya dinga yimata yana fad'in ALLAH yabar zumunci kafin yajuyo wajen mahaifiyar tasa amma ga mamakinsa sai yaga tayi fuuuu..tabar wajen ranta ab'ace, kwashe kayan yayi yanufi wajen baffa dasu yana mai yabawa qoqarin 'yan uwan nasa, sunyi masa abunda kaf dangi babu wanda yayi tunanin yimasa kuma yaji dad'i sosai, haka shima baffa cike da jin dad'i yayita sanya masu albarka,
Yaya hawwa taci alwashin cewa koda ansa kayan alefen d'anta saita ciresu a gaban bilkisu tasa masu kalanzir ta qyasta ashana ta qonesu, ita ba ayi mahaluk'in daya isa ya nuna mata cewa ita da d'anta gajiyayyu bane balle ace za'a wani taimako masu har ayimata gori agabanta, ALLAH ALLAH ta dingayi gobe tayi kayan sudawo hannunta don tagwadawa inna bilkisu ita bata isa amma kash koda k'arfe 10 na safe yayi har baffa yasa ankira masa wani mak'wabcinsa dake da mota gwab irin ta haya d'innan yace da baffa Usman da kuma baffa Ali suje sukai kayan babu buqatar sai ankwashi ayarin mata guda anje kai lefe don d'ai d'orawa mutane hidima, duk yanda baffa Ali yaso zagayawa yazo ya sanar da yaya hawwa abun yacutara don baffa zaunar dashi yayi cikin d'akin yace karya kuru yatashi har sai angama kammala komai, baffa Usman shiya kwashe kayan yana kaiwa cikin mota yana dariyar yanda yaga baffa Ali na faman mutsu mutsu da qafafauwa yana son tashi amma baffa ya hanashi, bayan angama kaf baffa yaciro dubu goma aqarqashin katifar da yake kwance yaba baffa Ali yace idan sunkai lefen subayar asayi kayan wanka da ake kaiwa a al'adance.
Kallon baffa Ali yayi had'e da cewa "tashi kutafi kuma wlh karka sake inga kanufi cikin gidannan ina kallonka babban kwabo kawai"
Baice komai ba yamiqe yafita yana waiwayen cikin gida, ji yakeyi har wani cizonsa maganar keyi amma baffa ya kasa ya tsare ga kuma baffa Usman biye dashi yana gimtse dariyar dake cinsa, kamar yaro haka ya dinga kumbure fuska har suka bar qofar gidan,
Hamdala baffa yayi kafin nan yatura yusufa daya hango zai shiga cikin gida yace yakirawo masa Yaya hawwa, da qunquni tashigo cikin d'akin tare dayin tsaye bakin qofa fuskarnan ba annuri ko kad'an saboda fushin da takeyi dashi akan abunda yayi mata tace "gani lafiya?" Shikam dariya ma tabashi ganin yanda take cika tana batsewa akan d'an qaramin abunda yafaru tun kwana biyu da suka wuce, to inata da wannan baisan mezai faruba shiyasa yace qara yafad'a mata da kansa da ace taji ga wani, wannan dalilinne ma yasa yahana baffa Ali komawa cikin gidan don yasan halinsa tsab zai iya qarawa wutar fetur, cikin tsokana yace,
"Haba hawwa wannan irin cika da batsewa da kikeyi haka sai kace ba uwar ango ba, yihaquri zo muyi magana fushi ba naki bane kinji."
"Malan nifa inada aiki cikin gida inzaka fad'amun abunda zaka fad'a to kafad'a sauri nakeyi."
"To yihakuri kishigo mana." Badon taso ba haka taqaraso cikin d'akin tayi masa tsaye qiqam akai, murmushi yayi sannan yace,
"Dama zancen lefennan ne.." bai qarasa ba tace,
"Sai akayi me, ai jiya munriga mungama magana da yarona baza'a kaishi yauba sai gobe don haka nima inada hakk'i da d'ana yau nakira 'yan uwana abamu lefe suma sugani daga nan zamu fidda wud'anda zasuje kai kayan gobe in ALLAH yakaimu don wlh baza'aje da kowace shegiya acikin gidannan ba naji kana kawomun wasu kalan dangi ehe." Baki bud'e baffa ke kallonta har ta dasa aya kafin yace, "ikon ALLAH, waike kam hawwa har yaushe zakiyi hankaline?, Meye amfanin maido da hannun agogo baya da kikeyi yanzu bayan da yardar ALLAH nasan lefennan da kike magana har yakusa isa inda yakamata, don ALLAH kidinga tunani kirege fitina domin in mune aduniya gobe bamu bane, mutuwa na tare damu akoda yaushe saboda haka muzama masu hak'uri.." bai rufe bakiba yaga tajuya da qarfi tana kallon inda aka ajiye akwatunan had'e da lailayo asshar ta tule saboda ganin wurin da tayi wayam shiya tabbatar mata da abunda yake fad'i gaskiya ne, dole yariga da yasan hakan saita faru don haka ya gyara qafafuwansa had'e da mik'esu yayi kwanciyarsa,
Masifa tadinga zazzaga masa had'e da miyagun kalamai tana bubbuge abubuwan dake cikin d'akin tamkar wata mahaukaciya yayi tamakar baisan tanayi ba har tagaji don kanta tabari, amma yinin ranar mutanen gidan sunsha zagi manya da yara acewarta duka sunsan da zancen suka munafucceta, shi kuwa Nuraddeen da mahaifinsa sunsha tsiga da miyagun kalamai kala kala, Kai inkaji kace ba d'anta da mijinta take yiwa suba, yayi mata ranstuwa yana magiya akan baisan da baffa zaisa su baffa Usman suje kai lefen ba yafi aqirga amma fir taqi yarda, saboda tsoron fushinta har kuka yadinga yi yana roqonta Amma tace yafice mata daga d'aki Bata son ganinsa, itama saboda takaici da baqincikin rashin cikar muradinta har da k'walla tayi tana tsinewa yarinyar albarka.🤭🤣
••• ••• •••
A can garin yarimawa kuwa tarba tamusamman baba da qanensa malan balarabe suka yiwa su baffa Usman, sosai sunji dad'in karramawar da aka yimasu don musamman baba balarabe yasa aka gyara masu kaji ga fura da nono mai sanyi sannan aka yimasu abinci da abunsha musamman, ko kad'an baffa Usman baiso tsayawaba bayan sun bada kayan amma malan balarabe yayita roqonsu dole ganin girmansa yasa suka haqura suka tsaya, sunci sun sha sunyi nak sannan su baba sukayi masu godiya, musamman baffa Ali da har saida yayo guzurin nama a aljihunsa don yaji dad'in bawa yaya hawwa labari, dubu uku malan balarabe yabasu yace susha mai ahanya angode sosai baffa Usman yace bazasu karb'a ba hakan kuwa ba qaramin b'atawa baffa Ali rai yayi ba don har yafara hango lalurorin da zaiyi da nasa kud'in idan anbashi, haka aka rabu cikin farinciki da murna tsakaninsu baffa Usman da iyayen Rashida kowanensu na yabawa karamcin da suke dashi.
Duk da ba wasu kayane masu yawa ba ayanda ake qaryar lefe azamaninnan duk wanda yaga lefen sai ya yaba kyansu tare da qoqarinsaa matsayinsa na malami kuma mai matsakaicin k'arfi,
*A gurguje*