← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 160

Sashe 159

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai alokacin tafahimci dalilinsa na ranar daya dinga cewa kada tazo ita kuma ta nace badon tasan da abunda ke faruwa ba, Wanda badon girman addu'ar iyayen nata ba data tabbata babu abunda zai hana mafarkinsa ya tabbata ko don bijirewar data yimasa da yace kada tazo, tabbas tayi kuskure Amma daga yau bazata koma bijirewa iyayenta ba da yardar ALLAH.

Ganin yanda tad'an canza yasa Abba yayi murmushi had'e da cewa.

"Ki kwantar da hankalinki dota, komai yariga daya wuce babu abunda zai faru in sha ALLAH, ni abunda ma yafi bani mamaki a mafarkin, shine wasu mutanen dana gani wanda bangansu yanzu atare daku ba cikin family d'in nasa."

Dariya su uncle h sukayi harda hajia mama tace.

"Ikon ALLAH, to alhaji ai ba lallai bane ace duk abunda kagani a mafarki dole ka ganshi azahiri ba, tunda gashi kaga batool ta haukace gata da hankalinta, little ya rasu gashi kuma raye don haka badole sai kaga komai ya bayyana ba."

"A'a hajia mama, da gaskiyar Abbana, amma dole yayi mamaki, Abbana zainab d'in daka gani a mafarkinka autace, d'iyarsu Dr da mama Fatima tazo maka a matsayin qanwarsa, qila antabayin zancenta agabanka, shi kuma wannan abokin nasa inaga dai Dr ne har yau zancen shi barrister ne shi kuma matsayin gwaggone mafarkinka ya qwace yabawa abokinsa na mafarki daka gani"

Aikuwa batool narufe baki da wannan dogon bayani nata duk aka kwashe da dariya a falon kowa na ganin wautarta ciki harda little da har yasoma hawaye, kaikaita idanuwan iyayenta tayi takai masa mintsili a gefen ciki tare da watsa masa harara, hajia mama tace,

"Ahaf! In dai shirmen batool ne ai tafiye nan, bari ni naje na kwanta don bazan iya dashi ba"

Bayan kwana biyu Abba yafara fita office said gashi ranar ya dawowa Rashida da takardar shedar samun aiki a federal high court dake nan cikin kano, ta matuqar mamakin yanda yayi neman mata aikin har ya gama batare daya sanar da ita ba, don ko takardunta batasan lokacin daya d'auka ba, shiru tayi tana tunanin ta ina ma zata fara yimasa godiya don har ga ALLAH tana sha'awaryin aikin kuma taji dad'in wannan kyautatawar da yayi mata sosai, Bata tab'a kawowa ranta cewa zai amince tayi aikin ba don gwargwado ALLAH yarufa masu asirin da koda da ita har shi basu nemi aiki ba zai ishesu arayuwa don babu abunda suka nema aduniya suka rasa sai gashi cikin ruwan sanyi da yake babba yake cikin gwamnatin kuma takardunta sunyi kyau sosai yasama mata aiki, kamar yasan abunda take tunani aranta yace.

"Kidena matsawa kanki da tunanin mme zakiyi mani akan haka ko a ina nasamu takardunki ko kuma yanda na amince dayin aikinki duk da bamu rasa komai ba domin kin cancanci inyi maki fiye da hakan, sannan zuciyarki da tawa abu d'ayane duk abunda kike so nasani kinga kuwa dole nayi makishi matuqar zai sakaki farinciki, fatana kawai kici gaba dayi mani soyayya mai yawa tare da kula dani yanda yakamata."

Murmushi tayi sannan ta kallesa had'e da cewa.

"Shi kad'ai kake buqata...?"

Kafin tarufe baki yayi saurin bud'e hannayensa had'e da cewa.

"Tare da wannan."

Cike da dattijantaka irin tamanta tayi murmushi sannan tashige tsakiyar hannayen nasa d'aya bud'e ya mayar ya rufe yana mai d'ora kansa saman kafad'arta, tace

"Hmm! Gaba d'aya kai baka tsufar da wannan soyayyar taka habiby."

"Habibty kenan, ai soyayya bata tsufa matuqar nagartacciyar ce, mutanen da keyinta kad'ai ke tsufa ni kuma awajena tsufa baya hana soyayya.

Yaqarasa maganar had'e da kissing d'inta saman kai.

" _Thank you habibty, thank you so much for your kind gesture it really made my day more special, you took time and did something magical i won't ever forget this all my life, thanks! a word is straightly from my heart for being so considerate and kind thanks a lot! and really luv you so much._"

Ta fad'a tare da qara shigewa jikinsa.

Hannu yasa cikin aljihu ya ciro makullin sabuwar motar daya siyo mata don fita aiki sannan yacirota daga jikinsa ya riqo hannunta ya aza mata akai, ware idanuwa tayi zatayi magana ya aza yatsansa abakinta had'e da cewa.

"Me zai hana kici gaba da qara yimun addu'a a maimakon wannan godiyar, wannan makullin motar kice anjima sai muje ki d'auko."

Yaqarasa maganar had'e da kashe mata ido d'aya yayi kissing forehead d'inta yana murmushi sannan yabar wajen.

Wannan karon Rashida kam harda hawayen farinciki tayi, tare da d'aga hannye sama tayi masa addu'a Mai tsawo sannan tabi bayansa.

Cikin sati d'aya Dr Nuraddeen yaje da Rashida sukayi duk abunda ya kamata wajen aikin nata sannan tasoma zuwa.

Umma tayi farinciki sosai da tasamu labari Kuma taroqi ALLAH daya tsare mata 'yarta sannan ya sanya alkhairi mai yawa acikin aikin nata, taso ace mahaifin Rashida naraye taga irin farincikin da zaiyi na cikar burinsa daya tabbata ga 'yarsa amma inaaa, mai rabawa tariga taraba saidai fatan ALLAH yajiqansa mukuma yasa mucika da imani.

*BAYAN SATI BIYU*

Bayan sati biyu da komawarsu batool borno ALLAH ya sauketa lafiya anyi mata tiyata aka fiddo mata da kyawawan yaranta gaba d'aya maza sak ita, inda murna ba'a magana awajensu Rashida da Dr Nuraddeen tamkar su tashi sama tsabar farinciki don har sunfi iyayen jariran murna, wanda kasancewar kwananta uku aka sallameta saboda tiyatar tayanzu anci gaba sosai sati na zagayowa aka rad'awa yaran suna, Hassan yaci sunan baffa Usman wato (Usman), shi kuma Hussain yaci sunan Abba mahaifin batool wato (umar faruq), batool taso abarsu da sunayensu amma little yace a'a haka yakeso adinga kiransu, tabari idan tahaifi wasu 'yan biyu maza sai abarsu Hassan da Hussain, Babu yanda ta iya dole tabi ra'ayinsa tare da fatar ALLAH yaraya matasu rayuwar musulunci, Amma azuciyarta taraya cewa itakam da haihuwa ba yanzu ba balle yace idan ta sake haihuwa kuma waima wasu 'yan biyun sai kace akuya, Sosai Abba yaji dad'in samun takwara haka ma baffa yaji dad'in takwaran da aka yiwa d'an uwansa tare da saka masu albarka.

Baba balarabe ma yamiqa dukkannin haqqin Rashida na gado da umma agaresu tare da dabbobin dake hannunsa daya jujjuaya masu da wasu kud'ad'e da ake karb'a na haya, wanda nan yayi masu bayanin cewa daga baya da yaga gidan na shirin mutuwa ne ya yanke shawarar zuba 'yan haya aciki tunda yayiwa umma magana tuntuni akan gadon tace duk yanda yayi daidaine tunda gwargwado suna cikin wadata ita da Rashida yayi amfani dashi har lokacin da buqatar karb'arsa zai taso, duk da haka saida yasa aka raba aka cire masu haqqinsu shine yasayi dabbobi yana yimasu kiwonsu, acikin kud'in hayar da ake bashine yake cida dabbobin da sauran abubuwa, yanzu kuma yamiqa komai ne agaresu saboda ganin yayi rauni ta ALLAH zata iya kasancewa kansa akoda yaushe shiyasa ya hannunta masu abinsu, sukayita yimasa godiya sosai bayan sunyi masa alkhairi.

Rashida kam kud'ad'enta da baba balarabe ya bata da wudanda baffa yakawo mata acan qauyensu tahad'asu tabayar tace agina masallaci sadaqatul jariya zuwa ga mahaifinta, da Basu isa ba Dr Nuraddeen ya qara mata wasu aka Ida kammala ginin.

Yaya hawwa kuwa cikin taimakon ALLAH da Nuraddeen ya kaita asibiti aka aunata akace bawani magani da za'a yimata idanuwanta ba zasu iya warkewa ba balle ganinta yadawo Rashida ta nace da daddare wajen yimata addua'a tana tofa mata ga ruwa ita da baffa Ali tana basu susha kuma su shafe jiki ita kuma idanuwa tun da safe kafin suci komai sai gashi duk sun warke gaba d'aya bisa yardar ALLAH, qurajen baffa sun b'ace kamar bai tab'a yi ba, ita kuma yaya hawwa ganinta yadawo tas. _('yar uwa kinada buqata ko wani abu dake damunki?, to kijure kuma kijajirce dayin wannan addu'ar👇, wlh tallahi matuqar baki gajiyaba dayi kuma kikasa yaqini akan ubangijinki to zakiga biyan buqata da waraka da yardar ALLAH, itace Rashida tayi har baffa Ali da Yaya hawwa suka samu waraka ga cutukkan da ake tsammanin sai mutuwa tsakaninsu dasu)_

A kullum takan tashi da daddare misalin qarfe uku tayi arwala saita sallaci raka'a biyu ta nafila tare da 'yan ruwa agefenta kamanin rabin kofi.
_*A raka'a ta farko tana karanta suratul ikhlas, wato qul'a'uzu birabbin nas qafa goma(10) saita tofa acikin ruwan sai tayi ruku'i, idan ta d'ago daga ruku'i saita karanta wata (suratul ikhlas) qafa ashirin(20) ta tofa cikin ruwan sannan taje sujada ta farko idan ta d'ago saita karanta suratul ikhlas d'in qafa uku(3) ta tofa saita koma sujada ta biyu, idan ta d'ago ta sake karanta qafa uku(3) ta tofa duka acikin ruwan sannan saita miqe zuwa raka'a ta biyu ta sake karanto suratul ikhlas qafa goma(10) saita tofa taje ruku'i, idan ta d'ago sai ta karanta qafa ashirin(20) ta tofa sannan taje sujada, idanta d'ago saita karanta qafa uku(3) ta tofa sannan ta sake komawa sujada, to anan idan ta d'ago bazata karanta suratul ikhlas d'in ba sai tayi tahiya tagama kafin ta sallame saita karanta qafa uku(3) ta tofa sannan tayi sallama, tana sallamewa bayan tayi istigfari saita karanta ayatul kursiyu qafa d'aya(1) ta tofa duka acikin ruwan sannan tayi salatin annabi sau d'ari(100) ta tofa aciki, idan ita keda matsala bayan tagama addu'o'inta saita rufe ruwan ta ajiye, tun da sassafe kafin taci komai saita sha ta kuma shafa a inda matsalar take idan kuma ba ciwo bane to saita shanye ruwan kawai basai ta shafa ba musamman in nacan cikin jikine daba bayyananne ba, idanma tana tsoron kada shed'an ya mantar da ita da safe zata iya tana gama sallar da daddare bayan tayi addu'o'in ta saita shanye, in kuma wani akayiwa to sai arufe ruwan a ajiye kuma ayi qoqarin bashisu yasha kafin yaci komai da safe, in Sha ALLAH ko menene damuwa ko tsananin ciwo in aka nace dayin wannan sallar to tabbas za'a samu waraka da izinin ALLAH, ammafa sai an jajirce don la'anatullahi yakan bijiro da kasala sai anyi da gaske*_ (wannan addu'a sadaka ce zuwa ga mahaifina Ina bara duk wacce ALLAH yabawa ikonyi data sakashi cikin addu'o'in ta ALLAH yajiqanshi kuma yayi masa rahama da shi da dukkanin musulmi baki d'aya, ALLAH kasa adace👏)
Chapter 159 · 0% Book details