← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 160

Sashe 24

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya bari naje wajen musa ya aro mana mota akaika asibiti" yana k'ok'arin d'agasa daga jikinsa ya kwantar dashi akan katifa, cikin muryar dake nuna yana jin jiki yace,

"A'a Usman ba sai munje asibiti ba Alhamdulillah nasamu sauqi, amma Ina so don Allah Aliyu yafita daga d'akinnan bana son ganinsa yanzu, bantab'a tsammanin cewa duk wannan fitinar dake faruwa acikin gidannan ba yana ciki kuma koda fad'amun akayi wlh bazan yarda ba, amma sai gashi da idona nagansa zaune shida matarsa iyalinmu nafad'a anrasa wanda zai rabasu shida ita, wannan wace irin rayuwace haka ace d'an uwan bazai iya karewa 'yan uwansa mutuncin suba, da ranmu kenan yayi haka inaga bama raye." 'bata rai yayi yana qunquni wai aishi baisan yanda zaice masu ba tunda duka matan yannens ne Amma anaso aga lifinsa, cike da takaici baffa Usman dake kallonsa yace, "Bakomai Aliyu duniya ce, idan mutum ya gyara kansa, idan kuma ma yab'ata kansa, rayuwa da kake gani batada tabbasa kuma shi zumunci ba wasa bane, don haka duk abunda kayi don kanka, mudai iya fatanmu da kai ALLAH yagyara maka halinka" juyowa yayi wajen baffa yaci gaba da cewa "ka k'yaleshi yaya indai duniyace ta ishesa riga da wando" mik'ewa yayi ransa ab'ace yabar d'akin yanaci gaba da qananan maganganunsa, baffa ya kalli Nuraddeen dake gefe idanuwansa sunyi jawir saboda b'acin rai da kuma kukan da yayi yace "Nuraddeen ya hidima?"

Murmushin qarfin hali yayi masa sannan yace "Alhamdulillah baffa, ya jikin naka?"

"Alhamdulillah Nuraddeen, ubangiji ALLAH yayi maka albarka ya albarkaci zuriar da zaku samu, gobene d'aurin auren ko?."

"Amin baffa, Amma don ALLAH a d'aga d'aurin aurennan har kasamu lafiya, kaga sai muje asibiti gobe adubaka tunda yanzu marece yayi sosai"

"Hakane yaya, gaskiya yakamata muje asibiti, zamannan gida naga babu wani sauqi da ake samu abunma sai qara tsamari yake." Baffa Usman yafad'a had'e da kawo mafici yana yimasa fiffita.

"Kul! Usman kada in koma jin zancen d'aga auren nan yakoma fitowa daga bakinku da kai har Nuraddeen, wlh ko rasuwa nayi banyafe ad'aga d'aurin aurennan ba kunji nafad'a maku, lafiya da kuma rashinta duka daga ALLAH ne haka itama rayuwa da mutuwa duk ahannun ALLAH suke, aure kuma hukuntawarsa ce adaidai lokacin daya so, don haka ban lamunta ad'aga aurennan ba saboda rashin lafiyata, mutuwa da kuke gani bata hana komai aduniya balle rashin lafiya, don haka abar komai ynda aka tsarashi da yardar ALLAH Kuma zan samu sauqi kunji ko nafad'a maku?"

"Eh Yaya" suka amsa masa atare kowane najin wani abu azuciyarsa.

Sosai baffa yasaki jiki don ya nuna masu yaji sauqi sosai sukayita fira har bayan isha'i, amma cikin jikinsa shikad'ai yasan meke damunsa, duk wannan hali daya shiga Yaya hawwa bata koma tunanin koda leqa ta gefen da d'akin baffa yake ba balle taje tadubo sa saboda fad'an da baffa Usman yayi masu wanda hakan ba qaramin sake qonawa baffa rai yayi ba har yake tunin tabbas koda mutuwa yayi yasan hawwa bazata tab'a damuwa ba balle yasa ran zata tuna dashi tayi masa addu'a, hawayene suka gangaro masa a fuska yayi saurin gogewa don kada sugani, baffa Usman bai bar d'akin ba sai kusan qarfe d'aya na dare shi kuwa Nuraddeen kwancensa yayi wajen baffa sukaci gaba da firarsu wacce rabinta duk nasihace yakeyi masa akan rayuwar aure da kuma amana da hak'k'ok'an da ALLAH ya d'ora masa na matarsa, yayi mashi nasiha sosai akan muhimmancin hak'uri da iyali da kuma kyautata masu har aka kira sallar asuba, da kanshi ya riqasa sukaje baye yayo arwala sannan ya maidosa shikuma ya koma yayo tasa had'e da wucewa masallaci acan sukaci karo da baffa Usman shima ya zauna bayan anyi sallar asuba yayi masa nasiha sosai, bayan sun dawo ne masallaci lokacin rana tafito baffa Usman yasa aka kirawo masa yaya hawwa da bilkisu anan d'akin da baffa yake, Amma har matarsa bilkisu tazo Yaya hawwa nacan abunta zaune don cewa tayi baza tajeba saboda jiya agaban mutanen gida yara da manya ya wulaqantasu don haka Babu inda zataje tunda bashi ya ajiyeta ba.

Sun jima suna jiran isowarta amma fiye da minti talatin babuta ba tsammani, hakan yasa baffa Usman ya maido hankalinsa ga bilkisu batare da yajira bayanin komai abakin taba yayi mata tas dama tun jiya da daddare yafara sauke fushinsa akanta yau kuma yasake d'orawa hak'uri tayi ta basa tana roqonsa gafara ya katsa mata tsawa had'e da cewa,

"Kiyimun shuru ba wannan nake son ji daga bakinki ba, wlh daga yau nakoma jin kin tankawa yaya hawwa acikin gidannan sai ranki yayi mummunan b'aci don bazan lamunci garin shashanci irin naki kibiye mata kuna fitinar da zata haifarwa da d'an uwana matsala ba, daga yau duk abunda zatayi maki Ina so taci albarkacinsa matuqar ni inada muhimmancin agareki a matsayinsa na yayana."

"Shikenan zanyi yanda kace in Sha ALLAH, Yaya kai Kuma don ALLAH kayi hak'uri bisa damuwar da muka haifar maka da ita jiya" tafad'a tana goge hawayen jin d'acin hukuncin da maigidan nata ya yanke mata, taso ace yabarta takoyawa Yaya hawwa hankali idan ita mahaukaciyace amm dole tabar maganar ko don yiwa mijinta biyayya, girgiza kai baffa yayi don baiso baffa Usman yayi mata hakanba agabansa, yaso ace amtsayinsu na miji da mata sun kashe sun binne a d'aki amma sanin yanda zuciyar d'an uwan nasa take idan ransa ya b'aci yasa bai dakatar dashi ba, cikin taushin murya baffa yace,

"Babu komai bilkisu, kiyi hak'uri kema nasan duk dalilin jagorncin dana azaki ga aurennan ya haifar maki da wannan fitinar awajen iyalina, don ALLAH kuci gaba da hak'uri da ita kunsan hali zanen dutsi, ubangiji ALLAH ya shiryeta kuma ya ganar da ita, Usman don ALLAH kada kasa bilkisu tacire hannunta awannan hidimar domin burinta aduniya bai wuce a kunyata a wannan al-amarin ba, don haka Ina baku haquri na yau d'ai kujurewa duk abunda zatayi har agama lafiya kaji ko?" yaqarasa maganar yana kallon baffa Usman da gaba d'aya yaso iyalinsa tafita harkar sha'anin auren saboda matsalolin hawwa, wata ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli d'an uwan nasa yace

"Duk abunda ka yanke Yaya shine daidai kuma dole ayisa ubangiji ALLAH ya kauda fitina kuma yasa agama taro lafiya."

"Amin ya rabbhi Usman nagode, ALLAH ya zaunar dakai lafiya da iyalinka kuma yanda kake kula dani tare da yimani biyayya kaima ALLAH yabaka mai yimaka haka, yanda ka kula da sha'anin Nuraddeen kaima ALLAH yakula maka dana dukkanin zuri'arka nagode nagode sosai.." yaqarasa maganar yana mai fashewa da kuka saboda tunanin abunda zai faru bayansa don shikad'ai yasan yanda yakeji acikin jikinsa,

Abunda duk ALLAH yatsaro babu wani mai iya hanashi sannan ita matar mutum kabarinsa yau misalin qarfe biyu da rabi na rana masallacin juma'a na unguwar yarimawa yacika da tarin dan dazon mutane 'yan kasuwa da malamai don sheda d'aurin auren MALAN NURADDEEN IDRIS ALIYU (MALAN IDRIS) da kuma amaryarsa RASHIDA BASHAR MAI TAKALMA, inda nahango baffa zaune agefe sai kuma baffa Usman tsaye agefensa yana gaggaisawa da mutane cikin farin yadinsu boyel d'unkin babbar riga sunyi matauqar kyau kai kace tagwayene kowanensu sai fara'a yakeyi saboda tsammanin cikar burinsu, haka baba da qanensa malan balarabe suma sunsha manyan rigunansu kalar ruwan omo iri d'aya fuskokinsu cike da annuri suna yiwa baqi masauki kafin isowar ango, Nuraddeen na hango tare da abokanansa sai wasar hauru yakeyi cikin had'ad'd'iyar shaddarsa milik suna tahowa shima d'unkin babbar rigane ajikinsa ya matuqar zauna masa had'e da yimasa kyau sosai wanda ko ba'a tambaya ba kasan cewa shine ango, suna qarasowa aka nuna masu masaukinsu acan gefen dake tsakanin iyayensa dana amarya limamin masallacin juma'ar yafara gabatar da sigar aure kamar yanda yazo a musulunce sannan aka gudanar da yarjejeniyar karb'arwa Nuraddeen auren Rashida daga hannun iyayenta bisa sadaki dubu hamsin laqadan ba ajalanba yayin da iyayenta suka damqawa nuradden amanar aurenta tahannun iyayensa bisa yarda da amincewar cewa zai kula da cinta, shanta, suturarta da kuma lafiyarta sannan aka tofa addu'a, wani murmushi baffa yasaki had'e da cewa,

"Alhamdulillah, dama sannu sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba akaiba, ubangiji ALLAH ka amintar da wud'annan bayi naka bisa dukkanin alkhairanka awannan rana da dukkanin ranakun da zasu biyo bayanta har iya qarshen rayuwarsu" baffa Usman dake gefensa ya amsa masa da "Amin Yaya" yana dariya, shikuwa gogan naka ana gama d'aura auren lumshe idanuwansa yayi yanajin wani irin farinciki na ratsa dukkanin sassan jikinsa da kuma rouhinsa, yajima ahaka kafin d'aya daga cikin abokanansa ya zunguresa suka bushe masa da dariya suna yimasa sheri.

••• ••• •••

Acan gida kuwa bebeji gaba d'aya anguwar mutanen arziqi suna wajen d'aurin auren Amma banda baffa Ali da tun jiya da yayi fushi akan maganar da baffa suka yimasa yasha alwashin ko d'aurin auren bazai jeba, Babu yanda baffa Usman baiyi dashi ba amma yace babu inda zaije tunda suka had'e masa kai suka nuna masa cewa shi bawani tsiya bane acikinsu, ganin lokaci na qurewa yasa ya ajiye masa kayan da suka d'unka su uku suka wuce cike da tsammanin cewa zai biyosu abaya, Amma ga mamakinsu har aka gama d'aurin auren bai jeba wanda hakanma yasake tab'a zuciyar baffa sosai ganin cewa idan baya raye sukad'aine zasu iya karb'arwa 'ya'yansa aure amma ace yaqi halartar auren d'an nasa, awannan karonma sake danne damuwarsa yayi saboda gudun haifarwa da d'ayan d'an uwan nasa damuwa.

Bilkisu ma sake zage damtse tayi cike da farinciki tamkar wani abun bai tab'a faruwa ba jiya tayi duk abunda yakamata, duk wasu baqi da zasuzo kai tsaye Yaya hawwa kace masu suje wajen qirjin biki wato kinfi uwar ango bilkisu don ta tozartata amma ita hakan ko ajikinta don baffa Usman yabata isasahin kud'i tayi abinci ita da 'ya'yanta su kareema da sukazo, koda suka jewa Yaya hawwa yimata fatan alkhairi ko kallon banza basu isheta ba balle ta tankasu suka juyowarsu batare da sun damu ba don dama saida bilkisu taja masu kunne kafin sutafi, baffa Ali kuwa shida matarsa bini bini sun fito tsakar gida ko kunyar mutane basaji sun yadawa bilkisu magana au da Yaya hawwa itako tayi kamar bata masan sunayi ba.
Chapter 24 · 0% Book details