← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 160

Sashe 13

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashida kuwa tuni cikinta yad'uri ruwa ganin mahaifinta a makarantar, atunaninta yazone saboda abunda yafaru jiya, tsoronta d'aya kada yauma idan takoma gida ya doketa idan malan idi yafad'a masa sauran abunda tace, jikinta har rawa yakeyi atashi taje wajen malan Idris taji abunda yakawo mahaifinta don gaba d'aya ta manta da zancen da tayi dashi da safe akan yazab'a mata duk mijin da yaga dama kuma tunaninta bai kawo mata baba zai iya nema mata malan Idris ba, ana tashi tanufi office d'insa har suna cin karo dashi yana qoqarin rufe office d'in batare data damu ba cikin turo idanuwan dake nuna tsoro qarara a fuskarta tace "don ALLAH malan meya kawo baba makarantar nan!? Wlh inajin tsoron kar ace ka koma cemasa wani abun akaina ya sake dukana, ko ranar da kaje gidanmu saida yazaneni sosai da tsintsiyar shara" qura mata idanuwa yayi yana kallon yanda bakinta ke motsawa da yanda idanuwanta suka firfito saboda tsoro, ji yayi kamar ma bai tab'a ganinta ba sai yau saboda yanda yanayin tsoron nata ya bada wani fasionable atattare da ita, yanda take game hannu tana tambayarsa yasa jikkar hannunta fad'uwa da sauri ya duqa zai d'auko mata itama alokacin taduqo sukayi karo da juna,

"Yi hak'uri malan." tafad'a had'e da d'aukar jikkar ta rataya akafad'a, girgiza kai yayi kamar wani soko sannan yafara tafiya yana murmushi had'e dajin wani abu akanta, da gudu ta cimmasa tace, "malan baka fad'amun kome mahaifina yazoyi anan ba."

"Kashi yace abaki." Shine amsar daya Bata atakaice yanaci gaba da tafiyarsa, tsaye tayi kamar andasata awurin kafin tasake rugawa ta cimmasa, "malan, malan kashi fa kace!, to ni menayi kuma.?"

"Saboda bakyason karatu."

"Amma ai d'azu shiyace ya amince tunda aure nakeso zai yimun!" Tsaye malan yayi zuciyarsa nabugawar da baisan dalilinsa ba kafin yajuyo yana kallonta had'e da cewa, "waza'a aura makine?" gyara jikkarta tayi had'e da ware hannuwanta tana fad'in, "Ban sani ba, da akwai wani Rabe dake sona amma baba yace beyi masa ba, don haka shizai zab'ani miji da kansa" ajiyar zuciya ya sauke had'e da cigaba da tafiya tana biye dashi agefensa yaci gaba da cewa "Kuma ke kin amince?"

"Eh, ni nace ya zab'amun duk wanda take so"

"Kuma duk wanda aka zab'a makin zaki yarda ki auresa?."

"Eh mana zan yarda tunda ni nace na amince."

"Ko waye shi?."

"Eh, kowaye shi"

"Koda ace nine? zaki yarda"

"Eh, zanyarda man.." Bata ida fad'aba tayi saurin rufe baki tare da zaro idanuwanta tana kallonsa jin abunda yafad'a, juyowa yayi shima yana kallon cikin idanuwanta d'aya bayan d'aya sannan jinjina mata kai tare da sakar mata murmushi yace "ina sonki! Zaki aureni!" Yaqarasa maganar yana dariya tare da barin wajen batare daya jira jin amsar da zata bashi ba yana jin wani shauqi da kuma farinciki atattare dashi,

Ita kuwa Rashida gaban tane yayi mugun fad'uwa tare da sakin jikkar dake sagale a kafad'arta tafad'i k'asa, kallonsa takeyi har ya qurewa ganinta kalmar Ina sonki d'aya fad'a nayi mata yawo a k'wak'walwa, tafi mintuna biyar awajen tsaye kafin tad'auki jikkarta tanufi hanyar gida jikinta kamar wacce aka zarewa lakka,

A ranar yini tayi data motsa fuskarsa take tunanowa da kalamansa tayita murmushi, ganinta cikin wannan yanayin yasa umma ta sake tsorata da al-amarinta, don atunaninta tsabar farincikin amincewar da mahaifinta yayine akan zaiyi mata auren kesata wannan nishad'in, d'azu garin kallonta har k'walewa tayi ajikin bangon qofar shiga d'aki,

Haka ab'angarensa daya rufe idanuwa babu abunda yake gani sai yanda bakinta ke motsawa da idanuwanta, ahankali yakejin sonta nashiga acikin zuciyarsa da kuma sauran sassan jikinsa,

Rashida kyakkyawar yarinya ce irin black beauty d'innan, tanada tsayi sosai don takusa kaimasa a kafad'a, tanada manyan idanuwa da zarazaran gashin ido hancinta bayada wani tsayi sosai amma saboda ramin idanuwa da take dashi zaka d'auka dogon hanci ne da ita hakama bakinta d'an madaidaicine ciccif fuskarta, bai tab'a lura da hakan ba sai yau daya qura mata idanuwa,

Daga shi har ita matsuwa sukayi weekend taqare saboda mararin son ganin juna sai dai ab'an garenta takan shiga damuwa idan tatuna da cewa tariga da taba mahaifinta damar zab'a mata mijin da zata aura, gashi ba zato ba tsammani malaminta ya dasa mata soyayyarsa azuciyarta, duk wani motsi da zatayi tsananin sonsa ke sake shiga ranta, kuma ayanda tasan halinsa tunda har tafurta da bakinta kuma ya tambayeta ta amince da duk zab'in da zaimata to bata isa yanzu taje masa da wani sauyin magana ba,

Shikam malan idris safiya na wayewa ranar asabar ya isko mahaifinsa ya sanar dashi komai ba tare daya b'oye masa ba akan aminin nashi da suka had'u da kuma zancen 'yarsa d'aya gani yana so wacce ayanzu yake da nufin aurarwa, sosai mahaifinsa yaji dad'i kuma yayi murna ya tabbatar masa da cewa idan ALLAH yabashi lafiya nan da sati mai zuwa zaije suyi zancen ko yatura qannensa suyo masa maganar, anan yake sanar dashi cewa ai yasan halin aminin nasa yanada matuqar kirki amma akwaisa da zuciya da kuma kafiya, shiru malan idris yayi tuna yanda suka fara kwashewa dashi shekaran jiya wanda yatabbatar zuciyace tasa yayi hakan, nisawa yayi kafin yace

"To baffa don ALLAH kayi masa magana dawuri saboda ko yaushe zai iya bada aurenta ga wani, gashi kuma kace yacika kafiya da yawa" dariya baffa yayi tare da bubbuga kafad'arsa yace

"To Nuraddeen, ka kwantar da hankalinka in Sha ALLAH bazan bari haka tafaru ba, bari idan sunzo gobe d'in sai nafara b'ulguta masa maganar sai muji me zaice kaji ko?." haka sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar ciwonsa har yake cemasa shi dai yaso ace cikin 'ya'yansa wani yayi karatun kiwon lafiya kodon taimakon gida da waje, gashi yanzu sai faman kashe kud'i akeyi akan matsalar ciwonsa kuma sunk'i fad'a masu gaskiyar abunda ke damunsa balle a tsammani waraka nan kusa ko kuma nesa.

Ranar lahadi misalin karfe sha biyu na rana, baba da wasu abokanan kasuwancinsa su uku da kuma qanensa da shima duk tare ake akasuwa suka kama hanyar bebeji don gano malan idi, basu kaiba sai misalin k'arfe biyu na rana saboda yanayin injinin motar da sukaje da ita Bata cika kyauba sai an lallab'a, qannen malan idi su biyune suka tarbesu tare da shigowa dasu cikin gida inda yake zaune saboda hatta qugunsa yasamu matsala be iya tafiya.

Sosai farincikin ganinsu ya bayyana a fuskarsa kamar yatashi sama don murna, haka suma saidai su nasu farincikin ya surku da tausayinsa ga yanda fuskokinsu suka nuna, saboda malan idi mutumne mai dad'in sha'ani da kuma hak'uri, kusan ma halin sane malan Idris ya gado, murmushi ya dinga yimasu yana fad'in "karku damu alhamdulillah Ina samun sauqi, muyiwa ALLAH godiya da yasa fuskokinmu suka sake had'uwa badon haka ba ai shikenan rabuwarmu kenan tun ranar."

Abinci aka kawo masu yasa malan Idris daya shigo gaishesu ya zuzzuba masu abincin, bayan sunci sun sai gashi yasake shigowa da gorunan lemu da ruwa yakawo masu hadda mahaifin nasa da qannensa, har zai fita baffa ya kallesa had'e da cewa,

"Dawo nan kazauna" yana nuna masa gefen da baba take zaune, gaban sane yafad'i tare da sadda kai qasa sannan ya qaraso ciki ya zauna amma acan d'an nesa dasu, gyaran murya baffa yayi sannan yace....

_Tofah baffa zai fasa kwai agaban kowa🤣 Bari in gudu kafin kaina yayi girma saboda kunyar da zan tayasa ji😅 don son jin abunda baffa zai fad'a yau to inji ruwan comment idan ko ba haka ba kuda new update sai upper week😒_

*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU_*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___11💎

Gyaran murya baffa yayi yana kallonsu baba kafin yace,

"Malan bashar nasan kai kasan wannan" yana nuna d'an nasa sannan yaci gaba da cewa "don haka Babu buqatar in sake gabatar maka dashi saidai ko in wud'anna 'yan uwan nawa, amma ku su alhaji surajo, malan hashimu, sa'idu, malan shu'aibu da malan balarabe ga d'anku nan Nuraddeen wato d'an wajena koda ALLAH zaisa wata rana a had'u zaku iya ganesa shima yagane ku, wud'annan su biyun da kuke gani kuma qannena ne uwa d'aya uba d'aya wato Usman da aliyu, inafatar ko bana raye ace abota da kuma mutuncin dake tsakanina daku bai yanke ba, inaso ya zamana cewa idan anhad'u da juna za'a iya gaisa har kudinga tunowa dani kuna yimani addu'a"

"Ashsha malan idi! don ALLAH kadena fad'ar haka domin ita cuta ba mutuwa bace, mudai fatanmu d'aya shine ubangiji ALLAH yabaka lafiya kuma ALLAH yaraya manasu shi da sauran 'yan uwansa ya tashi kafad'unka acikin iyalinka." Haka suka dinga fad'a tare da yimasa addu'a,

Shiru baffa yayi yana kallonsu d'aya bayan d'aya nan take yaji wasu hawaye sun cika masa idanuwa, tari yafarayi wanda hakan yabawa hawayen dake maqale a idanuwansa damar zubowa, sannu duk suka dinga jero masa cikin jin k'warin guiwa ya kaikaita idanuwansu yana goge hawayen had'e da amsa masu,

Bayan tarin ya lafa masa ya maido kallonsa ga 'yan uwansa da kuma d'an nasa suma ya gabatar masu da aminan nasa inda har yak'ara masu da cewa shi awajensa abokan nasa sunfi qarfin yakirasu da abokanai ko aminai saidai yace sud'in 'yan uwan sane shaqiqai, don haka yana roqonsu dasu riqesu hannu biyu bisa kyautatawa da kuma girmamawa, gaba d'ayansu ji sukayi jikinsu yayi sanyi saboda yanayin yanda yake magana tamkar wanda ke barin wasiya, murmushi yayi ganin yanda fuskokinsu suka canxa had'e da cewa "kada kusaka kawunanku cikin damuwa akan maganganun dake fitowa abakina domin natabbata daga cikinsu akwai wud'anda zasu sanyaya zuciyoyinku kuma su sakaku cikin farinciki marar misaltuwa" juyowa yayi inda d'an nasa me zaune yace, "Nuraddeen tashi katafi, ALLAH yayi maka albarka" ajiyar zuciya malan Idris ya sauke had'e da mik'ewa tsaye yad'an sunkuyar dakai agabansu alamar girmamawa sannan yafice daga d'akin,
Chapter 13 · 0% Book details