← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 160

Sashe 138

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bai jira amsar da zai bashi ba yafara saran wajen yana, wasu irin sautukka ya soma ji kala kala Wanda azahirin gaskiya d'aya d'ago kai ya kalli d'an uwan nasa shi bayajin komai, hakan yasa yaqara cire tsoro aransa shima yayi kamar baiji komai ba, sannu ahankali yafara cin karo da wasu abubuwa masu kama da mutane aciki suna yimasa gizo a fuska cikin ramen wani irin hayaqi ya turnik'e wajen had'e da wari Mai mugun d'oyi, jiri ne yafara d'ibarsa amma cikin qarfin hali yaci gaba da tono wajen har yakai ga qullin maganin, ji yayi kansa ya wani sarawa duniyar najuya masa yafara karanto addu'o'in faya sani ga baki, wata irin dariya yaji ansaki mai qarar gaske had'e da amsar addu'ar da yakeyi anaci gaba da karantawa. "Muma musulmi ne kamarka, muna sallah muna addu'o'i don haka baza kaci galaba akanmu ba har sai ka amshi saka makonka daidai da laifinka, bazamu barku ba kamar yanda kuka nememu to tabbas sai alqawarin ALLAH ya tabbata akanku kamar yanda mummunar makomarsa zata tabbata akanmu." Yaji an fad'a cikin kunnuwansa tare da kecewa da wata irin muguwar dariya, kan yace wani abu yaga wata baqar mummunar halitta cikin sigar wani baqin hayaqi tana fitowa daga cikin ramen tare da nufatosa daga zaunen daya fad'i tun d'azu dafe da kansa, da sauri yasa hauyar dake hannunsa ya ida ciro maganin wanda kusan tare suka fito da wannan halittar ta lullub'esa sai dai baffa Usman dake gefe yaga iska Mai kamar guguwa tana nad'ed'e niya cikin jikin baffa Ali dako ganinsa bayayi sai dai muryarsa da yajiyo cikin wahalalliyar qara yana fad'in "Usman ka fiddo ashana ka qona wannan qullin maganin kuma kafasa tukunyar dake cikin ramin nan."

Cike da tsoro jikin baffa narawa yafiddo ashana dama sunzo da ita ya cinnawa maganin sannan yasa hauyar yaje cikin ramin ya faffasa tukunyar dake ciki bakinsa d'auke da addu'a yanayi yana kallon iskar data nad'id'iye baffa Ali, Yana gama fasa tukunyar yaga iskan yawani cure waje d'aya tare da duddun qulewa yayi can gefen daji yana gudu da qarfi shi kuma baffa Ali yashe awajen ko motsi bayayi wasu quraje duk sun feshikke masa tun daga fuska har zuwa tafin qafa, da sauri ya jefar da hauyar agefe ya qarasa wajensa jikinsa na rawa ya tallabosa yana jijjigarsa yana kiran sunansa amma ko yatsansa baya motsi, cikin qarar murya yace.

"Ataimakeni..."

Ko baki bai rufe ba sai ga mutane sun iso wajen, ganin yanayin da suke ciki yasama wasu shakku akan meya kawosu wajen, qilama wani abun zasuyi ALLAH ya mayar masu da abunsu don haka suka tafiyarsu, mutum biyu kad'aine suka tsaya suka riqowa baffa Usman baffa Ali aka tallabosa zuwa titi sannan suka tari napep aka sashi ciki baffa yayi masu sannan mai napep d'in yaja suka nufi asibiti dashi, tun kafin ya qarasa isa yakira baffa ya sanar dashi komai.

Baffa na tsaye gefen gado yayi saurin zaunawa saboda wani irin jiri da yaji ya d'ebesa.

Istigfari ya shigayi ALLAH yasa son kansa baisa asanadiyar rayuwa d'aya ba surasa har rayuka biyu, a wani gefe na zuciyarsa kuwa hamdala yayiwa ALLAH da akaci nasarar tono maganin yasan koba komai in Sha ALLAH d'ansa zai dawo hankalinsa kuma ya tuna dasu.

Kamar antsikaresa yayi saurin miqewa yabar gidan ya nufi asibitin da baffa yafad'a masa cewa can suka nufa.

Yana isa ana fitowa da baffa zuwa d'akin da zanyi jinya na 'bangaren maza wato (male medical ward) don har angama dubashi babu abunda ke damunsa, 'yar doguwar sumace kawai yayi sai qurajen da suka feshikke masa a jiki kuma Alhamdulillah ya farfad'o daga sumar har ansa masa drip bacci ya d'aukesa.

Zuba masa idanuwa sukayi suna kallo cike da tausayinsa, tabbas duk bawan da ALLAH keso yakan nufesa da tubamawa kura kuransa kuma yaqara masa da jarrabawa don tabbatar da imaninsa, fatansu d'aya shine ALLAH ya yafi kura kuransa albarkacin tubar da yayi kuma taubatan nasu da tasashi sadaukar da rayuwarsa don jadda tubarsa ga ubangijinsa.

Sudai likitoci sunyi masu bayanin babu wata matsala kuma in sha ALLAH kurajen dake jikinsa ma zasu b'ace saboda na infection ne acewarsu, amma kallo d'aya zakayi masa kasan yana jin zafin wud'annan quraje lura da yanda yake fitar da lumfashi.

A b'an garen inna ruqayya kuwa safiya na wayewa aka ganeta a sheme inda take kwana jikinta duk jini, ashe daren jiya 'yan iskan dake dakonta cikin tashar su kusan bakwai sunyo shaye shayensu suka farmata, saida suka qwace duk 'yan kud'ad'enta sannan d'aya bayan d'aya suka dinga amfani da ita ko tsufanta da qazantarta basaji, mutum d'ayane ya ganesu a tashar yana qoqarin fitowa sai gashi ya hango wata baqar mota qatuwa tayi parking wajen wanda ganin motar yasa samarin guduwa na qarshen dake kanta ma riqe da wandonsa yabar wajen, anfi mintuna uku kafin yaga wasu qatti su biyu sun fito cikin motar suna kallon gefe da gefensu, har bakin shigowa tashar da can gefen da samarin suka arta dana kare saida suka dibo suka tabbatar ba kowa sannan suka sunkuci Inna ruqayya dake kwance a sheme wajen sukasa cikin motar kamar yanda mutumen ke bayani, tsoro da fargabar abunda ke iya faruwa dashi tasa yakasa fitowa har motar tabar wajen, can gabanin asuba sai gashi yaga motar tadawo su sake fitowa da ita da sauri sun ajiyeta inda suka d'auketa farko, shine bayan sallar asuba gari yafara wayewa mutane suka ganeta a inda tasaba kwanci yashe jikinta duk jini, babban abunda yafi d'aga masu hankali shine, ancire mata ijiya d'aya sannan anfasa gefen cikinta da alama wani Abu aka cira daga ciki anka mayar anka d'unke don har filista akwai wajen, ga qasanta sai jini kefaman fita wanda basusan dalili ba, gaba d'aya ancire yatsunta na hannun hagu dana qafar dama amma duk da haka fata mutu ba lumfashi nafita ajikinta, hakan yasa nan take shugaban tashar nazuwa yayi gaggawar kiran 'yan sanda, ba'afi mintuna ashirin ba suka iso, yanda suka ganeta suma hankalinsu ya matuqar tashi, nan take yakira assibiti tunda da ranta bata mutu ba, tuni 'yan sanda suka zagaye wajen da wannan d'oruwan zare da suke sawa idan wani abu yafaru da suke rubutawa (don't across the line...) sukaci gaba da sauran bincike bincikensu kafin motar asibitin ta iso,

Mintuna shabiyar suma suka d'auka kafin su iso 'yan sandan suka basu damar isa wajen su d'auketa saboda subata taimakon gaggawa tunda da ranta bata mutu ba, amma kai kana kallonta ko ba'a fad'a maka ba kasan cikin azaba da bala'in rayuwa take, malaman asibitin na d'agota zanen dake rufe da jikinta daga qasa yafad'i, tsananin tashin hankalin abunda idanuwansu suka gane masu suda mutanen wajen yasasu sakinta, gaba d'aya abunda ya shafi al'aurarta daga qasa tsakankanin cinyoyinta anciresa wajen yayi jawur babu komai sai jan naman dake wajen, mutane kuwa ihu duk sukayi had'e daja da baya suna rufe bakinsa da qwalalo idanuwa, hatta 'yan sandan duk saida sukayi baya saboda firgita, abunda rayuwarsu Basu tab'a gani ba azahiri ko a finafinan hausa ko littafai sai gashi yau agabansu sun gani da idanuwansu, tabbas ko ba'a fad'a ba kasan wannan aikin masu sihirce sihircene da tsafi suka yayyanke mata sassan jiki,

Kan kace me tuni labari ya soma biye gari mutane sai rutatowa sukeyi cikin tashar don su tabbatarwa idanuwansu abunda sukaji ana fad'a, babu abunda yafi tsorata mutane irin yanda duk irin miyaku da cuwurwutar dake jikinta rad'ad'in baisa ta mutu ba, cikin qarfin hali da tausayawa d'aya daga cikin jami'an lafiyan da sukazo ta d'auki zanen ta nufi inda take da zimmar rufeta saiga wata irin guguwa daga sama tanad'o baqa qirin da ita ta turnuqe Inna ruqayya dake sheme wajen tana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya,

Banda qarar sautinta da kururuwa tana ihu babu abunda suke iya ji ko gani, wani irin ihu takeyi tana qarar da duk Mai sauraro zai tabbatar da cewa inba rahamar ALLAH ba babu abunda zaisa halittar dake fiddashi ta dace balle asa ran zata rayu, mutane kuwa duk wanda ka kalla yayi jugum yana kallon ikon ALLAH, wasu Kuma da qarfin hali suna vedioting ga wayoyinsu,

Saida aka kwashe fiye da mintuna goma wannan iskan na juyi da wani qugi akanta ita kuma tana qara sannan ya b'ace.

Koda likitocin suka dubata tuni rai yayi halinsa ta cika a bainar jama'a cikin wani mummunan hali tayi mummunar cikawa a idanuwan duniya bisa laifukka da zunubbai data aikata arayuwarta. _(wal iya zubillah, ALLAH kakaremu da mummunar cikawa kuma kasa sanya mu muyi kyakkyawar qarshe, dama haka rayuwa take, duk bawan dake aikata zunubi adoron qasa yaga ubangijinsa ya tona asirinsa to alamar yana qaunar sane sai ya hanzarta yin kyakkyawar tuba kafin lokaci yaqure masa, idan kuma kaga kanata sab'awa ALLAH ya qyaleka yana cigaba da baka nasara acikin alamurranka to kaiconka, wallahi talalace yayi maka, cikar wa'adi kawai yake jira yayi maka mummunar damqar da bazaka iya kuccewa ba, alokacin babu batun bud'ad'd'iyar qofar tuba agareka domin wuri ya qure maka, tabbatuwar alqawarin ALLAH akan kane kawai zai wanzu agareka, shikenan kazamo cikin tab'ab'b'u bayinsa kuma kayi asara, ya ALLAH ka aminta damu kabamu ikon tuba wa dukkanin laifukanmu da zunubbaban da muka aikata maka👏)_
Chapter 138 · 0% Book details