← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 160

Sashe 7

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan kwana uku Abba yasa aka kirawota ya bata takardun da aka samu acikin aljihun Abu sumayya bayan ya sake bata hak'uri da kuma yimata gaisuwa akan rashin da sukayi, karb'a tayi taduba takardun ta farko takar dace data qunshi address d'in data bashi daren da zasu zo, dake d'auke da sunan malan NURADDEN IDRIS ALIYU, tare da address d'insa ak'auyen bebeji, tabiyu kuma takardun wata makaranta ce daya siya ahannun wani mutum acan borno d'auke dasa hannunshi da kuma na mutumen, ranar da zasuzo ya tsaya ya karb'i takardun wajensa wanda shine dalilin da yasa ya sanyosu aljihu suka wucikke.

Kallon Abba tayi had'e da cewa,

"Wannan takardar adreshin qauyen da nake tunanin zai iya gano mahaifinsa ne daka dad'e kana tambayar waye ubansa har kana jifarsa da cewa shi shegene, na qyalene alokacin saboda yanda naga qarfin soyayyar d'ana a idanuwan 'yarka shiyasa banyi yunqurin sanar dashi inda zai iya nemo saba idan har yana raye, shine awannan karon nayi tunanin fad'a masa inda zai iya nemosa don in tabbatar maka da cewa shid'in d'an halak ne gaba da baya, Amma cikin ikon ALLAH Sai gashi hakan bai faruba ya karb'i abunsa" ta qarasa maganar tana kuka.

Shiru Abba yayi kamar wanda aka zarewa lakka yana mai nadama da baqin cikin abunda yayi, saida tayi kukan mai isarta sannan taci gaba da cewa, "wannan kuma bansan kota meye ba, a ajiye har zuwa lokacin da ALLAH zaiba iyalinsa lafiya mai yuyuwa ne ita tasan kota meye."

Hak'uri su uncle Hassan dake gefenta suka shiga bata tare da ban magana tace,

"Aini ku bakuyi mani komai ba tunda kuka nunawa d'ana gata aduniya kuma banida bakin da zanyi maku godiya saidai ALLAH yasaka da alkhairi, shima d'in daya yimana bawai nariqesa araine ba, kawai ina tuna masane."

Da haka dai suka samu suka sake bata hak'uri tare da tausarta sannan ta ajiye masu takardun tawuce tabar d'akin tana sharar k'wallah.

Tun ranar da aka yiwa batool aiki har zuwa yau kimanin kwanahud'ubata farfad'o ba, tun anasa ran yau zata tashi gobene har iyayen sun fara sarewa akan al'amarin tare da fargabar abunda kan iya zuwa ya dawo, ana gobe gwaggo zata wuce gida sunje asibitin ita da barrister kamal da kuma zainab suna zazzaune cikin d'akin da aka kwantar da batool riqe da jariran da aka faraba madara yanzu sukaga ga hannunta yafara motsi, cikin farinciki duk sukayo kanta yayinda tafara bud'e idanuwa ahankali tana kallonsu d'aya bayan d'aya tamkar wud'anda bata tab'a gani ba, wani irin farinciki ne ya rufe gwaggo da hajia mama suka rungume juna suna hawaye tare da yima ALLAH godiya, barrister kamal ne yayi saurin fita sai gashi yadawo tare da likita, matsawa yayi kusa da ita yana duddubata sannan yace su tayar da ita zaune, ahankali yafara kiran sunanta kanta na duqe a k'asa, "batool, batool, batool" yakira sunan har sau uku, anan ukunne ta d'ago kai tare da kafesa da idanuwa, biron dake hannunsa yafara nuna mata saiti idanuwanta yana yawo dashi a fuskarta. Ahankali take bin biron da idanuwa aduk inda yayi dashi kafin likitan ya maidashi cikin aljihu yana murmushi had'e da juyowa yana kallon barrister kamal da shurahbil dake gefe a tsaye yace

"Alhamdulilah, ansamu tafarfad'o kuma in Sha ALLAH babu wata sauran matsala, yanzu abunda ya kamata ahad'a mata ruwan tea abata tasha." sannan ya rubuta wasu magunguna yabasu yace aje asiyo akawo idan tagama shan ruwan tea sai akirasa, juyowa yayi yasake kallonta har lokacin idanuwanta na saman aljihunsa da taga yasa biron aciki yayi murmushi sannan yafita.

"Sannu maman twins" barrister yafad'a sannan ta maido idanuwanta akansa daga kallon likita da takeyi shima tanata kallonsa harda karkace kai,

K'ok'arin had'a ruwan tea d'in hajia mama tafarayi yayin da gwaggo dake rik'e da maccen tamatso kusa da ita cike da tausayawa tace,

"Sannu uwar biyu, ubangiji ALLAH ya baki lafiya" kamar da gaske batool ta d'ago kai tace

"Amin." tare da mik'a mata hannuwa, hakan yasa gwaggo ta mik'a mata jaririyar had'e da cewa zainab ta kawo mata d'ayan jaririn aka aza matasu saman jikinta tabisu da kallo d'aya bayan d'aya, so takeyi ta tuna kosu waye atare da ita amma takasa, hakan yasa taji kanta yafara jujjuyawa kamar ana yawo da ita cikin wata duniyar, dariya dariya kuka kuka tafarayi kafin can tasaki wata irin qara had'e da ture yaran daga jikinta tana wani ihu wanda nan take hankalinsu ya tashi, badon zainab tayi sauri taro yarinyar ba da tuni tafad'a akan k'arfen dake gefenta na qarin ruwa yayinda shikuma d'ayan tuni yafad'o k'asa tare da tsanyara ihun kuka da sauri gwaggo ta d'aukesa tayi waje tana k'walawa nurses kira ita kuma banda buge buge da takeyi tana sakin wata irin qara da duk wanda yaji sai tsikar jikinsa ta tashi, hajia mama na kuka tafara qoqarin riqota saboda kada tajima kanta takaimata wani irin cizo da yaga amma hakan bai hanata takamata tariqeta sosai tana maimaita kalmar "innalillahi wainna ilaihirrajiun, allahumma ajirni fi musi bati wa ahlifni khairan minha, ya ALLAH muntuba kayafe mana kada kajarabcemu da abunda bazamu iyaba." Dukanta takeyi da dukkanin qarfinta amma taqi sakinta saima sake rungumeta da tayi sosai tana kuka, itama zainab d'in kuka takeyi tana riqe da jaririyar agefe, saiga shurahbil da barrister kamal da sukaje wajen sayo magani sun dawo, da gudu suka ida qarasowa wajen suka kamama hajia kaka ita suka rirriqeta tana kucce kucce saiga wasu likitoci harsu uku sun shigo gwaggo na biye dasu abaya tana sharar k'walla saboda nurses sun karb'i jaririn yana can suna dubashi.

Nan take sukayi mata allurar bacci sannan sukace su saketa sufito, taimakon gaggawa suka fara bata tare da yimata binciken daya kamata, sannan suma suka fito fuskokinsu cike da damuwa, da sauri hajima mama tanufi inda suke tace,

"Don ALLAH likita awane hali 'yata take ciki" gaba d'aya kasa tanka mata sukayi suka shige cikin wani office, turowa sukayi aka kira masu shurahbil alokacin Abba da uncle Hassan sun iso saboda wayar da shurahbil yayi masu ya sanar dasu halin da ake ciki hakan yasa uncle hassan ya dakatar da shurahbil d'in suka shiga shida Abba, wata takarda suka mik'o masu bayan cikin natsuwa Dr na'eem wanda yana d'aya daga cikin likitocin da sukayi mata operation yayi masu bayanin cewa,

"Alhaji kuyi hak'uri akan abunda zan sanar daku amma patient d'inku tana cikin wani mawuyacin hali sakamakon buguwar da tayi ga kai,

bincikenmu ya tabbar mana da cewa tasamu matsala a kwakwalwarta, dama tuni wannan muke tsoro ga farkawar tata tun lokacin da aka gama mata aiki but alhamdulilah tiyatar tata tawarke sai d'an abunda ba'a rasa, don haka yanzu wannan takardar zakuje kubiya kud'in wani scanning ne da za'ayi mata zuwa anjima.

Yanda abun ya matuqar girgza Abba yasa daga nan inda yake zaune sukaga ya b'ingire sanadiyar hawan jinin da yake dashi, dole shima nan take aka bashi gado kafin kaceme 'yan uwa sun taru a asibitin cike da jimamin wannan irin jarabawa da Allah ya aikowa familyn nasu acikin wannan lokacin.

Little Hassan kam babu abunda ya sameshi don anyi masa checkup sosai, haka Abba shima yasamu sauqi duk da dai har yanzu yana qarqashin kulawar liikitocin, gwaggo kam fasa tafiya tayi saidai tace barrister kamal yawuce ita zata jira har nan da kwana biyu, al'amarin batool kam ya tsananta, hauka tuburan takeyi wanda likitocin suka tabbar masu da basusan iya adadin lokacin da zata iya warkewa ba sai dai kawai suci gaba da addu'a da kuma nemar mata magani, yanzu haka dalilin daya hana suyi deparing nasu zuwa asibitin mahaukata saboda sauran raunukan dake jikinta ne da kuma tiyatar dake jikinta da suke treating badon haka ba ayqnayin da take bai kamata ace an ajiyeta nan ba, shiyasa kullum cikin yimata allurar bacci suke kuma tahakanne kad'ai yaran kesamu suna shan nono awajenta.

Rayuwar batool tazama abun tausayi musamman idan ka kalli jariran dake gabanta da kuma yanayin da take ciki, su hassana kam tuni sun samu sababbin iyaye saboda kulawar da zainab ita da d'an uwanta shurahbil ke basu, abunka da yaro rayuwarsu sukeyi cike da farinciki cikin sauran 'yan uwansu yara sai baka rasa bane zakaga sun aza rigama suna kuka sai ankaisu wajen dady da ummiensu, musamman cikin dare ko kuma lokutan da zasuci abinci sai kaji suna rigima waisu bazasu ciba sai I
idan dady da ummie ne zasu basu,

Abba kuma yasamu sauqi sosai har anbashi sallama amma yanda yayi rama saboda tsananin baqinciki da damuwar da yake ciki kallo d'aya zaka yimasa ka zubar masa da hawaye, yayi kuka, yayi nadama tare dayin tir da zuciya irin tasa, tabbas yayi dana sani abu adadi alokacin da SANNU SANNU yafara karb'a sakamakon abunda yayi, dama anfad'a masa cewa but khairan da sharran wanda duk ka aikata da SANNU SANNU zai riskeka, dama SANNU SANNU bata hana zuwa.....gashi yanzu anzo wajen da abunda ya aikata ya riskesa.
Chapter 7 · 0% Book details