Sashe 58
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Daga masa kai kawai Nuraddeen ya iyayi hawaye nazuba ta gefen idanuwansa tare da kallon yanda duk baffansa shima yabi ya rame sosai, yasani yanada matuqar juriya da qarfin imanin daba don haka ba da tuni zuciyarsa tabuga, halshe yasa yalaso lab'b'ansa da suka bushe irin na maijin jiki sosai tare da miqa hannu ya riqo hannun baffa yace.
"Kayi haquri baffa bada son raina kake ganina cikin wannan halin ba, gazawar zuciyatane da kuma rushewar mafarkainane suka haifarmun da wannan rashin juriyar, Amma yanzu nayarda da muqaddarin da ALLAH yatsaro mani arayuwata, zanyi koyi dakai wajen jajircewa da kuma juriya had'i da yarda da qaddara maikyau da marar kyau nayi amfani da sauran lumfashina wajen sanyaka farinciki duk da nasan cewa ni nawa farincikin ya tafiyarsa har abada."
"Karkace haka Nuraddeen _laa taqnad'u min rahmatillah_ (kada kayanke qauna da rahamar ALLAH) domin shiya halicci farinciki kuma idan har addu'ar mahaifi nada tasiri inada yaqinin cewa farincikinka zai dawo gareka komai daren dad'ewa, kai dai kacigaba da haquri don SANNU SANNU Bata hana zuwa...da sannu in Sha ALLAH faricikinka zai dawo agareka kaji ko?"
Jinjina masa kai kawai Nuraddeen yayi hawaye naci gaba da zubo masa, sun jima a haka kowanensu na saqa yanda zai samu suyin rayuwa nan gaba acikin tafiyar da yakeyi arayuwar duniya kafin baffa yajawo redion sa ya kunna, shi kuma Nuraddeen idanuwansa narufe uyanaci gaba da saqawa da kuma kwancewa azuciyarsa, can sukaji anfara sanarwa cikin redion cewa malaman da gomnati ta d'auki nauyin cigaba da zuwa qaro karatunsu Jeri na farko dake dakon tafiyarsu nan da watanni uku an maidosa zuwa nan da wata biyu masu zuwa saboda wani dalili, don haka su zamo cikin shiri akodo yaushe za'a iya nemansu domin tantancesu (screening), gaban sane yayi wani irin fad'uwa had'e da tuna irin kalaman da Rashida tayi a ranar da yazo yasanar da ita cewa yana cikin malaman da sukayi nasara, dafe kansa dake yimasa barazanar tsagewa yayi da sauri baffa ya kashe redion yana tambayarsa ko lafiya don shi gaba d'aya yama manta da zancen tafiyar tasa saboda tashin hankalin da yake ciki, shi kanshi Nuraddeen wannan sanarwarce ta tuno masa da ita badon haka ba har lokaci ya wuce bazai tuna da komai ba.
••• ••• •••
A can b'angaren iyayen Rashida ko duk wani bincike daya dace ayiwa umma na qwaqwalwa anyi mata, manyan gwaje gwaje (scanning) masu matuqar tsada da zasu tabbatar da haqiqanin abunda yasamu k'wak'k'war tata duka anyi amma sun tabbatarda kwakwalwarta lafiyar klw take, tsananin tashin hankaline ya jefata cikin wannan matsananciyar damuwar da sai a hankali zata iya komawa daidai, shimad'in idan tasamu cikakkiyar kulawa.
Haka shima baba yananan ayanda suka kawosa b'aren jiki ya shanye, magana ma daqyar yakeyi gashi har sun buge kusan wata d'ya a asibitin, sosai d'an uwansa ke qoqarin basu kulawa da dukkanin qarfinsa da kuma dukiyarsa duk da shima yanada tashi hada hadar agabansa amma hakan baisa yagaza wajen bashi kulawaba, Aunty marwiyya ma haka ko yaushe tana tare da umma tana bata magana da ban haquri kuma hakan namatuqar tasiri agareta, ada ba abunda bakinta ke ambata idan ba sunan Rashida ba kuma bataci bata sha, Amma yanzu cikin iyawar ALLAH da addu'o'in da 'yan uwa keyi kuma suna da anayi masu duk sun fara samun sauqi kawai maganace umma bata fiye yiba, dama can ba ma'abociya surutu bace sai abun yahad'e mata yanzu amma jinta, ganinta, hankalinta da komai nata yakoma daidai iyakarta idan ana mgana ta tsurawa mutane ido batare da tace qanzil ba ko kuma tayita bacci.
Yauma kamar kullum tana zaune bisa gadon da aka kwantar da ita na marasa lafiya sukuma su aunty marwiyya da matan bab balarabe na zaune suna fira tana binsu da idanuwa, kamar an tsikareta tayi saurin matsowa bakin gadon had'e da sauko da qafafuwanta qasa zata tashi da sauri aunty marwiyya ta dafeta tana fad'in. "Ina zakije aunty.?" A hankali tabud'e baki tana kallonsu d'aya bayan d'aya kafin tamaido kallon nata ga aunty marwiyya had'e da cewa. "Wajen baban Rashida." Qilan hakan baya rasa nasaba da fitarsa da sukeyi akan wata jayayya da suka tab'ayi shida qanen nasa malan balarabe acan gidansa shine matansa keba aunty marwiyya labari anata dariya, hakan ne yasa tayi saurin fahimtar cewa ai shima yana cikin asibitin kamar yanda taji sun fad'a.
"Kina so kidubo sane?" Aunty marwiyya ta tambayeta tana kallonta, d'aga mata kai tayi alamar eh tana so tace
"To zauna anan Bari nakira likita, idan ya bada damar kije sai muje."
Dariya su hajia larai sukayi cike da zolayar son ganinta cikin farinciki hajia larai tace.
"A'ah, Yaya ko soyayyar ce tamotsa, anjima ba'aga juna ba?."
Umma dai bata tankata ba, saima kafeta da idanuwa da tayi, ahaka aunty marwiyya tadawo ta iskota bakin gadon, d'an matsawa gefe tayi kad'an taba likitan dake tare da ita waje ya dudduba umma had'e da yimata 'yan tambayoyi, ta amsa masa wasu, wasu kuma taqyalesa sannan yace zasu iya tafiya Amma sutabbatar ba guduwa (absconding) ne zasuyi ba.
Riqata sukayi dukda tana iya tafiya lafiya lau suka nufi ward d'in da aka kwantar da baba aciki, kasancewar ana 'yan share sharene da goge goge yasa wanda ke tsaron qofar yace bazai barsu shiga ba har sai angama, bayani aunty marwiyya tayi masa sanan yace to tashiga tare da ita su kuma sauran su tsaya waje har agama itama tana kaita d'in tafito.
Godiya tayi masa sosai sannan suka wuce don dama sun san qa'idar asibitin kenan idan ana aiki ko idan likitoci na round ba'a bari kowa yashiga sai in sun gama ko kuma in lokacin ziyara yayi.
Suna shiga suka iskosa kwance baba balarabe na zaune akan kujera kusa dashi ya duqo had'e da kara kunnensa saiti da bakinsa, da alama wata magana ce yakeyi masa bayaji shine ya kara kunnensa yanda zaijisa sosai.
Murmushi baba balarabe yayi had'e da d'ago kansa jin aunty marwiyya saman kansa nayi masa magana sai yaga ashe tare take da umma, fad'ad'a murmushinsa yayi yana kallon umma had'e da cewa. "'yar halak kinqi ambato, yanzun nan maganarki yakeyi mani shiyasa kukaga na d'ago murmushi ashe kina kusa." Miqewa yayi daga kan kujerar yanaci gaba da cewa.
"Zauna yaya, ya qarfin jikin?."
Bata tankasaba sai kallon baba dake murmushin jin dad'in ganin tasamu sauqi takeyi, yayinda ita kuma hawaye ke zubo mata, aza kanta tayi agefen gadon kus da hannunta ahankali tace "malannnn.." tare da fashewa da kuka.
Aunty marwiyya naganin haka ita da baba balarabe sukabar wajen, baba ya d'ora hannunsa akanta cikin maganarsa da bata fita sosai yace "sannu maman Rashida , muyi haquri."
Haka kawai ya iya furta mata batare da yayi yunqurin hanata ba shima yana nasa hawayen.
Sosai yake qoqarin fitar da damuwar rashin Rashida aransa saboda yasmu lafiyar da zasu iya yin nesa da garin domin hakanne kad'ai zai iya bashi damar cigaba da rayuwarsa batare da wani mummunan abu ya koma faruwa akansa ba amma matuqar suna garin kuma suna ganin abubuwan da zasu iya tuna masu da ita to tabbas yasan wata rana zasu iya rasa rayuwarsa akan tunaninta, musamman idan sukaga mijinta hakan zai dinga tado masu da mikin dake cikin ransu.
Sun jima tare duk da ba wata doguwar magana sukeba face tausayawa kansu da tunanin ko awane irin hali 'yar tasu ke ciki, sai misalin qarfe tara da kusan rabi sannan umma takoma ward d'in da take tanajin wani sassauci aranta duk da halin data gansa bataji dad'i ba ko kad'an, ta fannin baba ma anga sauyi sosai don ranar ya d'an sake, ko zazzab'in dake yawan rufesa da taso masa yau da sauqi sosai, wannan na d'aya daga cikin tasirin da ALLAH kesawa tsakanin mata da miji, tausayi da soyayyar dake tsakaninsu kan haifar masu da natsuwa alokacinda sukayi musayar matsalolinsu.
••• ••• •••
Dr Nuraddeen kuwa saida akayi kwana uku da maganarsu da Rashida sannan yashirya tsaf yanufi garin kano ta dabo tumbin giwa...dama ranarce takama zai koma wajen aikinsa, kasancewar ya kwana biyu bai jeba saboda matsalar rashin lafiyar yaron Rashida yasa koda yazo yatarar da aiki sosai agabansa, wanda hakanne yasa bai fara qoqarin neman iyayen Rashida ba sai bayan kwana uku aikin ya rage masa, tafe yake cikin motarsa yana sauraren wata waqa ta Abdul d one daya yayiwa mahaifiya yana mamin d'inta ahankali har yakai qauyen nasu data kwatanta masa, wata 'yar gajeruwar takarda ya fiddo agaban aljihunsa yana karanta address d'in gidan su data fad'a masa da sunanan mahaifinta da akasanshi dashi, wajen wani mai kayan miya ya tsaya lokacin daya iso anguwar tasu had'e dayi masa sallama sannan yace....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___44💎
Wajen wani Mai kayan miya ya tsaya lokacin daya iso anguwar tasu Rashida had'e dayin parking d'in motarsa gefe ya kashe be sannan yafito, nufo inda mutumen ke zaune cikin rumfar tasa da yake saida kayan miya yayi had'e dayin sallama, bayan ya amsa masa cikin girmamawa dr nura ya gaishesa had'e da cewa "Sannu baba, don ALLAH tambaya nakeyi."
Sai daya sallami wani yaro dake tsaye gabansa da yazo sayen kayan miya ledar dake hannunsa sannan ya d'ago kai yana kallon Dr nura had'e da cewa.
"Yawwa d'an saurayi, yi tambayarka inaji ALLAH yasa nasani."
Murmushi kwance a fuskar Dr nura ya gyara tsayuwarsa sannan yace, "Dama gidan malam bashar mai takalma nake nema."