← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 160

Sashe 118

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To shikenan, bari naqyaleki tukuna kafin hukuncin da zanyi maki akan wud'annan maganganun da kikayi tsaye kina fad'amun da abunda kika aikata yabiyo baya mugani idan zaki iya dakatar da abunda ALLAH ya tsaro, mugani idan kinada girman shaqiyancin da zaki iya ja da ikon ALLAH, ni dai natabbata wud'annan bayin ALLAH da kike gani ALLAH ne garkuwarsu kuma babu wani abu da zai samesu face yazamo alkhairi agunsu, sunyarda da Allah kuma shi suka riqa acikin al-amurransu, don haka nasan shine zai tayasu wannan fad'an da basuma san kinayi ba, kije ki binciki qarshen wacce tafiki fitsara da tanemi yimasu kaidi yanda ALLAH ya mayar mata dashi akanta!"

Yana gama fad'ar hakan yafice abunsa ya barta da tarin tambayoyin da batada mai amsa mata su.

Bayan sati uku da faruwar hakan dady ya kirawo Dr da qanensa faruq sai shakur don sune manyan 'ya'yansa maza ya kuma aika aka kirawo masa little, bayan duk sun hallara ya d'auko takardun wasu gidaje guda biyu d'aya takardun gidan dake laqe dana faruk ne, d'aya kuma takardun gidansa ne dake can laqe da shagonsa wanda marigayi baba yayi tsare masa kafin yarasu, kallon Dr yayi yace.

"Nura kaine babban d'ana, kuma kasani cewa dukkaninku ni nabaku gidajen da zaku zauna lokacin da zakuyi aure, don haka yanzuma Ina so inbawa d'an uwanku shakur nasa saboda sati nasama nakeso da yardar ALLAH muje muyo maganar aurensa asamana rana da kuma sadaki."

Ciro takardun gidan dake kusa dana faruk yayi yamiqa masa had'e da cewa.

"A matsayina na mahaifinka nabaka wannan gidan dake kusa dana faruk halak malak kamar yanda nabawa sauran 'yan uwanka alokacin da zasuyi aure, saboda haka daga yanzu zaka iya zuwa kayi 'yan gyare gyaren da kake buqata kafin lokaci yayi, Kai koma saidashi kake da ra'ayin yi kasai wanda kake so zaka iyayin hakan nakane babu wanda zai hanaka."

Godiya Shakur yashiga yiwa mahaifin nasa yana wasar baki tare da kallon 'yan uwansa yace.

"Broth's kutayani yiwa dady godiya ALLAH yaqara bud'i."

Duk suka amsa da Amin har da little dake gefe zaune yana kallonsu, saida suka gama yimawa dady godiya gaba d'ayansu sannan ya ajiye takardun d'ayan gidan dake hannunsa agabansu had'e da cewa.

"Wud'annan takardun kuwa na gidan dake laqe da shagon da marigayi bashar kakan little yayi tsare mani ne, ALLAH shine sheda tun ranar da kai Dr inbaka manta ba kazo kasanar damu cewa matarka Fatima tasamu juna biyu yana tsaye araina naqudurta cewa zan bashi wannan gidan ya d'auki iyalinsa sukoma can saboda yiwa ALLAH godiya akan ni'imar da yayi mana takarb'uwar addu'o'inmu da yayi kaima ya nuna maka naka jinin aduniya, sai gashi kuma ALLAH yayi nashi ikon akansa, ganin hakan yasa naquduri cika wannan niyar tawa ga iyalinsa, nan ma ALLAH bainufi hakan tafaru ba dalilin kasantuwarsu aqarqashin inuwarmu, don haka yau Ina son ALLAH da mala'ikunsa da kuma ku 'ya'yana kuzama sheda ko bana raye na mallaka wannan gidan halak malak ga jikansa don cika wannan alqawarin dana d'aukarwa kakansa cewa zan bashi wannan gidan tun farko,"

"Dady mun sheda hakan uabangiji ALLAH ya saka maka da alkhairi ya lullunka maka da gidan aljannah," Shakur yafad'a yana dariya tare da jujjuya nasa takardun gidan dake hannunsa, duk da dai faruk bai tanka ba da zaran ka kallesa yanayin fuskarsa zai tabbatar maka da cewa baiji dad'in hakan da mahaifinsa yayi ba.

Takarda da biro dady yaciro yayi rubutu akai sannan yafara ba Dr yace yasa hannu shida 'yan uwansa, bayan sun sa ya amshi takardun yamiqawa little dake zaune tamkar andasa shi, banda hawaye babu abunda ke zubo masa saboda ganin irin gatar da dady yayi masa tamkar yanda yayiwa 'ya'yansa, wannan bawan ALLAH wane irin mutunne shi da kokad'an babu qyashi da hasada acikin al'amurransa, yana karb'a yafashe da kuka hannunsa na kakkarwa,

"A'a Dady ban cancanci haka ba daga wajenka, abubuwan da kukayi mana nida mahaifiyata da kakannina kawai sun wadatar don ALLAH kabar takardun gidannan."

"A'a! Little meye haka?, Wannan kyautar tun asali cancantar kakan kace shiyasa tazo hannunka, shi kuma alkhairi danqone idan kayishi watarana zai dawo maka, bamusan me gobe zata haifar ba, abunda muka bayar shine namu wanda Kuma mukayi amfana dashi sharar banzane, rabon bawa kuwa duk inda yake bai wucesa don haka kawai ka amsa kayiwa ALLAH godiya domin shine yabaka ni kawai nazamo silane sai kayi mani addu'ah"

Godiya yayita zuba masa tare da sake miqawa Dr takardun ya amsa ya sanya masu albarka tare da miqo masa yana fad'in.

"Karb'a amma kafin nan bari nima amatsayina na uba agareka infad'a maka irin abunda dady yafad'awa Shakur d'insa, wannan gida nakane halak malak kaje idan akwai gyare gyaren da zakayi kayi kafin lokaci yayi, idanma bakada ra'ayinsa zaka iya sayar dashi kasai wanda kake buqata babu wanda zaice kayi laifi."

Gaba d'aya dady dasu shakur sukasa dariya, sun d'an jima awajen suna tattaunawa akan maganar auren kafin dady yasallami kowanensu yana maijin farincikin sauke wannan nauyin alqawarin daya dad'e dashi acikin zuciya har na tsawon shekaru, faruq baiji dad'i ba ko kad'an amma da yaje wajen ammie yana qunquni ya sanar da ita fad'a tayi masa sosai tare da nuna masa cewa idan mutum ya tallafi bayan wani to shima ALLAH zai tallafi bayansa, alkhairi kuwa danqone baya fad'uwa qasa banza, sucire qyashi da son duniya suyi koyi da mahaifinsu wajen taimakon wanda bayada, musamman shi faruq d'in don ta tabbatar Dr yariga daya gama hawa kyakkyawar turbar mahaifinsa shi kad'aine yamzu kansa ke rawa wani lokacin don haka yatsaya yayiwa kansa fad'a domin duniya ba wajen zama bace, Dole ya sauka daga dokin naqin daya hau ya bata haquri tare da tabbatar mata da cewa zai kiyaye.

Rashida kuwa har gida ta isko dady da guntayen hawayenta tayi masa gdy bisa kyautar da yayiwa little, umma kuwa ba'a magana don haka ta tashi cikin dare tayita zuba masa addu'a bayan tayi masa godiya, gawata kulawa ta musamman da riritasa data qarayi tamakar qwai a faranti.

••• ••• •••
Acikin sati ukun da aka kwashe kuwa banda qara cikakken bincike akan bayanin dasu baffa suka basu uncle h babu abunda sukayi saboda maganar da yayan nasu yazo da ita cewa wai hayar mutanen da sukazo amatsayin iyayen little akayi, sunyi hakanne don qara tabbatar da zancensu baffa akan hukuncin da suka gama yanke shawarar d'auka akan yayan nasu, kafin sukai ga zartar da hakan kwatsam saiga wani Abba yakawowa batul akan shi zata aura nan da sati biyu kuma ba gudu ba ja da baya, wayyo ranar batul qaramin hauka kawaine batayi ba, tayiwa mahaifinta kuka tayi masa magiya kamar ranta zai fita amma yaqi saurararta, kwana d'aya da zancen aka kawo lefe set d'in akwati uku, duk inda ran su uncle h yake ya b'aci don gaba d'aya bai bid'esu ba shi kad'ai ke sha'aninsa.

Haka batul ta dinga kuka tare da isko su uncle h tana riqon qafafuwansu akan kada subari abbanta ya aura mata wanda bata so amma saboda b'acin rai akan abunda yayi masu suka kauda kai akanta, ganin yanda sukayi biris da ita yasa ta iske iyayenta mata tana roqonsu akan su dakatar da mahaifinta kada yayi mata auren dole nan ma suma suka qyaleta, matar uncle Hassan ce da bazata iya jurewa kukan nataba tana hawaye tariqo hannuntata nufi d'akin Abba da ita, yana zaune falo tayi sallama suka shiga lokacin yana waya har dasu qyaqyatawa da alama yanajin dad'in firar wanda suke waya dashi, yana gamawa ya d'ago kai yana kallon matar uncle hassan d'in da hawaye ke kwance a fuskarta yace.

"Lafiya hajia Naga kamar hawaye afuskarki? Meyake faruwa?"

Nuna batool data durqusar masa agabansa tayi had'e da cewa.

"Bakaga wud'annan hawayen na wannan yarinyar ba data kwashe kwanaki tana zubarwa akan abunda kanada ikon tsayar mata dasu tahanyar dakatar da qudurinka sai nawa?, Haba Yaya wannan wace irin zuciyace da kai da bata tausayawa abunda ta dad'e tana iqirarin tana so?, Naroqeka kayiwa ALLAH da girmansa ka amincewa yarinyar nan ta auri wanda take so don ALLAH yaya?"

"Shegen?, Marar asali."

"Kodai waye shi kabarta ta aura, ai ita zata zauna dashi bamu ba, sannan idan ma shegenne to meye laifinsa?, Iyayensa sune masu laifi kuma sune shegun bashi ba, katausaya mata kabata zab'inta."

Saida ya hard'e qafarsa d'aya akan d'aya sannan yace.

"Ni kuma nawa zab'in fa?."

"Ka haqura dashi mana, haba yaya don ALLAH kada karusa mata rayuwa."

Cikin b'acin rai yamiqe tare da katsawa matar uncle h tsawa yace.

"Ke wace da zakice nahaqura da zab'ina da nake ganin shine daidai akan 'yata, tuntuni ban rusa mata rayuwa ba sai yanzu da take ganin duk gatar da nayi mata bata yimata ba saboda tana butulu.?"

Cikin kuka batool ta had'a hannyenta had'e da cewa.

"Abba ba butulci bane nayi maka, abunda zuciyata kawai keso nake qoqarin fad'a maka kamar yanda abaya kafad'a mun cewa in sanar dakai dik wani abu aduniya da naji zuciyata naso zaka nemomin, Abba kayi mani duk wata gata aduniya da nake tunanin babu wani mahaifi da zai iya yiwa 'yarsa ita kuma ban rena hakan ba, ayau Ina sake roqonka a karo na ba adadi daka cikashe mani wannan gatar da kakeyimun tahanyar bani zab'ina, wlh Abba nagartaccen zab'i nayi maka, Nuraddeen d'an halak ne ba shege ba, yanada asali yanada tarbiya da duk wata nagartar mutuntaka, don ALLAH kada kahanani samunsa Abba domin bayan kai shi kad'aine ke iya bani irin kulawar daka bani, Ina sonsa Abba Ina son sa fiye da tunani, hanani shi zai iya dakatar da bugun zuciyata da kuma lumfashi na, Abba kaji tausayina ka aura mani shi ina matuqar qaunarsa sosai."

Taqarasa maganar tana kuka tare da d'ora kanta asaman qafafuwansa daga tsayen da yake, hanb'areta gefe yayi har saida kanta yabugi qarfen center table d'in dake tsakiyar falon yafashe da sauri matar uncle hassan tajuyar da kanta gefe had'e da runtse idanuwa tana fad'in.

"Shikenan, zaka iya kasheta ai 'yar kace kai kake da hasarar hakan," sannan tabar d'akin itama tana sharar qwalla.

Karo tayi da hajia mama ta d'auko abinci a try bakin qofar d'akin taja burki tana share hawayenta tace.
Chapter 118 · 0% Book details