← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 160

Sashe 48

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin darenhankalin kowa yabi yatashi anata sallalami, baffa Ali kuwa kallon inna ruqayya da itama ta dan shiga tsinke yayi yana nuna mata Yaya hawwa dake tsaye ta rafka uban tagumi fuskata cike da damuwa kamar da gaske ammaqasan zuciyarta cike take da farinciki yace.

"Dubi Yaya hawwa, narantse da ALLAH tasan komai, d'akin kalleta Zaki tabbatar da kawai tashuka tsiyar don farincikine tattare da ita bayan waccan damuwar da kika hangota aciki."

Murmushi tayi had'e da cewa. "Ranar bayyanar asalin tata damuwar nakusa tunda tagama cimma nata burin."

Ganin kowa yayi cirko cirko ana jajanta maganar b'atan Rashida yasa Nuraddeen yanufi qofar gida a hargitse yana sabbatu da sauri baffa Usman yariqesa yana fad'in, "Ina zakaje Nuraddeen acikin wannan tsohon dare, qarfe uku fa ake magana yanzu, kayi hak'uri har muga abunda safiya zatayi."

Wani irin kukane yazo masa yana kallon baffa Usman cike da mamaki yace

"Baffa da bakinka kake fad'in inbar iyalina acikin wannan tsohon dare batare da sanin awane hali take cikiba?, Baffa amana ce fa agareni, bayan haka katuna halin da take ciki idan akace salame ce baffa kanaga zamu iya runtsawa awannan daren muna jiran wayewar safiya sannan muje nemanta?, Don ALLAH baffa kabarni inje koma meye yasameni nida ita, zuciyata nayimun rad'ad'in da zan iya mutuwa awannan lokacin idan natsaya dakon jiran dawowarta." Yana gama fad'ar haka yabud'e gambun yafita batare daya jira amsar da zata fitowa daga bakin saba, dagudu ya fice cikin gidan ko fitila babu a hannunsa Saida yakusa kai farkon gari sannan yafara yawo yana kiran sunanta, inyayi nan yayi can batare daya damu da yanayin dare ko duhun dake da garinba., Idan yayi wancan lungu ya shiga wancan yakoma wannan haka yayita yawo yana kiran sunanta, kallo d'aya zakayi masa kasan kwanciyar hankali tagama gushewa a jikinsa, wasa wasa har qarfe hud'u tayi ba batun Rashida, kaf ya zagaye k'auywn nasu da qafa ko takalma bashida yana kuka yana ambatar sunanta tamkar wani k'aramin yaro duqewa yayi yasaki wata irin qara had'e da jin kansa yana jujjuya masa, yafi minti biyar ahaka kafin ya miqe tunawa da 'yar qramar kasuwar garin da yayi ya nufi can da gudu, rumfuna rumfuna yadinga bi yana leqawa amma began taba, hanyar asibiti yanufa lokacin biyar da rabi na asuba yafara zagayenta tamkar wani tsohon mahaukaci sannan yashiga ciki yana lelleqa d'akunan majinyata, ganin nan ma Babu labarinta yasa yafara shiga dazukka dake cikin qauyen tamkar wani mashayi saboda yanda yake tangad'i saboda tsananin tashin hankali da gajiya, tun yana kuka har hawayen nasa suka qare, haka suma su baffa suka shiga nemanta cikin qauyen Amma babu labarinta, misalin qarfe shida na safe ko salla basuyi ba suka wuce qauyukkan dake maqwabtaka dasu amma har qarfe bakwai na safe balabarinta, a hanyarsu ce ta dawowa suka cikaro dashi saman hanya yashe mutanen gari sun zagayesa, da gudu baffa yaqarasa kusa dashi cike da damuwa ya tallabosa, ckallon yanda yayi bijib bijib da jiki ga qafafuwansa duk sun yayayyanke qaya ta sossokesa yasa baffa ya fashe da kuka yana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, allahummah ajirni fi musibati wa'ahlifni khairan minha." Cikin yanayin dake nuna Nuraddeen nacikin matsananciyar damuwa ya d'ago kansa yace,

"Baffa kunga matata Rashida?. Baffa kubarni anan kuje kudubo mun ita, raina fansane agareta koda zan mutu kuje kutaimaketa, qarfina yaqare gaba d'aya, lumfashinanema yakeyi ya rabu da gangar jikina saboda rashin sanin a ina take, Kuma awane hali take ciki, baffa kutaimaketa jikina yana bani cewa Rashidata nacikin wani hali.." bai qarasa maganar ba sanadiyar lumfashinsa daya d'auke, jijjigasa baffa yashigayi yana kuku had'e da kallon baffa Usman da shima kukan yakeyi yace.

"Usman kataimakeni kada inrasa d'ana da nafiso aduk fad'in duniya." Kan baffa Usman yaqarso wajen har baffa ya ciccib'o Nuraddeen da sauri baffa yaqarasa wajen ya kama masa shi suka nufi hanyar asibiti dashi asheme ko motsi ba yayi.

Kan kace me batu ya gama zagaye qauyen nasu cewa matar Nuraddeen ta b'ata da tsohon cikinta wata tara.

Baffa Ali kuwa fad'a yakamayi yana fad'in tun farko Saida suka guji wannan auren saboda Babu alkhairi acikinsa yanzu gashinan zasu jawo masu abunda yafi qarfinsu don yasan iyayen yarinyar nan dole suje su kaiwa 'yan sanda rahoto azo adamesu da 'yan tambayoyi,

Su baffa na isowa asibiti likita yaduba Nuraddeen tare da yimasa wasu allurai ya fad'a masu sumace yayi amma yanzu zai farfad'o, yana rufe baki Nuraddeen na tasowa da qarfi daga kwancen da yake akan gadon asibitin cikin matsananciyar qara yana fad'in.

"Rashidaaaa...."

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU👏😭*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Amincin Allah ya tabbata agareku masoya littafin SANNU SANNU...haqiqa zan iya cewa tunda nafara littafinnan ban tab'a jin dad'in rubutunsa ba kamar jiya, saboda yanda naga ruwan comment d'inku har da wud'anda Raina bai tab'a kawomun cewa suna karatun saba, na matuqar jin dad'i har sai da zuciyata takoma tana rayamun cewa anya soyayyar da kuke yiwa Rashida batafi wacce kuke yiwa Billy ba?😰 What ever d case am feel a little jealous oo..😉lolz..nagode nagode sosai jazakumullahu bikhair, I LUV YOU ALL FILLAH_🤍❤️

Page___37💎

Juyowa su baffa sukayi tare da likitan suna rigegeniyar isa inda yake, tsaitsaye sukayi gabansa fuskokinsu cike da tausayinsa ganin yanda nan take duk yabi ya zabge kamar wanda ya buge watanni yana jinya, riqasa likitan yayi daga zaunen da yake ya maidashi kwance yana fad'in.
"Relax malan Nuraddeeni, in Sha ALLAH komai zai daidaita kaji ko?"

A hankali yarufe idanuwansa wasu zafafan hawaye suka zubo masa afuska, juyowa yayi yana yabud'e idanuwansa suka sauka saman na baffa Usman, kamo hannunsa yayi yariqe sosai har lokacin hawaye nazubowa daga cikin idanuwansa yace. "Baffa kun ganta kuwa?."

"Kayi hak'uri Nuraddeen, in Sha ALLAH za'a ganta, kafara qarfafa zuciyarka tukuna tayanda zaka iya fad'an nemo masoyiyarka aduk inda tashiga, kada kabari raunin zuciya ya bayyanarwa da duniya gazawarka ga masoyiyarka dake neman taimakonka takowane fanni."

Baffa usman ne yafad'i hakan yana rumqe hannunsa sosai, cikin yanayin dake bayyana dukkanin raunin da Nuraddeen ya samu ta fannin zuciya, gangar jiki, kwakwalwa da kuma ruhinsa yace, "kaicona da riskar wannan lokaci da nayi, meyasa mutuwa batayi gaggawar d'aukata ba kafin wannan ranar tazo mani?, Meyasa rayuwa zata yanke mana wannan hukunci a daidai lokacin da muke tsananin buqatar juna?, Meyasa soyayya tayimun d'aurin goron dana kasa gano alfanun dake cikin komawar Rashida agaban iyayenta saboda kawai Ina buqatar kasancewa tare da ita akoda yaushe? Meyasa duniya zata juya mana baya a lokacin da ALLAH keshirin yimana kyautar da zata bamu jin dad'in zamanta?, Meyasa?, Meyasa baffa?" Yaqarasa maganar yana qara fashewa da wani irin matsanancin kuka maicin rai, da sauri baffa yajuya yabar d'akin saboda bazai iya jurar sauraren kukan d'an nasa ba, kowace hawainiya dake d'igowa daga cikin idanuwansa jinta yakeyi tamkar saukar qyanqyashe a saman zuciyarsa, baffa Usman kuwa sake rumqe hannun Nuraddeen yayi sosai cikin dakewa yace.

"Kayi haquri, kayi haquri, kajure kada zuciyarka tasa ubangijinka yayi fushi dakai, Babu dalilin dakesa ALLAH yayiwa bayinsa jarabawa kamar tsantsar imaninsu agaresa, wlh wlh Ina tabbatar maka da cewa duk inda matarka take bazata tab'a walaqanta ba domin ita yarinyace mai tawali'u ga ubangijinta, yarinyace mai tsananin riqo da addini da kiyaye dokokin ALLAH don haka dole ALLAH zai jarabceta harma damu dake tare da ita, saidai abu gudane nake da tabbaci akai da kuma kyakkyawan zato zuwa ga ubangijinmu cewa zai kula mana da ita aduk inda take fiye da kulawar da zamu yimata, mumunin k'warai shi ALLAH ke jarabtar kuma duk tsananin ibadarka da tsoron ALLAH bazai hana ajarabci imanin kaba saboda aqaramaka d'aukaka awurin ubangiji idan kaci jarabawarka, kayi haquri in sha ALLAH za'aganeta yau d'innan kaji ko?."
Duk da dai babu wani rad'ad'i da ya denaji azuciyarsa da kuma quncin dake damunsa ya yarda da duka kalman baffa Usman kuma zai gwada amfani dasu, kalaman data dinga fad'a masa daren jiya ne suka shiga yimasa yawo a kwakwalwa _Haba Nuraddeen, hasken idaniyata, zuciyata da kuma ilahirin gangar jikina, Kai kuwa meye zai tayar maka da hankali bayan kasan kanada ALLAHnka akoda yaushe kuma yana tare da kai, me zaka jiwa tsoro aduniya kai dake tare da sa albarka iyayenka, me kake shakku acikin rayuwarka bayan kana da yaqini akan zamu kasance atare, don ALLAH kadena fargaba akan komai koda kuwa wani abunne zai sameka ko kuma ya sameni, natabbata cewa tsantsar imaninmu da miqa wuya ga ALLAH shine kan iyasa ajarabcemu, muzama masu juriya cikin al-amurranmu alokacin da wani abu kenema ya gitto mana cikin rayuwa, sai musamu kanmu masu riskar ubangijinmu amadakata kyakkyawa, kacire komai aranka in Sha ALLAH babu abunda zai faru, nasan harda tunanin haihuwarnan yasa kakejin haka, to kasanyawa ranka salama in sha ALLAH zan sauka lafiya kuma zan haifa maka chuluv d'inkacikin qoshin lafiya kaji ko_

Tsananin jin yanda kansa keyi masa ciyo tamkar zai tsage yasa yai saurin dafe kansa da hannu bibbiyu yana sakin wata qara, da gudu baffa yadawo cikin d'akin ya tsaya yana fad'in. "Nuraddeen kayi haquri karka jawo nima in rasaka."

"Baffa kaina zai fashe." Nuraddeen yafad'a hawaye na dararo masa ta gefen idanuwa, juyowa baffa yayi yana kallon likita dake gefensa yace. "Likita don ALLAH kuyi masa allurar bacci koya samu koda 'yar qaramar natsuwa ce azuciyarsa."

"Abunda nake tunanin yi kenan nima." Likitan yafad'a tare da ciro biro a aljihunsa ya rubuta masu allurar bacci yace aje asiyo, baffa Usman ne yakarb'a da sauri ya nufi gefen da pharmacy take acikin asibitin ya siyo yakawo masa, daidai bakin qofar da zai shiga d'akinne yaci karo da baffa Ali suka shiga tare, miqawa likitan dake can gefen wani marar lafiya yana sa masa drip allurar yayi yace yadwo nan inda Nuraddeen d'in yake ya jirasa, shi Kuma baffa Ali tsaye yayi saman kan Nuraddeen yana kallon yanda ya zabge lokaci d'aya, ajiyar zuciya yayi sannan ya maida kallonsa ga baffa dake tsaye yace.
Chapter 48 · 0% Book details