← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 160

Sashe 54

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Maman baby." Don da haka take kiranta sannan taci gaba da cewa. "Kiyi hak'uri, duk da dai nasan cewa awannan yanayi da kika tsinci kanki dolene kiyi kuka amma idan kinduba duk wata gata da ALLAH keyiwa bawa yayi maki, idan saboda ki cutu akayi maki wannan abun ALLAH yahana tunda gaki da ranki kuma da lafiyarki, idan kuma saboda a cutar da abunda ke cikinkine shima ALLAH ya karesa tunda gashi kin haifi abunki cikin qoshin lafiya kuma ya rayaki, idan kuma don asalwantar maki da rayuwane, ALLAH yadubeki da idanuwansa na rahama ya kad'oki a hannun da baza'a tab'a cutar dake ba, don ALLAH ko meye kiyi haquri, in sha ALLAH dakin samu sauqi zamu hannuntaki ga iyayenki, wannan kukan naki bana sonsa sai inga kamar nayi raggwancin baki kulawar daya kamata nabaki ne, keda yakamata kiyi farinciki ALLAH yabaki babynki kyakkyawa tubarkallah kamar ke, natabbata idan mahaifinsa ya ganesa baqaramin jin dad'i zaiyi ba, ko yanzu kika mutu kinbar magajinki mai kama dake da zai gani ya dinga jin sanyi, kiyi haquri kinji ko? In sha ALLAH komai zai daidaita."
A maimakon Rashida tayi shiru sai kukan nata ya sake tsananta, awannan karon ba abunda takewa kuka irin rashin sanin halin da habibynta ke ciki, meyasa duniya tayi masu haka? Me yasa za'a rabasu?, Meyasa za'a haramta masu renon d'ansu da bashi tarbiya atare?, wud'annan tambayoyin kad'aine keyi mata yawo a qwaqwalwa yayinda alokaci d'aya kuma suke sake tunzura zuciyarta wajen sata zubar da qwalla, yanda take kukan yasa nan take b.p d'inta ya sake hawa kasancewar har bayan ta haihun bai koma mata normal ba, da sauri Fatima taje ta kira likita tana d'auke da babyn, allurai akayi mata kafin alaqa mata gorar drip a hannu, nan take bacci yayi awon gaba da ita, ita kuma Fatima taje ta maida jaririn d'akin da ake kula dashi don dama kawoshi sukayi yasha nono.

••• ••• •••
Nuraddeen kuwa yana fita bai zame ko ina ba sai qauyen yarimawa gidansu Rashida don sanarwa da iyayenta halin da ake ciki, abunda bai sani ba tuni su baffa sun sanar masu har dalilin haka ya haifar masu da shiga wani halin, bakin qofar gidan ya tsaya ya ganesa arufe, waige waige yafarayi yana so yaga ko wani yarone ya tambayesa saiga makwabcinsu ALLAH yakawo masa, da sauri yaqarasa wajensa ya gaishesa had'e da tambayarsu ko Ina masu gidan, nan yake sanar dashi halin da suke ciki da abunda ya samesu, wani irin jirine ya d'ebesa da sauri ya dafe iccen dake kusa dashi yana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun."
Anan maqwabcin nasu yatafi yabarsa anan tsaye don da alama bai san cewa shid'inne surikinsu da ake zancen matarsa ta b'ace. Da sauri yabi bayansa ya tambayesa awace asibiti suke ya fad'a masa yayi masa godiya sannan ya wuce asibitin cike da damuwa aransa.

Yana shiga cikin asibitin ya hango Baba balarabe yafito da ward d'in da aka kwantar da umma riqe da wasu takardu a hannunsa, d'aga qafarsa yayi don yasamu ya cimmasa kafin ya b'acewa ganins,

"Baba.." Nuraddeen yafad'a daidai lokacin daya isa inda yake, juyowa yayi yana ganinsa yad'anyi murmushi. "A'a Nuraddeen kaine tafe a wannan lokacin."

"Eh baba ina wuni.?"

"Lafiya klw. Zo muje musamu waje muzauna ko? Wai takardu ne na amso da zamuje scanning da ummanku gobe idan ALLAH yakai ranmu." Baba balarabe yafad'a yana tura tamardun ahannu, gaba d'aya Nuraddeen jinsa yayi kamar wani soko saboda sakacin da take ganin kamar yayi ya b'atar masu da 'yah Wanda har hakan ya jefa mata iyaye cikin matsala amma duk da haka babu wani sauyi d'aya gani atattare dashi da zai nuna yana jin haushinsa.

Tafe suke shi da baba balarabe yana jajanta masa abunda yafaru tare da yimasa 'yar nasiha akan haquri da kuma yarda da qaddara har suka iso ward d'in da aka kwantar da baba, Baqaramin tashin hankali Nuraddeen ya shigaba ganin halin da baba yake ciki, gaba d'aya b'aren jikinsa na hagu ya shanye bakinsa ya karkace baya iya magana, duqewa yayi bakin gadon ya fashe da kuka yana maijin gaba d'aya yatsani rayuwarsa ta duniya, a hankali baba ya d'ago hannunsa na dama ya aza saman kansa yana so yayi masa magana amma yakasa sai dai kawai ya dinga d'an shashshafa kansa hawaye shima nafito masa agefen idanuwa.
Ganin kukan nasa bazai qareba yasa baba balarabe d'agosa daga duqen da yake yariqo hannunsa suka fito tare,

"Baba meya kamata kirani dashi aduniya? Sakaran miji, ko shashasha ko kuma wanda baisan abunda yakeyi ba? nayi sakacin b'acewar matata gashi nacilla iyayenta cikin wani hali kuma nakasa gano wace mafita zan samu don gyara wud'annan kurakuran da nayi, baba bansan ya akayi ba, bansa ta ina aka shiga har cikin gidana ba aka rabani da matata, nashiga waqi'ar da banida mataimaki aciki sai ALLAH, damuwata d'aya shine me yasamu Rashidata, Ina take yanzu, meya faru da ita duka ban sani ba..."

Ganin yanda yake suruttai kamar wani zararre yasa baba balarabe yayi saurin katsesa tare da cewa.

"Nuraddeen rashin Rashida ba kaikad'ai ya shafa ba, hattamu iyayenta da muka haifeta muna cikin wannan damuwar amma dole zamuyi haquri mubarwa ALLAH komai har zuwa lokacin daya qaddari muganeta, baffan nan ka sunyi qoqari matuqa wajen zuwa dubota sannan shi baffanka Usman yakai cigiyarta a kafafen yad'a labarai, don haka kayi hak'uri ka koma gida kayita addu'a, natabbata ubangijinmu yana tare da ita aduk inda take ko don tausayin halin da take ciki."

Sosai yayita bashi magana kafin ya rakasa har bakin gate d'in asibitin bayan ya kaishi yagano umma da har zuwa lokacin kwance kawai take tana ambatar Rashida, Rashida. Nan ma d'in sai dai yayi kuka sosai tare da addu'ar ALLAH ya bayyana ta kodon iyayenta sufita cikin wannan yanayin rayuwa da aka jarabcesu da ita.
Kid'in daya fito dasu da niyar zai shiga can cikin gari yabada gidan redio da telebijin asa cigiyar Rashida da baosan ko nawa bane yaciro cikin aljihu ya miqawa baba balarabe tunda har baffa Usman yariga da yakai sanarwar.

"Baba ga wannan aqara ayi amfani dasu, in Sha ALLAH gobe zan dawo."

"Haba! Ina Nuraddeen, Kai dake cikin wannan halin mezaisa nakarb'i kud'inka, kabarsu ko wani abun kayi dasu kaji ko."

"Don ALLAH baba idan har kad'aukeni d'anki tamkar Rashida ka karb'i kud'innan hakan ba qaramin zafi zai rage mani azuciya ba." Karb'a yai sannan yayi masa godiya tare da fatar ALLAH kabayyana masu Rashida aduk inda take kuma yakareta.

••• ••• •••
Baffa kam tun ranar da abun ya faru bai sake waiwayar gidanba kayansa ma saidai yasa baffa Usman ya kwaso mashi su yakoma warsa acan gidan yayi zaunensa, kusan kwana biyu yayi yana zuba idanuwa ko ALLAH zaisa aga Rashi kafin ya d'auki matakin daya qudurce aransa amma har lokacin shiru babu wani bayani akanta, da kansa yaji sanarwar b'atanta da akasa agidan redio kano da sauransu, haka ga telebijin wani maqwabcinsu ya fad'a masa yaga anyi sanarwar hadda hotonta tana saye da hijabi don daga baya baffa ya shawarci nura dake nan zaune tare dashi akai hoton nata, makarantu islamiyoyi dana almajirai duka yakai sadaka ayi masa saukar alqur'ani da addu'a amma ko mai kama da ita babu wanda yazo yace ya gani, hakan yasa ranar tunda sassafe ko Nuraddeen bai sani ba yaje har central policetatio dake can cikin gari yakai report akan b'acewar surukar tasa, tare da zayyane masu wud'an yake tuhuma akai, nan take 'yan sanda sukayo mota biyu suka kama hanyar bebeji tare da baffa da yanzu gaba d'aya zuciyarsa ta qeqashe, Babu wani sauran tausayi tsakaninsa da kowa keda hannu akan b'atan 'yar mutane, ko yaso ya rarrashi zuciyarsa aduk lokacin da yaje asibiti yaga halin da iyayenta ke ciki da Kuma Nuraddeen daya zabge yayi baqi ya lalace saboda tunaninta sai yaji bazai tab'a iya qyale b'atanta ya tafi ga banza ba.

Address d'in gidan yabasu lokacin da suka shigo garin shi kuma yawucewarsa gidansa bayan yatabbatar masu da cewa karsu qyale mutun ko d'aya daga cikin wud'anda ya lisaafa masu. Kasancewar ya zube masu kud'i masu tsoka don gaba d'aya dabbobinsa dake can go ya saida abunsa yasa 'yan sanda karb'ar umurnin daya basu tamkar wani shugabansu.

Adaidai qofar gidan suka tsaida motocinsu da sai faman ruri sukeyi, yaro suka samu sukace ya shiga ciki yace ana sallama da baffa Ali, yaron nashiga sambai ya wuce shiyarsa yace.

"Wai ana yiwa babansu muneera sallama."

Inna ruqayya dake zaune bakin qofar d'aki tana gyaran goro ta d'ago kai had'e da cewa

"Inji waye..?"

"'yan sanda." Yaron ya bata amsa atak'aice had'e da juyawarsa yafice daga gidan, sai alokacin Inna ruqayya ta tuna da taji rurin motar 'yan sanda ai da gudu tamiqe har tana kifar da kwanon da take gyaran goro ta shige d'aki jiki na rawa ta turo qofa....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_😅Gara nafara da dariya saboda you guzs are amazing, just two day's fa nayi babu update kunata qorafi har dasu kira nasha awaya!🤔 to Ina baku haquri sosai kunsan jiki da jini abun sai a slow🤥 nagode da qauna, kulawa da kuma addu'o'inku agareni, jazakumullahu bikhair, ALLAH duka yabaku aljannah da rahamarsa👏 yanzu kam zaku dinga yimani uzuri saboda ba kullum zakuna dinga samun update d'ina ba saboda wani dalilin, taku a kullum mai qaunarku ALBIEN ROUHI❤️_ if u no u know kawai🤪🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

Page___41💎

Muneera dake gefe zaune tanata kuitar kai ta kwashe da dariya had'e da cewa. "Kaga Inna meye abun gudu don ankira 'yan sanda, ni wallahi bana tsoronsu barima naje nafad'a masu cewa sudena jira saboda baffanmu baya nan" tafad'a had'e da miqewa,
Chapter 54 · 0% Book details