← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 160

Sashe 51

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yawwa nace ina nura take?, Nifa tunda yafitarnan hankalina ba kwance yake ba kar yaje garin neman gira ya rasa ido..."
Ai kafin tarufe baki baffa yamiqe tsaye yana nunata da d'an yatsa had'e da cewa. "Qarya kike, wlh qarya kikeyi kice kindamu da Nuraddeen, wai yanzu ke a tunanin ki ke uwace ahaka? tir da halin uwa ko in haka take, maqaryaciyar banza maqaryaciyar wofi, shashasha da batasan abunda takeyi ba, sakaryar uwa kawai to kitambayeni Nuraddeen damuwa kikayi dashine ko a'a?"

"Ya haka malan sai kace wanda ke jiraye dani daga tambayarka yarona saika rufeni da kwandon fitina?"

"Naji hawwa jiraye nake dake amma idan harda gaske kikeyi kina son ganin d'anki sai kifad'a mani ina 'yar mutane take tukuna, don bana haufi akan cewa duk inda yarinyarnan taje ko aka kaita kinada sa hannu aciki, don haka kifad'amun inda yarinyar mutane take naroqeki da ALLAH."

"Buhun ubannan, lallai malan kace wani abu, meya dameni da wannan yarinyar da har zakace akwai sa hannuna aciki, to wlh kul kar inji..." Bata rufe baki ba ya d'auketa kyakkyawan marin da saida ta birkita, kafin ta taso yaqara mata wani, zuciyarsa na tafarfasa yace.

"Anzo wajen hawwa, ahalin yanzu bana yimaki kallon daraja da kimar cewa ke matatace, baki isa kiyi mani jan kunne ba agabana, ayau kimanta da cewa ni Idris d'innan ne da kika sani mai sanyin hali da kuma haquri, wannan Idris d'in dake gabanki shirye yake daya sallamaki har abada, ahalin yanzu ba duka kad'ai da ALLAH ya haramta miji yayiwa matarsa ba hatta azabtarwar da zata iyasa kirasa rayuwarki na har abada zan iya yimaki saboda zaluncin da nake tuhumarki da aikatawa yarinyar mutane, don haka tun wuri ina fad'a maki kitanadi kalaman da Zaki fad'awa jami'an tsaro idan sunzo takanki don wlh bazan bar duk wanda keda hannu acikin b'atar yarinyar nan ba.

Tsaye Yaya hawwa tayi tabisa da kallo cike da mamaki don ko amafarki Bata tab'a tsammanin cewa baffa zai iya yimata hakan ba, tureta yayi daqarfi daga gabansa da take yawuce yabar d'akin, yanajin yanda tafad'a akan qarfen gado kanta yabuge qum..amma ko juyowa beyi ba balle ya kalleta ya wuce abunsa zuciyarsa cike da tsanarta ,
Shikuwa Baffa Usman yana fitowa daga asibiti kai tsaye tashar mota yanufa ya shiga motar da zata kaishi cikin birnin kano, gidajen redio da telebijin yaje yabada iya kud'ad'en dake hannunsa don asa masa sanarwar b'acewar rashida ta kafafen labarai saida ya tabbatar anyi komai tukuna sannan yashiga motar da zata kaishi qauyen yarimawa, cikin sa'a ya tarar da malan balarabe yazo wajen baba, cike da karramawa suka tarbesa duk da dai fuskarsa ta gama nuna baya cikin yanayi mai dad'i.
Bayan sun gaisane cikin natsuwa yayi masu bayanin halin da ake ciki ya qara masu da cewa yanzu haka shima Nuraddeen d'in yana asibiti rai a hannun ALLAH,

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun" kad'ai baba ya iya furtawa daga nan bai koma cewa komai ba saidai sukaga ya b'ingire qasa daga zaunen da yake, ranar baffa Usman yaga tsantsar tashin hankali wanda ba'a samasa rana domin adaidai lokacinne itama umma data shigo d'akin kawo masa ruwa ashe duk abunda baffa Usman ke fad'a taji da kunnenta ne saidai sukaji fad'uwar kofin dake hannunta kan kace me itama tafad'i wajen a some...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___39💎

Cike da tashin hankali baba balarabe yaje ya d'ebo ruwa cikin gida aka yayyafa masu, kusan atare suka farfad'o amma babu wanda ke iya magana acikinsu, banda hawaye babu abunda kezuba daga cikin qwayar idanuwansu, ganin haka yasa malan balarabe yaje wajwn nemo mota don akaisu asibiti, yace wa baffa Usman dake gefe ya rabka uban tagumi cikin yanayi mai wuyar fassarawa yajirasa nan da mintota zai dawo.

Kallo d'aya zakayi masu kasan akwai maganganu acikin bakinsu saboda yanda suka qurawa baffa Usman idanuwa Amma Babu bakin magana sai hawayen kawai da zasu iya fassara maka yanayin da suke ciki, ba'a jima ba malan balarabe yadawo da mota da Kuma matarsa d'aya don seda yakoma go ya d'auko kud'i, nan take suka d'aukesu suka nufi asibiti,

Waya baffa Usman ya d'aga yakira baffa yace ya iskosa yarimawa ga abunda ke faruwa yanzu haka suna asibiti, cikin azama baffa yakamo hanya batare daya sanarwa da kowa halin da ake ciki ba, tafe yake yana addu'o'i abakinsa har yasamu mota, tund'azu ALLAH ne kad'ai yasan awane yanayi baffa kejin kansa saboda tunanin yanda zai fuskanci iyayen Rashida ya sanar dasu zancen b'atar 'yarsu ashe har d'an uwansa yaje yasanar dasu, saidai ayanayin daya ce suke ciki yanzu kuma shine babban abunda yafi d'aga masa hankali, har aka iso qauyen yarimawa baffa baisan an iso ba saboda tsananin yanda damuwa tayi awan gaba da dukkanin ilahirin natsuwarsa.

Kai tsaye asibitin ya nufa yatarar dasu baba balarabe da baffa Usman tsaitsaye cikin halin jimami suna jiran fitowar likita, qarasowa wajensu yai jikinsa duk Babu qwari, cike da jin kunya had'i da damuwa yaba malan balarabe hannu suka gaisa, fuskarsa asake ya amsa masa yana mai tambayarsa halin da Nuraddeen ke ciki tare da jajantawa juna akan abunda yafaru, suna nan tsaitsaye likita yafito ya nufo inda suke, tambayarsa suka shigayi ya jikinsu baba da umma yace su biyoshi office tukuna,

Baffa da malan balarabe ne zaune saman kujerun dake kallon likitan shi Kuma baffa usman na tsaye, seda Dr yayi gyaran murya sannan yafara fad'a masu halin da suke ciki,

Sanadiyar tashin hankali da baba yashiga a lokaci d'aya ya haifar masa da ciwon hawan jini wanda ahalin yanzu yakamu da mutuwar sashen jiki ma'ana yasamu (stroke), ita kuma umma sun dubata amma sun kasa gano abunda kedamunta ba abunda take kira inba Rashida ba, wanda hakan yasa dole sai munyi mata gwajegwaje a qwaqwalwarta ko anan ne tasamu matsala.
Wannan shine cikakken bayanin da likita yayi masu akan binciken da sukayi, gaba d'ayansu sun shiga tashin hankali jin abunda likita yafad'a "innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, ALLAH Kai kasan dalilin jarabta wud'annan bayi naka, ya ALLAH ka samasu hak'uri da juriya kuma kabayyana masu 'yarsu aduk inda take." malan balarabe yafad'a had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya.

Baffa da Baffa Usman kuwa jin duniyar sukayi gaba d'aya tayi masu k'uncin da suka rasa sanin ina zasusa kansu.

••• ••• •••
A 'bangaren Nuraddeen kuwa tun safe bai farko ba har sai bayan sallar la'asar, ko daya farfad'o yad'an samu sauqi sosai amma yana tuna zancen b'atan Rashida zazzab'i yataso masa, cikin qarfin hali yamiqe ya sauko daga kan gadon yana yatsina fuska, ganin bakowa wajen yasa yamiqi hanyar fita cikin asibitin don baffa Ali da aka bari ya kula dashi tuni yabar wajen, acan bakin wata bishiya ya hangosa shida wasu yasa andamamasa furarsa hankali kwance yana sha suna fira, bai tsaya bi takansa ba ya wuce gida, tafe take yana harhad'a hanya har ALLAH yasa ya isa gida lafiya, sashensu yanufa ya shiga cikin d'akin, tsaye yayi yana kallon ko ina cike da fatar zaiga Rashidarsa ta iso gare adaidai lokacin, yafi minti biyar ahaka kafin ya duqe wajen yasaki wani irin kuka mai tsima ran duk wanda ke saurare, jin yayi andafo kafad'arsa da sauri yaciro kai yana kallon sama cike da zimmar ganinta amma sai yaga ashe Inna Bilkisu ce, hannu tasa tagoge masa hawayen da suka jiqa masa fuska sannan ta riqosa ya tashi ta azasa saman kujera, cikin sanyin muryar dake nuna tattare take da damuwa tace. "Nuraddeen bazan hanaka kuka ba, domin b'atan Rashida ba kai kad'ai yashafa ba har mu, Amma Nuraddeen Ina so infad'a maka cewa yanzu ba lokacin kuka bane agareka, lokacine da zaka tattaro dukkanin natsuwarka kayi yaqin gano matarka aduk inda take, Ina so kayi amfani da kud'in da kake dasu ahannunka, iliminka da kuma qarfin jikinka kaje kagano matarka aduk inda take, wannan kukan da wani kwanciya duk ba mafita bane agareka, kazuba kud'inka a kafafan yad'a labarai asa maka cigiyarta, kayi amfani da iliminka wajen tsananta addu'a kuma kasa malamai ayi maka, kayi amfani da qarfin jikinka wajen shiga lungu da saqo kadubo matarka, idan ALLAH yayi za'a ganta Ina tabbatar maka da zaka had'u da ita tunda baka zauna ba kaji ko, don ALLAH kadaure duk yanayin da kake jin kanka aciki kanunawa duniya cewa kana son iyalinka ko tana tare da kai ko bata tare dakai, damuwa dolece amma kada kabari tayi tasirin da zata cutarwa da Rashida kai, don na tabbata aduk inda take matuqar tana a hayyacinta kaine mutum nafarko da zatayi fatan kasancewarsa cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali, don haka kayi haquri kuma karb'i qaddararka hannu biyu ta hanyar qarfafa zuciyarka kaji ko?."

"Eh Inna Bilkisu nagode." Yafad'a yana goge hawayen da suka jiqa masa fuska, miqewa tayi tafita tana fad'in, "Ina zuwa.?"

Binta da kallo yayi aransa yana burin inama ace itace mahaifiyarsa, daya rungumeta yayi kukan sosai yanda zata fahimci yanayin da yakeji koya samu sassauci, yana wannan tinaninne Inna Bilkisu tadawo riqe da kwanon abinci da wani kwanon ruwa da damammiyar fura aciki, saida tad'an riqe fuska tukuna ta ajiye masa kwanon abincin agabansa tace

"Maza sauko kaci abinci kaji."

"Bazan iyaba Inna Bilkisu, wlh bana tunanin abinci zai iya shiga bakina bacin bansan halinda Rashida ita da abun cikinta ke cikiba."

"Ungo wannan to kasha, ai haquri zakayi, idan bakaci ba taya zaka samu qarfi ajikinka har ka iya zuwa nemota. kadaure ko rabine kasha kaji ko."
Inna Bilkisu tafad'a had'e da bud'e kwanon ruwan takai abakinsa, awannan karon Babu yanda zaiyi dole yafara tsutsar furar ahankali yana sha tamkar wani jariri, cike da tausayi ta raja'a akallonsa kawai sukaji anbuge kwanon furar yafad'i qasa gaba d'aya tazube, d'ago kai dashi har ita sukayi da sauri don ganin wanda yayi wannan aika aikar, dik da dama gaba d'aya zukatansu sun gama hakaito masu dako wacece, cike da masifa Inna hawwa tafara magana.
Chapter 51 · 0% Book details