← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 160

Sashe 85

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gamawa takoma takwanta tana cigaba da saurarar kukan nasa, ahankali tafara jin sautin kukan nasa na ragewa har tadena ji gaba d'aya, ajiyar zuciya tayi sannan tagyara kwanciyarta har bacci b'arawo yazo ya saceta.

Haka sukayi ta fama dashi har kwana biyu duk da qarfin hali kawai ne Fatima keyi itama kullum da zazzab'i take kwana, amma saboda shi take jurewa, arana ta uku ne safiya nawaye koda Dr nura yatashi yaganta a qudundune cikin bargo jikinta sai faman rawa yakeyi,

"Subhanallahi, Fatima bakida lafiya ne?" Yafad'a yana yaye bargon, yanda yagata ba qaramin tayar masa da hankali yayi ba da sauri ya Ida cire bargon yatada ita had'e da rungumota ajiki yana tattab'a wuyanta da goshinta,

"Fatima ko ciwon kanne?"

Yafad'a arud'e da sauri ta d'aga masa kai had'e da cewa.

"Inajin sanyi sosai."

Yatabbatar da haka don gaba d'aya jikinta yayi zafi sai rawar sanyi takeyi,

First-aid d'insa yatashi ya d'auko yaciro maganinta na ciwon kai da take yawanyi ya b'alla mata yabata tasha ya had'a mata dana maleria sannan ya maida ita ta kwanta ya lullub'a mata bargo yana yimata addu'a.
_As'alallahul azhim, rabbil arshil azhim, anyashfiki, laa ba'asa d'ahurun in sha ALLAH_

Ya tofa mata had'e dayi mata sannu sannan yayi kissing d'inta a goshi yabar d'akin, bayan mintuna biyu yadawo ya d'auki little dake sharkar baccinsa hankali kwance dama haka yakeyi, ya hanasu bacci da daddare da safe kuma yayita sharkar abunsa har rana, yanufi wajen Rashida dashi yace tagyarashi zai kaishi wajen ammie Fatima batada lafiya, nan take Rashida taji ba dad'i aranta sai take ganin kamar rigimarshi ta haifarwa da Fatima rashin lafiya.

"Uncle baka ganin zai dami ammie sosai tunda baya bacci da daddare."

"Nooo..Bakomai ki gyarashi, ai taso akaimata shi tun farko mu mukaqi ganin zaifi sauqi tunda yafi sabawa damu, amma yanzu tunda ga dalili sai akaimata shi, koba komai zata sama mashi maganin da ake ba yara na yaye tunda mu bamuyi dubarar haka ba?"

"Shikenan uncle." tafad'a tare da karb'arshi agurguje tashiga shiryashi, koda yadawo d'auke da akwatinsa har tagama shiryashi yakarb'esa sannan yanufi wajen ammie dashi.

Satinshi biyu a hannun ammie kuma yana samun kulawa sosai wajenta da kuma umma da kusanma yayen awajenta yake, don matuqar dady na part d'in ammie to awajenta yake kwana, little kam har zazzab'i yayi shima kusan sau biyu amma Rashida bata tab'a zuwa dubosa ba saidai Fatima da Dr suje duk da har yanzu itama tana fama da zazzab'in, babu yanda fatima batayi da Rashida ba akan taje taduboshi don har saida aka kwantar dashi asibiti na kwana d'aya amma taqi zuwa.

Baba balarabe kuwa da aka sanar dashi safiya nawayewa yaje ya sanar da Yaya Maryam suka yanke shawarar zasuje ganinsa idan ALLAH yakai ranmu gobe,.....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___65💎

Nanfa dady yayi gyaran murya had'e da cewa.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, inaga yakamata ace kowa yanemi waje ya zauna hakanan tunda ubangiji ya nuna ikonsa yanda yake so, alokacin da yake so kuma adaidai inda yake so, duk da dai azahirance wannan abun daya faru abun mamakine da kuma ban al-ajabi agaremu saidai bazai kuma hanamu fahimtar ko meye ke wakana awannan wajeba duba da kuma la'akarin yanda alokaci d'aya ALLAH ya dunqule ahalin da muke tunani biyu ne atare damu yakoma ahali d'aya, wannan abun farincikine da kuma murna agaremu, don haka ina mai neman alfarmar kowa yanemi waje yazauna ko don baqinmu da suka shawo hanya na tsawon awanni akwai buqatar ace sunci, sun sha kuma sun huta tukuna sai acigaba da jajantawa juna wannan al'amarin inaga hakan shiya kamata."

Takowa baba yayi zuwa wajen alhaji ubale fuskarsa d'auke da farinciki marar misaltuwa yamiqa masa hannu suka gaisa, murmushi alhaji ubale yayi tare da riqe hannun har suka nemi waje suka zauna yana fad'in.

"A gaisheka mai gayya mai aiki."

Juye juye baba yafarayi yana neman Dr nura wanda shine yaje yakirawosa ganin abunda kefaruwa, cike da mamaki ya hangosa ajikin qofa yanad'e hannayensa aqirji yana tunano ranar daya fara ganinsu baba, sai yau yatuna da muryar umma dako yaushe idan yai yake tunanin inda yasanta ashe ta maman boy ce, lalle ALLAH gagara misali ne kuma huwarrahmanu yau yaqara imani akan cewa tabbas duk yanda bawa yakai maqura wajen son had'a abu aikin banza yayi matuqar ba ALLAH da kansa yaso hakan ba, yamatuqar sha wahala wajen neman iyayen rashida don ya had'asu amma ALLAH bai yarda da hakan ba sai yau da yaga dama, sai gashi cikin sakanni ya had'asu da kansa, haqiqa al'amarinsa abun girmamawa ne kuma duk wanda baiyi imanin cewa shi kad'ai keda iko wajen had'awa da kuma rabawa ba, ansa da hanawa, qaddartawa da kuma jarabtawa, iko akan komai aduk lokacin da yake so, ayanda yake so,a kuma inda yake so haqiqa yayi asara duniya da lahira.

Da hannu baba yayi masa alama da yaqaraso daga ciki sannan yabaro wajen yana murmushi, duqawa yajeyi agabansa da sauri ya rungumesa yana fad'in.

"Nagode sosai dr."

Rashida kuwa gaba d'aya ta naniqe ajikin umma takasa bari tamatsa konan da can, so take ta tashi tariqowa ammie abinci ashigo dashi amma itama shauqin soyayyar 'yar tata yahanta motsawa wajen, gani take kamar inta saketa zata sake dawo ta tadda bata nan, gashi bazata iya barin ammie taci gaba da kaida kawo ita kad'ai ba, don haka sai tamiqe riqe da hannunta kamar wacce za'a kwacewa tanufi kitchen d'in da ita, gaba d'aya falon sukabita da kallo musamman Dr. da yau yamatuqar qara gaskata kamar dake tsakaninta da umma da kuma little dake hannun fatima yana zallo ta d'aukesa da sukazo wucewa taqi.

Suna kaiwa bakin qofar shiga kitchen sukaci karo da ammie ta d'auko kuloli da sauri umma tamiqa hannuwa zata karb'a tace.

"A'a umma, ai kuma yanzu shikenan wannan aikin yadawo hannun maishi dama taimaka mani ne kikeyi, gashi da alama yau maman boy bazata bari ko lumfashi kiyi ba."

Sai alokacin umma talura da yanda ta k'wak'wume hannun Rashida sosai da sauri tasaketa cike dajin kunya tana karb'ar kulolin hannun ammie sannan tabar kitchen d'in.

Ganin ammie naqoqarin d'auko wasu kayan yasa Rashida itama ta taimaka aka jejjere abincin kowa yaci ya qoshi,

Bayan sun kammala aka shiga maida maganganu inda Dr yashiga basu labarin adadin mayannun da yayi wajen nemansu da had'uwar da yayi dasu atasha da irin halin daya tsinci Rashida aciki tare da irin ciwon da little yayi tamkar bazai rayuba, duk dasu baffa da daddy sunsan da labarin tawani b'angaren yanzu su baba yake baiwa hakan bai hanasu jin tamkar yanzu suka fara jinsa ba, umma da baba sun zubar da hawayen cike da tausayawa 'yarsu sosai kafin baba yamiqa hannu yakarb'i little Nuraddeen dake hannun Dr.

"ALLAHU akabar, duk wannan abun daya faru anyisa ne saboda kada kazo duniya karayu, amma da yake kai alqawarin ALLAH ne saida ya tsaro fitowarka tahanyar jarabta mahaifinka da mahaifiyarka, haqiqa rashin sani yafi dare duhu sannan alqawarin ALLAH tabbatacce ne ko ana so ko ba'a so, badon haka ba dabanyi kwad'ayin aurar da mahaifiyarka abagiren da ba'a buqatar taba duk da dai nasan cewa matsalar ba daga mahaifin kabane."

'Dago kansa yayi had'e da yima Dr godiya marar adadi kafin suma su dady yayi masu godiya sosai shida sauran 'yan uwansa san mazan suka tashi suka tafi wajen sallah su kuma matan suka tsaya nan part d'in ammie sukayi tasu,

Rashida kam bin umma tayi sashenta sukayi sallarsu atare, addu'o'i sosai da washi da yabo umma tayi ga ALLAH tana mai godiya daya maido masu da 'yarsu agaresu cikin qoshin lafiya, haka shima baba har kowa yafito masallaci aka barosa shikad'ai yanata yiwa ALLAH godiya.

Bayan sun dawo suna zazzaune falo ana sake maida firar yaushe gamo can sai ammie dake zaune tare dasu ummu taqara volume d'in makekeyir tv d'in dake laqe a bango tana fad'in. "Alhaji gafa maimaicin shirin da kake so nakiwon lafiya uwar jiki, da baka samu ka kalla jiya ba."

"Af sun fara?" Dady yafad'a had'e da maido hankalinsa ga tv sannan yace.

"Ai inaga saidai nahaqura wannan karon tunda banida lokaci, ki saurar inyaso anjima saiki maimai tamani tunda naga kema yanzu kina son shirin."

"Eh gaskiya Ina so saboda akwai abubuwa masu muhimmanci da ake qaruwa dasu ciki ko umma?"

Taqarasa maganar tana kallon umma dake zaune ita dasu Yaya Maryam suna fira, Rashida kuwa nacan d'aki ita da fatima da little.

Sosai ammie tanatsu tana sauraren bayanin da likita keyi akan wata cuta da matar da ake nunowa wadda ke d'auke da ita su kuma sunaci gaba firarsu.

"Yawwa 'yata zo kiga maimaicin labaran jiya da nakiraki na fad'a maki cewa yau ki kalla saboda it's very important to all the marry woman."

Ammie tafad'a tana kallonsu Fatima dake fitowa daga cikin d'aki,

Wata irin qara sukaji Rashida dake bayanta tasaki had'e da cewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, umma..uncle.baba."

Gaba d'aya duk tabi duk ta rud'e ta kasa yin magana sai nuna tv takeyi da ake nuno irin yanayin da Yaya hawwa keshiga idan ciwonta ya tashi.

Kafin kace me duk sun maido hankalinsu akanta Fatima na rirriqetatana tambayar ko lafiya, yanda sukaga hankalinta ya tashi yasa suka maido hankalinsu ga tv suma suna son fahimtar ko meye dalilin da yasata firgita hakan, iya kallon da zasuyiwa matar da ake nunowa a tv sunyi amma basu gano komai ba saboda da yawansu ma basu santa ba balle su iya ganeta cikin wannan lalurar da take ciki.

Saida aka d'au d'an lokaci ammie dake riqe da hannun Rashida jikinta har tsima yakeyi tace.

"Alhaji inaga bari akashe kallon nan, domin yarinyar nan jikinta har wani cira yakeyi."

Har tamiqa hannu zata kashe Yaya Maryam tace.
Chapter 85 · 0% Book details