← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 160

Sashe 100

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fad'a Rashida tayi masa sosai tare da umurtarsa ya ajeyi zancen duk wata soyayya agefe har sai lokacin daya kammala karatunsa domin bayada gatar data fimasa karatu alokacin, kasancewar yana matuqar yimata biyayya tare da martabata acikin duk wani umurni da zata bashi yasa ya amince da maganarta kuma yayi mata alqawarin zaiyi yanda tace matuqar hakan zai faranta mata rai, sannan yanemi alfarmar tabashi izinin sake had'uwa da batool d'in sau d'aya daga nan bazai sake kulata ba dama duk wata mace har sai zuwa lokacin daya kammala, taji dad'i sosai tare da saka masa albarka kafin ta shiga sanar dashi saqon Dr ya barmata cewa ta fad'amasa yaje wajen dady yakarb'o saqo ya ida kammala shireshirensa in sha ALLAH jibi zai wuce makaranta don har anfara karatu satin daya wuce ya amsa mata da cewa anjima da daddare zai tafi, sun jima suna firarsu irinta d'a da uwa kafin akira sallar la'asar yayi arwala sannan yanufi masallaci, ana gamawa ya dawo sukaci gaba da firarsu alokacin harda fatima da yaranta gaba d'aya, Rashida na tsokanarsa wai yazama kiyashe ja abunda yafi qarfinka had'e da labartawa Fatima abunda kefaruwa anata dariya, d'an sosa kai yashigayi saboda jin kunya Fatima tace, Kai qyaleta big son, haushi takeji nakusa zama suruka kafin ita, in sha ALLAH indai batool ce kad'auka har tazama matarka komai daren dad'ewa, ai SANNU SANNU bata hana zuwa....kamar gobene zakaga ka kammala karatunka musha buki, ranar aga b'arin nera awajen Fatima surukar Fatima uwar ango da kanta.

Taqarasa maganar tana dariya, d'an kallon Rashida yayi ta qasan idanuwa data mere baki itama tana dariyar yace, wlh ko mama, ranar saidai su gwaggo surab'e agefe sai inkinga dama kince su shigo adama dasu kuma mama kinsan meyasa nake son batool?, A'a big son sai kafad'a, Fatima tafad'a tana kallon Rashida da alamu tafara gajiya da shirmen nasa da tabiye masa sunayi yace, saboda kawai sunanki da take dashi, kinga sai adinga cemani d'an fa....bai qarasa fad'ar abunda zaice ba Rashida ta d'auki throw pillow d'in dake gefenta ta jefesa dashi tana fad'in, ungo nan marar kunyar yaro yatashi da gudu yana dariya yabar falon, maido kallonta tayi ga Fatima had'e da cewa, ALLAH yaron nan naki idan yayi wani abun har mamaki yake bani, duk wannan shiru shirun nasa da nike gani idan yaganki awaje haka yake sake baki yayita zaro suruttai cike da rashin ta ido sai kace bashi ba.

Ah to! barshi yayi, shida mamansa ne balle ayi masa gori, ni kaina mamakinsa nakeyi, zuwa nan da anjima kuma in kika gansa bazakice shine ba, musamman idan dadynsu na awaje, sai kiga gaba d'aya ya tattaro natsuwarsa waje d'aya, yana matuqar girmamasa fiye da lissafi,

Ai aunty shiyasa in za'a kwana ana kawoma uncle laifinsa bazaya tab'a yarda ba, Fatima tace.

Ai kuwa wlh, yo inama yai laifin balle har afad'a masa ya yarda,

Hmm! aunty kenan!, Rashida tafad'a tana murmushi,

Shikuwa bai jima da fita ba aka kira sallar magrib don haka saida yawuce masallaci yayi sallah sannan yanufi gidan dady, yana shiga batool nafitowa daga cikin part d'in ammie, dama yau tayi mayannu sunfi aqirga part d'in don tagansa tasa bayada wajen zama idan ba canba, cike da farinciki tanufi inda yake tana sakar masa wani qayataccen murmushi, ta qasan idanuwa yake kallonta yana susar gefen idonsa har taqaraso, zagayarsa tashigayi hanuuwanta duka nazube abayanta kafin tadawo gabansa ta tsaya tana qare masa kallo tundaga sama hara qasa, shima kallon nata yashigayi yana 'yar dariya sannan yafara zagayarta kaman yanda tayi masa had'e da cewa, ALLAH bazan yarda ba kishanyemun jini nima sai narama, hakan yasata sakin dariya had'e da d'aga hannu kamar zata dokesa, d'an kaucewa yayi had'e daja da baya, tace, kai ko?, Ina kashigane yau tun safe nake nemanka ban ganeka ba kasa gaba d'aya har bugun zuciyarta na neman tsayawa?, taqarasa maganar had'e dasa hannuwa a qugun tana kallonsa, Saida yasa hannuwansa guda biyu ga kunnuwa yariqe yana d'an yatsina fuska sannan yace da ita, tuba nake gimbiya, yau wajensu gwaggo naje shiyasa baki ganeni ba, amma zuciyata da kuma rouhina gaba d'aya suna nan wajenki, zo muje nafad'a maki wani sak'o kafin dare yayi inwuce.

Kana nufin yauma ba'a gidannan zaka kwana ba?, nida nake son musha firarmu har mugaji sai kuma kace haka!, taqarasa maganar tare da juya baya tana turo baki had'e da qoqarin barin wajen, bayan nata shima yabi yana cemata,

Ke gimbiya!, Ina kuma zakije daga magana,

Dena cemun gimbiya ni, kawai kace mun batool d'ina tunda munyi fad'a dakai, 'yar dariya yakama yimata tare da cigaba da binta yana fad'in.

Kai yaushe kuma akayi haka?, to tsaya mushirya mana,

Inaaa!, tafi kawai.

Shikenan! Bari kawai natafi, kicewa su ammie Ina gaishesu. yajuyawarsa kamar zai koma, da sauri tajuyo tabiyoshi baya da gudu shima yad'an ruga saida yaga yakusan kai bakin gate tana qoqarin cimmasa sannan ya baud'e mata tare da nufar gefen da wasu fararen kujeru suke kakkafe tsakankanin part d'in umma dana hajia nafeesa ya zauna yana dariya, tana qarasowa wajen tayi tsaye kamar zatayi kuka tana kallonsa da sauri yamiqe had'e da qamewa ya d'aga qafa yabuge qasa sannan ya Sara mata da hannu yana fad'in, sorry mah! Bushewa tayi da dariya ganin yanda yawani qame tare da zaunawa saman d'aya daga cikin kujerun har tana riqe ciki, Saida tayi dariyar mai isarta yana kallonta shima yana murmushi sannan yanemi waje ya zauna, cikin wani irin kallon qauna takallesa had'e da cewa. Abu sumayya a gaskiya zakayi kyau da soja sosai, ka ganka kuwa dake qame d'innan?

A'a gimbiya, amma tunda ke kingani ya wadatar, saidai ni bana sha'awar duk wani aiki na kaki saboda bana qaunar duk abunda zaisa nayi nesa da mahaifiyata, karatunnan ma da zanje garinku inyi saboda babu yanda na iyane kuma ita tagoyi bayan hakan da babu inda zanje.

ALLAH sarki, shiyasa nake qara sonka abu sumayya saboda kana matuqar girmama magabatanka musamman gwaggo, ya ALLAH kabani ikon qara qarfafa maka hakan idan munyi aure.

Amin gimbiya, wai nikam na tambayeki?, Cikin kashe murya tana kallonsa tace, Ina jinka Abu sumayya.

Meyasa kike kirana da Abu sumayya?, tunda muka had'u dake ban tab'a jin kin kirani da sunana ba, meyasa?

Shiru ta d'anyi kafin tace, sunanka nada matuqar nauyin da bazan iya kiranka dashi ba, kaga sunan abbanmu ne sannan kuma sunan babban Yaya agidannan so bazan iya kiran sunan gatsau ba, Abu sumayya kuwa da nake kiranka dashi mafarkina ne da kuma burina da nake fatan ya tabbata idan munyi aure muka haifi 'yah Ina son taci sunan sumayya, Ina matuqar son sunan tun lokacin da malamin islamiyarmu yayi mana tarihin irin gwaggarmayar da tasha acikin musulunci, to tun alokacin nak'uduri cewa idan nahaifi 'yata sumayya zan saka mata kuma duk mijin da zan aura komai dad'insa ni da Abu sumayya zan kirasa.

Iyyeee to idan shi kuma baya so fa?,

Saida ta d'an d'aure fuska sannan tace dashi, Dole ma yaso tunda nima naso sunan da yake yimani, murmushi yayi sannan yace da ita,

To shikenan, ubangiji ALLAH yacika mana burinmu na alkhairi, ni kaina inajin dad'in sunan sosai kuma Ina sonsa fiye da yanda kike sonshi, tace dashi ALLAH? Ya amsa mata da sosai kuwa.

Saida suka sha firarsu sosai sannan yabijiro mata da maganar da sukayi da mahaifiyarsa kuma ya tabbatar mata da cewa zaibi umurninta koda hakan na nufin zai mutune, duk inda hankali ke tashi hankalin batool yatashi, nan take tafara girgiza kai hawaye nayimata zarya a fuska,

Don ALLAH abu sumayya kada kayimun haka, Ina tsananin sonka kuma saida kai zan iya rayuwa, don ALLAH kataimakeni kada karabu dani har bayan cikar mafarkaina, idan ba haka ba zan iya lalacewa.

Haba gimbiya, meyasa zaki fad'i haka, taya za'ayi in saka idanuwa inaji Ina gani ki lalace adalilina, yakamata ki fahimceni gimbiya, bawai ina nufin murabu bane, ina so mujingine wannan maganar agefene har zuwa lokacin daya kamata, aduk fad'in duniya ban tab'ajin zuciyata zata iya son wata da sunan aure ba daidai da second d'aya, ke ce kad'ai azuciyata kuma ke kad'ai nakeda wannan buri akanki, amma hakan bazai yuyu ba har saina gama cika burin tawa mahaifiyar.

Amma mekake tunani zai haifar akaina lokacin da muka jingine wannan maganar agefe?, ita fa macce ba iyaye na renonta bane don d'ai su zauna suyita kallonta ko su ajiyeta ba har zuwa lokacin da cikar burin wani zaya gama cika, don ALLAH kafahimci wannan abun da kake shirinyi ba komai bane illa kuskure da kuma ganganci da zai jawo rabuwarmu d juna akowane lokaci, kasani ina sonka tun daga zuciya, jinin jiki, rouhina da kuma dukkanin sassan jikina, Abu sumayya zan iya rantse maka akan cewa kaine bugun kowane lumfashi nawa dake fita daga jikina.

Nasani gimbiya, amma nima Ina so kisani mahaifiyata da kuma cikar kowane muradi nata sune rayuwata, don haka kiyi haquri mu ajiye wannan soyayyar agefe har lokacin da zan kammala karatuna, nayi maki alqawarin cewa bazan kula kowace macce ba da sunan soyayya balle aure kuma zan reni soyayyarki cike da tausaya da kulawar da bazan tab'a bari wani abu ya tab'ata ba balle har tasamu wata tangard'a tamkar yanda mahaifiya kerenon 'ya'yanta har zuwa lokacin da zasu girma su koma ga ALLAH batare data bari wani abu yatab'a mata suba bisa son ranta, Ina fatar kema haka?.

Yana gama fad'a yajuya zaibar wajen qwalla nazubo masa, durqushewa tayi had'e da saurin kamo qasan rigarsa, ya rufe idanuwansa da sauri.

Cikin sheshshekar kuka taci, shikenan katafi izuwa cikar dukkani muraddan mahaifiyarka ni kuma zan jiraka komai daren dad'ewa, zan kula da soyayyarka har sai natabbata ta lullunku fiye da yanda zaka tafi kabarta, zan tanada maka kaina batare da gazawa ba har zuwa lokacin da zaka dawo gareni.

Sosai yaji tabashi tausayi, yatabbata soyayyarta agaresa mai girmace da darajar data lunka darajar lokaci, yatabbata tana yimasa son da ko rabinsa baya yimata kuma in sha ALLAH shima ya d'auki alqawarin da SANNU SANNU zai rama mata dukkanin qaunar data nuna masa.
Chapter 100 · 0% Book details