Sashe 18
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ok to, Masha Allah" suka sake gaisawa sannan yawuce, yana wucewa tasaki wata irin ajiyar zuciya tare da fitowa a qarqashin kujerar data b'uya tana watsawa nakusa da sit d'insu wani mugun kallo saboda yanda taga sun maido hankalinsu gaba d'aya akanta, da sauri suka d'auke idanuwansu daga kallon da sukeyi mata gudun karta tata masu rashin mutunci, wani juya idanuwanta tayi had'e da aza kanta saman bencin dake gabanta tayi kwancenta,
malan Idris nafita yanufi ajin da yake da period ransa duk ajagule, yaso ace yana shigowa yayi tozali da fuskarta saboda yanda yayi matuqar kewarta sai gashi hakan yacutara, haka nan ya daure yana koyarda d'aliban nasa sama sama amma gaba d'ayan tunaninsa da natsuwarta na wajen d'alibar tasa akan dalilin daya hanata zuwa makaranta yau duk da dai wani gefe na zuciyarsa na tabbatar masa da cewa tana cikin makarantar kawai biyi nasarar ganinta bane, adaddafe yasamu period d'insa ta k'are yafice daga ajin, wata d'aliba yakira yace taje ajinsu Rashida tace yana kiranta duk dako agaban idonsa wani malamin ya sake shiga cikin ajin nasu bayan nafarkon yafita.
Daidai bakin qofar yarinyar ta tsaya tare da cewa "escuse sir, malan idris yace yana kiran Rashida bashar." ai Bata rufe baki ba rashida tasake shigewa qarqashin kujerar, dube dube malamin yafara yana kiran sunanta amma taqi amsawa, sukuwa ajin gaba d'aya tsoronta sukeyi saboda sanin halinta shiyasa babu wanda yayi yunqurin tonata gudun kada ta taresaidan antashi tabashi kashi don haka takeyiwa duk Wanda ya takaleta acikin aji.
Juyowa malamin yayi had'e da cemata, "kije kifad'a masa bata zo ba."
Yana nan a inda take zaune yarinyar tadawo tafad'a masa cewa, "malan ance bata zoba" yace
"Ok wuce aji Kuma karki sake ink'ara ganinki waje kafin afito breakfast kinaji na ko."
"Eh malan" tafad'a tare da rugawa tashige ajinsu,
Tunanin zuwa gidansu yayi ya dubota, sai kuma yaga kamar hakan ba daidai bane tunda bai tabbatar da batazo ba d'in, don shi har yanzu jikinsa nafad'a masa tana cikin makarantar saidai in akwai wani abu dake faruwa, hanyar clinic d'insu ya nufa ko tana can Amma ga mamakinsa bai iskota ba hakan yasa yawuce dining hall d'insu da kitchen duk bata can, wasa wasa malan idris ya zagaye duk wasu building na makarantar amma baiga Rashida ba, hankalinsa ya matuqar tashi da hakan, don bai tab'a ganin tayi fashin zuwa makaranta ba duk da rashin son karatunta saboda yanda baba keson tayi karatun shiyasa baya d'aukar mata hakan, office d'insa yakoma ya zauna tare da aza kansa saman jikin kujerar yana jin rayuwarsa duk ba dad'i, tun lokacin bai sake leqawo wajen harabar makarantar ba sai da yaji antashi breakfast, miqewa yayi da sauri yakoma jikin tagar office d'in nasa yana kallon qofar ajinsu yanda d'aliban kefitowa d'aya bayan d'aya Amma har suka gama fitowo ko mai kama da ita bai gani tafito ba balle itad'in, cike da takaici yakaiwa jikin bangon naushi had'e da juya zai bar wajen, kamar ance ya sake juyowa ta tagar ya hango ta azo qafarta sannan yaga ta leqo da kanta tana kalle kalle kamar mai neman wani abun, ganin yayi tana yiwa meenah qawarta magana ga kunne had'e nuno office d'insa wanda yasa aransa yaji dad'i atunninsa maganarsa takeyi, abunda bai sani ba Rashida tasa aduba matane idan yana cikin office don tasamu tafito ta sayi abunda zata saya kafin ya rutsar mata, yana kallo tafito tana d'an waige waige har ta isa inda zatayi sayayyar tasaya da sauri kuma tajuya tabar wajen, a maimakon takoma cikin aji sai yaga tanufi bayan class d'in da sauri meenah na biye da ita.
Murmushi yayi had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya sannan yakoma bisan kujerarsa ya zauna yana dariya saboda yagano dalilin da yasa tab'uya bai gane taba, dariya yasakeyi had'e da cewa, "kunyata Rashida keji kenan!?" Jikkar da yazo da ita yajawo yaciro kwalin wayar daya siyo mata yana kallo sai kace shine ita, a hankali yafurta da taimakon wannan wayar zan tabbatar matar maki da irin soyayyar da nakeyi maki, zanyi iya qoqarina wajen yakice maki wannan matsananciyar kunyar dake nema tazama shamakin da zaya zamo silar takurawa rayuwar aurenmu, maida kwalin wayar yayi cikin jikka ya rufe sannan yamik'e yafito daga office d'in, Saida yad'an jawosa sannan yamik'e ta d'ayar hanyar da zata sadashi da bayan ajinsu Rashida, zaune ya iskota saman wani dutse sunacin dankali da awara sai zob'o da ruwan sanyi dake ajiye gefensu ita da meenah qawarta dake fad'in,
"Waike Rashida lafiya malan Idris yazo nemanki d'azu kika b'uya kuma ya sake aikawa akiraki kikaqi zuwa? Naga dai kuna shiri dashi balle ace wani abun, kodai laifi kika yimasa." Saida ta d'auki ledar ruwan tafasa tasha sannan tace, "wlh meenah babu wani abun dana yimasa kawai Ina cikin damuwane kuma kinsan halinsa ko kad'an baya son ganin d'alibinsa cikin damuwa, bansan irin amsar da zan bashi bane idan ya tambayeni."
"To amma ai wannan shiya Aiko kiranki ma'ana shike nemanki, bakya tunin ko akwai dalilin da yasa yake nemanki?." Tana rufe baki kamar ance ta d'ago kanta tahangosa tsaye ajikin bangon ajin ya nad'e hanneyensa akan qirjinsa yana kallonsu, k'ok'arin yin magana tayi ad'an tsorace yabud'e mata idanuwa had'e dasa yatsansa akan bakinsa alamun tayi shiru, ita kuwa Rashida dama kanta naduk'e tana cin abincinta don haka bata masan abunda ke faruwa ba, alama ya sakeyiwa meenah da hannu ta tashi ta tafi, cikin tarin qarya data k'irk'iro tace
"Emm...Rashida Bari naje naqaro mana ruwa qwaya biyu don wud'annan bazasu ishemu ba" takarb'i sauran nahannunta data fasa tasha tabar wajen, tana wucewa yayi gyaran murya had'e da dawowa tagabanta ya tsaye, a tsorace ta d'ago kai jin murya da qafafuwan data gani agabanta wanda bako shakka ta tabbatar namijine, suna had'a ido dashi tayi saurin mik'ewa tsaye tare da duqar da kanta tana qoqarin rab'awa ta gefenshi tawuce, hannunsa ya d'ora ajikin bangon ya tare ta inda zata wucewa had'e da cewa.
"Ina kuma zaki jene?"
"Aji zan koma." Tafad'a har lokacin kanta na sunkuye a qasa, gyara tsayuwarsa yayi sannan yaci gaba da cewa, "to ki zauna ki qarasa cin abincinki mana."
"Naqoshi."
"Saboda nazo?"
"A'a"
"To meyasa?, Bakya son ganina anan ne?."
"A'a" tasake bashi amsa atak'aice,
"Meyasa naje nemanki kika b'uya kuma na aika akiraki kikak'i zuwa?." Shiru tayi saboda bata san ta Ina zata fara bashi amsa ba, har zai sake jefo mata tambayar yaji anbuga qararrawar komawa aji hakan yasa yace, "ki tabbatar kin jirani idan aka tashi ina son magana dake kinji ko?," yafad'a yana kallonta, kad'a masa kai tayi alamar eh sannan ya koma tahanyar daya biyo ya wuce, ahankali tajuyo tana kallonsa har ya b'ace kafin takoma saman dutsen data tashi ta zauna, hannuwanta tasa ta dafe kanta dasu wasu zaffan hawaye na zubo mata, tambayar kanta tashigayi akan meyasa malan idris ya shigo rayuwarta a daidai wannan lokacin, meyasa yafurta mata kalmar da zata saurin narkar mata da zuciya alokacin da batayi zato ko tsammani ba?, Meyasa tabari zuciyarta tafara sonsa bayan tasan batada iko akan zab'awa kanta abokin zaman da zatayi rayuwa dashi alokin?, Wani irin kuka ta fashe dashi tana mai jin rad'ad'i da kuma zugi acikin zuciyarta,
Tafi mintuna biyar zaune ahaka tana kuka har saida tayi mai isarta sannan ta tashi tawanke fuskarta da sauran ruwan dake wajen ajiye takoma cikin aji.
Ana tashi tayi saurin d'aukar jikkarta tagudu don batasan abunda yake son fad'a mata ba, Bata so yasake jifarta da wasu kalamai da zasu tunzura zuciyarta har sukaita ga bijirewa zab'in da mahaifinta yayi mata, Amma sai dai kash! cikin rashin sa'a tasamu yana nan tsaye abakin k'ofar ajinsu yana jiranta, k'ok'arin shigewa cikin 'yan uwanta d'alibai tayi tagudu yayi saurin riqo jikkarta dake sagale a kafad'arta, tsaye tayi cak batare data juyoba yace,
"Ina kuma zaki je?" Juyowa tayi saboda d'aliban dake wucewa kada suyi zargin wani abun ta jaye jikkarta ahankali daya rik'e sannan tace,
"Gida zanje." Yanda yaga wasu d'alibban sunyi tsaye suna kallonsu yasa ya shafa kansa yana fad'in muje inrakaki dama tuni ya d rufikke office d'insa ya tsaya nan zaman jiranta don yasan zata iya guduwa, babu yanda ta iya dole tabisa suka nufi gate d'in zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, meenah dake can gefe tana jiranta na ganin haka tawuce abinta zuciyarta cike da tambayoyi akan meye tsakanin qawar tata Rashida da kuma malan Idris.
Tafiya yakeyi ahankli tamkar wanda baya son su isa gidan yana tambayarta meye dalilin da yasa gaba d'aya yau ta sauya masa ba kamar yanda suka saba ba amma takasa cemasa komai, adaidai bakin wata bushiya dake kan hanyar ya tsaya tare da cewa,
"Rashida meyasa inata yimaki magana kika yimun shiru? shin ko bakya sona ne shiyasa kika zab'i wannan hukunci a matsayin amsar da zaki bani don tabbatar mani da cewa bakya sona d'in." Yaqarasa maganar cike da damuwa a fuskarsa, da sauri ta d'ago kanta tana girgiza masa idanuwanta cike da k'walla kafin tace,
"Ko kad'an malam ba haka bane, asalima azuciyata babu wani namiji da nake so kuma nake burin qare rayuwata atare dashi kamarsa, Amma kash kazomun a qurarren lokaci, kazo alokacin da banida ikon zab'awa zuciyata abunda take so face wanda aka zab'o mata, tabbas ina sonka amma nasan wahalace kurum zansha don bazamu tab'a kasan cewa a inuwa d'aya ba" taqarasa maganar tana share hawayen da suka zubo mata a fuska, cike da mamaki yake sauraren kalamanta kafin yace
"Rashida ban fahimceki ba, kamarya bazamu lasance a inuwa d'aya dani dake ba bacin kince kina sona kuma kinsan nima Ina sonki, to meye kuma zai dakatar damu daga cimma burukanmu."