← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 160

Sashe 130

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Malan balarabe kayafeni bisa maganganun dana fad'a maka cewa, yayana da d'an uwana Usman sun zauna acikin gari suna zaginku akan cewa sunyi nadamar had'a zuria'a daku saboda sanadiyar auren 'yarku yarusa mana farincikin gida da kuma ahali, ba gaskiya nafad'a ba da nace maka sunce Nuraddeen ya tafiyarsa wajen karatunsa batare daya sanar daku ba saboda zaku iya sa akamashi arufe da sunan shiya halakar maku da 'ya, ba gaskiya nafad'a maka ba da nace maka yayana yace bada son ransa ya bari 'yarku ta auri d'ansa ba don dama bai yarda da tarbiyarta ba don ance ita dakanta ke bud'e baki tana iqirarin cewa aure take so kuma qiyi mata wai lallai sai tayi karatu, shine data fara bin maza kuka rufesu da d'ansu yace yana sonta kuka aura mashi ita, shine data gano cikin dake jikinta ba nasa bane tagudu tabar gari, gashi yanzu tasaka shi cikin baqin cikin da dole suka qarfafa masa ya tafiyarsa, sannan tajawo matarsa tasamu damuwa da tab'in hankali saboda qazafin da akayi mata nacewa ita ta halakar da yarinyarku, har nake fad'a maka cewa aranar suka wuce asibitin sokoto da ita sunata ALLAH ya isar had'a jini daku, wlh balarabe duk wud'annan maganganun dana fad'a maka ba gaskiya bane, qagaggiyar qaryace na shirya don cimma wani burin nawa sai gashi sanadiyar hakan najawo matsaloli da dama arayuwar mutane, don ALLAH da girmansa kayi haquri kayafemun wataqil nasamu rangwame acikin hukuncin da ALLAH ya tanadar mun, na nayi kuskuren d'aukar mata a matsayin abokanan shawarata, nayi nadamar cutar da 'yan uwana da nayi dama ku kanku don ALLAH kuyafeni."

Shiru duk sukayi kowane yarasa abun cewa sai faman jinjina kawunansu sukeyi saboda giraman kalaman da sukaji nafitowa daga bakinsa, Banda kallonsa yana faman sheshshekar kuka tamkar wani qaramin yaro babu abunda sukeyi, tabbas ko ba'a fad'aba kasan rayukansu sun b'aci musamman baffa Usman, duk da kallo d'aya idan kayiwa baffa Ali zaka iya tabbatar da cewa daga kalamansa har zuwa yanayin fuskarsa yayi nadamar abunda ya aikata daga qasan zuciyarsa, jiki a sanyaye baba balarabe da tuni ya dad'e da gano qarya daya fad'a masa wanda har yasashi nadamar abunda yayiwa su baffa ya nemesu gafara, ajiyar zuciya yayi had'e da cewa.

"Wannan shi ake kira da ranar nadama da kuma dana sani, haqiqa baka kyautawa 'yan uwanka ba ka zaluncesu da yawa sannan kasa nima nacutar dasu tahanyar d'aukar hukuncin da bai kamata ba, nazamo silar raba zukatan daya kamata ace rouhinsu da gangar jikinsu nawaje d'aya awannna lokacin, saidai hakan yafaru duk bisa shiryowar ubangiji, ni tuni nayi nadamar abunda nayiwa 'yan uwanka don nagane ba gaskiya kafad'a mani ba kuma na nemi yafuwarsu duk da ban fad'a masu dalilina na aikata hakan ba saboda gudun lalacewar zumunci tsakaninku, sannan d'an uwa da d'an uwa dama sai ALLAH idan akayi qoqarin shiga tsakani kunya akeji, nasan komai daren dad'ewa matuqar muna raye sai wannan gaskiyar tafito kuma sai ALLAH ya bayyanata, don haka tunda yanzu kafad'i komai da bakinka inma kanada laifi awajena nayafe maka, saura naka kanemi yafiyar d'an uwanka domin shine mafi qololuwar cutarwa acikin wannan al-amarin, ubangiji ALLAH karabamu da biyewa zukatanmu da kuma aikin dana sani."

Yana gama fad'ar hakan yayi saurin juyawa yafice don gaba d'aya ji yake yau komai ya dawo masa sabo, da ace bai yarda da maganar daya fad'a masa ba aranar da yanzu Rashida da yaronta basu fuskanci baqin cikin da suka shiga cikiba akwanakin baya, wataqil da tuni Nuraddeen yadawo zuwa garesu, da yanzu d'an uwansa daya rasa ta dalilin hakan yana raye duk da dai mutuwa ita batada fashi.

Sallama mijin Yaya Maryam shima yayi masu sannan yabi bayansa cike da ta'ajabin hali irin na baffa Ali.

Kallonsa baffa Usman yayi cikin b'acin rai yace.

"Yanzu hakan da kayi daidai ne?, Kayi farinciki ka lalata sunnar annabi?, Kayi farinciki kasaka mu cikin damuwa? Kai kuma gakanan acikin farinciki madawwami ko?, tir wlh albasa batayo halin ruwa ba, iyayenmu kaf babu mai baqar zuciya irin taka, wace ribace zakaci don ka hana asanar damu dawowar Rashida alokacin daya kamata dahar tasa ka tafka mana irin wannan qaryar! Wlh Yaya duk abunda malan balarabe yayi sai yanzu nafahimci bayada laifi kuma wallahi da nine shi sai na aikata fiye da abunda yayi saboda banga yanda za'ayi wannan qaryar takasa samun gurbi azukatan da aka gama cutarwa ba tunda gabakin jininmu shaqiqinmu da muke tare waje d'aya dashi akajita, to mezaisa akasa yarda da ita tunda ba mutum yayi kanshi ba, bashi keda ikon zuciyarsa ba balle yahanata b'aci akan wannan baqar qarya wacce batada tushe balle mafari, Kai kam..."

"Ya isa haka Usman, kada ka la'ancesa mana, kome zai faru yariga daya faru ALLAH ya shiryesa, yayi hakanne cike da tunanin zai d'auki fansar qarar dana kaisu ga hukuma ne aka kullesu, indai yarage wannan zafin da rad'ad'i azuciyarsa ai shikenan Bakomai, ni nayafe masa Ina roqon nima ALLAH ya yafemun daku baki d'ai, ka qyalesa kada kasaka mashi wata damuwar bayan wannan lalurar da yake ciki don ALLAH"

Wani irin takaici baffa Usman yaji aransa, Wai shi wane irin mutunne daya fiye sanyin hali haka, babu ta yanda za'ayi a qure haqurinsa har ya nuna b'acin ransa sai inta b'aci sosai, fiii yayi yabar wajen don baima san abunda zaice masa ba.

Baffa kuwa dake jin wani qunci aransa binsa yayi da kallo har ya fice yayi murmushi had'e da cewa.

"ALLAH yakyauta yasa mufi qarfin zukatanmu."

Hannuw baffa Ali yasake had'awa waje d'aya hawaye kwance a fuskarsa zai sake roqonsa gafara yayi saurin riqewa yana fad'in.

"Karka tashi hankalinka, nace nayafe maka duniya da lahira, bawai don banji zafin abunda kayi mani bane a'a, kawainayi hakanne saboda kwad'ayin nima ALLAH ya yafemun don mukam yanzu gangara kad'ai ya rage mana mu ida tare da fatan cikawa da Imani, saidai ina roqonka daka kasance mai iya sarrafa zuciyarka akoda yaushe bawai ita ta sarrafaka ba kaji ko Aliyu.?"

"Zan kiyaye haka Yaya in Sha ALLAH."

Murmushi baffa yayi tare da riqe hannunsa ya gyara masa kwanciyarsa sannan yace.

"Bari naje wajen d'an uwanka indawo kafin likita yazo muji ko zamu samu sallama cikin satin nan."

Yana gama fad'ar haka yafice aransa yana addu'ar ALLAH yasa shiriyar daya dad'e yana nemawa d'an uwan nasa ce tazo kuma yaqara had'e kawunansu waje d'aya.

••• ••• •••
A 'bangaren mahaifin batool kuwa gaba d'aya ya hana ko sunanta yaji an ambata a gidan, gashidai yanajin kewarta atattare dashi Amma baqar zuciya tahanasa fahimtar cewa itad'in wani b'angarece arayuwarsa dake da matuqar muhimmanci atattare dashi, tun yana keb'e kansa daga mutane izuwan duk fushine yakeyi har yagaji ya bari, su uncle h kuwa girman da suke basa ada sai sake lunkashi sukayi awajensa, ko kad'an sunqi nuna masa sun damu da fushin da yakeyi dasu da kuma shashsharesu har shima yagaij ya sauko don kansa ammafa har lokacin yaqi bada damar da za'a iya tunkararsa da zancen batool ko kad'an, sau da dama takan kira lambar wayarsa yaqi d'agawa ko kuma takira tasu uncle idan suna waje d'aya ya fahimci da ita ake wayar sai yatashi yabar wajen, hakama hajiya mama itama idan tana tare dashi yaji ankirata kuma takira sunan batool zaice ta tashi tafice masa daga d'aki ko tabar wajen daon baya buqatar jin koda sautin muryar tane, ganin yanda fushin nasa ya tsananta yasa gaba d'aya duk abunda ya shafi batool ba'ayinsa idan yana kusa saboda azauna lafiya, kuma hakan yasa yafara dawowa da yanayinsa nada duk da shi kad'ai yasan irin wahalar da yakesha aqoqarinsa na ganin cewa lallai lallai sai ya manta da ita arayuwarsa.

Batool kuwa kullum addu'arta ALLAH kajuyo mata da hankalin abbanta ya manta da abunda yafaru don wani zubin damuwar har hanata bacci takeyi tayita kuka sai little yata faman lallashi ko yakira hajia mama yafad'a mata tayi mata nasiha tare da kwantar mata da hankali tukuna sannan yasamu takwanta har tayi bacci.

Baya ga wannan batada wata damuwa aduniya saboda tana samun kulawa sosai awajen mijinta da kuma ahalinsa, wata irin soyayya Rashida keyimata tamkar ta mayar da ita cikin ciki, duk abunda zai b'ata mata rai Rashida taja kunnen little daya nisancesa ko don halaccin data yimasa arayuwa, tana matuqar jin batool aranta da har wani lokaci take tunanin idan har ahaka akejin sarakanai ma'ana 'ya'yan d'anka arai meyasa ita tata uwar mijin bata so taba? Meyasa tanuna mata tsanar da ko kishiyarka bai kamata ka nuna mata ba don taga ummanta bata tab'a nuna cewa tatsani hajia nafeesa ba duk da irin cin kashin kare da aibatawar da take yimata ita da jininta.

Batool tazama 'yar gata, ba awajen mijinta kad'ai ba hatta su Dr da dady suna kulawa da ita sosai ba'a batun umma data d'auketa tamkar little jikanta, duk abunda ta yayo duniya ita dai akaiwa batool, ammie ma na iya qoqarinta don duk abunda zata yiwa matar faruq to saita had'a da batool da kuma imaan matar Shakur d'and'an hajiya nafeesa.
Chapter 130 · 0% Book details