← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 160

Sashe 76

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___57💎

••• ••• •••
Sosai wan saheke Rashida tasamu sauqi zuwa azahar aka basu sallama, kai tsaye gidan Yaya maryam aka nufa da ita duk da baba balarabe yaso ace gidansa zata zauna, Amma ganin yanda Yaya Maryam d'in ta kafe kai da fata lalle wajenta zata zauna yasa ya
haqura tunda itace yayarsa babu yanda zaiyi,

Tunda Rashida ta bar gida yaune karo nafarko da taji tana son had'uwa da mijinta wato habibinta mahaifin d'anta Nuraddeen, suna kan hanyarsu ta zuwa gidan Yaya maryam da yake Dr nura ne ya d'aukosu a mota, Fatima na gefensa riqe da little sai Yaya Maryam da aunty marwiyya da ita Rashida abaya, shi kuma baffa mijin Yaya maryam ne ya d'aukosa saman mashin d'insa suka biyo bayansu, takalli aunty marwiyya tace.

"Aunty ya nura fa?"

Wata uwar harara ta zabga mata had'e da juyar da kanta gefe, ganin haka yasa ta kama bakinta har suka isa gida,

Dr nura nayin parking su baba balarabe dake biye dasu na tsayawa da mashin d'insu, Yaya Maryam ce tafara fitowa sannan aunty marwiyya suka nufi cikin gidan, hakama Fatima itama tafito tare da riqo hannun Rashida dake qoqarin fitowa tayi mata jagora sukabi bayansu,

A can cikin gida aunty marwiyya tafara fad'a tana fad'in. "Yaya wannan yarinyar batada hankali, kinji tambayar da takwyimun a mota wai ina ya nura? Wlh badon batada lafiya ba da saina d'auketa mari don ko sunan garinsu bana sonji balle sunansa."

"Hmmm banni da ita marwiyya Ina jinta, bi izinillahi ko shikad'ai ya rage namiji aduniya bazata koma gidansa ba, ai tunda haka tafaru to ta tabbata komai mahaifiyarsa zata iya yimata saboda qiyayyar da take yimata kuma mu shedane akan haka, shikenan kuma don muna sakarkari sa mubarta takoma masa a kashe mana ita, narantse kozai mutu sai yasaketa tunda ba ita kad'ai bace macce aduniya ba."

"Wannan shine daidai Yaya Maryam, in yaso yaje can uwarsa ta aura masa wacce take so." Aunty marwiyya tafad'a a qufule.

Tana rufe baki suna shigowa, ta sakarwa Fatima murmushi had'e da cewa.

"Wucikke matar Dr." Batare data kalli inda Rashida take ba.

A falo suka shiga suka zazzauna kafin mijin Yaya maryam yashigo shima su Dr da baba balarabe nabiye dashi abaya.

Bayan sun zauna Yaya Maryam tamiqe taje takawo masu ruwa da lemuna masu sanyi da 'yar sauran samosar data had'a da safe da take sayarwa ta ajiye masu,

"Balarabe kutab'a wannan kafin kuwuce."

Saida suka fara tab'a hira ana tayiwa little da Fatima ta ajiye tsakar falo yana faman yimasu qyaqya dariya sannan tamiqe taje ta d'ora masu dahuwar taliya da kifin gwangwani ga 'yar qaramar tukunyar gas cooker d'inta saboda tayi saurin nina, ai kuwa cikin mintotan da basu wuce goma ba ta nina ta zuzzubo a flate ta kawowa kowa, sake d'auko had'ad'd'en zob'onta na siyarwa da takeyi tayi ta kawo masu sannan itama ta zauna tana cin nata,

"Kai amma zob'on nan yayi dad'i yaya maryam ya akeyinsa?" Fatima tafad'a tana sake kai cup d'in zob'on abaki.

"Kai matar Dr Banda zolaya, zob'on na siyarwa?"

"Eh mana, gaskiya kina gyarasa sosai, ai wannan zob'on ko shugaban 'yan hasada yasha dole ya yabashi balle masu so da gaske."

Dariya duk suka samata harda Rashida da tun d'azu takasa kai koda cokali d'aya abaki sai faman cakularsa takeyi,

"Hmmm! Yakamata nabiya kud'in zobonnan tunda yasa madam Santi har na tsinkayo ana yimata waigi."

Dr nura yafad'a yana dariya ganin aunty marwiyya na gyarawa Fatima hilon dake bayanta, juyowa tayi had'e da cewa.

"Au..Ashe da gaske yakeyi, kai aunty marwiyya zakija yadinga tsokanata kuwa."

Kallon Rashida baba balarabe yayi had'e da d'aure fuska yace.

"Ke Rashida maza kici abinci kinji ko?" Ganin bada wasa yakeyi ba yasa tafaracin abincin tana b'ata fuska tamkar wacce keshan magani.

Yanda su Dr suka saki jikinsu cikin 'yan uwan Rashida Kai ka rantse kace Abu d'aya suke ko kuma sun jima da sanin juna, hakan Kuma ba qaramar shaamquwa da yarda ta sake shiga tsakaninsu.

Bayan kowa yaci yasha ya qoshi, baba balarabe yayi gyaran murya had'e dayin doguwar addu'a da nasihohi masu ratsa jiki bisa abunda ya faru sannan yarufe dayiwa su dr.nura shida matarsa godiya sosai shida su Yaya Maryam, irin godiyar da suke yimasu da kyawawan addu'o'i had'e da fatan alkhairi har seda suka fara jin kunya, daga qarshe aunty marwiyya tace.

"Mungode sosai Fatima matar nura uwar nura, muna roqon Rabbissamawati wal ardi daya azurtaku da 'ya'yaye nagari masu albarka da zakuyi alfahari dasu duniya da lahira, ALLAH yakareku daga dukknin sharrin abinqi ya lullub'eku da rahamarsa da tausayinsa yayi maku arziqi mai yawa ya share maku dukkanin kukanku."

"Amin ya ALLAH aunty."

Suka amsa cike dajin wani dad'i da sanyi da farinciki azuciyarsu,

Itama Rashida hawaye nazubar mata a idanuwa ta rungume fatima tana fad'in.

"Dukkanin alqawurranku agareni wanzazzune hakama alkhairanku tabbataccine akaina, karamcinku da halacci masu girmane da mizaninsu yakai girman da bazan iya biyanku aduniya ba, amma har zuwa fitar lumfashina zuciyata da Kuma rouhina cike da qaunarku mai tsanani take, duk wani fitar lumfashi nawa cike yake da fatan alkhairan ALLAH agareku da kuma farinciki mai d'orewa, ina roqonku da kada kucireni acikin rayuwarku kada kumanta dani kubani damar da zan iyaci gaba da rayuwata tare daku matsayin 'yan uwa batare da zumunci ya yanke a tsakaninmu ba har izuwa ranar da zan kwatanta faranta maku zuciya kamar yanda kuka faranta tawa data ahalina koda sau d'aya ne."

"Bazamu mantaki ba Rashida, bazamu rabu dake da little ba don kunzamo wani yankin daya sama mana farinciki na wani d'an lokaci arayuwarmu wanda muke fatan yatabbata atare damu har abada" Fatima tafad'a itama had'e da rungumeta tana kuka, kuka sukeyi sosai sai kace wud'anda suka rabu kenan har saida Dr nura ya cewa Fatima ta taso sutafi yana mai mamakin yanda shaquwa mai tsanani haka tashiga tsakaninsu a qanqanen lokaci,

'Daukar little tayi ta sumbacesa agoshi tare da wucewa gaba suka rakosu qin miqasa tayi har saida ta shiga mota Dr nura na Shirin tayarwa sannan ta badashi tana goge qwallan da suka zubo mata, shi kanshi Dr nura saida yaji ba dad'i Amma babu yanda suka iya dole yaja motarsa sukabar wajen.

Su kuma yana tafiya rigima ta kaure tsakanin baba balarabe da yace a dole akira Nuraddeen da ahalinsa asaanar dasu yayinda sukuma su aunty marwiyya sukace atafau bazai yuyu ba, daga qarshema Yaya Maryam bugawa Rashida tsatsauran Jan kunne tayi akan karta sake koda mafarkine tayi tunanin zata koma gidan Nuraddeen tunda mahaifiyarsa bata sonta.

Shikuwa baba balarabe duk da Yaya Maryam na sama dashi haka yatabbatar mata da cewa dole sai yasanar da Nuraddeen anga matarsa saboda haqqinsane kuma har lokacin tana aqarqashin igiyar aurensa, hakan yasa suka rabu baran baran, rayuwakan kowanensu a b'ace.

Yana komawa gida yashiga Kiran lambar baffa data baffa Usman Amma shiru kowace switch up, hakama ta Nuraddeen yakira yafi a qirga itama akashe saboda bai fara anfani da sabon layin daya siya acan.

Hakan yasa hankalinsa tashi sosai marece nayi yanufi garin bebeji, yana isa yaci karo da baba Ali ya tsaya yana tambayarsa, sunjima suna magana kafin baba balarabe yabar wajen jikinsa a sanyaye, wata 'yar iskar dariya baffa Ali yayi sannan yawuce yana fad'in "da sannu duk sai kun gane kurenku har ita wacce sanadiyar b'atanta aka rufemu nida iyalina aka yimana dukan mutuwar da gangar jikinmu takasa d'auka"

Kwana baba balarabe yayi yana juyi akan abunda baffa Ali ya sanar dashi duk da dai wani b'angaren na zuciyar tasa bai yarda da hakan ba.

••• ••• •••
Su Baffa kuwa a maimakon kwana d'aya da zasuyi agarin sokoto sai da sukayi kwana biyu saboda shawarar da wani likitan yabasu akan sukai marar lafiyarsu kware shine abunda zaifi masu sauqi, hakan yasa suka sake kwana d'aya acan har saida suka gama shirya duk abunda yakamata acan asibitin kware suka biya kud'in da za'a basu mota da jami'an lafiyar da zasu d'aukota sannan suka juyo zuwa gida bayan sun bada address d'in da za'a tura masu motar nan da kwana biyar, gaba d'aya wayoyinsu sun mutu saboda rashin charji da basuda wannan ne dalilin da yasa baba balarabe yayita kiransu bai samu ba.

Saida suka iso zamfara don dama motar da zata ajiyesu acan sai daga nan su shiga wacce zata kaisu kano suka shigo kafin motar da suka samu ta kano ta cika suka shiga masallacin dake cikin tashar sukayi sallah sannan suka samu wani saurayi ya ara masu chargarsa sukasa wayar baffa charji, minti talatin sukayi sannan motarsu tacika lokacin baffa har yasamu d'igo biyu a 'yar wayar tasa qirar kamfanin itel mai madannai.

Mintuna biyu yayi da kunnata kiran baba balarabe ya shigo.

Cikin natsuwa baffa ya d'aga had'e da amsa sallamar da yayi masa sannan suka shiga gaisawa.

"Am dama wata magana naji cewa Nuraddeen yabar qasar nan shine nace bari nakira naji shin ko gaskiya ne.?"

Wani irin nauyi baffa yaji Amma bayada wata hanyar da zai iya basa amsar tambayar da yayi data wuce eh ko kuma a'a, tamkar baffa nagabansa ya duqar da kai had'e da cewa.

"Eh malan balarabe hakane amma..." Kafin yaqarasa baba balarabe ya katsesa ta hanyar cewa.

"To madallah, shikenan nagode." Had'e da kashe wayarsa, duk inda ransa yake in yayi dubu ya b'aci, Ashe akwai ranar da Nuraddeen zai nuna irin wannan halin ko inkula agaresu adaidai lokacin da suka rasa 'yarsu a hannunsa, Ashe har yanada qwarin guiwar da zaya iya barin gari acikin yanayin da yake kuma har yatafi batare daya yimasu sallama ba?, Me suka yimasa da suka cancanci haka daga wajensa? Ai koba komai ana bankwan saboda ba'asan halin rai ba, kuma ai yakamata ace ko don kaucewa zargi yazo yayi masu bayani, wud'annan tambayoyi sune suka dinga Kai da komo acikin zuciyarsa da kuma qwaqwalwarsa, rashin samun amsar sune yasake tunzurasa sosai,
Chapter 76 · 0% Book details