← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 160

Sashe 158

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

••• ••• •••
Da safe bayan sun gama karyawa suka shirya tare suka nufi part d'insu baffa, kai tsaye sama Dr Nuraddeen yanufa wajen mahaifinsa ita kuma ta tsaya nan qasa wajen baba nusaiba suna gaisawa, bayan sun gama gaisawa takira mata baffa da alokacin yafito wanka shima yagama shiryawa tsaf suka gaisa, wata irin kunyarsa ce tarufe Rashida don sai ayanzu take ganin rashin kyautawarta na waiwayarsa duk da irin tarin soyayya da qaunar daya nuna mata, daya fahimci hakan yayi murmushi tare da yimata nasiha akan ta manta da komai bawa bai Isa yakaucewa duk wani tsari da ALLAH yayi masa ba arayuwa, nan ya shiga qwalawa yaransa kira duk da kuwa kowace tagirma abunta don karatu sukeyi sosai batare da baffa yadamu da girmansu ko ganin cewa su yara bane, Rashida ma tuni ta kammala jami'a yanzu haka tana wajen sarvice, wanda sosai gwaggo Rashida taji dad'in takwarar da baffa yayi mata kuma taqara tabbatar da qaunarsa agareta, haka ma mai sunan mahaifinta auta bashar (Abba) da take kira da aminina da Rashida taganesa harda qwalla tayi jin sunan mahaifinta ya saka mashi, shima dai masha ALLAH ya girma don yanzu matakin farko take na junior secondary School, sun d'an jima ana fira kafin baba nusaiba tace tazo suje can sama wajen Yaya hawwa.

Gabanta ne yafad'i tayi saurin yin ta'awizi had'e da bin bayanta har suka isa d'akin Dr Nuraddeen na zaune yana bata ruwa abaki yana yimata firar Rashida.

"'yar halak, kingata nan tashigo innarmu, nazata ma jira takeyi sai nakoma qasa nad'auko maki ita,"

Yaqare maganar yana matsa yatsun qafar Rashida dake kusa dashi, ita dai ko kulashi batayi ba saboda yanda taga Yaya hawwa takoma, tsananin tsufan da tayi yasa ta tamuqe waje d'aya tamkar irin qananan yarannan, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata tana Mai qara jin tsoron ALLAH yarufeta, tabbas mutum ba komai bane arayu kuma idan ka d'au duniya da zafi akwai ranar da zata qonaka da kanka, in Kuma kana kallon kanka wata tsiya da SANNU SANNU duniya zata nuna maka kai ba kowa bane.

Gaisawar da taji baba nusaiba nayi da Dr Nuraddeen yasa tadawo hayyacinta daga tashin hankalin da tashiga, cikin tausayawa ta duqa kusa da Yaya hawwa tana gaisheta, juye juye yaya hawwa ta shigayi tanabin sautin Rashida ta yanda zata iya ganinta amma inaaaa, babu ganin idanuwan balle taganeta.

Cikin kuka da muryar nadama tashiga roqon Rashida gafara tana mai nuna mata irin halin da tashiga duk saboda haqqinta data d'auka, don ALLAH tayafe mata.

Cikin kuka Rashida tace.

"Inna nayafe maki duniya da lahira, Ina roqon kema kiyafemun abubuwan dana aikata maki da sune suka jagoranci zuciyarki wajen aikata abunda yafaru."

"A'a ni bakimun komai ba, son zuciya kad'aine yasa nayi maki haka, gashi ALLAH ya nuna mani ikonsa aqoqarina naganin cewa sai kin rabu da d'ana ni anrabani dashi na tsawon shekaru, idan ma wani abunne kamar yanda baki moresa ba haka nima ALLAH yahanani moriyarsa alokacin da nake matuqar buqatarsa, shi ubangiji ba'ayi masa dubara kuma ba'a isa a Hana wanzuwar ikonsa ba a yanda yaso, gashi ALLAH yaqara had'aku a qarqashin inuwar da nayi qoqarin tunb'ukeki a qarqashinta, ni kuma an shafe mani idanuwan da zasu iya gano mani abunda yahaifar mani da shiga cikin wannan halin awancan lokacin."

Sun jima suna Abu d'aya har dai kowanensu ya yafi juna, Wanda sai alokacin taji mutuwar Inna ruqayya, tayi kuka sosai kuma tayafe mata tare da roqa mata gafarar ubangiji sannan suka baro wajenta.

'Bangaren baffa Usman tanufa ita da yarinyar baba nusaiba shi kuma ya tsaya wajen baffa su gaisa, acan ta tarar da baffa Ali aka gaggaisa shima ta tausaya masa halin da taganesa aciki sosai ya kuma roqeta gafarar abunda yayi mata tare da roqawa matarsa kuma duk ta yafe masu tana kuka, ji take aranta da gaba d'aya Bata kyauta ba da tun farko batacewa ubangiji tayafesu ba har haqqinta da na sauran mutane ya illata rayukkansu haka, koba komai tasan matuqar tayafe nata zasu samu sassaucin hukuntawa ko kad'an ne.

Tana zaune dasu Inna Bilkisu saiga muneera ta shigo, dashe baki tayi cikin farincikin ganin Rashida tana fad'in.

"Ahhh, kaga uwargidan kuma amaryar Yaya nura ashe rai kanga rai?"

Rashida na murmushi tace.

"ALLAH yanufa hajia muneera kece haka.!"

Muneera tawashe baki tare da Bata hannu suka tafe, saida suka gaisa sosai sannan Rashida tashiga yimata gaisuwar rashin mahaifiyarta Inna ruqayya itama tayi mata ta baba kowanens cike alhinin rashin mahaifan nasu, daga nan kuma fira ta canza tsakaninsu kai kace wasu aminan junane har muneera taqara roqon Rashida akan ta yafewa mahaifiyarta.

Ana haka Dr Nuraddeen ya shigo, muneera na ganinsa ta d'auke kai cike da kunya, saida suka gama gaggaisawa dasu baffa da Inna Bilkisu sannan ya kaikaita idanuwansu had'e da juyowa yana kallon Rashida ya kashe mata ido d'aya tayi saurin kauda kai gefe, dariya yayi sannan yakalli muneera data sunkuye kai qasa yace.

"Aunty muneera badai har kin shigo ba?, Ina kika baro mijin naki kika tahowarki."

"Yana wajen sauran matansa ya nura, yau nice aunty kuma?"

Tafad'a tana dariya,

"Eh mana, ai yanzu kin zama babbar aunty koba haka bane habibty."

Ita dai Rashida tsabar kunya miqewa tayi hade da yimasu sallama takoma part d'insu.

Kasancewar qarfe goma za'a gabatar da walimar da gwamna ya shiryawa Dr Nuraddeen yasa koda qarfe tara da rabi tayi har ancika gidan da wud'anda zasuje, tuni Dr Nuraddeen yasa aka d'auko wacce zata gyara masa Rashidarsa tafito kalar matar manya Wanda nan take kan kace me har anyi angama don dama matar qwararrace sosai, kallo daya zakayiwa Rashida ka d'auka itace matar gwamnan jahar gaba d'aya saboda yanda tayi kyau, ga sarqoqi masu kyau da matuqar d'aukar hankali da suka hau jikinta daidai tafito masha ALLAH abunta.

Qarfe goma da rabi aka fara gabatar da walimar wanda koda sha biyu da rabi tayi har angama, walima kam tayi kyau abun ba'a magana komai anyisa cikin tsari da tsaro saboda manya manyan mutanen da suka samu halartar wajen,

An karrama little da kambu kala biyu na farkon daga fannin sashen lafiya ne, na biyu kuma daga wajen gwamna, sannan kuma aka qaddamar dashi a matsayin kwamishinan lafiya na jahar don sun tattauna da gwamnan tun kafin yau yanuna bayada buqatarci gaba da aikin likitanci Amma zai bada gudun mawa ga dukkanin asibitotan dake buqatar taimakonsa wannan dalilinne yasa gwamna ya nad'asa matsayin kwamishinan a fannin lafiya ta jahar, Rashida itace wanda tayiwa Dr Nuraddeen jawabin godiya bisa wannan karramawar daya samu, Wanda mutane da dama taburgesu yanda sukaji tana speach agaban mutane cikin girmamawa.

Bayan an watsene Abba dasu uncle h suka sake bayyana agaban Dr Nuraddeen da matarsa Rashida suka tayasu murna, nan dai Abba ya sake daurewa suka roqi yafiyar juna da Rashida akan abunda yafaru abaya sannan suka wuce.

Kusan ranar yini su Dr sukayi suna karb'ar baquncin mutane masu zuwa tayasu murna da kuma barka da arziqi wanda saida Dr Nuraddeen yayi daqyar yasamu yaja iyalinsa suka bawa junansu kulawar daya kamata.

Da marece su Rashida na zaune dasu batool da yake itama agidan tawuni baffa yashigo shida baffa Usman bayan angaisa yaciro wasu kud'ad'e masu yawa a aljihunsa yamiqawa Rashida had'e da cewa.

"Wud'annan kud'ad'en da kike gani haqqinki ne halak malak gasu nan dubu d'ari hud'une da tamanin, bayan b'atanki da rashin dawowar mijinki mukaga kayan d'akinki na Shirin lalacewa nida Usman muka yanke shawarar saidasu mu jujjuya maki kafin ALLAH ya bayyanaki, a lokacin mun saida komai akan dubu d'ari biyu da saba'in, da muka juyasu ne suka zamo haka, sannan acan wancan gidan dana taso akwai gonar kaji da nake kiwo Ina saida su to gaba d'aya naki ne, sai wani d'an qaramin fili shima ga takardunsa duka haqqinkine,"

Yaqare maganar yana karb'ar takardun daga hannun baffa Usman yamiqa mata.

Shiru Rashida tayi tana kallon baffa, gaba d'aya Bata sanma wane irin mutunne shi da ALLAH ya halitta mai tsananin qana'a da kuma taka tsantsan, little ma sakin baki yayi yana kallon baffa, don bai tab'a fad'a masa wannan sirrinba, asalima yanada yaqinin Babu Wanda yasan da wannan sirrin idan bashi da d'an uwansa ba.

Tajima shiru kafin tahad'a kud'in da takardun ta sake mayarwa da baffa tace tabar masa su gaba d'aya duniya da lahira amma yabuga kai ga qasa yace bazai karb'a ba.

Dr Nuraddeen kam burgesa mahaifinsa yayi ya d'aga hannuwa sama yana roqa masa amincin ALLAH duniya da lahira tare da tsawon rai, tanaji tana gani baffa yaqi amsar komai sukayi tafiyarsu, acewarsa don ALLAH yayi don haka yafison ALLAHn yabiyasa da kansa.

Kiran umma tayi ta sanar da ita dasu baba balarabe, suma sun sha mamaki sosai don maganar gaskiya su har ga ALLAH sun ma manta da wasu zancen kayan d'akinta, kiransa sukayi suka roqesa akan yakarb'a tunda ita ta bashi Amma yace a'a yadai gode, ummace tayi saurin rantsewa akan to bazasu karb'i gonar kajin ba, don haka sun barmasa idan ma bayaso to shima yayi kyauta da ita.

Badon yaso hakan ba yace shikenan ya amince kuma yagode.

Godiyar da yazo yayiwa Rashida tasa Dr Nuraddeen da yaji yaquduri rushe wancan gidan na baffa ya zuba masa wasu kajin masu yawa kuma ya mayar masa dashi wajen kiwon kaji ya zuba masa wud'anda zasu dinga kula masa da wajen.

••• ••• •••
Da daddare su batool na zaune suna zancen ranar komawarta da little don ya dage akan dole gobe tabisu Dr da dady su koma saiga Abba ya shigo paloun don dama su kad'aine a zaune su hassana da hussaina suna can wajen gwaggo Rashida da sukaje zasu dawowa suka tsira rigima sai an barosu wajenta Dr Nuraddeen yace su qyalesu, dole suka haqura suka barosu,

Suna ganin Abba yashigo suka saki firar suka shiga d'auko wani sabon babi ana tayi haddashi yana dariya, SANNU SANNU falon yafara cika har dasu uncle da shurahbil da sauran matan gidan,

Cike da tsokana uncle Hussain ya shiga Basu labarin mafarkin Abba yana dariya tuno yanda ya rud'e ranar har yana cewa batool "ya kamata tad'an sakarwa sauran 'yan uwanta space a zuciyar abbanta don soyayyar da take yimata tayi yawa."
Chapter 158 · 0% Book details