Sashe 83
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya tayi had'e da cewa. "A'a aunty barni in kalli wannan aljannar duniya, tunda nake ban tab'a shiga cikin irin wud'annan gidajen ba koda kuwa a mafarki ne saidai in hangosu a tv."
Hannunta Fatima taja tana d'auke da little sukabi bayan Dr nura daya wuce yana murmushi,
"ALLAH kidena wannan qauyancin, idan ba haka ba kuwa nida yarona bazamu sake fita tare dake ba kada ki kofsa mana ko little?." Taqarasa maganar tana dariya had'e da kallonsa.
Dariya yayi tamkar wanda yafahimci metake fad'a yana qoqarin zillewa ya sauka qasa ganin annufo part d'in ammie, dama haka yakeyi duk sanda sukazo yafiso a ajiyesa yashiga da qafafuwansa, haka kuwa akayi ta ajiyesa da gudu yanufi cikin falo tana fad'in.
"Little kadena gudufa?"
Ita kuwa Rashida dariyar gudun nasa tashigayi tana fad'in
"Wayyo ni ALLAH Rashida, wlh aunty yaronnan naki idan naganesa da daddare sai gudu, kingasa kuwa qurqur dashi sai kace d'an aljanu."
'Dago kai tayi tana kallonta had'e da harararta sannn tace.
"Mungode, wato nida Dr mune aljanun ko?, Bari mushiga ai zanfad'awa uncle d'in naki abunda kikace."
Hango ammie sukayi da tuni dr nura daya shiga yasanar da ita zuwan nasu tafito cikin shiga ta alfarma tad'auke little Nuraddeen da sai faman wangalar dariya yakeyi yana d'aga hannuwa.
"Wowwww...Masha Allah, oyoyo maigida, wannan wanka haka gaskiya nasayeshi, iyyeeeee yaron Abba kasha kyau tubarkallah yau nikam auren dakai nakeyi."
Shi kam banda dariya da gwarancin maganarsa da ba'a fahimta babu abunda yakeyi, d'ago kai ammie tayi lokacin da suka qaraso tana fad'in.
"Maraba da 'yata takaina, kice yau tafe kuke da manyan baqi, bisimillah sannunku da zuwa"
Tawuce gaba suna biye da ita har suka qaraso cikin falon,
Bayan sun zazzauna suka shiga russunawa suna gaisheta cikin girmamawa yayinda shi kuma Dr nura kecan gefe zaune riqe da remote yad'ora qafa d'aya akan d'aya yana kallon wani shiri a tv.
Gaba d'aya ammie ta manta dashi sai faman firarta takeyi dasu Fatima suna dariya kai kace ba surukarta ceba idan kaga yanda sukeyi, Rashida kawai ce bata wani saki jiki sosai ba,
"Rashida kisaki jikinki mana, kemafa 'ya na d'aukeki tamkar su Fatima, don haka kid'auka nan gidanku ne har zuwa lokacin da zama zaiyi halinsa tsakanin mu dake kinji ko, koda inafatar ko hakan tafaru zumunci bazai tsinke a tsakaninmu ba ko?"
"Insha ALLAH." Tabata amsa tana murmushi,
Ganin sukayi Dr Nura yataso yana kumbura fuska ya d'auki little dake jikin Rashida yana faman jaye mata mayafi da alama nono yake son sha.
"A'a son Ina zakaje kake qoqarin d'aukar Nuraddeen" don ita haka take kiran little, acewarta wai qara ariqa kiransa da cikakken sunansa yafi akan litte d'in.
"To ammie fita zamuyi tunda yau gaba d'aya kin manta dani ta 'ya'yanki kawai kikeyi."
"Ikon ALLAH, shine kake kumbura fuska haka?"
"Eh mana, Nima ai da umma nan nasan zata kulani dani tunda kin shareni.?"
"To da batanan fa?"
"Nazama so lonely, waima Ina take ne? Yafad'a yana duba gefe gefen kitchen.
"Aw sai yanzu kake tambayarta?, Ina tunda kashigo baka nemeta ba kuma kasan inhar dai tananan bazata barka haka ba idan kazo ko?"
"Wlh shirincan ya d'aukemun hankali, ina tajene ammie?"
"Babu inda taje, zazzab'i ke damunta yau shiyasa baka ganeta ba, Amma dai da sauqi don ban jima dabaro wajenta ba"
"Ya Salam! ALLAH yasawaqe, Bari muje nida maigidanta mudubota."
"To ai shikenan ka kyauta kuwa, kagaisheta idan kunje."
'Daukar little daketa faman rigimar shan nono Rashida tayi kamar bata fahimta ba yayi suka fice, Fatima tad'an harareta sannan tamaida kallonta ga ammie tace
"Kingata ko ammie?, Yaro nason yasha nono tahanasa shida kayansa, sai kace jiqawa zatayi tasha, ALLAH haka takeyi masa ko agida tayi kamar bata san rigimar me yakeyi ba."
"A'a Rashida kidena yimasa haka, yaro fane sosai ina watansa goma akace ko?"
"Eh." Tafad'a a kunyace.
"Haba ai har yanzu yana buqatar ruwan nonon ajikinsa don sunada matuqar tasiri wajen basa garkuwa ga lafiyar jikinsa data qwaqwalwarsa, kidena ganin wannan girman d'an jikin da wayau da ALLAH yayi masa tunda bai shekara ba kina bashi nono isashshe yana sha kinji ko?."
"Ai zakiga wasu yaran da wata tara har sun iya tafiya ga kuma d'an banzar wayo atattare dasu amma sukai har kusan shekaru biyu iyayensu na basu nono batare dasun damuba balle shi dake da wata goma da 'yan satukka akai."
Dr nura kuwa d'auke da litte yanufi sashensu umma yayi sallama a bakin qofar shiga d'akin baba dake ciki ya amsa masa tare da bashi izinin shigowa, koda ya shiga kwance ya iskota lullub'e kanta na bud'e ya gaisheta tare da yimata ya jiki, shi kuwa little wajen baba yanufa ya d'aukesa yan dariya.
"Kai babban mutum wannan gayun dai bazai burge amaryar kaba tunda kwance take tana fama da zazzab'i, abunda kawai za'ayi kabani kayannan naka sai in lallab'a maka ita ta tashi kugaisa." Baba yafad'a d'auke dashi yan gyara masa zaman hular kansa shi kuma sai hannuwa yake turawa cikin babbar rigar yana wasa da ita."
Dariya yaba baba yace.
"A gaisheka alhajin baka jeba, kodai alkhairi zakamun intaro hannu."
Hatta umma dake kwance saida suka bata dariya, batasan meyasa yaron ke matuqar shiga ranta ba, ita dai har ga ALLAH jitake tana yimasa wani irin so nadaban, tana wannan tunanin taji ya hayikke jikinta yana qoqarin leqo fuskarta, shi kuma Dr nura suka fita tare da baba suna gaisawa yana tambyar mike damunta.
Zaune umma ta tashi ta jawosa ajiki tana kallonsa, haka kurum taji tafashe da kuka wanda bako shakka kukan tunawa da 'yarta data hango kamarsa da itane, shin taya wannan yaron ya zamo jinin alhaji bayan jikinta da kamanninsa nafad'a mata akwai alaqa mai qarfi tsakaninsa da ita, wannan shine tmbayar da tashiga yiwa kanta tanaci gaba da kuka.
Acan waje kuwa kud'd'i Dr yaba baba yace yaje yakai umma asibiti adubata saboda bai kamata ta zauna da zazzab'in ba tunda ba'asan meke damunta ba.
Godiya yayi masa sosai sannan yakoma cikin d'akin ya d'auko little daya isko lafe ajikinta yana kallo yanda take kuka.
Bayan Dr nura yawuce ya taimaka mata tashirya yana yimata fad'an tacire damuwa aranta kar azo ace itace keneman yimata barazana a lafiyar jiki sannan suka wuce asibitin.
Basubar gidan ba sai bayan isha'i ammie tarakkosu har part d'in hajia nafeesa don su gaisheda dady tunda a part d'inta yake.
Dr nura yafara shiga kafin su ammie da Fatima su shigo suma yana zaune shida hajia nafeesa da yaranta suna kallon wa'azin shaikh Ahmad tijjani Yusuf a tashar Sunnah tv, dama matuqar yana part d'inta to tashar ake kalla gaba d'aya saboda tarbiyar yaransa, idan kuwa baya part d'in basuda aiki sai kallon tashoshin waqe waqe da cartoon,
Sallama d'auke abakunansu suka shiga aka amsa masu.
Yaranta ko gaisuwa Babu suka mimmiqe zasu shiga d'akunansu dady ya katsa masu tsawa.
"You stupid, bakuga mutane bane zaku shige baku gaishesu ba? Maza kudawo kugaisheshu." Yafad'a ransa a b'ace, kumbure fuska hajia nafeesa tashigayi tana binsu da harara har yaran suka duqa suka gaishesu suka tafi,
Ita dai ammie naganin haka tagaida dady tare da d'aga wayarta da ake kira tafita don bazata juri walaqanci ba ko kad'an,
Gaisheta dr. dasu Fatima sukayi ta amsa ciki ciki tana wani hurar hanta, Dr ya d'auke kansa daga kallon da yake yimata zuwa ga mahaifinsa yace.
"Am dama dady Rashida ce tazo gaisheku, kullum tana son tazo ALLAH bai yarda ba sai yau."
"Af ikon ALLAH, maman little Nuraddeen kuke kiransa ko wa?"
"Eh baffa."
"ALLAH sarki, sannu kinji Rashida, ayita addu'a ana jurewa kowace irin jarabawa in sha ALLAH komi zai zama tarihi."
"Hajia nafeesa kinga maman wannan yaron da kike tambaya kwanaki kina ganin Dr nashigowa tare dashi."
"Au sannunki, ai nazata wlh agidan reno suka d'aukosa har ina cewa ALLAH dai yasa ba shege bane."
Da sauri Dr suka d'ago kai su duka suna kallonta kafin dady ya girgiza kai cike da takaici yace.
"Nafeesa kenan, to bahaka bane, da uwarsa..." Kafin yaqarasa yaji tace
"Ai to baza'a gane hakan ba tunda ba'asan kowaye uban sa ba, Ina tsintar uwarsa akayi ko?."
Bata qarasa ba ya katsa mata tsawa had'e da cewa ta tashi tabashi waje.
Bayan tatafi dady yayita ba Rashida haquri kamar zaiyi kuka ita kuma tanuna ko ajikinta tunda tasan yanada ubansa, kawai dai dole zataji ba dad'ine ko kad'an, Fatima kuwa harda hawaye tana ganin da ace tana haihuwa baza'a tab'a jifarsu da zuwa gidan reno d'auko d'a, juyowa yayi gareta yaci gaba da cewa. "Fatima kada kibari kalaman auntynku suyi tasiri azuciyarki, ALLAH shi yake badawa bai manta daku ba in sha ALLAH jikina nafad'amun rabonku na kusa kusa domin akoda yaushe bamu cire qauna ga rahamar ALLAH ba, don haka kuyi haquri, kuyi haquri kunji ko?"
K'wafa Dr yayi tare da miqewa yafita ransa ab'ace, dama shiyasa tun farko baya shiga sha'aninta ko kad'an saboda gujewa irin wud'annan matsalolin, dama albarkacin mahaifinsa takeci amma daga yau tagama.
Sallamar Fatima yayi yarage daga shi sai ita da kuma little sannan yakira hajia nafeesar tafito daga d'aki, nuna mata kujera yayi ta zauna tana wani shashshan magani yace.
"Nafeesa kinsan ALLAH."
"Eh" ta amsa masa ciki ciki.
"Wlh idan baki ba yarinyar nan haquri ba bisa abunda kika jefeta dashi narantse da ALLAH abakin aurenki kenan!" Da sauri Rashida tad'ago kai had'e da cewa.
"A'a dady wlh babu komai nahaqura, ni batama yimun laifi ba idan ma tayi naya..."
Bata qarasa ba sanadiyar juyowar da yayi fuskarsa a d'aure ya d'aga mata hannu da sauri tayi gum takama bakinta.
"Zaki iya zab'an duk abunda yayi maki arai, amma hukuncin da nayanke yana nan babu ja da baya,"
Har zai miqewa yafita yaji muryar hajia nafeesa tace.
"Kiyi haquri." Ciki ciki tana Mai jin wata iriyar tsanar Rashida da d'anta aranta.
"Jeki Rashida, ALLAH yayi maki albarka." Yafad'a tare da ciro kud'i da batasan ko nawa bane yamiqawa little a hannu.
Bayan tafita yakalli hajia nafeesa yace. "Kiguji duniya nafeesa da qyalqyalin dake cikinta, wannan rayuwar da kika d'auka bamai b'ullewa dake zuwa ga kyakkyawan qarshe bace shiyasa nake qoqarin aduk lokacin da kika tozarta wani agabana innuna maki kuskurenki saboda ko meye yazo maki da sauqi."
"Amma alhaji.."