← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 160

Sashe 111

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi little yayi tare da d'an russunar da kansa qasa yace.

"Eh, Ina wuni?" Fad'ad'a murmushin sa baffa Usman yayi tare da qarasowa wajensa yayi saurin miqa masa hannu tare da yimasa sallama, cike da yaqinin cewa tabbas wannan jinin d'an d'an d'an uwansane baffa Usman ya amsa masa sallamar yana qare masa kallo tare da tunano kammannin Rashida acikin fuskarsa.

Kusan secod biyar suka kwashe ahaka kafin can baffa Usman yayi firgigit kaman wanda yafarka daga bacci yajawo hannnunsa su shiga ciki, tunda suka shigo baffa ke kallonsa har suka qarasa, shidai little sai bin ko ina nagidan yakeyi da kallo kafin can ya ajiye idanuwansa akan baba balarabe, ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in.

"Kai wlh ALLAH tsohonnan yau ka wahalsheni da yawa, gaba d'aya ka tada mani da hankali gabana sai fad'uwa yakeyi."

"To ai seyadena yanzu tunda gani kagani cikin qoshin lafiya."

Matsawa yayi inda baffa yake had'e da zaunawa kusa dashi yasa hannu ya dafo kafad'unsa, "sannu kaka, anwuni lafiya?"

"Lafiya klw Abu sumayya, ya kake?"

"Ina lafiya kaka, yanaga kamar jikinka a sanyaye.."

Muryarsa na rawa ya juyo duka jikinsa yana fuskantar little tare dasa hannayensa yariqo fuskarsa dasu yace,

"Farincikine yahaifar da haka jikana tare da samun kyakkyawan albishir daga bakin da bazai tab'ayimun qarya ba akan cewa kai d'in jinina ne, katuna nasha fad'a maka inada wani d'a tafiyarka da maganarka sak irin nasa, har kake tambayata yana ina? Kana so kasanshi katuna,"

Kasa amsa masa yayi saboda yanda yaji gaba d'aya jikinsa ya mutu yana kallonsa, juyowa yayi yana kallon baba balarabe ya jinjina masa kai alamun tabbatar mas da zancen baffan.

"Hakane Nuraddeen, wannan shine kakanka wanda yahaifi babanka, nazab'i nahad'aka da sune batare da sanin mahaifiyarka ba da kuma 'yan uwana saboda gudun lalacewar zumunci tsakanina da 'yar uwata, koba komai ni kaina na sauke wani nauyi da d'an uwana yamutu yabarni dashi aransa,

Little baisan lokacin da wasu hawayen da zai iya kira dana dad'i ba suka zubo masa da sauri yataso ya rungume baba balarabe yana fad'in.

"Nagode d'an tsoho da kazamo nafarko wajen cika mani muradai na da kuma mafarkaina, kayi mani abunda duk duniya Babu Wanda zai iya yimani, ka haska mani rayuwata alokacin da take cikin duhun rashin sanin makomarta anan gaba, ba shakka kakana yafi kowa sa'ar samun d'an uwa aduniya, yayi saurin tafiyane saboda yanada yaqinin cewa goben ahalinsa zatayi kyau a hannun d'an uwansa, nagode maka nagode maka sosai d'an tsohona mai ran qarfe, ka dad'e kayi qarko har zuwa qarshen ahalinmu."

Yasake rungumesa sosai kamar zai tsaga jikinsa ya sakasa,

"Kai meye haka? Meye haka kakeyi lele? Cikani mana kasan ba qwarine da qashina ba yanzu, wannan abu haqqine akaina duk da nasan hakan zai iya haifarmun da matsala, amma nayi farinciki sosai, wannan addu'ar taka bana fatar karb'uwarta domin banaso qarkona yawuce lokacin da zanga jininka, don haka kama dena fatar hakan kaji ko?"

Yaqarasa maganar qwalla nazubo masa a fuska, d'agowa little yayi daga jikinsa yasa hannuwa yagoge masa hawayen fuskarsa yana fad'in.

"Kadena kuka mana d'an tsohona, kayi Abu mai kyau, ka sada yaron da akeyiwa kallon shege da danginsa na uba, ka gyara zumuncina don me da ALLAH zai tsaida rayuwarka ga iya ganin jinina bayan shi yafad'awa manzonsa cewa duk wanda ya kiyaye game da sha'anin zumunta zaiyi masa tsawon rai tare da gyara gobensa?, Natabbata koda baka kai lokacin da nakeyi maka fata ba in Sha ALLAH zaka wuce lokacin da kai kake fata, na dad'e da dason sanin dangin mahaifina, amma yanayin da mahaifiyata keshiga da alqawarin dana d'aukar mata akan bazan sake tambayarta abunda zai sakata cikin damuwa ba shi suka hanani tsaurara son sanin hakan saboda gudun na kaucewa umurninta duk kuwa da shegantani d'in da akeyi"

Miqewa yayi yakoma wajen baffa da duk wata kalma da yake ajewa ke dad'a tunkud'o da fitar hawayenta saboda tausayinsa da yakeji da kuma rad'ad'in kalmar da yaji ana jifarsa da ita, kamo hannuwansa yayi yana murzawa ahankali tare dayin murmushi alokaci d'aya kuma hawaye na zubo masa yace.

"Kakana kaima kuka kakeyi?, Kaida zakayi farincikin bayyanar jikanka agaresa mezai saka kuka Kuma?" Sa hannuwansa yayi akan fuskarsa shima yagoge masa hawayen dake zubowa sannan yaci gaba da cewa.

"Kana kewar mahaifina kamar yanda nima nake matuqar kewarsa ko?."

Girgiza masa kai yayi had'e da saurin rungumesa yana cewa.

"Ko kad'an jikana, kai kad'ai nake kewa da kuma mahaifiyarka, ka manta dashi tunda bayada buqatarmu na tabbata zaka maye mani gurbinsa."

"A'a kakana, zaiyi matuqar yimani wahaka na iya maye maka gurbinsa, kayi haquri kada kayi fushi dashi, duk da Ina son jin muryarsa, Ina son ganinsa, Ina son na rab'i jikinsa nayi fira dashi na fad'a masa damuwata nayi kuka ya sharemun hawayena amma nakasa samun haka saboda yayi nesa damu banyi fushi dashi ba, natabbata SANNU SANNU bata hana zuwa..kamar yanda bamuyi tsammanin zamu had'u da juna ba sai gashi ahankali ba zato ba tsammani ALLAH yahad'a fuskokinmu shima in Sha ALLAH da sannu zai dawo garemu, da kanshi zai cike gurbinsa da kake tunanin zan maye maka da yardar ALLAH."

Wani irin sanyi baffa yaji na ratsa zuciyarsa jin kalaman jikan nasa, d'ago yayi daga jikinsa little yayi saurin maidashi yana fad'in "Rowa zaka yimun bazaka barni naji d'imin jikinka ba?"

Gaba d'aya duk sukasa dariya, baffa ya cikasa yana fad'in nawa kad'ai bazai wadatar da kaiba har sai ka had'a dana wannan kakan naka." Yaqare maganar yana nuna masa baffa Usman da bakinsa yakasa rufuwa saboda farincikin da yakejin kansa aciki, haka little yaje ya rungumesa shima tare da d'an tsokanarsa sannan suka shiga wata firar mai cike da jin dad'i kowannensu naji tamkar karsu fita cikin wannan yanayin, saidai ita rayuwa haka ta gada wani lokaci farinciki wani lokaci baqinciki, Abu d'aya baya tabbata balle sudawwama acikin wannan yanayin.

Sun jima suna shawarwarin yanda cigaban rayuwar zata kasance inda baffa da kansa ya roqi little akan cewa subar wannan zancen a tsakaninsu har zuwa lokacin da mahaifinsa zai dawo, yasani bayada matsala ta b'angaren baffa Usman haka ta b'angaren baba balarabe shima bazai bayyanata ba kodon gudun lalacewar zumuncinsa da Yaya Maryam har zuwa lokacin data buqata, little d'in dai yake tsoron yabud'e sirrin shiyasa yaroqesa, abunda bai sani ba shima kansa baya buqatar fitar zancen saboda gudun b'acin ran mahaifiyarsa har sai lokacin data buqaci ita da kanta tahad'asa dasu sai ya bayyana mata gaskiya, nan yayiwa baffa alqawarin zai riqe wannan sirrin har zuwa lokacin da ALLAH yayi nufin bayyana komai batare da matsala ba tunda dai yasamu wani sashen farincikinsa kamar yanda yake mafarki,

Shiru baffa yayi kafin can yace,

"Saidai yakamata ace Ali yasani tunda shid'in d'an uwana ne bazai yuyu ace na waresa daga sanin hakan ba."

"Idan nima d'in d'an uwanka ne dana isa ga dukkanin abunda yashafeka to nace harshi bazai san komai basai ranar da gaskiya zatayi halinta." Baffa Usman yafad'a cikin b'acin rai.

"Saboda me Usman, karka manta shimafa jinin mune, duk mugun halinsa dai bazamu iya cire jininsa daga namu ba kamar yanda shima bazai iya cire namu anasa ba."

"To nidai nafad'a Yaya, wlh baza'a fad'a masa ba kaji kuma na rantse."

Daga haka baffa bai sake cewa komai ba ya qyalesa, little yayi dariya don yafahimci kakan nasa baiji dad'in hakan da d'an uwansa yace ba.

"To nidai ku taimaka ku gwada mani amaryata, itama ina kewarta Ina so naganta."

'Dago kai baffa yayi yakallesa don ya fahimci kakarsa yake nufi wato Yaya hawwa, aransa yace ALLAH sarki gaba d'aya sak d'abi'unsa na mahaifiyarsa ne, matuqar yasan abunda tayiwa mahaifiyarsa har take buqatar ya had'u da ita to tabbas yacika d'a nagari mai ramakon alkhairi ga mugunta, nan shima baba balarabe yabuqaci yashiga ya dubota ita da baffa Ali suka miqe gaba d'aya suka shiga cikin gidan.

Ita Yaya hawwa saboda tsananin kukan da takeyi ako yaushe yasa idanuwanta gaba d'aya sun dena gani ga yanayin tsufan da taqarayi duk ta nad'e waje d'aya kai ka d'auka ba mutum bace, don ma ALLAH yasa tana samun kulawa gwargwado, tsabar tausayinsa da little yaji da suka shiga harda kukansa, koda suka shiga babu abunda takeyi sai kuka tana kiran nura.nura.nura, da qyar Inna Bilkisu dake zaune gefenta ta rarrasheta sannan tasamu tayi shiru suka gaisa da baba balarabe tare da yimasa yajiki, little kuwa sunan mahaifinsa da yaji tana kira yasa yakasa yin magana saboda kada ta ida rud'ewa idan taji muryarsa tayi tsammanin shine, bayan sun fito ita dai Inna Bilkisu sai kallon little takeyi saboda kamarsa da Rashida gashi har taji zasu tafi ba'ace komai akansa ba, hakan yasa zuciyarta tabata cewa qilan cikin 'yan uwanta ne tunda gashi tare yake da qanen mahaifinta malan balarabe,

A hankali lokacin da suka kawo wajen shiyar da Nuraddeen da Rashida sukayi zama baffa Usman ya rad'awa little a kunne, nan ne mahaifiyarka da mahaifinka suka zauna ka ganshi nan tunda suka barshi sau d'aya aka bud'asa har zuwa yau.

Juyawa little yayi yakalli wajen da kyau kawai sai ya tsinkayo mahaifinsa da mahaifiyarsa tsaye abakin qofar, murmushi yayi tare da shafa kansa sannan suka wuce ta can d'ayar qofar inda baba Ali ke jinya don awancan zaurenne na qofar baya suka zauna shiyasa ma Basu samu wurgewar mutane ba sosai balle asan abunda yafaru.

Suna shiga baffa Ali yayi ido hud'u da baba balarabe dake shigowa bayan baffan Usman da sauri ya noce kansa qasa saboda tunawa da abubuwan daya fad'a masa ashekarun baya, gaba d'aya sai yashiga gashi gabansa yashiga fad'uwa yayi tunanin sunzo ne domin su turkesa akan abunda yafad'a amma abunda bai sani ba gaba d'aya baba balarabe bai fad'a masu maganar daya fad'a masa ba, don yasan idan yayi hakan to zai iya tab'a masu zumunci musamman daya fahimci irin soyayyar da baffa keyiwa 'yan uwansa ta hanyar kalamansa, kawai sai ya b'oye gaskiyar yabar duka laifi akansa don baya buqatar ya lalata zumuncin tsakaninsu da shima yake neman gyara nasa, yatabbata komai daren dad'ewa gaskiya zata bayyana domin ita SANNU SANNU bata hana zuwa...,

Girgiza kai kawai yayi sannan suka shiga gaggaisawa tare da yimasa yajiki, ba qaramar razana yayi ba da yaji muryar little wanda saida hakan ta bayyana qarara a fuskarsa.
Chapter 111 · 0% Book details