← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 160

Sashe 34

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Saida safe yayi masu sannan yawuce agaba tana biye dashi abaya, adarare baffa Ali ke satar kallonta aransa yaji natsuwar yarinya ta kwanta masa arai duk da dai zuciyarsa bata buqatar haka, Amma Babu yanda zaiyi don yabon gwani yazama dole, ko maqiyin ALLAH ya kalli Rashida yasan batada makusa ta ko ina gata da shawar kallo a fuska, kallo d'aya zakayi mata taburgeka idan kuma ka zauna da ita cikin qanqanen lokaci zata shiga ranka wanda hakanne yasa cikin lokaci qalilan soyayyarta tayiwa Nuraddeen mugun d'auri azuciya.

Kwanci tashi babu wuya awajen ALLAH tuninrashida tabuge sati d'aya agidan, abubuwa da dama sun faru na b'acin rai gareta amma bata tab'a tada kai ta kalla ba, kullum addu'arta shine kada ALLAH yabarta da dubararta acikin alamurranta kuma yabata haquri mai yawa agidanta, tana samun kula sosai awajen Inna Bilkisu dasu baffa Amma awajen yaya hawwa banda tsangwama da kyararta babu abunda takeyi, Babu ranar da zatazo bataje ta gaisheta ba kuma duk take saita b'ato mata rai, hakan kuma bazai hana gobe ta koma ba, musamman tacire kular da take zuba mata abinci kullum safiyar ALLAH Amma bai hana ta iskota da kwano tace tazubo mata abinci, wanki da sharar gida duka yimata takeyi amma koda yaushe dad'a tsigarta takeyi, kulawa da tarairayar da take samu awajen Nuraddeen yasa bata ajiye abubuwan agabanta balle su dameta, gashi akullum idan umma takirata cikin yimata wasiya da haquri take Wanda hakan yaqara zame mata linzami wajen gudanar da rayuwarta agidan, baffa kuwa tun tana jin kunyarsa har tadena ta d'aukesa tamkar mahaifinta, lokuta da dama takan shiga wajensa idan Nuraddeen baya nan da littafanta na arabiya ya dinga qaramata daga inda ta tsaya agida, wasu lokuttan kuma tayi masa gyaran d'aki ta share ta kawo masa abinci yaci, hakn kuwa ba qaramin tai maka masa yayi ba don daka kallesa zaka fahimci yasamu sauyi arayuwarsa,

Wannan dalilin yanqara haifar mata da tsana mai qarfi azuciyar Yaya hawwa fiye da wacce take yimata ada, hakan yasa tasake d'aura d'amarar ganin tafidda ita gidan tako wane hali, duk ranakun da Nuraddeen yake gida Yaya hawwa batada wajen zama imba shiyarsu ba, haka zata ararrashe akan kujera tace akunna mata kallo adafa mata wannan a soya mata wancan, duk wani motsi da zasuyi akan idonta basuda wani shaqat, ga Nuraddeen mayen soyayyane yanaso akoda yaushe yadinga rab'ar jikin matarsa Amma bayada wannan damar saboda yanda tayi masu kane kane, tun Rashida Bata damuwa har taso ma jin daban saboda tun hutun sati biyun daya d'auka yagama sangartata da kuma lalatata da kalolin soyayyarsa, sun koma saidai suyi soyayyar a kitchen idan tace ta d'ago mata wani abun sai yayi kamar zai fita shi kuma anan yake samu ya lallab'a sushige suyita soyayyarsu kamar wasu munafukai, randa Yaya hawwa tagani kusan Tara masu jama'a ta tashiyi saboda masifa sai kace ba miji da mata ba, wai sun maida ita 'yar iska sun barta a d'aki ita kad'ai,

A ranar baffa yakirata yayi mata fad'a sosai akan taqyale yaran nan tadena shiga shiyarsu inbada qoqqwaran daliliba kada mutuncinta yazube, ai kuwa tayi masa tas tace bazata Dena ba in ya isa ya taso ya riqe mata qafafuwa ta hanata shiga, tsananin b'acin rai ranar daqyar yayi bacci saboda ciwon daya nemi taso masa kamar zai kashesa.

Haka aka d'aukesa akayi asibiti dashi da safe aka duddubasa had'e da yimasa allurai sannan suka dawo,

Aranar data tashi shiga shiyar duk saida tasa aka kirawo mata yaran gidan tace su ahigo suyi kallo suma su d'ebe qeyar ido, adako korarsu takeyi tana hantararsu muneera ba kunya itama tabisu sukaje suka cika d'akin tab ko masokar tsintsiya babu banda hamami babu abunda ketashi aciki, da yake lokacin har tagama girki kawai ta d'auki na baffa tanufi qofar fita riqe dashi zata kaimasa bayan tasa takunna masu kallon, tana wucewa Yaya hawwa tayi tsaki had'e da cewa "yarinya indai wannan gidanne sai nasa kinficesa da kaifin qafafuwanki."

Nuraddeen kuwa dama yana uwar d'aki kwance yana bacci sai dai kawai yajiyo yayar yara afalo da sauri yafito don ganin ko lafiya,

Tsaye yayi cak yana kallon ikon ALLAH sake da baki tare da kallon mahaifiyar tasa data ashisahire saman kujera, tsabar b'acin rai baisan sadda yayi kukan kura ba yafara fatattakar yaran daga d'akin, aguje duk suka fita in banda muneera da tayi tsaye tana kallonsa had'e da susar kanta, wani irin zazzafan mari ya d'auketa had'e da cewa.

"Uban me kikeyi anan."

Kallon yaya hawwa data miqe tsaye tana gyara zanenta tayi dafe da kunci tana kuka tace,

"Inna ce.." tare da nunata,

"Buhun uba!, yaushe nace kishigo ba yara nakira ba kika taso da wud'annan gwalmammin qafafuwa naki kika biyosu don kina sakarai, Kai kuma akan me zaka koresu suna kallonsu."

Shiru yayi hannunsa riqe da kunkuru ya sa d'ayan ya shafo kansa sannan cikin b'acin rai ya sake d'auke muneera mari yana fad'in, "maza kibar d'akinnan kafin naji maki" b'are baki tayi tare da fad'uwa zaune wajen tasa wata irin muguwar qarar da saida Yaya hawwa dake shirin komawarta tazauna akan kujerar tazabura tana fad'in.

"Ke munafukar ALLAH tashi kifita kafin nima naqara maki."

Rashida, Rashida, Rashida, Nuraddeen yashiga k'wala mata kira ransa ab'ace, dama gashi cikin b'acin rai ya wuni saboda halin da mahaifinsa ke ciki, basu jima da dawowa daga asibiti bane yasamu ya kishin gid'a sai ga wani b'acin ran mahaifiyarsa na neman qara masa....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___26💎

Rashida kuwa dake can d'akin baffa takai masa abinci bata san wainar da ake toyawa anan ba saida Aysha yarinyar Inna Bilkisu ta iskota aguje tafad'a mata, murmushi kawai tayi batare data nuna abun yadameta ko kad'an ba taci gaba da yiwa baffa yankan farcen da take yimasa don koda tashigo ta iskosa yagama cire na hannuwa yana dubarun yanda zai duqo ya cire ta qafafun shine takarb'i rezar tana qarasa masa suna d'an fira jefi jefi.
Chapter 34 · 0% Book details