← Book details Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 160

Sashe 140

Sannu Sannu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar ance ya duba gefen gadon dake d'akin wajen bed side ya hango jikkarsa acan sakad'e wacce da itace ya zubo wasu kayansa da zaizo qasar, da sauri yaqarasa wajen ya cirota duk ta d'anyi qura duk da bawai sosai bane tunda shi mutumne mai tsananin tsabta akoda yaushe cikin gyaran d'akin da kakkab'esa yake ko kuma yasa ayi masa, Amma kasancewar bai fiye amfani da ita ba yasa ta d'anyi datti yasa wani d'an qaramin towel ya kakkab'e sannan ya bud'eta, abubuwan daya ta bid'a duk ya watse d'akin sune aciki wato hoton habibty d'insa da wayarta daya shiga part d'insu ya d'auko ranar da zai tafi, bin photon yayi da kallo yana murmushi saboda tsananin farincikin kallonta da yakeyi, ko yanzu ya habibtynsa takoma?, Shin anganeta ko kuwa?, Tana nan da ranta kota mutu?, Shin idanma tana raye tana tunawa dashi ko kuwa tayi aurenta da wani ta manta dashi?, Ina abunda ke cikinta?, Shin tahaifesa yana raye shima ko baya raye duka bai sani ba, Wud'annan sune tambayoyin da ya dinga yiwa kans kenan don ya tabbata tsawon wud'an nan shekaru daya kwashe baya nan dole sai d'aya daga cikin hakan sai tafaru, ji yayi zuciyarsa na wani irin bugawa da sauri da sauri wanda ya tabbata rashin fatan faruwar d'aya daga cikin abunda yake tunanine ya jawo hakan, addu'o'i yadinga karantowa abakinsa na neman tsari kafin yaci gaba da qoqarin kunna wayar Rashidar dake hannunsa amma taqi tashi.

Murmushin qarfin hali yayi yana ganin wautarsa na tunanin cewa wayar zata tashi bayan yasan cewa jiya ba yauba, koba komai yasan cewa tuni baturin cikinta ya lalace ya dena aiki, miqewa yayi ya shirya kansa tsaf cikin qananan kaya suit royal blue sai farar riga 'yar ciki da necktie shima kalar royal blue da d'ige d'igen fari acikinsa, kallon kansa yayi a madubi yaga yanda farin gashi yasoma d'an feso masa cikin kai yayi wani irin murmushi dake d'auke da ma'anoni kala kala.

Takardar daya rubuta ta ajiye aiki ya d'auka ya saka cikin aljihu sannan ya nufi wata babbar psychiatric hospital da ake kira (Columbia Asia hospital) babbar asibitin masu tab'in hankali ce aqasar da ake matuqar alfahari da ita wacce aqarqashinta ne yake aiki, kai tsaye office d'in shugaban asibitin ya nufa wacce ta kasance macece 'yar qasar China, cikin girmama ya shiga ya gaisheta da yaren turanci ta bashi izinin qarasowa ciki ya zauna, bayan ya zauna yayi mata bayanin abunda ke tafe dashi tare da miqa mata takardar ta karb'a, Saida tagama karantawa tsaf sannan ta linke tamayar tana kallonsa kafin tace.

"Yana da kyau kafin ace kayanke wannan hukunci kayi tunanin makomarka, anan muna matuqar girmamaka tare da baka daraja kasancewarka zaqaquri kuma haziqin likita da muke dashi, bana tunanin cewa komawarka qasarka zai Haifa maka d'a mai ido saboda basusan darajar kaba, bazasu iya gane irin qwazon da kake dashi ba balle har subiyaka albashi mai tsoka da zai iya riqeka yanda kake buqata, Ina baka shawara da kayi zamanka anan, idan har salary d'in da muke biyanka ne beyi ba zamu lullunka maka shi har sau uku matuqar zakaci gaba da aiki damu." Duk wannna surutun da takeyi da yaren turanci take yimasa shi kuma ya zuba mata ido yana kallo cike da mamakin yanda kowane d'aya daga cikin 'yan qasashen nasu keda son Kai da son cigabar qasarsa sab'anin tashi qasar da a saninsa nada ba haka suke ba sai in ALLAH yasa yanzu sun canza, ajiyar zuciya ya sauke kafin shima cikin qwarewar yaren nasu na turanci da idan kaji zaka d'auka dashi aka renesa har ya girma yayi murmushi had'e da cewa.

"Ina bada haquri mah! tare da yimaku godiya sosai bisa karramawar da nake samu daga wajenku akoda yaushe, kalmomi kawai bazasu iya tabbatar maku da hakan ba amma daga qasan zuciyata zanci gaba da alfahari da aikin da nayi a wannan asibitin taku tare da yabawa agareku aduk inda nashiga had'e da kuma addu'o'in fatan alkhairi har iya qarshen rayuwata, kuyi haquri! Bazan aje aiki bane don bana so ko kuma don qasata, zan aje aikine saboda ni Ina buqatar qasata awannan lokaci kuma Ina son nakoma cikinta a matsayin cikakken d'an qasar dake alfahari da ita, qasata uwace mai matuqar girma da daraja, qasata uwace data reneni kuma tabani ingantaccen ilimi, Bata barni ahaka ba har saida ta turoni don insamu ilimin da zan taimaketa da 'yan uwana dake cikinta tare da bani cikakkiyar kulawar da duk yakamata, ashe kuwa wannan uwar baici na wofantar da itaba, baici namance da nauyin mutanen dake d'auke a kanta ba tana basu kulawa wud'an da sun kasance sashen jikina da kuma rouhina, ni Dr N.I ALIYU na amince zan ajiye wannan aiki koda zaku yimani salary da zalar gwalagwalai ne, kuma nazab'i na koma qasata in tayi mata bauta koda bazasu bani naira ba acikin kud'insu domin sun cancanci haka, infact ina da buqatar iyayena, iyalina, ahalina, abokanaina da kuma 'yan qasata don haka zan koma garesu."

Shugaban makarantar data bud'e baki tana kallonsa had'e da sauraren kalaman da yakeyi bata san lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba tashiga tafa masa, sosai ya burgeta yanda yanuna mata yana kishin qasarsa kuma yana martabata haka, kawai dai taji ba dad'ine saboda rasa zaqaqurin likitan daya san aikinsa da zasuyi shiyasa tazubar da qwallah, miqewa tayi had'e da miqa masa hannu daidai lokacin da shima ya yamiqe daga zaunen da yake ya miqa mata hannu sukayi sallama sannan tayi masa bayanin yanzu zata gabatar da takardarsa zuwa can samanta don haka ya kasance cikin shiri ko yaushe zasu nemesa.

Ko kad'an baiso hakan ba don a ranar yaso barin qasar amma hakan ta cutara saboda basu nemesa ba.

Nan take yashiga sa duk wasu qaddarori daya mallaka kasuwa ya sayar dasu, hatta gidan da yake ciki da motocin hawansa guda biyu duka ya sayar don dama gidan sane yayiwa abokin nasa d'ahiri ya zauna, yanzu kuma da zai bar qasar sai yakoma wani wajen shi kuma ya saida abunshi, Saida aka kwana biyu sannan aka nemeshi wajen aikinsa ashe wata gagarumar walima suka shirya masa don karramasa da kuma appreciating d'insa akan qoqarin da yayi wajen kawowa asibitin tasu cigaba sosai.

Cek d'in maquddan kud'in da idan aka canzasu i zuwa na qasar nageria zasu kai kimanin miliyan ashirin da wasu d'aruruwa akai suka bashi tare da kambun karramawa a matsayin qwararren likitan da yafi iya kula da marassa lafiyansa da kuma kambun likitan da yafi kowa hazaqa da kuma sanin aikinsa, yayi masu godiya sosai bisa karramawar da suka yimasa bazai tab'a mantawa dasu ba sannan aka watse bayan anci ansha anyi hotuna Wanda mafi yawa daga cikin ma aikatan asibitin na sama dana qasansa Saida sukayi qwallar rabuwa dashi kuma sun tabbatar masa da yanada alfarma a asibitin ya turo duk wanda take son a d'auka aiki matuqar ya amince da hazaqarsa da kuma jajircewa, sannan shima suna marava dashi aduk lokacin da yayi sha'awar dawowa qasar yaci gaba da aiki dasu.

Murmushi kawai Nuraddeen yayi aransa yana raya cewa shi da qasar waje kuma indai ba saudiya ba to sai bayan ransa, don ko kwana biyun daya qara saboda matsalar visa ne ita ta tsaida shi da tuni ya tafiyarsa qasarsa saidai suyi walimar ba dashi ba.

Duk mutanen da yake huld'a dasu saida yaje yayo bankwana dasu har wajen shugabar makarantarsu inda yayi karatu da ita tafara riqesa don awajenta ya zauna kafin yakafu da kansa, matar kama itama yanzu ta tsufa sosai yayi mata bankwana bayan yamata bayanin zai koma qasarsa, tayi kuka sosai don ta matuqar sabawa dashi tamkar d'anta na cikinta ya yimata alkhairi sannan ya wuce.

Dama tuni ya gyara komai yana dawowa abokinsa d'an qasar Thailand ya d'aukesa zuwa airport, wani irin farinciki yakeji azuciyarsa marar misaltuwa awani b'angaren na zuciyarsa kuwa tsorone fal da fargabar abunda zaije ya isko qasar tasa bayan ya shafe tsawon wasu shekaru batare daya wai wayota ba.

••• ••• •••
Kimanin sati d'aya kenan kusan kullum sai hajia mama tayiwa baffa nasiha akan yayi haquri ya yafe 'yarsa ta dawo gida, fushin ya isa haka ace shekaru kusan bakwai amma yakasa mantawa da abunda yafaru, tsananin damuwa da baqinciki yasa aduk lokacin da batool tayi yunqurin shigowa garin in ta tunada mahaifinta ya haramta mata shiga gidansu saita fasa, saboda bata san da wud'anne idanuwa duniya zata kalleta ba ace tazo mahaifarta inda iyayenta amma an hanata shiga gidan kuma matuqar tashiga garin bazata iya d'auke idanuwanta daga gidansu ba saboda qaunar da takeyiwa mahaifinta da 'yan uwansa da kuma sauran ahalinta, hakan yasata haqura tun ranar da aka d'aukota daga garin aka kawota gidan mijinta bata sake waiwayar garinba saboda kada takasa bin umurnin mahaifin nata ta taka gidansu tsinuwarsa da yafetan da yace zaiyi sutabbata agareta, taci gaba da haquri cike dasa burin cewa zai sauko kowane lokaci ya nemeta ya dawo da ita cikin ahalinta ko don qaunar da yake yimata amma fushin zuciya yasa yakasa haqura har yanzu, hakan yasa haqurin mahaifiyarta ya qare take tunkararsa da maganar akoda yaushe kimanin sati d'aya kenan, kullum saita nuna masa illar abunda yayi na tsawon shekaru bakwai da abunda fushin nasa ke iya jefa 'yar tasa aciki, yakanji zafi da rad'ad'in hakan da yayi shima amma yaqi fahimtar abunda take son fahimtar dashi, jiya da daddare bayan ya watso ruwa ya kwanta ita kuma tana gefen gado tagama sallarta ta shafa'i da wutri tayi addu'a tajuyo tana kallonsa yana sanye da farar riga doguwa jallabiya tayi murmushi.

Murmushin shima yayi mata fuskarsa ba yabo ba fallasa yace.

"Hajia mama lafiya wannan kallo haka.?"
Chapter 140 · 0% Book details