← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 160

Sashe 50

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take yafara ba nurses d'in umurnin miqo masa kayan aiki, cikin k'warewa da hikima irin wadda aikinsa ya koyar dashi yafar qoqarin jujjuya yaron da zimmar mayar dashi ya koma daidai, fiye da mintuna ashirin ya kwashe yana abu guda amma hakan ya cutara, kallon irin wahalar da tasha yayi amma duk da haka bata sare ba da sauri yasa hannu ya goge hawayen da suka zo masa tare daba nurses d'in umurni dasu canzo masa kayan aikin da zai karb'i haihuwar ayanda yaron yazo koda kuwa za'a rasa ranshi saboda aceto rayuwarta,

Nan take aka had'a komai yashiga fara aikin cike da addu'ar ALLAH yasa ayi nasara, kusan wasu mintuna ashirin ya kwashe sannan yayi nasarar fiddo da yaron lafiya, yana fiddosa na'ura nagwajin d'aukewar lumfashin Rashida, haka shima yaron tsabar wahalar daya sha koda aka cirosa ko motsi baya yi, da sauri yajawo oxygen d'in dake can gefen gadonta ya harhad'a ya jona mata da taimakon nurses d'in dake wajen....

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___38💎

Juyowa yayi yana kallon Dr dake wajen tare dashi wanda yakamata ace shine ya karb'i haihuwar ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace.

"Nagode sosai, in Sha ALLAH zata samu lafiya, ayanayin wahalar da tasha dole nasan hakan zata kasance, nayi abunda na Nemo alfarmaryi sauran kuma nagareku." Yaqarasa maganar yana cire handglove d'in dake hannunsa, murmushi Dr yayi yana yabawa qwarewar Dr. nura tare da jinjina masa akan namijin qoqarin da yayi, wanda badon haka ba babu ko shakka saidai suyi mata tiyata gudun abunda zai iya faruwa da ita ko d'anta, solutin nasa yayi shima had'e da cewa. "Weldone sir, sunana Dr sani Bilal Ina zaunene d'aya daga cikin gidajen dake cikin asibitinnan, naji dad'in had'uwa dakai sosai."

"Masha ALLAH sunana.." saurin katsesa yayi tahanyar fad'o masa cikakken sunansa daya gani arubuce jikin i.d card d'insa ta asibiti wato

"Dr. nura shu'aib k'wararren likita afannin matsalolin mata dake aiki da asibitin aminu kano dake garin kano."

Murmushi yayi sannan yanufi gefen da nurses d'in ke gyara babyen har lokacin be koka ba, karb'arshi yayi ya d'aga qafafuwansa sama kansa na qasa yad'an twad'i d'uwawunsa sai gashi ya canyara ihu, murmushi farinciki yayi sannan ya miqa masu shi yana kallonsa, yaron kyakkyawane sosai gashi da girma tubarkallah, kallo d'aya zakayiwa jaririn kafahimci ba qaramin kulawa yasamu ba alokacin da yake cikin ciki, yana wannan tinaninne yaji wata nurse a firgice tace.

"Dr...." Saboda ganin yanda yaron yafara amai yana fizge fizge, da sauri ya qaraso wajen ya karb'esa nan take yagano yaron yasha ruwan naquda, qoqarin zuqe masa su ya shigayi da taimakon Dr sani da gaba d'aya hankalinsu ya tashi, miqa masu shi yayi yace suyi maza maza su kaishi sashen ba jarirai taimakon gaggawa, haka kuwa akayi kafin kace me har sun isa wajen nurses d'in b'angaren suka karb'esa suka fara bashi kulawa kafin likitan dake b'angaren yaqaraso, yana zuwa yashiga duddubasa cikin k'warewa da iya aikinsa.
Bayan komai ya daidaita shima yaron aka saka masa oxygen saboda yanda lumfashinsa ke kokuwar barin jikinsa.

Dr. nura kuwa nurses nafita da jaririn ya nufi inda Rashida ke kwance ya qura mata idanuwa, gaba d'aya kamannunta dana yaron sunsha banban, wataqil shi mahaifinsa yabiyo,

Yafad'a aransa, ficewa yayi daga d'akin yana tura hannuwansa cikin aljihu, sai alokacin ya tuno da wayarsa daya ajiye a can gefen gadon da Rashida take kwance da sauri yakoma ya d'auko, kusan 10missed call yagani Kuma duka na matarsa ne fatima wacce take da tabbacin tashigo asibitinne shine takirasa taji inda take, murmushi had'e da danna lambar ya sake kiranta, bugu d'aya ta d'aga tana fad'in.

"Swthrt kana inane? Tun d'azu kabarni a tsaye." Tafad'a cike da qorafi akan haka.

"Fatima kenan! Yihaquri ki qaraso tanan gyani emergency Ina tawurin tsaye Ina jiranki."

"To." Tafad'a had'e da kashe wayar sannan tanufi hanyar da zata sadata da wurin, daidai lokacin shima yanufo qofar fitowa daga wajen sukayi kicib'is da ita d'auke da kwandon kuloli har dasu qatuwar leda da flaks, zaro idanuwa yayi yana kallonta cike da mamaki yace. "Fatima duk meye haka?" dubon agogon hannunta tayi taga kusan qarfe goma da rabi na safe ta dafe kai had'e da cewa.

"Kayi haquri nadad'e ban qaraso ba ko?, natsaya had'a mata wud'annanne, Ina jarin da aka haifa? tahaihu ko?"

Tafad'a tana gyara zaman mayafinta cike da tausayi yabita da kallo, daga jin cewa ya tsinci maiciki a hanya suna asibiti zata haihu shine Fatima zata had'o wud'an abubuwa haka saboda tsananin son haihuwa da take da ita, ya ALLAH kadubemu da idon rahama muma kabamu namu masu albarka, yaqarasa fad'a aransa yana goge 'yan kwallan tausayinta da suka zubo mata.

••• ••• •••
Dr nura da Fatima mijine da mata dakeda matuqar kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, kalla d'aya zakayi masu kafahimci aurensu auren soyayyane saboda yanda suke matuqar son juna, sunyi aure tun shekaru goma sha uku da suka wuce amma har zuwa tsawon wannan lokaci basu samu haihu ba, Fatima macece mai matuqar son yara amma jarabawa ta ALLAH ko b'atan wata bata tab'a yiba, anyi masu duk wasu gwaje gwajen da bincike bincike don agano dalilin rashin haihuwar tasu amma likitoci sun tabbatar masu dashi har ita duka lafiyarsu qalau basuda wata matsala data hanasu haihuwar kawai lokacine beyi ba, hakan yasa gaba d'aya suka tattara komai akan batun haihuwa suka watsar gefe suka rungumi junansu hannu biyu cikin so da qauna da kuma kulawar juna, fatarsu akoda yaushe da addu'arsu shine ALLAH ya basu masu 'ya'ya masu albarka aduk lokacin daya so kuma yanufa, Dr nura cikakken d'an asalin jahar borno ne amma wasu lokutan suna zama a kano saboda aiki daya kaishi can, dalilin fitowarsa yau tunda asuba shine kiran gaggawar da akayimasa tun jiya da daddare ne cewa ana buqatar ganinsa gobe qarfe takwas na safe akwai matar da zasu yiwa tiyata, shiya yayi asubancin tashi zuwa filin jirgin da zai tashi qarfe biyar na asuba don ya isa dawuri, ashe rabon ya taimaki Rashida a wannan lokacin ya fiddosa.

••• ••• •••
Wata irin ajiyar zuciya Dr. nura ya sauke had'e da riqo hannunta yace, "Kai fatima daga fad'a maki zancen matar nan zata haihuwa shine zaki tsaya kwaso kaya haka!."

Dariya kawai tayi masa batare da tace komai ba saboda Babu abunda takeso alokacin irin taga matar da yace ya tsinta da babyn data haifa, d'akin da Rashida ke kwance yanufa riqe da hannunta har suka shiga.
A bakin gadon Rashida yaja burki ya tsaya yana nunata da hannu. "Fatima kinga baiwar ALLAH da nake fad'a maki nagani tafito daga cikin wani daji tashigo gaban motata, badon ALLAH yatsare ba dana bugeta gata da tsohon ciki." Cike da tausayi tariqe hannunsa gam kamar zatayi kuka yace.

"Swthrt meya fiddota waje a lokacin gata qaramar yarinya mai qanan shekaru, yanzu haka sharri da baqincikin d'a namiji yasata fitowa, kai walh wasu mazan basuda imani."

"A'a fatima karkice haka tunda bamusan dalilin daya fiddota be daga gida ba, wataqil wata matsalarce daban."

"Hmm! Bazaka gane ba swtht wlh yanzu hakan mijinne yakorota saboda wani banzan dalilinsa, ya ALLAH kadubi maraicinmu."

Tafad'a tana d'aga hannuwanta sama hawaye nazubo mata daga cikin idanuwa, qara matsowa tayi kusa da Rashida taduqo had'e dasa hannu tana shafa fuskarta,

"ALLAH sarki yarinya, ALLAH yatashi kafad'unki, wlh swthrt da ganin yarinyar nan akwai ban tausayi cikin al-amarinta, yanzu I babyn nata yake?"

"Yana can shima anbashi gado bayada cikakkiyar." Yafad'a tare da juyowa yafito wajen tana biye dashi ya zuba hannayensa acikin aljifan wandonsa, kallonta yayi yaga yanda gaba d'aya jikinta yayi sanyi, murmushi yai sannan yaci gaba da cewa "muje can kiga yaron nata, so nake idan kin amince nabar komai ahannunki kafin nadawo nan da zuwa jibi idan yafarfad'o muji daga Ina take, thank God ma nayi waya da Dr qasim can wajen aiki yace anyi shifting theater da zanyi sai nan da 24hrs saboda jinin patient d'in daya hau sosai."

"Babu damuwa swhrt ALLAH yabasu lafiya, idan da imani da tausayi a qirjin bawa ko bakasan mutumba ai katausaya masa, shikuma taimako bakasan ta inda zai yimaka rana ba wataran, na amince Babu wata damuwa akan haka."

"ALLAH fatina?" Dr nura yafad'a yana dariya.

"Sosai kuwa, yanzu kafasa bin jirgi kenan?"

"Eh da motar haya zanje sai inbar maki wannan koda wani abun zai taso, zan kira Salim ya kasance kusa idan kina buqata."

"Noo..kabarshi kasan bama inuwa d'aya da qanennan naka yafiye reni da yawa."

"To shikenan muje kigano yaron."

••• ••• •••
Baffa kuwa na fitowa daga asibiti kai tsaye gida yanufa ransa duk a dagule, gaba d'aya ya rasa mekeyi masa dad'i aduniya, yana shigowa cikin gidan ya tarar da yaya hawwa zaune a bakin rumfarsu Inna ruqayya takira mai tallar fankasu (na alkama) ta tasashi agaba sai ci takeyi tana dangwala yaji, tana ganin lokacin da baffa yawuce ta gabanta fuskarsa cike da damuwa amma ko kallon banza bi isheta ba, saida taci mai isarta taqoshi sannan tamiqe had'e da cewa yaron ya jirata tana zuwa ta karb'o masa kud'insa.

'Daki ta iskosa zaune abakin gefen gado ya rabka wani uban tagumi yana tunanin ta inda zai fara sanarwa da iyayen Rashida halin da ake ciki, cikin nuna halin ko inkula akansa tace. "Malan bani naira d'ari in biya yaron can kud'insa na fankasu dana ci." Tafad'a had'e da tura yatsa cikin baki tana qwalqwalo wanda ya laqemata a hauru, hannunsa yasa cikin aljihu yaciro d'ari biyu ya miqa mata ta amsa ba gode balle nagode taficewarta, ba'a jimaba tadawo tamiqo masa canjin naira d'ari ya sake miqa hannu ya karb'a yatura cikin aljihu,
Chapter 50 · 0% Book details