Sashe 156
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannayenta tasa ta share fuskarta tana kallonsa cikin zafi da rad'ad'in qunar da zuciyarta keyi tunawa da kalaman da taji yayi ashekarun baya a cikin tv tace.
" _There is no place for forgiveness in this relationship, we've being separated for along time ago b'cos of so many embarrassed you couse to me and my son, always had issues but we held for too long, I do not have any more patience to be strong now, So i choose to breaking up with you peacefully, b'coz the love lost between us since!,_"
Tana gama fad'ar hakan tabar wajen batare data bari sun sake had'a idanuwa ba.
Kallo Dr yabita dashi bud'e da baki jin yanda take watso masa turanci tamkar ga bakinta aka halittosa, gaba d'aya ko kad'an kalamanta basu b'ata ransa ba, asalima farinciki yaji data bud'e baki tayi masa magana da harshen da baitab'a tsammani ba, wai matarsa Rashida, d'alibar nan tasa daya sani marar son karatu itace yau tsaye agabansa tana mayar masa da magana da kalaman dake nuna baqaramin gogewa tayi wajen karatuba kafin takai wannan matsayin da zata iya hakan, ji yayi kaso arba'in cikin damuwarsa ta ragu don ya tabbata da sannu zata haqura domin akwai banbanci tsakanin fushin mai cikakken ilimi da kuma marar ilimi matuqar zaiyi aiki dashi, murmushi yayi sannan yamiqe yafito ya samu har lokacin su Dr da little nanan waje zaunensu suna fira harda abbaty daya shigo lokacin.
Gaishesa yayi yana kallon fuskarsa sannan ya kalli ta little yana so yagano ko akwai kamanceceniyar tsakaninsu amma hakan ta cutara don shi little sak kamar mahaifiyarsa ce garesa d'an duhun fatar kad'aine ta mahaifinsa, maganar da abbaty yaji Dr Nuraddeen mahaifin little nayi da mahaifinsa yana yimasa sallama zai wuce ita tasa ya amince tabbas mahaifin nasa ne don batada banbanci data little d'insu.
Kasancewar yace nan zai kwana Amma hotel zaije ya kama kafin gobe yasa Dr da fatima suka roqesa daya kwana nan gidan amma fir yaqi amincewa, acewarsa zaifi wali acan fiye da nan don haka dole suka haqura, bayansa little yabi da zai tafi shima yace acan wajensa zai kwana abbaty nata yimasa dariya had'e da cewa.
"Yazama mayen babansa." Yace eh yadaiji,
Duk abunda akeyi Rashida na jikin window tana hangosu, sosai take kallon habibyn nata da bata samu ta kallesa da kyauba d'azun wanda little kad'aine ya hangota.
Ciro wayarsa yayi yana dariya yakirata da take tana hannunta ta d'aga batare data duba ba yace.
"Gwaggo ya kikaga habibynki?, Ki koma kadasu mama Fatima su hangoki, don babu mai rabaki dasu yau, nidai wajen baban zan kwana..."
"Marar kunyar yaro aje waya..."
Tafad'a tare da jayewa tasaki labulen,
Sosai little yasha mamaki da mahaifinsa ya fad'a masa yanda sukayi da mahaifiyarsa, murmushi yayi aransa yace lallai al_amarin Mata babba me, wato duk yanda suke son mutun sai sun ja masa aji idan yazo hannunsu, Ashe abun ma baga qanan mataba har da manya, azuci take maganar amma ashe bai sani ba tafito fili sai da yaji mahaifin nasa yajawosa ajiki had'e da laqqamosa tawuya yana dariya yace.
"Commoon my son, to meye laifin hakan, ai momynka ko makaranta taja ba aji ba ta cancanci tayi hakan, ko ka zata irin wannan a tsakaninkune kad'ai banda iyaye?."
Cikin jin kunya little ya shiga susar kai yana jin wata irin qunar mahaifin nasa aransa.
Kusan kwana Dr yayi yana kiranta taqi d'agawa, ya tura mata messages sunfi aqirga ba amsa, da safe ma sun koma shida little taqi saurarensa hakan yasa yakoma badon yanada ra'ayin hakan ba sai don ya fahimci tana buqatar lokaci kafin tahuce.
Saida akayi kusan sati ana abu guda da rarrashi Rashida taqi saukowa amma azuciyarta tuni tahaqura kawai tanayin hakan ne don tarama itama shikuwa da yariga da yasan laifin nasane sai bai damuba yaci gaba da bibiyarta,
A cikin satin ya sai wani qaton fili anan cikin bebeji aka aza masa gini part uku, kan kace me da yake ya riga daya tara kud'i nan take aka gama sashen d'aya tanadar masu shida Rashida da kuma mahaifiyarsa, shi kuma sauran akaci gaba da aiki ba dare ba rana wanda kusan little ne ke kula da komai.
A sati na biyune baaffa ya shirya da kansa shida baffa Usman suka fara zuwa gidan baba balarabe da Yaya Maryam suka roqi alfarmar da aba Rashida haquri tadawo mijinta tunda har yanzu aurensu nanan, sai alokacin baba balarabe da Yaya maryam suka san da shegantakar da Rashida keyi Wanda hakan ya matuqar basu mamaki, bayan kwana biyu suka sake shiryawa awannan karon kam booking little yasa aka yomasa na jirgi tafiyarsu da dawowarsu baffa da baba nusaiba sai Yaya balkisu da baffa Usman Wanda ahankali tuni rayuwarsu har tafara canzawa suka tafi borno wajen yamasa bikon Rashida, su kam su Dr abunma har dariya ya soma basu, musamman umma da ita kanta Rashidar wai biko tsofai tsofai da ita, a lokacinne ma su baffa suka samu damar had'uwa da Rashida da mahaifiyarta suka yimasu gaisuwar baffa tare da Basu haquri sosai kamar zasu yimasu sujada, umma da kunyar baffa takamata harda hawaye tayi na tausayin ganin yanda yakoma itama tabashi haquri, Basu koma ba saida dady yabasu tabbacin cewa in Sha ALLAH cikin satin ranar juma'a Rashida zata koma kenan idan ancire yau saura kwana hud'u, sunji dad'i sosai had'e dayin godiya sannan suka juya suka koma cike da farinciki azukatansu, musamman baffa da yakejin ko yanzu ALLAH yakarb'i rayuwarsa burinsa yagama cika aduniya.
Haba ana sanar da Dr Shire Shire suka koma sabbi yanda kukasan wanda za'a kaiwa sabiwar amarya, dama tuni ankammala duka ginin apart d'in uku har anyi fentin, part ne guda biyu plat sai d'ayan part d'in shi kuma hawa biyu wanda shine inda Dr Nuraddeen ya tanadarwa mahaifins, d'ayan plat part d'in kuma nashine, d'aya kuma na baffa Usman da baffa Ali, Amma duka an zagayesu waje d'aya anfitar masu da gate d'aya.
Hakama akwai wani qaton fili daya saya acan g.r.a dake cikin kano yasa ayi masa tsarin ginin gida biyu kowane sama da qasa, shima duka aka zagayesa amma gate d'in kowane gida aciki daban, wanda yayisu ne shi d'aya little d'aya Amma ba'a qarasa ginin ba ana kan yine.
Tuni dady yasa akazo aka zubawa Rashida kaya naji na fad'a a part d'insu ko ina Saida aka cike d'akunan tsaf da kaya masu kyau da tsada wanda tuni Dr Nuraddeen yayi niyar hakan Amma dady yace kawai yayi saving d'in kud'insa ga wasu matsalolin, Rashida kuwa abunma dariya yake Bata yanda taga anata Shire Shire sai kace za'ayi bukin amare ne, d'aukar abun takeyi tamkar wata almara don gaba d'aya ta kasa gasgata hakan wai itace yau zata koma gidan mijinta bayan wasu shekaru, wannan abu da ban mamaki tafad'a aranta duk da kuwa tuni suka daidaita da habibyn nata kullum suna maqale awaya kai ka rantse irin soyayyar nan ce ta samarin yanzu da 'yanmata, bata gasgata ba sai ana gobe zata tare, ranar kam tayi kuka sosai, haka ummanta, ba'a maganar Fatima da gaba d'aya kusan zazab'i soma kamata yayi amma babu yanda suka iya tunda dolene, roqon Dr Rashida tayi daya taimaketa yabata zainab 'yar autarsa lokacin tanada shekara goma sha 17, ko kad'an bazai iya hanata don haka yayi Mata alqawarin zai kaimata ita da kansa har gida idan lokacin yuyuwar hakan tayi Amma bada yanzu ba, Dole tahaqura tayita yimasu godiya tare da addu'ar ALLAH yabar zumunci tsakani.
Ticket d'in Jirgi d'aya Dr Nuraddeen yayi ooking ga duk wanda ke sha'awar zuwa rakiyar Rashida tun daga zuwa har dawowa don akwai gagarumar walima ta musamman da gwamna yasa aka shirya masa ranar asabar saboda rashin samun halartar ta ranar daya dawo da beyi ba, wanda hakan yayi masa dad'i yaroqi amaida masa da ita ta ganaral da kowa zai iya halarta don tayasa murnar reunion d'insa da iyalinsa, Kuma agidan gwamnati za'ayi,
Don haka gaba d'aya dady da familynsa kwai da kwarkwata manya suka hallara wajen rakiyar Rashida,
Koda suka Isa sun tarar da kayan sawa tun daga sutura mayafai takalmi man shafa, turarukka da sarqoqi masu tsada Dr Nuraddeen ya cika Mata wardrobe dasu, duk inda ka duba da akwai abunda kejere agefen.
Kowa sai murna da farinciki yakeyi tare da yimata barka da arziqi.
Batool kuwa tanajin zancen batun dawowar Rashida tabuga tsalle bazata koma ba sai angama.
Kasancewar su baffa baffa tuni suka tare tun kwana biyu da suka wuce yasa ba'a wani sha wahalar nemawa mutanen borno wajen kwana ba, wasu suka tsaya nan wasu kuma sukayi gidansu batool,
Dady da Dr da sauran maza mazan da aka zo dasu kuma suka tafiyarsu yarimawa gidan baba balarabe, umma kuma tatafi wajen 'yar uwarta aunty marwiyya, little ma tafiyarsa yayi wajen Batool d'insa don akwai d'aki na musamman da aka tanadar masu shida ita acan gidan don ya dad'e da zama d'an gida tuntuni.
Rashida kuwa aka barta ita kad'ai a part d'inta Babu Wanda ya tsaya har zuwa dare da Dr yadawo.
Saida yafara zuwa wajen mahaifiyarsa dake can pay din sama ita kad'ai sai wani d'aki dake gefe wanda anan ne aka saukar dasu zainab da hussaina da Fatima wato familyn Dr, qasa kuma nan baffa da baba nusaiba suke, gaishesu yayi tare da basu abunda ya siyo masu, Yaya hawwa ma ga baki yabata har taqoshi sannan yayi masu Saida safe yawuce part d'insa inda ya tarar da Rashida kitchen tana qoqarin dafa indomie don tasoma jin yunwa gashi dare yamiqa babusa ba labarinsa.
Tsaye yayi bakin qofar yana binta da kallo kafin yace.
"Ikon ALLAH, ni habibyn habibty yau wace irin amarya ce aka kawomun haka da zan tsinta a tsakiyar kicin."
Saida tayi dariya sannan yace.
"Amaryar da angonta ya shekara ashirin da tara batare daya sanyata a idanuwansa ba har ta tsofe, don haka metake dashi da zata tanadar masa balle har yasa ran zai iskota ad'aki Kuma a tsakiyar gado lullub'e kamar sauran amaren?."
_Gaisuwa ta musamman agareki sister *SALIHA MUSA* alkhairin ALLAH yakaimaki aduk inda kike, Ina godiya da yanda kike bibiyar littafinnan hakan yasa naga dacewar nayi maki kyautar wannan page sukutum, ngd sosai Allah yabaki aljannah da rahamarsa_👏