Sashe 87
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
••• ••• •••
*FEDERAL NEUROPSYCHIATRIC HOSPITAL (KWARE) SOKOTO.* canne asibitin da Yaya hawwa ke jinya, duk wani qoqari da yakamata ayi wajen bata kulawa anyi amma abun sai sake hab'b'aka yakeyi, allurori, magunguna da gwaje-gwaje don gano matsalarta da kuma yimata maganinta kullum cikin yimata ita ake, baffa yakashi kud'i da baisan iya adadinsu ba amma babu wani sauyi ko cigaba da aka samu, kullum al'amarinta jiya iyau, kimanin shekara d'aya da watanni kenan yanzu.
Duk wanda yasan Yaya hawwa duniya ya kalleta ba lallene ya iya ganeta ba saboda yanda tabi talalace haukan dake saman kanta yafi hauka muni don hatta mahaukatan dake tare da ita sunfara tsoronta saboda tana cutar dasu, hakan yasa aka killace ta ita kad'ai batare da kowa ba, idan abun ya motsamata saidai jami'an lafiya suga tana lallaqe ailin da bango tamkar wata halintar daba mutum ba, sunaji suna gani zata dinga buga kanta ga jikin bango har sai yayi jini kuma duk wanda yaje cetonta in sunkai su goma suna fitowa da wata kamar tadaban daba tasu ba, kasancewar ma aikatan lafiya mutanene masu matuqar qoqari da kuma jajircewa wajen ganin sunyi yaqi da duk wata cuta dake damun marasa lafiyarsu batare da sun nuna gazawarsu ba yasa gaba d'aya likitocin suka zauna suka yanke shawarar had'a taron gaggawa na qarawa juna sani daga b'angaren mabanbanta likitoci kamarsu daga wasu asibitoci da sauran garuruwa akan wannan sabuwar cutar da Yaya hawwa ked'auke da ita wacce suke tunanin tana nema tafi qarfinsu don samun mafita mai d'auke da topic _HOW TO TREAT PATIENT WITH UNKNOWN NEUROSIS.._
Cikin qanqnen lokaci taron ya wakana, manyan likitoci daban daban sun tashi sunyi bayani kala kala akan wannan matsala tare da samun solution d'aya da suke tsammanin shine qarshen matsalar,
Haka kuma tundaga sokoto wani babban likitansu yaje kano don samun cikakken bayanai akan asalin yanda lalurar tasami yaya hawwa, da baffa Usman suka fara cinkaro kasancewar sun sanshi tunda sune suka kaita asibitin, duk wasu tambayoyi da suka yimasa qin amsa masu ko d'aya yayi har saida ya aika aka kira baffa, gefe suka keb'e dashi yayi masa bayanin abunda ya kawo likitan, d'ari bisa d'ari baffa yayi masu bayanin cewa cutace kawai da suka wayi gari suka ganta da ita, wacce bazasu iya cewa ga dalilin daya haifar mata da itaba, duk yanda likitan yakai qwarewa wajen ganin yasamu wani labari da zai iya basu haske aikai bisa tattaunawar da sukayi wajen taron qarawa juna sani cewa cutar nafaruwa ne tadalilin wasu kalolin halittu masu tsananin tsoratarwa dake bijirowa marar lafiya daga nan sai tasirin ya halbu ga qwaqwalwarsa tayanda zata riqa juyawa tana qara d'auko masa hoton abubuwan, daga nan kuma sai zuciya tafara aiki da sauri sauri saboda tsananin tsora sai kuma suriqa ganin duk wani abu da zai fuskantosu to cutar dasu zaiyi daga nan kuma sai tana tunzura jiki wajen baiwa kai kariya ko kuma neman kub'uta daga inda mutane suke zuwa wani wajen da suke ganin shine zai basu kariya idan sun kad'aita, duk hakan nafaruwane ta dalilin yawan mu'amalar da marar lafiya yayi da wajajen dake d'auke da abubuwan ban tsoro inda ba'afiya samun mutane awajen ba da kuma mu'amala da wani abun da kake tsoron zai iya cutar dakai alokaci d'aya ko rasa wani abun da kake so, amma baffa yaqi cewa komai akan haka, saboda yana kallon fallasa dalilin faruwar haka agareta amatsayin zubar da kimarsa da kuma ta d'ansa.
Haka likitan yaqari masu tambayoyin yagama amma bai samu wani haske akan wancan bayaninba balle sutabbatar da hakan, har zai tafi saiga baffa Ali shida matarsa sun dawo daga wani wajen da ako yaushe suke zuwa tare, tsabar gulma shida bawani shiri yake da 'yan uwan nasa ba amma saboda yaga babban mutum d'an birni tare dasu yanufi wajen.
"Assalamu alaikum, ahhh baqo akayi?"
Yafad'a yana kallon baffa Usman, eh, yabashi amsa ataqaice yana qoqarin jan hankalin likitan subar wajen, d'an matsowa baffa Ali yayi yana kallon likitan had'e da goge hannunsa ga rigarsa sannan yamiqa masa yana fad'in.
"Assalamu alaikum, sannu bawan ALLAH, yanzu ake tafe."
Kallonsa likitan yayi kafin yamaido kallonsa gasu baffa yan tambayarsu shima tare yake dasu saboda ganin yanda sukayi kama su ukun sosai, baffa ya d'aga masa kai, cike da qyanqyamin yanayin da yaganshi na qazanta likita yamiqa masa hannu suka gaisa yana washe baki donshi yazata wani alkhairi ne zasu samu shima ya lakata.
"Ok ko zan iya tambayarsa ko yanada wani bayani d'aya sani akai tunda tare kuke a gida d'aya?"
"A'a Dr iya bayanin da muka yimaka shikenan daga shi babu wani abun, Aliyu zaka iya wucewa."
Baffa Usman yafad'a yana tura baffa Ali cikin gidan, rigima suka soma yi baffa yariqe masa hannu.
"Barshi Usman, Aliyu zo kafad'i abunda kasani.
Cikin jin haushi baffa Ali yagyara rigarsa yana hararar baffa Usman, tambayarsa likita yashigayi akan matsalar Yaya hawwa ko akwai abunda yasani ai kuwa baffa yabud'e baki yanda kukasan indararo yanata zubawa likita bayani akan zuwan Yaya hawwa dajin qare kukanka har zuwa silar haukacewarta.
Sosai likitan yaji dad'i kuma yasamu amsar da suke buqata yayi sallama dasu yawuce, ahasale baffa Usman yayi kan baffa Ali yakai masa naushi yafad'i qasa bakinsa yafashe da jini, cikin b'acin rai yashiga nunasa da hannu da hannu yana fad'in.
"Anya wai kai mutun ne?, Wace irin zuciya gareka mai cike da son cutar da 'yan uwanka, wai kaima d'an uwane koko d'an wuta?..tir da halinka wlh kahi hasarar rayuwarka aliyu matuqar baka canza ba."
Wani naushin yasake kaimasa lokacin daya taso yana son fad'a masa magana yasake fad'uwa yabishi qasa zai dakai baffa yayi saurin riqe masa hannu, idanuwansa na zubar da qwalla yace.
"Don ALLAH Usman ka qyalesa, kada kabiyeshi duniya ta zagemu a matsayin munfito ciki d'aya muna wannan hasuma, meye laifinsa ga abunda yafad'a Usman?, Wannan shine sakamakon abunda yakamata yamayarwa da hawwa bisa tonawa da binnewar da sukayi atare, wataqil inhar yad'a labarin suke sonyi akan cutar dake damunta don mutane su kiyaye sai yazame mata kaffara tahanyar rage mata zunubanta, kuma tazamo silar d'aukar darasi ga duk wani mutum mai hali irin nata ko son aikata abunda tayi don gujewa gobensa, ka qyalesa zo mutafi."
Yafad'a tare da jan hannunsa sukabar wajen.
Tofar da yawu cike da jini baffa Ali yayi yashiga d'ura masu zagi kala kala yana fad'in daga yau babushi babu su.
haqiqa ba qananan kud'i asibitin suka kashe ba wajen ganin sun yaqi wannan lulura da suke ganin kamar wata sabuwar cutace kuma suke fatar asibitinsu tazamo tafarko wajen kauda ita kafin ta watsu ga duniya,
Nan take manyan kafafen yad'a labarai a qasar nan da kuma gidajen jaridu sukayi
dandazo a asibitin don samun tattaunawa da manya manya likitocin da suka jagoranci wannan shiri nakawo qarshen cutar da suka rad'awa suna _neurosis2020_ kan kace me tuni cikin qanqanen lokaci labarin lalurar haukar yaya hawwa yazaga ko ina ta kafafan yad'a labarai tahanyar fira da babban likitan asibitin yana wayarwa da mutane kai akan lalurar ana bayani ana nuno Yaya hawwa da irin yanayin da take ciki da wanda take shiga idan yamotsa, wasu idan sungani tabasu tausayi wasu kuma suyi ALLAH wadda da ita, wasu kuma subita da addu'a.
Nan take suka maida kud'ad'en da suka kashe har riba tabiyo baya, kuma Alhamdulillah bisa sabuwar kulawar da aka koma bata tamusamman sun fara ganin canji akan gwaje-gwaje da suka sake yimata daga baya duknda dai har yanzun akwai sauran rina akaba.
••• ••• •••
Su baba balarabe basu isa garin borno ba sai kusan qarfe d'aya na rana, baba balarabe yakira Dr yasanar dashi zancen isowarsu lokacin yana zaune sungama shiryawa shida Fatima suna fama da ita akan taje ta sako mayafinta suje ganin little Nuraddeen agidansu ammie amma taqi, sai da taga Dr yad'aga wayarsa yana fad'in.
"Na'am baba har kin iso, eh to kutsaya adaidai junction ganinan zuwa."
Waro idanuwa waje tayi had'e da cewa "laaa uncle wane baban?"
"Baba balarabe." Yafad'a in I don't care d'innan yana fad'in Fatima ta tashe suje don dama bai sanar da Rashida batun zuwansu ba su ammie kad'ai ya fad'awa.
"Aunty dama zasu zo shine baku fad'an ba.?"
"Eh to, aiba wajenki zasu zoba shiyasa ma ba'anan zasu sauka ba, gidansu ammie zamu saukesu tunda yarona sukazo dubawa kuma kinga ke kince baki zuwa shiyasa ban fad'a maki ba."
"Amma dai zasu zo ko?"
"Ina, Ina kibar wannan zancen kawai, idan kina son ganinsu kizo mutafi idan kuma bakya so to kizauna warki anan, mu muntafi"
Dr yafad'a yana gumtse dariyar shi had'e da ficewa Fatima nabiye dashi abaya.
Ganin hakan yasa taje ta d'auko mayafinta ta lullub'a tana turo baki itama tabi bayansu.
Suna kawowa titi yayi parking da motar yace Fatima tajesu sutafi shi zai hau mashin yaje yazo dasu baba balarabe.
Cike da kunya Rashida tashiga gidan tana wani nonnoce kai qasa Fatima sai dariya take yimata har suka isa,
Kuda suka shiga part d'in ammie tana kitchen suna girki ita da umma, Kai tsaye Fatima taja hannunta suka wuce bedroom d'in ammie saboda warin girkin da taji yabugar mata hanci,
"Kai aunty meye bazamu tsaya a falo ba har sai munzo d'aki."
"Maman boy bana son qamshin abincin, mu zauna warmu anan bari nakirata awaya." tafad'a tana ciro wayarta cikin jikka.
"Hello ammie mun iso gamu a bedroom d'inki?"
"Ok Ina zuwa." Tabata amsa, tana shigowa sukayi ido biyu da Rashida databi yanda d'akin yatsaru da kallo, da sauri ta jid'ar da kanta qasa tana wasa da 'yan yatsun hannunta.
"A'a 'yata kice yau bikon maman Nuraddeen kika yomana, koda yake nasan badon mijina tazo ba don taga iyayenta ne ko Rashida." Ammie tafad'a tana dariya.
Saukowa daga zaunen da suke kan doguwar kujerar dake cikin d'akin sukayi had'e da duqawa har qasa suka gaisheta tadafa kansu tana fad'in.
"Lafiya qlw 'ya'yan albarka, kutashi ku zauna ALLAH yayi maku albarka." Itama ta zauna bakin gado.
"Agaisheki Rashida sarkin fulanin duk duniya, wato haka kika yiwa maigidana sai yau don kinji su gwaggonki zasuzo ko?"
Murmushi kawai Rashida tayi batare data tanka ba har lokacin kanta naduqe aqasa.
"To ai shikenan kin kyauta, ALLAH yarabaki da wahala, 'yatah ya jikin naki da sauqi ko?"