Sashe 104
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"A'a kabarsu kai kuwa ai yanzune zamu qarasa." Baffa yafad'a yana qoqarin wucewa, adaidai lokacin little yafito yana d'an yatsina fuska sanadiyar hasken ranr daya bugar masa idanuwa had'e dayin miqa don tuni yasoma komawa baccinsa dayaga bedawo ba, kamar ance baffa ya d'ago kai sukayi ido biyu da little gabansa yayi wani irin mugun fad'uwar da har saida kwandon dake kansa ya soma fad'uwa, da sauri little yaje ya riqesa tare dasa hannu yatare kwandon yana binsa da kallo, sunfi minti biyu ahaka baba balarabe na tsaye yana kallonsu cike da tausayi, tabbas jini jinine duk inda naka yake ko kuma yashiga kana ganesa, goge 'yan qwallan da suka zubo masa yayi had'e da qoqarin shigewa shagon riqe da kayan tea daya karb'o masa ya karya dake neman hucewa yana fad'in.
"Ka amsar masa kayan mana kutafi kada ka gajiyar dashi garin kallo irin naka." Yayi maganar cikin d'aga murya batare daya sake juyowa ya kallesu ba, karb'ar kwandon little yayi tare da azawa saman kai yacewa baffa.
"Mutafi kaka."
Wani irin yarrr...baffa yaji ajikinsa har kafafuwansa na neman rinjayarsa, gaba d'aya babu wanda yake gani atattare da yaron sai d'ansa, musamman da yayi magana, sak irinta d'aya data d'ansa Nuraddeen, kamanninsa ne kawai suka rinjaya izuwa na Rashida wacce sanin alaqarta da baba balarabe yasa yayi tsammanin ko cikin 'ya 'yansane, juyawa yayi yana kallon baba balarabe da yayi saurin noce kansa kamar yana wani abun lokacin da yaga yajuyo, amma ganin hankalinsa baya wajen yasa yawuce gaba shi kuma little yabisa baya, bini bini baffa ke juyowa yana kallon little dake biye dashi yana 'yan kalle kallen yanda yanayin wajejen kasuwar yake har suka isa, gaba d'aya hankalin baffa yatashi don jikinsa nabashi wani Abu akan wannan saurayin saidai kuma meye?, shine abunda bai sani ba.
Bayan ya ajiye kwandon yajuyo yana kallon baffa had'e da cewa.
"To kaka sai anjima, ALLAH yabada kasuwa mai albarka, Amma kadena d'aukar irin wannan kwandon gaskiya akwai nauyi, koba don kajin dake ciki ba ynayin girmansa kad'ai ya isa yasa nauyin ya gijyar da mutum balle ga kajin sunfi a qirga aciki, ga yanayin tsufa uma qara kadinga axowa yara kana biya, ni kaina da nakeda d'an qarfi yanzu haka nagaji balle kai da shekaru suka ja ga wajen da d'an nisa sosai" don can qasan kasuwar rumfarsa take inda 'yan kaji ke tsayawa.
Tunda little yafara magana baffa ke kallonsa har yakai aya ya juya zai tafi, da suri baffa yakirasa yaciro d'ari biyu a aljihu yana kallonsa ya miqa masa had'e da cewa.
"Karb'a kasha ruwa nagode kaji ko?, Nima ba'a son raina nake wannan wahalar ba yanayin rayuwarce tazo mani ahaka, ga qananan iyali da suka taso kaga ai saida neman nakai ko."
"Eh kaka da gaskiyarka, Amma kada awahalda kan da yawa idan akwai makarkata ko kuwa?, Kabar kud'inka kaka nagode."
Har yajuya zai sake tafiya baffa yasake cewa.
"Karka maida hannun baiwa mana, ai saka makon kyautatawa kyautawa." Ko kad'an baffa baya son yadena jin muryar yaron, wani irin farinciki yakeji marar misaltuwa idan yana saurararsa shiyasa baya son yabar wajen yake jawo wata maganar.
Murmushi little yayi had'e da dawowa yana kallon baffa, shima kansa ji yake kamar tuncan ya sanshi ko kuma yasaba dashi, koma dai meye shidai tsohon yayi masa kuma ya matuqar kwanta masa arai, amsar kudin yayi ya koma mayar masa ga aljihu had'e da cewa.
"A maimakon wud'annan kud'in da zaka bani kaka, kasa mani albarka mana."
A wannan karon dariya baffa yayi idanuwansa cike da hawaye yana fad'in.
"To shikenan ALLAH yayi maka albarka yasa kagama da duniya lafiya."
"Amin kaka, nagode sai anjima, idan zakaje gida ka aika akirawoni idan baka samu wanda zai riqa maka sauran kayan ba, kada ka d'auka da kanka zanxo in d'aukar maka" sannan yabar wajen,
Tsaye baffa yayi yana binsa da kallo har ya b'ace sannan yayi wata irin ajiyar zuciya aransa yana maijin dole zai ajiye alqawarin daya d'auka abaya ya sake tunkarar baba balarabe akaro na ba adadi bayan tsawon shekaru, ayanzu yanaji yayi kuskuren fusata a wancan lokacin daya dena bibiyar labari akan matar d'ansa da abunda ke cikinta, akwai buqatar yamaido komai baya don yasan ko waye wannan yaron?....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___76💎
Binsu Abba yayi da kallo har suka fice kafin yadawo inda take zaune tajuya masa baya ya riqo hannunta, juyowa tayi tana kallonsa idanuwanta cike da hawaye ya girgiza mata kai alamun tayi shiru, yanayin yanda taga jikinsa yayi sanyi ya tabbatar mata da cewa ya sauko daga fushin da yakeyi, batare data yimasa musu ba tamiqe tabiyo bayansa har lokacin yana riqe da hannunta suka nufi wajen dining table inda hajia mama ta ajiye mata abincin ya jawo mata d'aya daga cikin kujerun dake wajen ya zaunar da ita sannan shima yajawo wacce ke kusa gareta ya zauna ya bud'e abincin ya zuba a plate, miqewa yayi yaje ya wanko hannunsa sannan yadawo ya zauna ya dinga d'ibar abincin yana bata abaki, ci take tana zubar da hawaye saboda ganin irin girman soyayyar da yakeyi mata, a d'ayan b'angaren zuciyarta kuwa tunani takeyi yanda zata iya haqura da soyayyar da takeyiwa Abu sumayyanta don tabiya mahaifinta d'imbin qaunar da yake nuna mata.
Ba tare daya cire hannunsa a plate d'inba har saida yaga tacinye abincin dake cikinsa tas don yasan baqarama yunwa take jiba sannan jawo gorar ruwa da lemu yayi ya tsiyaya mata a cup tasha sannan yasa hannu yagoge mata hawayen dake neman bushewa a saman fuskarta had'e da cewa.
"Meye kuma na kuka yanzu?."
Riqo hannunsa tayi da dukkanin hannayenta biyu tana fad'in.
"Don ALLAH Abba kayi hak'uri, ba Ina nufin zan bijire maka neba ko kuma na b'ata maka rai, kawai nidai ina son.."
Saurin dakatar da ita yayi kafin taqarasa tahanyar d'aga mata hannu had'e da cewa.
"Bana son jin komai tunda kinzab'i rayuwa da Wanda bakisan asalinsa ba, don haka tunda kin girma yanzu bakya son farincikina kamar yanda nake son naki, na amince kije ki auresa?"
"A'a Abba ba haka nake nufi ba,"
"Ya isa, kice yazo Ina nemansa."
"Abba bazai yuyu ba."
"Saboda me?"
"Karatu yakeyi, kuma mahaifiyarsa tace ya ajiye zancen soyayya ko wani aure agabansa har sai ya kammala."
Shiru Abba yayi yana kallonta cike da mamaki, wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke cike da takaici yace
"To ya kike so ayi?, Nidai bazan zauna dake agabana Ina kallonki ba Dole ashekararna zanyi maki aure, shi kuma kince karatu yakeyi kuma mahaifiyarsa tace ya ajiye zancen aure agefe, to ya kike so ayi?"
"Abba ayi haquri yagama, ni zan jirasa har ya kammala ko kuma nima naci gaba da karatun idan jarabawarmu tafito?"
"A ina?, Ke wace yarinya kika tab'a ganin mun bari taci gaba da karatu a makarantar gaba da secondary acikin gidannan?"
"Abba Babu, Amma ai kamawa takeyi wlh Abba shi kad'ai ne nake tunanin zan iya rayuwa kuma insamu isashshen farinciki atare dashi kuma kaima nasan zaka so hakan agareni, don ALLAH Abba ka amice mani"
"Zanyi tunani akai, Amma idan aka samu qamshin gaskiya akan zancen da 'yar uwarki hajia nafeesa tafad'a mani koda kuwa makamancinsa ne acikin rayuwarsa to bazaki auresa ba koda kuwa hakan na nufin zaki qarasa rayuwarki me acikin d'aki baci ba sha." yafad'a tare da miqewa yabar d'akin ransa duk adagule, kawai ya amince da hakanne saboda bayason taci gaba da zama cikin yanayin da take ciki, amma aransa ya d'au alwashin tunda har mahaifiyarsa bata buqatar aurensa nan kusa to zaiyi amfani da wannan damar ya aurar da ita ga wanda ya dace acikin shekarun kafin lokacin da zai sake waiwayarta yayi.
Binshi tayi da kallo har yafita, aranta tana mai shakkun abubuwan daya fad'a don kar tasan mahaifin nata, tunda har ya furta baya son shi to babu yanda zai iya fahimtar abunda zayatarrar akan kowaye masoyinta don kusan tasan duk wasu abubuwa akansa bai b'oye mata ba, musamman data tambayesa dalilin da yasa hajia nafisa ke kiransa da shege akoda yaushe, amma dai ko meye zataci gaba da rayuwarta yanda tasaba batare data ba wani fuskar da zai iya tunkararta da maganar soyayya ba har zuwa lokacin da Abu sumayyanta zai kammala karatunsa yadawo gareta.