← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 160

Sashe 148

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannayensa yasa ya goge fuskarsa da idanuwansa da suka soma kumbura sukayi jawur saboda kukan da yayi sannan ya fuskanci 'yan jaridar yana kallonsu d'aya bayan d'aya, yanda yake kallonsu yasa sai duk sukaji jikinsu yayi sanyi suka nonnoce kai qasa, babu wata tambayar daya rage suyi masa don gaba d'aya sun samu amsoshinsu abakin qanen mahaifinsa, izuwa yanzu suna ganin yakamata su dakata da wannan bibiyar da suke yimasa har zuwa wani lokaci idan buqatar hakan tasamu don ayanayin da suke kallonsa duk rashin imanin mutum dole zai tausaya masa, kusan mintuna biyar suka kwashe babu wanda yace uffan shi kuma bai ce komai ba domin ayanzu yanada qwarin guiwar da zai iya amsa dukkanin tambayoyinsu, can cikin qarfin hali wani d'an jarida yace.

"Ranka ya dad'e ko me zakace ga abunda yafaru da kai ta sanadiyar qanen mahaifinka daya cutar dakai tahanyar yin asiri ya rabaka da qasarka iyayenka, da kuma iyalinka kamar yanda yafad'a.?"

Cikin zafin rai Dr Nuraddeen ya d'agawa d'an jaridar yatsa had'e da cewa.

"Kuskurene yin hakan agareka domin shi d'in mahaifina ne, don haka kada kaui yunqurin shigahurumin da ba nakaba, kada kayi qoqarin fad'in kalmar b'atanci akansa domin shi d'in babban mutum ne kaji nafad'a maka.."

Yana rufe baki wani ya sake kad'o wata tambaya kamar hakan.

"To Amma ranka ya dad'e baka ganin hakan da kayi kamar kabud'e qofar da wani na nesa ko kusa zai iya sake qoqarin cutar dakai ganin yanda ka kasa d'aukar mataki akan wanda ya cutar..."

Bai qarsa ba Dr Nuraddeen yace.

"Kaima ka kiyayi harshenka akansa, ko bakajin nafad'a masa cewa shid'in mutumne mai girma, ni awajena bayada sauran laifi, na yafesa ga duk abunda yayimun kuma nayarda da cewa kuskurene wanda ni da kai da Kai da kuma kai duk zamu iya aikatawa," yaqare maganar yana nuna kansa da wanda ya tambayesa farko da kuma shi wanda yake bawa amsa yanzu.

"To wane yanayi yanzu da kadawo qasarka kake jin kanka aciki yallab'ai?"

"Alhamdulillah!, Yanayine da bazan iya misaltasa ba saboda farinciki, amma duk da haka inajin damuwar wani sashen atare dani, wanda nake fatan had'uwa dashi nan kusa bada jimawa ba."

"Ranka yadad'e idan na fahimceka kamar kana magana akan iyalinka ne ko?"

"Qwarai kuwa amma bazance komai akansu ba domin bansan wane irin aiki qundin qaddara ya wanzu atsakanin ni dasu adaidai wannan lokacin, sai dai koma meye na tabbata cewa rouhi bazai rabu da gangar jiki ba kuma har asamu cigaban wanzuwar rayuwar."

"Wane irin qalu bale ka fuskanta ayayin da kake zaune awaccan qasar?"

"Babban qalu bale shine rashin rouhi a gangar jikina da kuma rayuwar kad'aicin abokanan da zasu tayani ingantacciyar rayuwa inba kayan aiki naba."

"Yallab'ai Inna fahimta kenan bakada iyali acan?"

"Taya zanyi iyalin bayan suna anan!?"

"To taya akayi kadawo hayyacinka har kabuqaci dawowa qasarka."

"Wannan daga ALLAH ne da kuma qarfin addu'ar iyaye da suka dage da yimun, duk da inada yaqini akan akwai wata addu'ar ta musamman dake tare dani tana bani kariya."

"Ya batun aikinka daka baro, shin zakaci gaba dayin sane aqasarka ko ka ajiyesa kenan!"

"Banida amsar wannan har sai yuyuwar hakan tasamu, Amma Ina so qasata ta sani nadawo da zimmar taimakon duk wanda ke buqatar taimakona a fannin abunda nakaranta."

"Wane sqao zaka miqa zuwa ga 'yan qasarka?."

"Su zamo masu yadda da qaddara aduk yanda ta riskesu, su zamo masu uzuri, yafiya da kuma kyautata zato ga wanda suke tunanin ya zaluncesu, qaddara abace da batada shamaki ga dukkanin mutumen dake da rayuwa, wani tazo masa da sauqi wani kuma tazo masa a akasin hakan, to aduk yanda tazo maka ka amsheta hannu biyu kuma kayi haquri, in Sha ALLAH zakaga qarshenta domin ita mai zuwa ce da kuma wucewa, arayuwa kuwa duk nisan abu to SANNU SANNU bazata hana zuwa ba..Kuma zaka riskesa da yardar ALLAH,"

Haka yayita sauraren tambayoyinsu daki daki yana amsawa har suka gama sannan yayi sallama dasu.

Nan suka nufi wajen baffa shima suka yi masa tambayoyi shida baffa Usman suka basu amsa fuskokinsu a sake Wanda hakan ke nuna irin tsantsar farincikin da suke ciki, sunso abarsu su gana da mahaifiyar Dr amma baffa yaqi amincewa da hakan, hakan yasa suka harhad'a inasu inasu suka fara tafiya bayan sun gama d'aukar hotunan wuraren da duk suke buqata da suka shafi Dr da kuma rayuwarsa batare dasu baffa sun hanasu ba.

A daidai lokacin da suke fita qauyen mashin ya ajiye little qofar gidan yana faman binsu da kallo sannan ya nufi cikin gidan, bakin zaure ya tsaya yana kwad'a sallama wanda hakan yasa Dr Nuraddeen dake zaune agaban Yaya hawwa ya rirriqeta yana kuka tana kuka saurin juyawa.

Baffa bai cemasa komai ba yafita d'akin yayi wurin little ita kuma Yaya hawwa sai faman kuka takeyi tana shashshafa fuskarsa tunda ba gani takeyi ba tana fad'in.

"Ina kashigene nura kabarni?, Meyasa zaka gujeni bayan kasan yanda nake tsananin sonka?, kayi haquri nura kayafeni, na tubarwa ALLAH nayi nadamar laifina, kayafe mani kada ka koma tafiya kaji nura, bazan sake ba kaga nariga da nazo gazgara don ALLAH kabari karufeni da kanka idan na mutu."

"Haba innarmu bazaki mutu yanzu ba kidena fad'ar hakan, ba guduwa nayi ba, ba fushi nake dake ba domin banida wannan zarrar da zanyi fushi da mahaifiyata da nake matuqar qauna, sharrain shed'anin mutum dana miyagun aljani ya nesantani daku, amma yanzu nadawo agareku nahar abada in sha ALLAH innar mu, iyaye ai ba'a fushi dasu."

"Shine katafi kabarni kullum cikin kiran sunanka amma baka amsa ba balle kazo." Taqarasa maganar tar da fad'awa jikinsa tana cigaba da kukan, rungumeta yayi sosai yana fad'in.

"Kiyi haquri innarmu, bazan sake ba."

"Ka tabbata bazaka sake tafiya ka barni ba?."

"Eh innarmu bazan tafi nabarki ba har abada."

"To Ina kabaro Rashida, itama fushi take dani ko, ka kirata naroqeta tayafemun kafin namutu da haqqinta, duk da idanuwana basa gani amma ina so nasake had'uwa da ita naroqeta ko zata yafemun abubuwan dana aikata mata."

Gabansa ne yayi wani irin mugun fad'uwa jin abunda ta ambata saboda tsoran kar ace dai ana nufin ba'aga Rashidarsa bane!, A daidai lokacin little ya shigo d'akin shikuma da gudu saboda albishir d'in dasu baffa suka yimasa cewa mahaifinsa ya dawo, wani irin burki yaja abakin qofar d'akin ganin mutum zaune tsakar d'aki rungume da Yaya hawwa, tafiya ya dingayi tamkar wanda qwai ya fashewa acikin ciki har ya iso cikin d'akin ya duqa ya tab'o Dr Nuraddeen don dama yaba qofa baya ne, juyowa Dr yayi da nufin ganin kowaye Wanda hakan yasa little ja da baya da sauri har yana shirin fad'uwa ganin mutumen da suka rabu dashi d'azu bada dad'ewa ba.

Shima qoqarin cire Yaya hawwa yafarayi ajikinsa yana kallon little amma sai tafashe da kuka tan fad'in.

"Karka tafi kabarni nuraaaa." Taqarasa maganar cikin irin yanayin da kai da kaji kasan muryar tsofaffin dake cike da tsoron faruwar wani abune akansu, cike da rud'ewa gaban little ya fad'i sai kuma yaji baffa Usman dake shigowa shi dasu baffa ya dafosa yayi saurin zabura had'e da juyawa, qarasa turosa baffa Usman yayi acikin d'akin cikin rawar murya little yace

"Tsa..tsaya, tsaya baffa, nakasa fahimtar wani abu anan, shin waye wannan mutumen da tun jiya a borno yake bibiyata? kuma Ina mahaifin nawa da kukace ya dawo?"

"Natsu mana Abu sumayya, wannan da kake gani shine mahaifinka, shine babanka Nuraddeen yau yadawo qasar nan."

Wata irin razana little yayi tare da Isa gaban Dr Nuraddeen da tsananin kunya tasa shi duqar da kansa qasa yana hawaye.

Hannu yasa ya d'ago fuskarsa had'e da furta cewa.

"Mai gida kaine mahaifina?,"

Dr da bayada zarra da kuzarin da zai iya kallon qwayar idanuwan little ya amsa masa cewa shi d'inne saboda yanda suka had'u har kusan so ukku Amma yakasa tabbatar masa da cewa shine mahaifinsa sai yanzu ya d'ago kai yana kallonsa yace.

"Bazan iya amsa wannan tambayar ba domin bancika duk wasu sharud'd'a d'aya kamata mahaifi yacika ga d'ansa ba, baici in amsa wannan suna agareka ba b'acin nakasa amsar kulawa da rayuwarka tunda kazo duniya, bansan da wane ido zan kalleka ba ince nine babanka, bansan da wud'anne idanuwa zan kalleka nace Kai d'ana bane don ALLAH kayafeni."

Ya qarasa maganar yana had'a hannayensa waje d'aya, wani kuka Yaya hawwa ta fashe dashi jin hawayen Dr dake rungume da ita ajiki na zuba mata a fuska tana fad'in.

"Wayyoo.. ALLAH wayene yasa d'ana kuka, don ALLAH kada kub'ata masa rai yagudu ya barni."

Dafata little yayi yana fad'in,

"Kaka taya kike tunanin zan b'ata ran mahaifina Dana dad'e Ina mararin gani?, Na dad'e Ina mafarkin had'uwata dashi kafin nakoma ga mahaliccina?, Na dad'e Ina tanada soyayyar da nake yimasa araina har zuwa lokacin da zai dawo agaremu?, Ko kad'an bazanyi hakan ba kaka domin Ina matuqar qishin son ganinsa."

"Waye kai Kuma.?" Tafad'a tana qoqarin lalubo fuskarsa, riqo hannunta yayi ya d'ora akan fuskarsa yace.

"Nine jikanki kaka, d'a awajen gwaggona Rashida Kuma jinin d'anki dake gabanki."

"Wayyo ALLAH na kada kuyau dareni don bana gani, jikana kuma?, Ina kabaro mahaifiyarka?, Ita bazata zoba fushi take dani?,"

"Ko kad'an kaka babu yaudara ni jikanki ne, kiyarda dani ko don ta hanyar muryar mahaifina dana d'auko."

"Nayarda amma shine kaima ba ka zuwa kana dubani?, Kayi haquri kada ka tsaneni sharrin shaid'an da zuciya sukasa na aikata abunda nayiwa mahaifiyarka, don ALLAH kace tayafeni nayi nadama"

"Taya na tsaneki kaka bayan ko yaushe nakanzo na dubaki, wannan kukan naki da kike yawanyi kina ambaton mahaifina shiyasa bazan iya yimaki magana ba don kada kid'auka shid'inne kukanki ya tsananta."

Cike da sha'awa da kuma burgewa Dr ke kallonsa, gaba d'aya sak d'abi'unsa basada banbanci dana mahaifiyarsa haka sautin muryarsa data dad'e tana yimasa yawo a qwaqwalwa don tunano mai irinta batada banbanci da tasa, Ashe shid'in d'ansa ne, jininsa ne shiyasa jikinsa ke bashi kamar yanada alaqa da habibtynsa ashe shid'in d'an sane, hannu little yasa ya rungumosu gaba d'aya shida Yaya hawwa da tabi ta naniqe ajikin mahaifinsa wasu hawayen farinciki nazubo masa yace.

"Alhamdulillahilazi bini'imatihi tatimmusswalihaat."
Shiru yabiyo bayan wasu mintuna kafin Dr Nuraddeen yace.

"Mahaifiyarka kuwa?, Anya kanaji zata iya yafemun?"

Da sauri baffa yace
Chapter 148 · 0% Book details