Sashe 57
Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina tsira anan kin maidani uwa gwaggon biri, kinga dai ni banyi komai ba kika yimani wannan dukan? To su kiyi masu dukan mutuwa wallh, karki raga ma waccan yaya hawwar ita da kanta takai Rashi wajen boka ayi mata kurciya, sukuma su Innata da had'in bakinsu don kawai su auramun Yaya nura, to ni nama Dena sonsa wlh nafasa aurensa, don haka kimaida masu nasu fuskokin uwa na angulu, ALLAH haka zaisa su fad'i inda bokansu yakai Rashidar ya nura, Abba, Inna sai kun dawo," tafad'a tare da juyawarta tabar station d'in,
Dariya Yaya hawwa dake zaune fuskarta duk jini tayi had'e da cewa.
"Ahaf, ai indai waccan Mai gwalmad'ad'd'in qafafuwace nafad'a maku sai kunyi nadamar haihuwarta, kad'an kenan daga cikin aikin waccan mai kama da 'yan ruwan, Bata rufe baki ba Inna ruqayya da takaicin muneera ya isheta tayo kanta da duka, fad'a suka kaure dashi sunata murzar juna acikin cell d'in, cikin sa'a Inna ruqayya tayi nasarar fashewa Yaya hawwa baki had'e da fitar mata da hauru biyu nagaba, hakan yasa itama ta mirgina ta hayeta tana kaimata naushi a fuska tana tofa mata yawun bakinta daya koma jawur saboda jinin daya surku dashi, kan kace me ta kumbura mata fuska, saida suka gama wahalar da juna sannan don kansu suka tsaya da fad'an, inspector najida dake gefe zaune ta aza qafafuwanta saman benci tana kallonsu ta tara police d'in dake wajen su kusan goma tace subud'e cell d'in su shiga suba su yaya hawwa pepe, ai kamar jira blessing keyi take tad'ebo ruwa bokiti hud'u sannan tabud'e cell d'in ta shiga dasu, saida tajiqesu da ruwan sannan taba 'yan uwan nata umurnin shigowada kulkayensu suka dinga dukansu har saida suka dena motsi sannan inspector najida tabasu umurnin su dakata hakan,
Baffa kuwa tsananin azabar da suka basa tasa tun jiya baisan inda kansa take ba har yau, gaba d'aya sun bubbuge masa qafafuwa da hannaye sai kin sukeyi ga wani qaton qololo daya fito masa ga goshi gwanin tausayi....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___43💎
Duk wahalar daya kamata abama su yaya hawwa don su fad'i inda Rashida take anbasu amma maganarsu d'aya shine basu san inda take ba, sai daga baya baffa Ali da Inna ruqayya da sukaga wahala na neman kashesu suka zauna suka yiwa inspector najida bayanin komai da suka sani dangane da matakin da yaya hawwa tafad'a masu cewa zata d'auka akan surukar tata saboda saboda su samu sassaucin azabar da ake basu dake shirin hallakasu alokacin suna cikin sati na uku da 'yan kwanaki da kawowa wajen amma daidai da rana d'aya baffa Usman da baffa basu tab'a tako qafarsu duba suba balle har susa ran zasu je belinsu, Nuraddeen kad'aine lokacin daya samu labarin cewa harda mahaifiyarsa nacan kulle wajen 'yan sanda yaje sau d'aya, kukan baqin cikin ganin wai yau mahaifiyarsa ce kulle a hannun 'yan sanda ake tuhuma akan b'atan matarsa yasa kafin yafara yimata magiya tare da roqonta idan tanada wata masaniya akan maganar ta taimakesa tafad'a kodon afitar da ita wajen, Amma tsabar rashin imanin Yaya hawwa ta fatattakesa agaban 'yan sanda har tana fad'in Bata son ganinsa karya koma takowa da sunan zuwa inda take tunda dasa hannunsa mahifinsa ya tozartata a idanuwan duniya, sun zab'i bare akanta da take uwarsa kuma matar shi baffan, don haka tunda anan take farincikin ganinta tunda matarsa ta b'ace yaje tayafe mata shi, ranar Nuraddeen yashiga damuwa da tashin hankali sosai, kuka yake yana riqon qafafuwanta akan bayada wata masaniya akan haka tayi haquri Amma fir tace dashi idan har baibar wajenba kuma ya qauracewa ganinta wlh saita d'ebe masa albarka, wannan dalilin yasa Nuraddeen barin policetation d'in cikin wani hali marar misaltuwa, ayanzu Babu banban tashin hankalinsa irin zaman mahaifiyarsa a hannun 'yansanda domin duk lalacewar uwar mutum uwarsa ce, daqyar yasamu yakai gida wajen baffa yafad'i agabansa yana kuka yana roqon yasa asaki mahaifiyarsa, koma meye zai rungumi qaddara yaci gaba da addu'ar ALLAH yabayyana masa matarsa amma baya buqatar ganin mahaifiyarsa awajen, duk da yasan wannan ita kad'aice mafaitar da za'a iya samun bakin zaren sanin inda habibty d'insa take amma ya zaiyi dole ya haqura, sosai baffa yafahimci damuwarsa don haka sai yariqa hannunsa yana biye dashi yana sharar hawaye suka nufi tasha, bai zame dashi ko Ina ba sai asibiti wajen iyayen Rashida dake kwance cikin mawiyacin hali, d'aya bayan d'aya yashiga dashi yana nuna masa irin yanayin da sukeji akan b'atan 'yarsu, idan har yace asaki mahaifiyarsa ya yakesu suyi da alhakin wud'annan bayin ALLAH da aka zalunta tare da 'yarsu, haquri ya shiga baahi tare da nuna masa cewa bawai don yanajin dad'in ganinsu acanba yasa yayi hakan, yana sone asamu koda wani haskene kad'an da zaiyi masu jagoranci wajen gano inda 'yar mutane take, Kuma idan har yace asaki mahaifiyarsa su kuma d'an uwan nasa da matarsa dake ciki fa?, Bayanda Nuraddeen ya iya dole ya haqura tunda iyaye basufi iyaye ba, Amma tun daga ranar yakwanta ciwo cikin matsanancin hali, Kuma yaqi amincewa aje asibiti, yana matuqar shan wahala amma ya gwammaci zama cikinta tunda mahaifiyarsa da matarsa ma yasan basa cikin jin dad'in.
Baffa Usman kuwa duk da baya zuwa station d'in haka yasa Inna Bilkisu nadafa masu abinci ana kai masu shima d'in saida yayi da gaske baffa ya amince saboda duk lalacewar hannunka bazaya ru'beba ka yanka, sosai inspector najida tasa aka sake tsananta masu bincike bisa bayanin da suka bayar har suka tabbatar da cewa suma su baffa Ali basada sa masaniya akan b'acewar Rashida, amma sunada sa hannu domin sunada masaniyar akan abunda aka aikata, duk da gaba d'aya laifin na Yaya hawwa ne suma d'in sun taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa mai laifi aikata laifinsa.
Hakan yasa suka yanke shawarar kiran baffa su sanar dashi don dama shima tun ranar da yaje yasa aka kamosu bai koma takawa station d'in ba sai dai yakirasu awaya ya tambayesu ko sun fad'i inda Rashidar take suce a'a daga nan kuma bai sake cewa komai zai kashe wayarsa, bugu d'aya sukayi masa ya d'aga wayar lokacin yana zaune gefen da Nuraddeen yake kwance duk yayi baqi ya rame tamkar bashi, bayaci baya sha sai baffa ya tsareshi tare da nuna masa b'acin ransa sannan yake samu yasha damammiyar fura itama d'in 'yar kad'an, kallo d'aya zakayi masa kafahimci tsantsar damuwar da yake ciki shida mahaifinsa, cike da fatar ALLAH yasa kiran nasu yazama alkhairi baffa yayi sallama had'e da cewa.
"Ranki shidad'e ALLAH ansamu wani bayani daga bakinsu ne?"
Girgiza kai inspector najida tayi tamkar tana agabansa kafin tace "kayi haquri baba, munyi iya qoqarinmu don muga cewa sun amsa laifinsu har suyi mana bayanin inda take amma hkan ya cutara, a iya bincikenmu mungano d'an uwanka da matarsa basuda masaniya akan inda take saidai an had'a baki dasu wajen b'atar da ita, domin duk abunda hawwa ta aikata sunada masaniya akai, ita kuma hawwar mun gana mata azaba kala kala amma taqi bud'e baki tayi magana akan komai wanda hakan ya tabbatar mana da cewa itace ta aikata duk wani abu da yayi sanadiyar barin yarinyar gidan don haka mukaga tunda ga wacce mukeda tabbaci akan aikata laifin da ake tuhumarta akai babu buqatar muci gaba da tsare d'an uwan naka shiyasa muka kiraka don mu sanar dai" wata irin ajiyar zuciya baffa yayi kafin yace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, ranki shidad'e inaga tunda har akwai sa hannunsu a b'atan yarinyar bai kamata a sakesu ba, acigaba da tsaresu koda kuwa ba'ayi masu komai ba har sai lokacin da akaga yarinyar saboda aja masu kunne, domin yanzu haka su d'in barazanane akan d'ana da suke neman takowace hanya sai sunga sunyi galaba akansa sun aura masa 'yarsu, bawai Ina tsoron hakan da zasuyi bane kawai idan ansakesu, Ina tsoron abunda zan iya aikata masu bayan fitowarsu idan wani abu yasamu yarona, wanda bana fatan hakan shiyasa nagabatar dasu ahannunku akaro na farko, don ALLAH kuduba yuyuwar hakan kozai koya masu hankali da zaman rayuwar duniya."
"Shikenan baba, ai dama wannan shine qa'ida tunda suna cikin suspect namu, dama naduba abun ne atawani b'angare koda za'a samu sauyi, Amma tunda harga qudurinsu zamuci gaba da tsaresu har lokacin da za'a samu masaniya akan inda 'yar mutane take."
"Yawwa nagode sosai, ALLAH yayi maki albarka." baffa yafad'a idanuwansa cike da hawaye,
"Amin baba, kayi haquri in sha ALLAH zamusa hawwa dole tayi magana, kaui hak'uri kaji." Taqarasa maganar tare da kashe wayar, tana matuqar tausayin halin da baffa yake ciki, tsohon nabata tausayi sosai duba da yanda yadamu da case d'in yarinyar tamkar 'yar daya haifa da cikinsa, hakan yasa ta d'auki alwashin zata tirsasa hawwa tayi magana da kalolin nau'ukan azaba kala kalan da zata tanadar mata.
Shiru baffa yayi yana tunanin irin wannan rayuwar da ake ciki duniya, ace saboda son ran mutum d'aya ta tarwatsa farincikin zukata da yawa, Aiko ba'a hukuma bata hukuntata ba ya tabbatar ALLAH bazai tab'a barinta ba,
Kallon Nuraddeen dake kwance Kai kace ya shekara yana jinya yayi tare da dafa kansa yace.
"Nuraddeen, Ina so kayi haquri, kasawa ranka dangana, Kai kad'ai karagemun da aduniya nake kalla naji sanyi sai kuma baffanka Usman, don ALLAH kada kabari damuwar nan tasa kaima narasaka hakan zaisa duniyar tayi mani quncin da nima zan iya rasa kaina mubar Usman cikin mawiyacin halin da bayada Mai tausayinsa sai ALLAH, indon Aliyu natabbata zuciyarsa bazata kareba akan wannan abun daya faru saima sake tunzurasa da zata sakeyi inba wata shiriya daga ALLAH ba, mubarwa ALLAH komai shiyasan dalilin da yasa yayi mana wannan jarabawar kaji ko?."