← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 160

Sashe 30

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nad'e d'ayar kazar tayi ta tura aqarqashin filo tare da gorar youghout d'in d'aya, shi kuma sauran takoma ta kwanta tana sha tana suruttanta har bacci ya soma d'aukarta, can cikin bacci taji kamar ana Kiran sallar asuba da sauri tamiqe tanufi sashensu Nuraddeen tafara bubbuga qofar, kasancewar baaccin ya soma yimasa nauyi sosai shiyasa baiji ba saidai baffa Usman ne yaji qarar ana dukan qofa daga wajen sashen Nuraddeen da sauri yafito don ya zata shine, ganin Yaya hawwa tsaye bakin qofar yasa yaqarasa wajen yana murzar idanuwa cikin rage murya yace

"Lafiya Yaya hawwa kike buga masu qofa awannan lokaci?."

"Aiho Usman ashe kaima kafito, ja'irin yaro kaji har ankira sallar asuba bai fitoba shine nace Bari na tadashi don Karya makara" kallon sararin samaniya baffa Usman yayi kafin yace.

"Ikon ALLAH! To aike yaya ba'a isa kiran sallar asuba ba, qarfe uku da rabi yanzu ko baki duba agogo bane."

"Kace wlh, Niko naji kiran sallah yanzu shiyasa nataso." dariya yayi don ya fahimci zallar damuwane yasa kunnuwanta ke hakaito mata kiran sallah awannan lokacin, dariya suka jiyo shiyarsu baffa Ali wanda har da zai fito Inna ruqayya tariqesa ta hanasa fitowa.

"Wlh waccan yayar tashiga uku, mace baqin hali sekace gareta farau suruka, shiyasa naso muneera ta auresa don ta gyara mata zama wannan takurawa har Ina, fita batunsu baban yusufa koma ka kwanta." Tafad'a tana dariya had'e da kashe wutar d'akin,

Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da cewa "ki koma ki kwanta Yaya hawwa idan asuba tayi zan tashesu."

"Asubar batayi ba kenan!"

"Eh" yafad'a tare da juyawarsa yakoma d'aki, Daren ranar kam kasa komawa bacci tayi in banda saqawa da kuma warwarewa azuciyarta babu abunda takeyi,

Baffa shima kansa abun dariya yabashi don duk abun dake faruwa akunnensa yanaji saboda alokacin shima ba bacci yake yiba, zaune take abunsa yana karatun al-qur'ani kafin yafara sallolinsa daga zaunen yajiyo bugun qofarta, rashin qafafuwa ya hanasa tasowa da sai ya riga baffa Usman fitowa, sosai matar tasa tabashi dariya ya d'aga hannuwa sama yana addu'a ALLAH ya shirya masa ita yaganar da ita kura kuranta tun wuri bai qure mata ba sannan yaci gaba da ibadunsa tare da roqawa d'an nasa samun dukkanin bud'i na duniya da zaman lafiya had'e da 'ya'ya nagari...

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___22💎

Yaya hawwa kuwa har akayi kiran sallar asuba na farko idanuwanta biyu tanaji anfara kiraye kirayein sallar tamik'e had'e da azo qafarta bakin qofar d'aki kawai taji saukar ruwan sama ya kuccike ba zato ba tsammani don tun wurairan biyu da hadarin ya kankama iska ya taso ta ko Ina sai kuma daga baya ya kwanta hadarin kuma ya wargaje cikin ikon ALLAH nan take kuma da asubar ya sake had'uwa saiga ruwa, tsaye Yaya hawwa tayi kamar tafashe da kuka tana kallon sama, wata irin walk'iya akayo da tsawa alokaci d'aya da gudu takoma cikin d'akin tanemi waje ta zauna gefen gado idanuwa sunyi mata qululu, yau take jiran ad'auke ruwa gobe take jira amma sai sake sauka sukeyi kamar da bakin k'warya, hakan yasa kosu baffa Usman basu samu fita masallaci ba balle malan Nuraddeen ango sai dai kowanensu yayi sallarsa a d'aki tare da iyalinsa,

Nuraddeen kuwa saboda sanyi da qyar yasamu yayi wankan tsalki ba tare daya tayar da Rashida ba da sai faman yatsine fuska takeyi cikin baccin saboda babu ruwan zafi, sallarsa yayi sannan ya shiga cikin kicin d'inta ko zaiga inda aka ajiye rishow d'inta, cikin sa'a ya hango kwalin electric stove ya jawo had'e da cirosa daga ciki ya jona ga socket d'in kitchen d'in sannan ya ciro tukunya cikin kwalinta itama ya d'ora bayan ya d'an kara hannunsa saitin electric d'in yaji yafara zafi ya d'ebo ruwa ya zuba sannan yakoma cikin d'akin, gefen gadon ya zauna tare dasa yatsansa yana d'an shafa lab'b'anta, ahankali yaga tafara bud'e idanuwanta suka sauka akan nasa daya qura mata, suna had'a ido tayi saurin rufewa had'e da cuno d'an k'aramin bakinta ta kauda kanta gefe, dariya yayi kafin yace "haba ta malan nura fad'amun waya tab'amun ke kike juyamun kai haka." Shiru tayi batare data amsa masa idanuwanta na arufe, hannunta ya cire daga saman qirji da yake ta riqe bargon yana shafa lallen dake jiki a hankali tare da yimasa kiss, jaye abunta tayi da sauri tana fad'in "kadena bana so.."

Kafin tarufe baki taji ya had'e bakinsa da nata ya sakar mata wani irin sihirtaccen kiss. Idanuwanta ta lumshe tanajin tamkar na'urar jikinta ta d'auke ta had'e da dawowa.

"Morning habibty kin tashi lafiya?" Kad'a masa kai tayi tana tunani abubuwan da suka faru jiya tsakaninta dashi kawai saita tsinci kanta cikin matsananciyar jin kunyarsa, "taso muje kiyi wanka yafad'a had'e da miqewa, har zai d'aukarta sai Kuma ya tuna bai had'a ruwanba ya. "Afuwa habibty bari naje na had'a maki ruwan wankan tukunna."

Yaqarasa maganar tare da barin d'akin koda yaje ruwan har sun tafasa ya juye a boket yakai toilet, wani bokitin ya sake d'auka yahad'a mata ruwan tare da detol sannan yakoma ya d'aukota tamkar wata baby,

Cikin jin kunya tace "don ALLAH ka ajiyeni zan iya tafiya da kaina."

Zaro idanuwa yayi yana kallonta had'e da cewa.

"Da gaske kike?"

"Eh ajiyeni kagani mana."

Tana turo baki agaba, Saida yayiwa bakin kiss sannan ya ajiyeta qasa tafara takawa ahankali yana biye da ita har takai bakin qofar shiga toilet d'in, tana aza qafarta d'aya ta d'ago d'ayar ta aza tayo baya baya zata fad'i da sauri ya tareta tafad'a akan jikinsa saboda wani irin masifaffen zafi da taji a tsakiyarta don ma ALLAH ya taimaketa bai jimataba saboda ba duka ya shigeta ba, binta da kallo yayi ganin yanda tsoro yasa taturo idanuwanta da suka cika tab da hawaye tana shirin yin kuka yace

"Sorry habibty, kibi a hankali mana kinga da yanzu kin fad'i" kafin tace wani abu ya d'auketa ya qarasa shiga da ita ciki, qasa ya direta sannan yajawo wata 'yar kujerar da kecikin bayin ya zaunar da ita had'e da nad'e hannuwan rigarsa yasa cup yafara d'ebo ruwan yana yimata tsarki dasu, ture hannunsa takeyi tana had'e qafafuwanta Amma yayi kamar bai ganta ba saida ya gasata sosai sannan yace tayi wankan tsarki sai tafito,

Ita kam banda satar kallonsa tana mamkinsa babu abunda takeyi, wai yau itace malaminta ke d'auka hadda suyimata tsarki, lalle aure wani babban alamarine daban, da sauri tasa hanuwa tarufe fuskarta tana dariya alokaci d'aya kuma tanajin qaunarsa naqara ruruwa azuciyarta, tajima zaune tana wud'annan tunanin kafin tayo wankan tafito tasamu harya shimfid'a mata abun sallah tare da fiddo mata da doguwar riga da hijabi yabata tasa ta tada sallah, waje yake son fita amma har lokacin ruwa akeyi sosai gashi har goma da kwata tayi yarinyar mutane bataci komai ba,

Yanke shawarar fita haka yayi sai gashi yaji qarar wayarsa dake ajiye saman bedside, da sauri yaje ya d'auka yaga lambar baffa Usman duk sai yaji wata irin kunya ta kamasa, kasa d'agawa yayi akaro na farko har sai akaro na biyu ya d'aga had'e dayin sallama ya gaishesa. murmushi yayi sannan yace

"Lafiya klw Nuraddeen, katashi lafiya."

"Lafiya klw baffa Usman."

"Ya kwanan iyalin naka? Yau mun tashi da ni'ima."

"Alhamdulillah kam ga ruwa nan masha ALLAH sai fatar alkhairin dake cikinsu" yafad'a tar da basar da d'ayar maganar, murmushi baffa Usman ya sakeyi kafin yace,

"Kabud'e k'ofa ga abun karinan Aysha zata kawo maka da sauri kasan ruwan nada qarfi kada su dokarmun auta tayi ciwo.." 'yar dariya Nuraddeen yayi had'e da cewa.

"To baffa Usman, ko abari inzo in karb'a kada ruwa sudoketa nayi laifi, dama yanzu nake Shirin fitowa."

"A'a jira gatanan zuwa, ai babban d'a baya laifi,"

"To baffa Usman mungode."

"Masha ALLAH ka gaida iyalin naka"

Yakashe wayar don yasan bazai amsa ba saboda kunyar da yake da ita, miqewa yayi had'e da zuwa bakin qofar don har yaji isowar ta, yana bud'ewa yace

"Aysha shigo da sauri mana kada ruwan ya jiqaki."

"A'a Yaya Inna tace inyi maza indawo kada natsaya, Ina kwana?"

"Lafiya klw autar baffa yasu Inna?"

"Duk lafiya klw suke, Ina aunty."

Juyawa yayi yakalli qofar d'akin bayan ya anshi kayan hannunta sannan yace "shigo mana tana ciki ku gaisa ko bakya sonta?"

Rufe baki tayi sannan tajuya da gudu tabar wajen tana fad'in "Ina sonta mana Yaya ka gaisheta anjima zamuzo ni dasu aunty fadila."

Juyawa yayi ya koma ciki ya tarar har ta sake gyara d'akin ta koma ta kwanta, amaimakon ya tada ita sai kawai shima yabi bayanta yakwanta abinsa had'e da jawota ajikinsa, tanaji yafara shafo cikinta yana yawo da hannunsa ta rintse idanuwa sosai irin tayi baccin nan, cakulkuli yafara yimata yana fad'in "kima bud'e idanuwanki nasan ba bacci kikeyi ba."

Yanaci gaba da yimata cakulkulin, juyowa tayi tana dariya tashige jikinsa tana fad'in "don ALLAH kadena bana so."

Cikin kwaikwayon muryarta shima ya maimaita abunda tace. "Shikenan to ni kiyimun Ina so."

Aikuwa ta taqarqare tana yimasa cakulkuli tana dariyar shima yanayi, jawota yayi ya rungume jikinsa sosai yana fad'in "to ya isa haka kibarni nima bana so" yana rirriqe mata hannuwa ita kuma tana qoqarin kwacewa, da wayo da wayo yasamu ya sake biyan buqatarsa amma awannan karon Mai gaba d'aya yayimata don seda yaji yasamu natsuwa sosai,

Kuka kam Rashida tashashi har dasu majina, sai faman rarrashi yakeyi fiye da jiya yana qoqarin jawota ajiki turesa ta dingayi tana fad'in "ni ka qyaleni tunda wayone da Kai bazan sake yarda da kaiba."

Dariya ya dinga yimata yana cewa. "Yi hakuri nadena bazan sake ba."

Saida yaga tayi shiru sannan ya tashi yaje ya juyo sauran ruwan zafin d'azu yakai masu toilet yadawo ya sake d'aukarta izuwa toilet d'in, nan ma saida ya cukulkulata sannan ya taimaka mata tayi wankan shima yayi suka fito, ji yake wani irin sonta na qara ruruwa azuciyarsa da bayajin zai iya rayuwa idan babu ita.
Chapter 30 · 0% Book details