← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 160

Sashe 36

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da jikin muneera yayi tib'is tukuna tafara qoqarin k'watar kanta daga hannunsa ganin babu sarki sai Allah, da jan gindi tafito shiyar Inna ruqayya na tsaye bakin qofar takasa komawa sai faman zunduma masa zagi takeyi, da sauri ta riqota had'e da ida jawota tafito sukayi shiyarsu tana kuka yace.

"Wannan shine abunda nayi mata, kuma kad'an tagani, idan nakoma ganin qafarta cikin shiyata saina maida ita gurguwar qarfi da yaji." Sannan ya juya yakoma ciki,

Toilet ya fad'a had'e da d'ibar ruwa acikin durom d'in dake ciki yafara sakarwa kansa yana sakin wata irin ajiyar zuciya. Yajima aciki kafin yafito ya hau gyaran falon had'e da sharesa tass, feffesa room freshener yayi soboda tsamin da yaji d'akin nayi sannan yanemi kujera mai zaman mutum uku ya kwanta rigingine kansa na kallon silin zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa

Acan shiyar Inna Bilkisu kuwa saman gadonta suka kwantar da Rashida, hannuwanta da idanuwanta tashiga duddubawa tana son gaskata abunda zuciyarta ke rayamata akanta tun kwanaki biyu da suka wuce saboda yanda ta canza, murmushi tayi had'e da cewa,
"Alhamdulillah ALLAH kaine abun godiya." har lokacin takasa Dena murmushin da takeyi, kallonta fadeela tayi had'e da cewa, "Inna menene?."

Bata tanka taba saidai kallon Rashidar data koma yi tana qoqarin rufe idanuwanta saboda baccin da take ji, baccinta mai isarta tayi kafin nan tafarko tana jin wata irin matsananciyar yunwa dama d'azun data gama abinci bata samu taci ba saboda tare sukeci dashi shikuma alokacin bacci yakeyi,

Kasancewar koda ta tashi bakowa ad'akin yasa tasauko saman gadon had'e da fitowa bakin qofar d'akin ta saki wata uwar hamma dake nuna ba qaramar yunwa take jiba.
"A'a Rashida har kin tashi?." Inna Bilkisu dake sharar cikin rumfar tasu tafad'a tare da d'agowa tana kallonta.

"Eh inna barka da marece, shara kikeyi?."

"Eh wallahi wajenne ya d'anyi datti ga baffanku yana kan hanyar dawowa ke sanshi baya son datti ko kad'an, ya qarfin jikin naki?"

"Alhamdulillah da sauqi Inna bari na riqa maki."

"A'a ki barshi ai nakusa qarasawa, maza jeki tun d'azu mijinki na ciki nasan ran nan nasa a cunkushe uake yanzu, kuyita haquri har ALLAH yakawo qarshen wannan al-amarin kinji ko."

Duqar da kanta qasa tayi tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana murmushi sannan tabar wajen, har takusa shigewa Inna Bilkisu tace,

"Au Rashida." Juyowa tayi tana kallonta taci gaba da cewa "dama nace ki kula da kanki saboda yanzu bake.." Bata qarasa ba saboda hango Inna ruqayya da tayi nafitowa daga cikin d'akinta sai tayi shiru had'e da cewa

"Jeki rashida maya magana dake anjima"

"Mtssss...munafucci kunun kanwa!."

Inna ruqayya tafad'a tana jefo wata tasar Inna Bilkisun data gani cikin rumfarta.

Batace mata qanzil ba taci gaba da shararta ita kuma tawuce shiyarta batare data fahimci kome Inna Bilkisun ke nufi ba.

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___27💎

Tana shiga Kai tsaye kitchen tashiga ta d'ebo abincin a plate, tun kafin taqaraso cikin d'akin tasomaci saboda azabar yunwar da takeji, kwance ta iskosa idanuwansa arufe amma babu alamun bacci yakeyi saboda yanda k'wayar idanuwansa ke rawa, qasan carpet a bakin kujerar da yake kwance ta zauna tana cigaba da cin abincinta hannu baka hannu akushi, a hankali ya jaye hannusa dake saman goshinsa yana kallonta fuskarta a sake tamkar babu abunda yafaru, abincin dake gabanta ya kalla sannan ya kalleta cike da tambaya, saboda iya saninsa tunda tazo gidan tare suke cin abinci yazu ko kimanin tsawon watanni hud'u kenan, to meye dalilinta nayin haka kenan ko haushinsa takeji ya tambayi kansa had'e da tashi zaunne yana kallonta.
'Dago kai tayi ta kallesa tare da sakin murmushi daga haka Bata cemasa qanzil ba Kuma shima bai cemata ba sai data canye abincin tas had'e dayin gyatsa.
"Alhamdulillah" tafad'a tana lashe yatsun hannuwanta har lokacin idanuwansa nakanta, turo baki tayi yasakar mata murmushi tare da miqewa ya d'auko mata ruwa a fridge ya miqa mata, karb'a tayi tasha sannan tamiqe tare da d'auke plate d'in takai kitchen, tray d'in data had'a abincinsu akai ta d'auko takawo agabansa ta ajiye sannan takoma saman kujerar kusa dashi ta zauna had'e da d'ora kanta saman kafad'arsa. "Malamina ka sauko kaci abinci, nabarka da yunwa ko?." Seda yad'an harareta sannan yace. "Bazanci ba!."

'Dan turo idanuwanta tayi awaje tana qyaqqyaf tasu had'e da cewa, "meyasa?. Abincin da kafiso ne nayifa!"

Taqarasa maganar tana b'ata rai tare da nad'e hannuwanta saman qirjinta, mintsili ya kaimata a kumatu had'e da cewa. "Saboda bakya son naci shiyasa kikaci naki bayan kinsan tare mukeci ko fushi kikeyi da nine akan abunda yafaru."
"Laaaa...wlh ba haka bane malamina, kawai yunwa nakeji sosai shiyasa na fara ci, atunanina ma bacci kkeyi, kayi hak'uri nazuba maka kaci nasan kana jin yunwa kaima."

"E.ehm bazanci ba." Yasake fad'a yana nad'e hannayensa akan k'irji kamar yanda tayi d'azu ya juya mata baya, saqalo hannayenta tayi ga wuyansa ta rad'a masa akunne, "afuwan habibyyy.." taja qarshen cikin wani salo daya sashi juyowar da bai tashiba cike da mamaki don bai tab'a jin takirasa da wani suna ba inba malaminta ba, "me kikace habibty?, Pls sake fad'a naji."

Maqe kafad'a tayi had'e da cewa, "o'oh sai in kaci abincin tukuna zan fad'a har sai kace ya isa" zamewa tayi daga kan kujerar tana dariya ta zubo masa abincin a plate, jallop rice ce tasha kayan ciki da kifi dasu irin baqin kifinnan gasashshe mai d'an karen dad'i, saman kujerar tadawo tana riqe da plate d'in abincin da cokali aciki, d'ebowa tayi a spoon takai masa abakinsa ya juyar da kai gefe,

"Meye?"

"Kifad'a mana." Yafad'a had'e da d'an d'aure fuska, dariya tayi sannan tace, "Shikenan! Nafad'a habiby, habiby, habibyyy.." bud'e baki yayi zaiyi magana ta tura masa cokalin abincin abaki had'e da sakin dariya, murmushi yayi tare da nunata da yatsa. "Ke ko?"

Haka tadinga bashi abaki yanaci har yaqoshi ta tattara kayan takai kitchen ta dawo, miqa mata hannu yayi ya zaunar da ita a tsakankanin kafafuwansa ya turo kansa tagefen wuyanta.
"Habibty!" Yafad'a cikin wata irin kasalalliyar murya, "uhmm, habibyn habibty!." Shiru yayi na wasu mintota yana nazarin irin kalaman da zaiyi amfani dasu wajen bata hak'uri akan abunda yafaru, juyo fuskarta yayi yayi mata kiss saiti inda ya d'an kumburo a goshinta sannan ya sake maida kansa agefen wuyanta yace, "kiyi hak'uri, kiyi hak'uri, kiyi hak'uri bisa abubuwan dake faruwa, nasan cewa ba kad'an kike kauda kanki ga abubuwan da mahaifiyat da kuma wasu 'yan uwan keyi maki ba, kwata kwata banajin dad'insu har ga ALLAH domin ke amanace agareni, nakan tsinci kaina cikin damuwa mai tsanani aduk lokacin da naga ana cutar mani dake, zuciyata na quna inajin wani d'aci a maqoshi domin babu abunda nake so araina duniya fiye da inganki cikin farinciki, zallar hak'urinki da tarbiyarki suke galaba akaina wajen kawar mani da damuwa badon haka ba inada tabbaci akan da tuni zuciyata da kuma rouhina sun daina aiki ajikina saboda kasa jurewa ganin duk wani abu da zai cutar dake, nayarda cewa shi so sa'ane kuma dacene tun a ranar dana had'u dake, domin kin zame mani gwana takowane fanni, a kyau kece gwanata, a hak'uri Banda yake, a iya kula da tarairayar miji kinfi mata dubu, girki tsafta da kawaici sai dai nace Masha ALLAH, Alhamdulillah domin duka nasamu awajenki, na tabbata kece alkhairina na duniya da kuma lahira don haka Ina mai sake baki haquri ga yanayin da muka tsinci kanmu aciki, natabbata wata rana zai zamo labari."
Tunda abubuwannan kefaruwa bata tab'a zaunawa ta zubar masu da hawaye ba sai yau, koshi saboda wani nauyine da takeji azuciyarta taji ya sauka saboda dad'ad'an kalaman daya fad'a mata hakan shine yayi silar zubowar hawayenta batare data shirya ba, wud'anda batasan da wace kalma zata fassarasu ba, na bak'in cikin abubuwan da suke faruwa da itane ko kuma na farincikin soyayyar mijinta dake lunkuwa azuciyarta. hannu yasa ya juyo da ita gaba d'aya suna kallon juna tare da tallabo fuskarta yana kallon kyawawan idanuwanta dake zubar da hawaye, bakinsa ya nufo dashi wajen fuskarta tayi saurin rufe idanuwanta hawayen dake maqale aciki suka samu damar gangaro, jira takeyi taji saukarsa akan nata amma sai taji akalarta sauya saboda harshensa da taji saman fuskarta yana lashe hawayen, sannan yadawo ga bakinta ya sakar mata wani irin french kiss daya sa ta sake lumshe idanuwa tana mayarnmasa da martani.
Sunfi tsawon mintuna biyar ahaka kafin ya zare bakinsa daga nata had'e dasa hannuwa yariqe fuskarta yana kallon idanuwanta d'aya bayan d'aya,

"Habibty kidena zubar da hawayenki domin duk d'igar da zasuyi suna yintane tamkar d'igar ruwan wuta abisa zuciyata, nasan ke jarumace kuma akoda yaushe nasara natare dake don haka kikara hak'uri kafin ALLAH ya yalwata mana mutashi nan kinji ko?"

"Habiby ba Ina zubar hawayene akan abubuwan dake faruwane ba, hawayena na zubane adalilin samun nagartaccen miji kamarka, kalamanka nada matuqar tasiri agareni domin ako yaushe d'auke suke da saqonni masu ma'anar dake gamsar dani irin soyayyar da kake yimani Wanda hakan shine babban burina arayu, bana son wannan haqurin da kake bani domin mahaifiyarka ai mahaifiyatace hakama 'yan uwanka nawane don haka duk runtsi zai jure komai akanka matuqar kana tare dani."

"Habibty bakyajin zafin abubuwan da ake yimaki ne?."

"Inaji mana amma girman soyayyarka bata barin hakan yayi tasiri azuciyata." Tafad'a tare da rungumesa. Rungumeta shima yayi sosai tamkar wanda za'a k'wacewa ita yace.

"I dont want to miss you in my life..., I love you for ever and ever and ever.."
Rashida da wasu kalaman tafahimta wasu kuma bata fahimcesu ba tayi murmushi itama tace "Nima haka." dariya yayi don yanada tabbacin ba duka ta fahimci meya ce ba amma tace itama haka duk da dai dad'ad'an kalamaine yayi bamasu illa ba.

"Habibty kema me?" Yafad'a yana sake shigar da ita ajikinsa sosai.

"Yanda kace mana."
Tabashi amsa atak'aice itama tana dariya,

"Tom nagode gobe kishirya zamu fara lesson in sha ALLAH."

"Ni bana so."

"Ai baki isa ba."
Chapter 36 · 0% Book details