← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 160

Sashe 43

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida Rashida tayi dariyar da duka haqoranta suka bayyana sannan tace, "a'a aunty muneera bazan yimaki ba domin duk son da kike yimasa baikai adadin wanda nake yimasa ba, saidai Ina baki shawara akan kema kije kiroqawa kanki ALLAH daya baki shi, amma nidai bazanyi ba." Taqare zancen cike da mamakin sakarci irin na Rashida,
Ture lab'b'a muneera tayi cike dajin haushinta tajuya tabar wajen tana fad'in "'yar baqin ciki, ALLAH ko bakyaso saina auri ya nura, bazaki zauna ke kad'ai ashiyar nan ba tundanima Ina qaunarsa, shegeyw mai tsawo kamar na iccen rama" dariya Rashida tayi sannan tawuce abunta had'e da turo qofar.

Na'ima da Aisha ma yaran Inna Bilkisu dake zaune dawowarsu daga wajen niqa kenan don duk abunda yafaru basa nan akayi suma suka sawa muneera dariya jin abunda yafaru tsakaninta da Rashida, kansu tayo tana susar kai suka tashi suka ruga aguje tabisu tana zunduma masu zagi dama Inna Bilkisu nacan d'akin baffa ana murnar samun lafiyarsa.

Ita ko Inna ruqayya sashen Yaya hawwa tanufa ta iskota cikin d'aki in tayi nan tayi can tana daddagar hannu had'e da cizon baki tana girgiza kai, "hmmm yanxu fa shikenan bakida abunyi yariga d'aya jawo maki reni ga yarinya, ya zubar maki girma agaban idanuwan d'anki sai yanda sukaga dama zasuyi acikin gidannan." Ina ruqayya tafad'a tana watsa hannuwanta baya tariqesu tana jiran amsar da zata fitowa daga bakin Yaya hawwa don tasan yanda zata sake tunzurata idan ta zubar da maka manta a fusace Yaya hawwa tajuyo had'e da cewa "inaaa wallahi qarya ne, bai isa ba matuqar Ina raye, ai fad'a da aljani sai anshirya kuma duk lalacewar bushiya tafi qarfin a takata da qafa koda kuwa da takalmi ne, ni hawwa ban tab'a sawa raina abuba nakasa, atarihin zuriarmu ba'a tab'a sakin mace ba don haka baza'a fara akaina ba, badai ya hana nura ya saki matar saba, to ni kuma zansa matar nurah tabar nura nahar abada koda hakan na nufin zan mutu wlh sai tabar cikin gidan nan ita d'in banza da wofi." Murmushi Inna ruqayya tayi kafin yace, "ahh to Nima dai shi nagani, wallahi idan bakiyi da gaske ba saita rabakinda d'anki da mijinki, yanzu haka fa Ina kallon wasu surqulle da tayi da wasu sabbatu ta tofa masa aruwa yasha sai gashi ya tashi da qafarsa, ke wannan yarinyar itama Ina ganin da nata shirin take don ko yayan Bata barsa ba tunda kikaga kimanin watanni goma sha yana zaune duk rigima da fitintinun da akeyi agidannan bai tab'a tasowa ba sai yau don yaji ance a saketa, aikam kema kinsan sedai ALLAH ya kayauta Amma tagama da Yaya balle nura."

Takai qarshen zancen had'e da fashewa da wani kukan munafucci,

"Ke ruqayya fita, fita kibarni inji da abunda ke damuna don yau dole in koma wajen malan bakada imani, wannan shegen cikin dake jikinta dole adakatar da zuwansa duniya da ransa kafin ita Kuma musn nayi da ita."

"Gaskiya kam Yaya hawwa, ai yarinyar nan wlhi tagama tona mana asiri."

"Mtss..zan zageki ruqayya kitafi nace, akwai mai tona maku asiri kamar hasararriyar yarinyar dake gabanku, ai bakiga tonon asiri ba sai ranar data bud'e baki tafad'a duniya cewa iyayenta shashashune da basu san ciwon kansu ba tukuna, ni nafara tunanin bazan iya had'a zuria da itaba a haifo mun jika sak aku kuturu da gwalmammin qafafuwa."
Yaya hawwa taqare zancen tana turo Inna ruqayya waje had'e da rufo qofar d'akinta. Tsaye Inna ruqayya tayi tana ayyana kalar abunda zata yimata duk ranar da burinta yacika akan wannan walaqancin da take yimasu ita da 'yarta sannan tawuce ranta ab'ace, d'akin da baffa yake tanufa fuskarta sake don kar afahimci yanayin da take ciki, lokacin mutane sun taru sai shigowa sukeyi suna fita ana yimasa barka da arziqi, baffa Ali da baffa Usman suma na zaune gefe fuskokinsu d'auke da farinciki duk da shi baffa Ali bahaka yaso aransa ba, yaso sai sungam shirinsu tsaf Mai faruwa tafaru koda zai samu lafiya gudun kada ya dakatar masu da shiri, yaqe kawai yakeyi amma haushi da takaicin taahin d'an uwan nasa yayi masa katutu azuciya, shi kam baffa yana tsaye yana gaggaisawa da mutanen dake shigowa,
Kallo d'aya Nuraddeen yayiwa Inna ruqayya ya d'auke kai had'e da barin d'akin don yanzu shi ko ganinta baya son yi, bayan an watse yarage su kad'aine mutanen gida zaune baffa sai faman zagaya falo yakeyi yana yiwa ALLAH godiya, kallo d'aya zakayi masa ka fahimci tsantsar farincikin da yake ciki saboda ynda ya bayyana a fuskarsa.

Wata irin muguwar dariya sukaji baffa Ali ya kwashe da ita harda tuntsirawa yana nuna baffa cike da isgilanci sannan yace.

"Ho.ho.ho Yaya kace yau ba zama, tun d'azu ka kasa zaune ka kasa tsaye sai faman zagayar d'aki kakeyi, halan tsoron zaunawa kakeyi gudun kada asake damqeka waje d'aya, koda yake gaskiya ka zaunu dole ka guji abunda zai sakesa ka zauna inba dole ba."
Wani irin dimmm...baffa yaji har jiri na neman d'ibarsa jin kalaman dake fitowa daga bakin d'an uwan nasa, badon yasan lokacin da mahaifiyarsu ta haifi baffa Ali ba da tabbas yace daqyar idan shi jinin sane, saboda gaba d'aya halayyarsa kwata kwata batada kyawo, Babu hankali da lissafi acikin kowane irin zance da zaiyi, amma babu yanda ya iya dole yayi haquri dashi tunda jinin sane, fatarsa d'aya ALLAH ya ganar dashi matsalolinsa ya gyara kafin wuri ya qule masa, murmushi yayi sannan yakoma inda yake zama lokacin da yake jinyar yana kallonsa sannan yace.

"Aliyu, ai ita jarabawar ALLAH takan zone ga bayinsa muminai, tabbas na zaunu anan wurin kuma nakanji na tawaya sosai, shiyasa yau da ALLAH ya yaye mun wannan lalurar nake ganin yakamata nayi farinciki na nuna masa cewa nagode da lafiyar daya bani, ba tsoro nakeji ALLAH yasake jarabtata ba domin shiyasan dalilinsa nayin hakan, nagode da irin naka farincikin daka nuna mun domin yasa nad'auki wani darasi aciki."

Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da cewa. "Ashsha Ali Kai kam wane irin d'an uwane haka? Shin kana ganin abunda kayi burgewa ne ko kuma zai samaa maka nishad'ine shiyasa kayisa? To kasani kayi kuskure mai girma domin kayi izgilanci da al-amarin ALLAH wanda shi keyin yanda yaso alokacin da kuma yaso.
"juyowa yayi ya kalli baffa sannan yaci gaba da cewa.
"kayi hak'uri da kalamansa in sha ALLAH zaiyi nadamar yinsu ko yaushene."
Baffa Usman nagama fad'ar haka yabar d'akin dama tuni itama matarsa Inna Bilkisu takoma cikin gida don cigaba da aikinta saboda marecen dake gabatowa, nan take baffa Ali yaji jikinsa yayi sanyi kuma yafahimci bai kyauta ba.

"Yi hak'uri Yaya." Yafad'a tare da miqewa shima yabar d'akin, Inna ruqayya nabiye dashi a baya...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___33💎

Ranar kam baffa kasa kwana yayi saboda abubawan da suka tarar masa azuciya, tsantsar farincikin samun lafiyarsa da irin kalaman da d'an uwansa ya jefesa dasu, Abu mafi cimasa rai shine yanda matarsa uwar d'ansa tayi biris da al-amarinsa, duk masoyansa na nesa dana kusa sunzo tayasa murnar samun lafiyarsa amma ita da take matarsa mallakinsa da tafi kowa ribantuwa da ita takasa zuwa ta dubasa balle tanuna masa farincikin da tayi, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana mai nadamar zab'enta a matsayin abokiyar rayuwarsa kuma uwar 'ya'yansa, ganin zai sake jawowa kansa wani b'acin rai da damuwa yasa yashiga bayi yayo arwala yatada sallah yana mai miqa godiyarsa ga ALLAH daya fitar dashi cikin jarabawar da take ciki batare da anrabasa da imanin saba,

Bayan sati d'aya da samun lafiyar baffa duk masu zuwa dubasa sun gama zuwa ciki har da iyayen Rashida, baba da umma da malan balarabe da matansa sai yayarsu hajia maryama da kuma aunty marwiyya, haka sukayo mota guda sukazo dubasa wanda ranarce tafarko da umma tazo gidan, duk da tanajin 'yan wasu matsaloli da 'yarta ke ciki tayi farinciki sosai ayanayin da taganta, don ba qaramar kulawa take samu daga wajen Nuraddeen ba, lokacin ne cikinta yacika wata biyar dam, tayi haske ta murje ko Ina na jikinta ya cika fam sai sheqi da kyalli takeyi abunta, ga d'an cikin daya fito ya zauna mata d'agwas ajiki gwanin sha'awa, duk wani motsi nata na akan idanuwan Nuraddeen da baffa, duk abunda take so taci suna bid'o mata batada wata matsala saboda yanzu komai tanaci kuma tadena yawan aman da takeyi si can baka rasa ba.
Rashida tayi farincikin ganinsu sosai har tanaji kamar takoma ciki, da zasu tafi baffa yahad'a masu sha tara ta alkhairi shida baffa Usman suka rakasu har bkin mota, haka kurum Rashida ta tsinci kanta da fashewa da kuka tanaji kamar karsu tafi subarta tariqe ummanta sosai, saida Nuraddeen yayi da gaske yasamu ya lallab'ata suka koma cikin gida sannan su kuma suka wuce cike dajin kewar 'yar tasu.
Duk wasu abubawa da baffa yasan nashine a d'akin da yayi jinya yana cika satin nan guda da warkewa ya kwashesu yamayar asalin shiyarsu wato d'akin Yaya hawwa dama jinya ce takaisa can shiyasa yanzu da ALLAH yabashi lafiya ya dawowarsa saboda yasamu damar tsawatar mata, sosai hakan da yayi ya matuqar b'atawa Yaya hawwa rai har tana cewa ita ya komawarsa can d'akin kar yazo ya takurata, yi yayi kamar bai jitaba yaci gaba da kwaso kayansa yana maidowa nan cike da burin dakatar da ita ga dukkanin mugun nufinta.
Chapter 43 · 0% Book details