← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 160

Sashe 3

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ALLAH sarki batool, Ashe rabon wu 'yannan jikokin nawa yasa kika iya jurewa rabuwa dani bayan kinsan irin tsantsar so da k'aunar da nanuna maki acikin 'ya'yana, wacce har takasa b'oyuwa azuciyata, har kikayi nesa dani ban dena jin wannan qaunar taki araina ba, ubangiji ALLAH ya tashi kafad'unki, ALLAH yabaki lafiya kiga yanda soyayyarki ta dinga lunkuwa a kowace rana cikin shekarunnan da bakya tare dani." Haka Abba yayita suruttansa tamkar wanda yafara zarewa yayinda yaran daya d'ora saman qafafuwansa suke jan d'an farin gashin dake shimfid'e a fuskarsa.

Tuni su uncle h suka kira matansu suka sanar dasu halin da ake ciki wanda nan take family da suka had'u don walimar tarbarsu da Abba ya shirya suka fara koke koke, baran mahaifiyar batool da kad'an yarage itama arasata saboda matsananciyar fad'uwar da tayi a some, tajima kafin asamu ta farfad'o, kuka takeyi sosai tana roqon ALLAH ya sassautawa 'yar tata kuma yajiqan mijinta, nan take duk aka watse jikin kowa a sanyaye, asibitin wasu suka nufa wasu kuma suka wuce gidajensu saboda basu sanar da mazansu ba, kafin kace me tuni asibitin tafara samun halartar 'yan uwa da abokanan arziqin Abba da 'yan uwansa tako ina, duk wanda yaji labarin abunda yafaru saiya zuddarwa da yaran hawaye domin har zuwa lokacin ita batool d'in bata farfad'oba,

Dr sadeeq ne yadawo wajensu uncle akan zancen gawar Abu sumayya da suka buqaci abasu akace sai zuwa gobe idan police d'in da suka tsaya sunzo sunsa hannu, hakan yamatuqar qonawa Uncle Hassan rai da yasa yanata fad'a har saida Abba yabashi haquri shida Dr sadeeq sannan yayi shiru.

Ita dai mahaifiyar batool hajia salmah abu yakashe mata biyu, nafarko damuwar halin da 'yarta ke ciki na biyu kuma maraicin da wud'annan qananan yara har su hud'u zasu fuskanta, tayi farincikin kyauta da kuma ni'imar da Allah yayiwa 'yar tata amma sam damuwa takasa barin haka ya bayyana a fuskarta, ita da mahaifiyar shurahbil ne suka zauna zaman jinyar batool da kuma kula jariranta, yayinda Abba yace matar uncle hussain da kuma abokiyar zaman hajia salmah wacce ake kira da Rabi'atu su zauna gida sukula da yara da hidimar abinci,

Tun daga Abba har su uncle h babu wanda yakoma sakama bakinsa wani abun tun safe, hakan yasa bayan sallar magrib hajia salmah da suke kira da hajia mama ta kallesu had'e da cewa, "ya kamata ace damu daku duka mun fawwalawa ALLAH komai, mudangana da tsarin da yayo mana domin bamusan dalilinsa nayin haka ba, don ALLAH ku daure ku zauna kuci abinci kada kuma wani abun ya sameku."

Wata qatuwar kula tajawo ta mik'awa shurahbil da isowarsa kenan shima yadawo daga masallaci tace, "ungo nan shurahbil je kazubawa iyayenka abincinan suci kuma kaima don ALLAH ka tabbatar ka zauna kaci naka"

"To hajia mama, Ina yarana suke?."

"Kagansu nan har sunyi bacci." Tafad'a tana miqa masa plates da spoons, karb'a yayi had'e da cewa, "yakamata hajia akirawo zainab tawuce dasu gida ta watsa masu ruwa, yau sun matuqar jigata sosai, donma yaro yana yaro ai da sai jikinsu yafad'a masu, amma kingansu nan yau sau uku suna barci suna tashi wannan shine na hud'u."

"Hmmmm! Shurahbil kenan!, ai dolene suyishi, baccin rashine ALLAH dai yajiqan mahaifinsu." ya amsa da amin sannan ya wuce inda ya hangosu acan cikin wata runfa da aka tanada domin patient relatives.

Gaida iyayen nashi yayi tare da qoqarin bud'e kular bayan ya ajiye uncle hussain ya dakatar dashi, "kaje dashi can cikin mota saboda bazan iya ci anan ba sai dai kosu alhaji idan zasu iya su." kallonsa Abba yayi sannan yace,

"Kana tunanin abunda duk baibar kaba zai barmune mu?, Aje dashi duka cikin motar gamunan zuwa." Haka shurahbil ya sake kinkimar kular abincin da plates yakai cikin mota ya d'ibi nasa a plate ya rufe da wani plate d'in sannan yabaro wajen, masallaci yakoma yaci nasa duk da bawani ci yayi ba d'an tsakurane kawai yayi saboda hajia mama data had'asa da ALLAH, badon haka ba bazai iya cin abinci acikin asibiti ba.

Saida ya kwatanta sun kammala ci suma sannan yaje ya d'auko masu lemu da ruwan da a kazo dasu na gora ya kai masu ya kwaso kayan da suka gama cin abincin ya maido wajensu hajia mama.

Sosai Abba yaso yaji takamammen bayani akan lafiyar batool amma hakan ya cutara saboda tsoron yanayin da zai iya shiga, tamatuqar wahala saboda ana gama mata tiyata lumfashinta ya d'auke, kusan likitoci bakwaine suka taru akanta kafin su samo da taimakon ALLAH lumfashin ya dawo, shima d'in da qyar take fiddashi wanda sanadiyar hakanne ake shiga da Oxygen aguje saboda ya taimaka mata, daga lokacin da akayi mata aikin zuwa dare ta shanye tukunya hud'u na oxygen, sai bayan sunga lumfashin nata ya daidaita ne kuma suka fara qoqarin treatment d'in raunin da taji a fuska duk da dai and'an bata emergency care kafin akawota nan. taji rauni sosai sabod duk glass d'in mota ya yanke mata fuska har saida aka ciccire mata wani da ya shige, idanuwanta kad'aine ALLAH ya kare basu samu wata matsala ta sokewa a xahiri ba ko kuma wani internal injury aciki ba, Amma hatta kanta ya bugu sosai wanda Dr odugun ya sanarwa dasu uncle h sai ta farka za'a iya gano cewa bata samu wata matsala acikinsa ba idan anyi gwaje gwaje, kallo d'aya zaka yimata kasan tanajin jiki saboda yanda aka nannad'e mata fuska da bandage ba'a bari kowa yashiga d'akin sai nurses da kuma masu jinyarta suma d'in saida dalili.

Jariran kuwa tunda aka cirosu Dr imaan ta karasu ga nonon mahaifiyarsu suka d'an tsots-tsotsa har yanzu ba'a basu komai ba, sunyi kukan har sun gaji amma Dr tace kawai asa masu drip zuwa gobe tunda har lokacin mahaifiyarsu bata farko ba,

Abba dasu uncle basu bar asibitin ba sai misalin qarfe sha biyu da rabi na dare bayan shurahbil yaje gida ya watso ruwa ya dawo shi da zainab sister d'insa ta d'auki su hassana sannan su Abba suka wuce da ita gida saboda anan shurahbil zai kwana Koda za'a buqaci wani abun....

_*ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU*_👏🏻😭
[8/17, 10:18] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___4💎

Suna isa gida zainab tawuce dasu part d'insu yayinda uncle hussain ya ciro wayar batool da aka basu da kuma takardun da alhajin daya kawo su Abu sumayya asibiti ya basu ya mik'awa Abba yana fad'in,

"Alhaji ga wud'annan takardun da wayar fatima"

"Karik'esu hannunka hussain, Amma yakamata ace antuntub'i iyayen yaron nan an sanar dasu halin da ake ciki koba haka ba?",

"Eh hakane gaskiya, dama tun d'azu ake kiran wayar narasa qwarin guiwar d'agawa, bari naba yaya sai ya lalabo lambar wanda yakamata." Mik'a masa wayar yayi ya karb'a tare da fara duba sunayen missed call d'in da yagani saboda yanada tabbaci akan nakusa da su d'inne suka kira, lamba uku ya gani, tafarko ansa gwoggwo, ta biyun kuma sister, sai ta ukun barrister kamal, shuru yayi yana nazarin wacce yakamata ace yakira Abba yace, "malan Hassan lafiya kuwa?."

"Lafiya klw alhaji. Kawai Ina nazarin lambar kdaya kamata inkira cikin ukunnnan da aka yimata missed call dasu, wannan ta farkon Ina tunanin qilan mahaifiyar sace wato surukar ita fatima ta biyun kuma qilan qanwar sace, sai ta ukun wacce nakasa fahimtar waye shi!, gashi dare yayi kada a d'aga masu hankali"

"Malan Hassan kenan! d'aga hankali kuma har na nawa agaresu?, ai tunda suka kirawo wayarsu sukaji basu same suba dole hankulansu su tashi, Ina tabbatar maka da cewa dakyar daga cikinsu in akwai wanda zai iya bacci matuqar Basu samu wani labari akansu ba, ya zamuyi tunda mai faruwa tariga da tafaru, ko ance abari sai gone babu abunda zamu iya canzawa don haka ka kira a sanar dasu shine daidai domin hakan zai sama masu natsuwa koda kad'ance, kaga at least tunda akwai 'yar tazara a tsakaninmu (kano da borno) idan aka sanar dasu tun yau zasu samu tasowa da wuri gobe" Abba yafad'a cike da damuwa, ganin shima gaskiya yafad'a yasa ya danna lambar barrister kamal kasancewar shine namiji aciki kuma shi zaifi iya karb'ar abun cikin kwanciyar hankali duk da dai bai san kowaye shiba, ringing d'in farko bai ida shiga ba yaji yad'aga Kiran da alama jiraye yake da hakan, lokacin shikuma yana part d'insu Abu sumayya don agida d'aya suke amininsa ne sosai wani aikine yakawosa agarin borno shida iyalinsa shine Abu sumayya yabashi wani b'angare daga cikin gidansa ya zauna har zuwa lokacin da zai gama, tunda rana mahaifiyarsa tayi masa waya hankalinta atashe tasanar dashi halin da ake ciki akan rashin samun lambar aminin nasa da takeyi ita kuma ta matarsa idan takira ba'a d'agawa, Nan shima yakira lambarsa bai samesa ba hakan yasa yakira ta batool ita Kuma bata d'aga ba, yanda hankalin mahaifiyar aminin nasa ya tashi tanata kuka yasa d'aya dawo sallar isha'i yawuce wajenta yana rarrashi tare da kwantar mata da hankali amma har tsawon wannan lokacin takasa dena kukan wanda hakanne yasa shikuma yakasa komawa part d'insa wajen iyalinsa,

"Assalamu alaikum" Yaya hassan yafad'a ya amsa masa cikin natsuwa tare da fargabar abunda kunnuwansa zasu jiyo masa, runtse idanuwa yayi cike da rashin sanin ta inda zai fara sanar dashi wannan mummunan awannan lokacin, karb'ar wayar Abba yayi ahannunsa tare da duba lambar sannan yakara a kunnensa had'e da cewa, "da barrister kamal nake magana?." cikin i'ina yace,

"E..e...eh shine."

"Kana magana da mahaifin batool ne wato alhaji Umar fari" wata irin ajiyar zuciya yaji ya sauke had'e da cewa, "Alhamdulilah!." sannan yace dashi, "Masha Allah, Abba ya gidan anwuni lafiya?."

"Lafiya klw barrister kamal, ya.." kafin ya ida abunda zaice cikin zaquwa barrister kamal yace
Chapter 3 · 0% Book details