Sashe 142
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawaya kwance a fuskarsa wanda ganinsu ya matuqar tayarwa da 'yan uwan nasa da hankali ya sake d'agowa yana kallon ta had'e da cewa.
"Sosai ina jin tsoron gyarasa kar mafarkin da nayi yanzu ya tabbata.."
Kusan atare kafin ya rufe bakinsa su uncle h suka had'a baki wajen cewa.
"Mafarki!"
"Eh mafarki."
"Ikon ALLAH, to Yaya ai kai shi mafarki ba gaskiya bane, don haka bama tsammanin zai faru don ka gyara kuskuren daka aikata,"
"A'a hussain, sau da dama mafarkin bayan sallar asuba ance yana zama gaskiya, bana son wani abu yafaru da batool domin bako shakka itace rayuwata, nasan zakuyi mamakin hakan dana fad'a lura da yanda nawofantar da ita na tsawon shekaru saidai abunda baku sani ba shine, duk tsawon shekarunnan narayune bisa d'imbin tunaninta safe, rana da kuma dare, nayi nasarar cin galabar zuciyata wajen korarta gidannan duk da irin son da nake yimata amma nakasa yaqi da qwaqwalwata da kuma ruhina wajen dena tunaninta, adaren jiya mahaifiyarta taganar dani abunda nagagara ganewa balle har na saurari gaskiyar da kuka yita qoqarin ganar dani, nayi nadamar abunda nayiwa 'yata ta cikina kuma naquduri gyara laifina yau Amma kash nayi mafarkin daya girgizani kuma ya raunata zuciyata har nake tunanin bazan iya ba."
"Haba alhaji sai kace ba musulmi ba!, Kayi Imani da ALLAHnka kayi abunda ya kamata, kada kayi Imani da abunda kagani a mafarki, tun d'azu sai kambama al'amarin nan kakeyi kaqi ka sanar damu ko meye?" Uncle Hassan yafad'a cike da damuwa, juyawa hajia mama tayi don bata son yafad'i ko mafarkin meye don annabi yace idan anyi mafarki mai kyau babu laifi afad'a idan kuma akayi marar kyau to ayi shiru ayi sadaka sannan kada afad'awa kowa, gashi 'yan uwan nasa na neman ya bayyana masu mafarkin da yayi Wanda ta tabbatar ba ai kyau bane tunda har ya shiga cikin irin wannan yanayin, wasu hawaye taji sun zubo mata tayi saurin sharesu don kada su karya mata zuciya ta wuce d'akinta tafad'a toilet ta d'auro arwala sannan ta shimfid'a abun sallah ta fuskanci ubangijinta tare da roqon ALLAH ya sauqaqa duk abunda yayi nufin zai jarabcesu dashi kuma kada ya d'ora masu abunda bazasu iya ba ko zai kautar masu da Imani,
Shi kuwa Abba shiru yayi kafin ya d'ago kai ya kalli 'yan uwansa had'e da cewa.
_"Acikin baccina dana farka a yanzu cikin wannan yanayi nayi mafarkin batool ita da mijinta sun kamo hanya zasuzo nan kano suda yaransu 'yan biyun data haifa sunyi accident, mijin nata ya mutu ita kuma ankaita asibiti anyi mata tiyata anfidda mata wasu jariran 'yan biyu macce da namiji, babban tashin hankali ko data farko tasamu mental problem akanta sanadiyar buguwar da tayi, ankiramu bayan faruwar had'arin anbamu yaran nasu basuyi komai ba, Babu abunda ya samesu d'ayar kawaice ta yanke a gefen fuskarta, gaba d'aya na rud'e batool d'ina ta haukace acikin mafarkina, duk abunda nayi mata amma Bata yadda da kowa saini, hatta likitoci da mahaifiyarta dukansu takeyi, Babu wanda take ambata bakinta saini, Babu wanda take saurara saini, nikad'ai ke iya kusantarta Bata jimani ciwo ba, hakan yasa soyayyar da nake yimata naqi bari akula da ita yanda ya kamata a asibiti, da kaina na d'aukota na dawo da ita gida Ina kula da ita hatta yaran data haifa in bani na riqasuba nakais tabasu nono bata tab'a shayar dasu , ni daku munyi magani har angaji amma batool d'ina takasa dawowa hankalinta, ga mijinta ya mutu, ga qananan yaranta tabar mana da duk inda muka kallesu sai mun zubar da qwallan tausayinsu, gashi mahaifiyar mijinta ta kasa mantawa da abunda nayi mata wanda ku baku sani ba har tana kuka dani akan laifin dana aikata tare da tabbatar mani da kowaye ubansa, na matuqar girgiza daa mafarkina ya nuna mani mahaifin yaron dana tsana aduniya kuma nake shegan tasa duk da anfad'a mani shine mahaifinsa yazo a daidai lokacin da nake buqatar taimakon tawa yarinyar da zimmar taimakonmu ba tare dana san shine mahaifin mijin batool ba, inajin tsoro kar wannan mafarki ya zamo tamkar isharace akeyi mani da abunda zai faru da 'yata da kuma mijinta...."_
Haka yaci gaba da basu labarin mafarkinsa da yayi wanda tun a farkon littafi ya zamo shine shimfid'ar wannan labarin har yakai qarshe yana Mai fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, hatta su kansu saida sukaji jikinsu yayi sanyi don tabbas mafarkin nasa akwai ban tsoro da firgitarwa acikinsa, ganin yanda duk yabi ya sare yayi loosing hop d'insa yasasu qarfafa nasu zukatan ta hanyar rarrashinsa tare da maganganu masu dad'i da zasu kwantar masa da zuciya, suka nuna masa shi cewa mafarki fa ba gaskiya bane in sha ALLAH babu abunda zai faru, binsu yayi da kallo suka jinjina masa kai alamun tabbatar masa da abunda suka fad'a, don ya sake samun natsuwar zuciya uncle hassan yace uncle Hussain yakira masa shurahbil ya d'auko masa wayarsa d'aki, shiru yabiyo bayan na wasu mintuna sanadiyar wayar da uncle Hussain keyi sai ga shurahbil wanda shine d'an uncle Hassan na biyu yashigo sanye da doguwar rigarsa jalabiya riqe da wayar uncle Hassan da alama bacci ya tashi,
Yana shigowa gaban Abba ya sake fad'uwa don bazai mantaba haddashi yagani cikin mafarkin don shine ma yayita kula da yaran batool kuma sanadiyar yaranne ya had'u da mutumen da shine mahaifin mijin batool har yakawo masu shi a matsayin wanda zai taimaki rayuwar 'yarsa, har yaqaraso cikin d'akin ya gaishesu ya miqawa uncle Hassan wayarsa yafita idon Abba na akansa.
Bugu d'aya uncle Hassan yayiwa wayar batool tashiga tafara ruri, cikin jin dad'i batool dake zaune tana karyawa little ya kawo mata wayar ta d'aga had'e da cewa.
"Uncle h barka da safiya, antashi lafiya?"
"Lafiya klw batool d'in Abba, ya kike ya nauyi?"
Akunyace ta amsa da Alhamdulillah tana cigaba da cewa.
"Uncle ya abbana yake, yana dai lafiya ko?"
Kallon Abba yayi daya runtse idanuwa wasu zafafan hawaye na zubo masa jin shine mutum na farko da tafara tambaya kaf acikin ahalinsu wanda dama hakan yazame mata jiki aduk lokacin da tayi waya da d'aya daga cikin gidan shine take fara tambayar ya yake kafin kowa sannan yace.
"Lafiya klw abbanki yake batool, 'yan matayen namu suke?"
"Suna wajen gwaggo uncle, kowa dai lafiya ko?"
"Eh batool, ya maigidan naki?."
"Muna lafiya uncle, Wai yaushe Abbana zai yafemun nadawo areku uncle, Ina matuqar kewarsa da kuma 'yan uwana sosai, kuroqamun yafiyarsa uncle kunga awannan karon ma likitoci sunce bazan iya haihuwa da kaina ba, Ina tsoron kada nakoma ga ubangijina abbana nafushi Dani don Allah kuce ya yafemun." Taqare maganar tare dasa yatsa tagoge 'yan qwallan da suka zubo mata tana kallon little dake faman mammatsa mata qafafuwanta, tsananin tausayin da taba uncle hassan yasa bai tsaya yin komai ba ya mannawa Abba da tun d'azu sautin muryarta da yake saurare tasashi rufe idanuwa qwalla na zuba wayar akunne.
"Hello, uncle!." Data fad'a daidai lokacin da wayar ta sauka akunnensa ya sashi saurin bud'e idanuwansa had'e da cewa.
"He..he.hello Fatima!"
Wata irin zabura tayi had'e da miqewa tsaye lokaci d'aya wanda seda abun cikinta ya juya tayi saurin dafe mararta tana qoqarin kiran sunan mahaifinta don gasgata abunda kunnuwanta suka jiyo mata, cikin rawar murya tace.
"A.a.abbana!"
"Na'am batool" yafad'a yana share hawayen idonsa, yanajin tashin sautin muryarta sadda take furta Alhamdulillah da qarfi tare da juyawa cikin qarfin hali ta kalli gabas tayi sujudush shukur sannan cikin muryar dake nuna kukan farinciki takeyi taci gaba da cewa.
"Natuba Abbana ka yafemun, gaba d'aya rayuwa babu kai Abba wahalane da ita, nayi kuskure matuqa wajen kafiyawa abunda zuciyata keso duk da kuwa alkhairine sanadiyar nisan tani da kayi da kanka, bazan qaraba Abbana kayafeni."
"Ki kwantar da hankalinki batool nayafe maki, ni kaina tirsasa zuciyata kawai nakeyi akan saita haqura dake amma Ina matuqar shan wahala adalilin kewarki da akoda yaushe ke addabar zuciyata, idanuwana cike suke da mararin son qaninki akoda yaushe amma son zuciya da kuma sharrin iblis la'anannen Allah ya sani barinsu cikin qishirwar son ganinki, kiyafemun 'yata bisa tsattsauran hukuncin da nayi agareki, kiyafemun haqqinki dana tauye tsakaninki da mahaifiyarki da kuma 'yan uwanki, nayi nadama sosai kuma ina buqatar na kasance tare dake har iya qarshen rayuwata, kimanta da waccan hukuncin da nayi agareki domin mahaifiyarki ta nuna mani kuskuren yin hakan, ni mahaifinki ne kuma nan gidan kune bakida wani shamaki tsakaninki dashi har iya qarshen rayuwarki kinji ko 'yatah!"
"Eh Abbana, Ina sonka, Ina matuqar sonka Abbana don haka bazan tab'a kallonka a matsayin mai kuskure agareni ba balle har kanemi yafiyata, nice mai laifi gareka da bazan dena roqon yafiyar kaba har qarshen rayuwata, ka yafemun Abbana Ina matuqar qaunarka sosai."
"Nayafe maki 'yatah nima ina qaunarki sosai." Yafad'a yana dariya lokaci d'aya hawayen nasa na qara kwaranya, wanda ga dukkan alama wud'annan sun banbanta da wud'ancan don su na farinciki ne.
Tun suna wayar a zaune har yamiqe sunaci gaba da wayar yana dariya, kallo d'aya zakayi masa kagano tsantsar farincikin dake tattare dashi saboda yanda wani annuri ke fita a fuskarsa, murmushi su Uncle h sukayi had'e da miqewa zasu bar d'akin yayi d'aga masu hannu alamun su tsaya wanda seda hakan yaso basu dariya, batool kuwa tuni tasamu qafafuwan little da shima farincikinsa ya kasa b'oyuwa tayi matashi dasu tanaci gaba da waya da mahaifin nata hankali kwance,
Cikin sanyin murya tace.
"Abbana Ina so nazo naganka, Ina matuqar kewarka sosai."
Wani irin fad'uwar gaba Abba yaji jin abunda ta fad'a da sauri yace.
"A'a batool!, Don ALLAH kada kuzo kinji ko?, Ina ance tsohon cikine dake ko?, to kibari bayan kin haihu sai kizo kinji ko?"
Shagwab'e fuska tayi tamkar tana gabansa had'e da cewa,
"Abbana da sauran lokaci fa!, Sai 13 ga wani watan tukuna za'ayi aikin, nidai zanzo naganka abbana."
"A'a batool kada kizo kinji ko?"
"A'a Abbana nidai kabarni inzo inyaso ko kwana ukune kad'ai sai nayi."
"Batool.."
"A'a Abba nidai zanzo, ko baka yafemun ne ba?"
Cikin rud'ewa da rashin sanin yanda zai fahimtar da ita ta gane me yake nufi, cikin wata irin qarfin murya yace.
"Aaaaaa..., kada kizo nace batool kinji ko?."
Tashi tayi zaune a tsorace kamar zatayi kuka had'e da cewa.