← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 160

Sashe 96

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk wannan abun daya faru bisa amincewar Dr da taimakonsa dady yayis hakan kuma dashi har Fatima sunyi farinciki sosai ba tare da wata hiyana ba, Rashida ce kawai kullum take cikin jin kunya tana ganin kamar hakan da akayi ba'a kyautawa ammie ba, bayan duk taimako da halaccin da tayi masu ita da d'anta har saida ammie tazaunar da ita tanuna mata hakan ba illa bane tunda musulunci bai hana ba sannan tafara samun sakewa daidai, duk da ako yaushe idan hajia nafeesa tahad'u da ita har mahaifiyarta cikin jifarsu take da miyagun kalamai cewa wai Rashida tayi cikin shegene shiyasa tagudo suma da abun kunya ya ishesu sun kasa gano uban d'and'an dake cikinta sai suka biyo bayanta, hatta ma little da baisan komai ba kullum cikin kyararsa take tana aibantasa agaban 'ya'yanta tana kiransa da shege wanda ba'asan ubansa ba, hakan yasa har 'ya'yanta ma ke kiransa da haka amma da yake baisan komai ba baya damuwa.

Haka rayuwa taci gaba Rashida nasamun kulawa da kuma gudun mawa sosai wajen karatunta da ita har d'anta ta b'angare biyu wato dady da kuma Dr, don tuni shima little Dr yasashi makaranta lokacin itama Fatima har tahaihu tasamu qaton d'and'anta suka rad'a masa suna basheer wato sukawa baba takwara, wannan ba qaramar kima da daraja yaqara jawo masuba a idanuwan umma da Rashida harma da 'yan uwansa, sunyi matuqar farinciki da jin dad'i sosai aransu harma suna ganin aduniya yanzu basuda masoya da suka fimasu su dady da Dr nura ba.

Rashida kuwa tun tana dakon dawowar mijinta izuwa gareta ita da d'anta har tacire rai, gaba d'aya ta tattara wata rayuwar aure data tab'ayi abaya dama auren ta ajiyesu gefe taci gaba da karatunta ita da yaronta, saidai duk da hakan daidai da rana d'aya Bata tab'a yarda tayi wani abun da zaya keta mata marta da kuma darajar auren taba har ta kammala secondary lokacin little na primary 2 amma babu wani labarinsa, a lokacin fatima har tayaye basheer da suke kira (abbaty) tasake samun ciki ta haifi 'yan biyu duka mata saidai rurrutsa ce tayi a tsakaninsu, inda aka barsu da sunayensu na asali wato hassana da hussaina, murna kam awajen Dr da fatima bata misaltuwa, gashi dai SANNU SANNU cikin iyawar ALLAH suma sunfara tara nasu 'ya'yan da suke matuqar qauna a cikin shekaru uku kacal ALLAH ya arzuttasu da 'ya'ya uku, Babu wata wahalar reno da fatima kesha saboda Rashida nanan, duk wata kulawa da yaran zasu buqata tana basu tamkar ita tahaifesu.

Shekarar Rashida d'aya tana jiran saka makon jarabawar tasu tafito kuma cikin taimakon ALLAH tayi nasarar lashe kowane darasin da kyakkyawan sakamako wato exelent gaba d'aya, ranar da ita har umma sunyi kuka sosai cike da son inama baba nada rai yaga yanda tafara taka mataki na biyu akaratu da kyakkyawan sakamako, godiya kuwa sunyiwa Dr da dady da ammie ba adadi har saida suka farajin kunya.

Umma da ammie kuwa bazaka tab'a ganinsu kace kishiyoyi bane domin akwai tsantsar fahimta da mutunta juna atsakaninsu, hakan yaqarawa hajia nafeesa tsanar umma da rashida dama little gaba d'aya.

••• ••• •••
A b'angarensu baffama acikin shekarunne ALLAH ya sauki nusaiba matarsa lafiya saidai ba'a samu namiji ba kamar yanda yaso ALLAH ya arzuttasu dai da samun 'ya mace kyakkyawa kamarta sak da nusaiba baffa ya rad'a mata suna Rashida, yana matuqar son yarinyar fiye da tunani saboda sunan data zauna, sau da dama yakan tuna da baba da Kuma 'yarsa Rashida aduk sadda aka ambaci sunan 'yar tasa da taci sunan Rashida, wannan yasa ko kad'an baya son jin kukanta balle abunda zai b'ata mata rai, hakama gaba d'aya yakasa mantawa da gudan jininsa daya kasa samun labarinsa, lokacin daya tuntubi ma'aikatar da aka turasu qasar waje don qaro karatu akan labarinsa sai suka b'oye masa ainahin halin da d'an nasa ke ciki, domin koda Nuraddeen suka isa qasae waje bayan anbasu wajen zama sai yanemi wayarsa sama da qasa yarasa, gashi gaba d'aya wud'an da aka had'asa dasu zama 'yan jahohin kudu ne acan nageria babu wanda yasani acikinsu, asalima gaba d'ayansu babu ruwansu dashi saboda shikad'aine bahaushe sai suka nuna mashi halinsu qarara na qyamar jinsin da banasu ba musamman ma ga musulmi d'an arewa duk da kuwa qasarsu d'aya, hakan yasake jefasa acikin wata damuwar akan wacce yake ciki yana son yasan halin da ake ciki anan gida nageria amma bayada waya, kud'ad'ensa ma daya zo dasu gaba d'aya an sace balle yasamu ya sayi wata, wata irin wahalalliyar rayuwa yafarayi aqasar da kud'in ma da zai samu yayi amfani dasu babu, ana haka d'aya daga cikin qabilun da yake tare dasu yafara qoqarin jawosa jiki yana son taimaka masa da sunan tausaya masa, amma azuciyarsa bashine dalilin silar taimakon da yake yimasa ba kawai yana so ya d'orasa akan hanyar da zata hanasa karatune balle yasamu yayi abunda yakawosa har yakoma qasarsa ana alfahari dashi sai dai duk da haka Nuraddeen bai tab'a wasa da karatunsa da tuni suka fara yiba a fannin koyon likitanci na psychiatric musamman idan yatuna da halin daya baro mahaifiyarsa aciki sai yaji yaqara samun qwarin guiwar maida hankali sosai, hakan yasa yazamo kusan shine zakara kuma zaqwaqurin da yafi kowane d'alibi amakarantar, tun daga kan fararen fata har zuwa 'yan uwansa baqaqe, wannan abun yaqara baqantawa natare dashi rai ganin shi bakowa bane acikinsu amma ace ya zartasu qoqari acikin aji, don haka suka sake d'aukar d'amara wajen ganin sun durqushesa tahanyar jansa ga jiki, sunyi amfani da yawan damuwar da yake shiga wajen ganin sun jawo ra'ayinsa tahanyar zagayawa dashi wajaje masu ban sha'awa da d'aukar hankali aqasar wanda nan take suka fara zuwa club club dashi suna nuna masa hanyoyin shaye shayen qwayoyi da barasa da sunan zasu taimaka masa wajen rage damuwar da take ciki, yau da gobe babu abunda tabari, tun Nuraddeen najin bazai iyayin hakanba har yafara sha'awar aikatawa batare daya ankara ba, akoda yaushe yakan zauna yana qoqarin tunano gida da abunda yafaru sai yaji yakasa tuna komai, sab'anin da da kullum cikin tunaninsa da abunda yafaru tsakaninsa da matarsa yake, wani abu daya sake d'aure masa kai shine yanda bayason tuna qasarsa gaba d'aya balle ahalinsa shiyasa nan take suka samu nasarar juyar dashi yanda suke so, idanma yace zai zauna yatuna wani abu akansa sai yaji kansa na matuqar sara masa da yimasa ciwo, bazaiji yasamu sauqin hakan ba har sai ya d'auki barasar da tuni ya amince da takan rage masa damuwa yasha.

Gaba d'aya rayuwarsa tagurb'ace amma wani ikon ALLAH babu abunda ya sauya ta b'angaren karatunsa, zai iya sha yabugu sosai sannan yaje aji suyita yimasa dariya yana wartsakewa zaije yanemi topic d'in da akayi yayi reasarch akai kuma nan take yafahimta, idanma yakasa zaije yanemi malamin duk inda yake ya sake yimasa bayani, malamai da yawa na mamakin halin da yaron yajefa kansa aciki wanda shi da kansa idan an tambayesa bazai iya fad'ar daliliba, iya abunda zai iya fad'a akai shine baya son tuna komai akansa, ahalinsa da kuma qasarsa, idan kuma yayi yunqurin hakan to halin da zai tsinci kansa aciki shine zai haifar masa da shan barasa don yasamu magancesa..

*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___71💎

Sunana Nuraddeen Idris Aliyu wanda akafi sani da Dr N.I Aliyu wato qwararren likita a fannin lafiya daya shafi matsalolin qwaqwalwa...

Waro idanuwa Rashida tayi had'e da qurawa masa idanuwa cike da farinciki, alokaci d'aya tashiga qwalawasu Fatima kira, aunty, aunty, aunty kufito kuzo kugani ga abban little a tv ana fira dashi, pls aunty kufito kugansa, habiby ne wlh, kufito don ALLAH kada agama firar dashi.

Tadinga fad'a tana k'walamasu kira, ayanda take kiran nasu yasasu fitowa da sauri ba shiri, musamman Dr. Nura har yana shirin fad'uwa sanadiyar tuntub'en da yayi, ita kuma Fatima daqyar take takawa saboda nauyin da tayi, gashidai girma nadad'a tarar masu amma har lokacin haihuwa bata tsaya masu ba tasamu daqyar ta qaraso ciki, Saida takai jikin tv tasa yatsa adaidai gefen da aka nuno hotonsa tana fad'in uncle wannan shine mijina, shine abban little aunty,

Dawowa tayi tariqa Fatima tana cewa, kuzauna aunty kusaurari firar da za'ayi dashi, gaba d'aya ya canza saida nakallesa da kyau da sunan sa daya fad'a sannan zuciyata ta gamsu da cewa shid'inne, taqare maganar had'e da zaunar ita saman kujera, kaima uncle kazauna tafad'a lokacin da take qoqarin zaunawa itama had'e da qura masa ido, wani irin farinciki take jin kanta aciki marar misaltuwa, addu'a tadingayi azuciyarta akan ALLAH yasa yafad'i cewa zai dawo garesu nan kusa bada jimawa ba,

Wayarta tajawo ta lalubo lambar umma lokacin tarako dady zai fita riqe da hularsa tana yimasa addu'a, kasancewar wayar na nan falo saman kujera yasa umma tad'auko tare da d'agawa, Saida tayi murmushi sannan tace Rashida kuna lafiya, cikin zumud'i ta amsa mata tana cewa umma ku kunna tv a tashar BBC ana fira da mijina, gaba d'aya tamanta da umma take magana saboda hankalinta gaba d'aya na wajen firar da akeyi da Nuraddeen yana bada amsa, jin da tayi umma tayi tsaki had'e da cewa marar kunya yasa takashe wayar tana girgiza kai yasa tayi saurin toshe baki tana dariyar da da zaran ka kalleta zaka fahimci tsantsar farincikin dake tattare da ita taci gaba da kallonta
Chapter 96 · 0% Book details